Washe gari, ina tsaka da shirin tafiya makaranta na, ANTY ta shigo d’akin fuskar ta a sake take duba na, ” MUNIBBAT dinna, zauna muyi magana dake kinji!!..” ta fad’a cikin sanyin murya..
A hankali na koma na zauna, cikin biyayya nace” Anty kun tashi lafiya? ya k’wana su Hannah!..” a lokacin baya na san bata amsa min sai ma dai ta kawo mun bugo, amma abin mamaki sai naji tace” duk Alhamdulillahi, me ya same idanun ki haka?..”
Da sauri nayi kasa da kai na cikin kasalaliyar muryar nace” humm dama dama jiya ne kafin na kwanta abu ya shigar min idanu na shine yake ciwo!..”
” Aiyya sannun kina kiyayye wajen abunda kike sabida gaba, yauwa dama nazo ne muyi magana dake game da _gidan rokon ki!_ ..”
Jin ta ambaci gidan roko na sai da gaba na ya fad’i cikin jimami nace” to!..”
” Da yamma in kin dawo Abba Hanna zai tambaye ji, menene zabin ki game da inda kika fi jin dadin zama, abinda nace so dake shine kada ki k’usk’ura kice nan gidan, nafi so ki koma can gidan yan gayun can dan abun duniyar nan da kin samu aiko mun dashi gida a matsayi na na uwar rukon ki, amma bari ba yanzu ba dole ne ki ce mai kinfi son zama a gidan Hajiya, akan wannan gidan! ba shawara nazo nema ba umarni ne na bakin matsayi na wace na isa dake, zan gani in naka matsayin danake harsahe…”
Tana zuwa nan a batun ta, ta fice a d’akin ko kallo na bata sakeyi ba, shiru nayi ina tunanin maganar ta, to yanzu tana nufin na bar nan gidan sabida abin duniya? shikenan Kawu na zaiyi min nisa? a ina zan nemo mata abun duniyar?..” to ganin zan b’atawa kai na lokaci da tunanin Anty yasa nayi saurin k’arasa abunda ke gaba na fice a gidan…
To kamar yanda tace, ko da na dawo da yamma banga kawu na ba, ashe yaje gidan su Hajiya ne dan ya sanar mata, duk ban san wainar da ake toya ba…
****
Cikin mutu’kar girmamawa, jamma’ar gidan suka tarbe shi, tamkar wani babban mutun haka aka kawata zuwan sa, ga abinci kala-kala da abin sha, an jere masa su, a gaskiya sun mutunta shi iya mutuntawa, Hajiya Daddah da kanta tafi ta shigo dashi har cikin falon bak’i, nan Kawu ya zage sai kalle-kalle yake a wayance, a zuciyar sa kuma tana hango Mai d’iyar sa yanda tayi rayuwa a cikin wannan tank’amemen gidan…
Sun gaisa cikin sakin fuska d’aga bisani Kawu ya fara da cewa” Hajiya maganace ta kawo ni, kamar dai yanda nayi miki alk’awari, to lokacin cika shi yayi Allah ya nufa, insha Allah gobe in war haka _MUNIBBAT tana tare daku_, domin nima zan wuce wajen aiki na tunda na ganta, hankali na ya kwanta na samu ingataciyar nutsuwa, nima a gobe zan wuce Legos, nazo na na sanar miki shin har yanzu kuna nan kan bakar ku na san rik’e ta ko kun canza ra’ayi?…”
Cikin mutu’kar farin ciki marar musaltuwa, Dadda ta mik’e jikin ta narawa gani zata samar wa matar d’an ta farin ciki tace” da gaske kake zaka iya bamu Aysha har cikin zuciyar ka!?..”
Tabbas Kawu na, nice zuciyar sa amma sabida na samu farin ciki, maradin zuciya ta ya tabbata, sai ya d’anne zuciyar sa yace” sosai ma kuwa ina mutu’kar k’aunar MUNI, ina son ta sosai haka kuma ko ban fad’a ba zanyi bala’in kewar ta, amma dole zan ha’kura domin nafi k’aunar farin cikin ta akan nawa, Hajiya Muni tana buk’atar ku a halin yanzu fiya dani! tana son kasancewa daku, farin cikin ta a yanzu shine kullum ta bude idanun ta ta ganta a tare daku, ba wai dan bana son ta ba ne a’a zan rabu da ita ne akan dole, Ina fatan bayan barin ta waje na bazaki bari tayi kukan maraici ba Hajiya? ki kula min da ita Hajiya karki bari tayi kukan bakin ciki, ga amanar ta nan na baki halak_ malak Allah ya tayaku ruko, in Allah ya kai mu zuwa safiya sai azo an d’auke ta…” da sauri ya mik’e zai wuce, cikin sauri Hajiya ta riko hannun sa, tausayin sa ya kama ta muryar ta na rawa tace” bazan k’asance me son kaina ba har abada, muddin zuciyarka bata kwanta da wannan kyautar ba, ka barta a wajen ka kawai inda rabo mu sake zama inuwa d’aya da ita sai kaga tazamo tamu…”
” A’A ya zama dole nee ta dawo inda kuke, ina so ta samu nutsuwa ne, burin ta na cikin ahalin ki duk ranar da ta dawo zaki tabbatar da haka, ni dai rokona a gareku shine ku kula min da marainiya ta!! domin ita amana ce a gareni…”
” Insha Allah zan mu kiyayye, zan bata kulawa kamar yanda nake bawa jikokina, Shafi’u ba kai ne zaka bani umarnin yanda na kula da baby! da zaka zauna ko da na awa d’aya ne zaka tabbatar da baby tana da babban matsayi a cikin gidan nan, kaje wajen sana’ar ka cikin nutsuwa ka sa ranka tamkar tana gaban ka ne, insha Allah bazakayi danasani da damu ba….”
” Allah ya yarda Hajiya, ni na wuce sai wata rana kuma in Allah yayi min dawowa…”
Nan sukayi sallama da Hajiya Daddah, cikin kwanciya hankali…
Kawu yana fita Hajiya ta mike cikin farin ciki ta koma d’akin ta zuciyar ta fal murna da an’nashewa…
****
” Yarinyar ta! kina jina?..”
Cikin nutsuwa nace” eh Kawu na!!..”
” Ina so ki saurareni da kyau, duk da a lokacin baya kinyi rayuwa irin wace, nake so ki koma yanzu, amma karki manta a lokacin baki da wayo ne bare dabara, ki k’asance me hak’uri da tausar zuciyarki, bana so ki zamo me son zuciya da hangen nesa, MUNI ko da wasa kar tsutsayi ya Kai hannunki d’aukar abinda ba naki ba, ki k’asance me janye jikin ki a duk inda kika fahimci matsayinki bai kai ba, girmama na gaba dake na san baki da rashin kunya bare rainuwa, dan Allah ki zauna a yanda na sanki, karki d’auko wani hali wanda bamu sanki dashi ba, biyayya itace abinda nake so ki k’asance akai, ki nuna duk wanda kika gani a gidan cewar shi me daraja ne, domin sune gaba dake gobe insha Allah zaki bar gidan nan, ma’ana zaki koma gidan su Aliyu da zama domin nima a goben zan koma wajen aiki na! kibi umarni na ki zauna lafiya, karki manta da darajarki mutuntukar ki shine mutuncinki, ki rike mutuncinki domin yana da mutu’kar amfani a rayuwarki, karki bare ko wanne na miji ya rabeki muddin ba mijin aureki bane, ki k’asance me hak’uri a duk halin da kika tsinki kanki, insha Allah burinki zai cika muddin kika zamo me rike alk’awari da amana, zauna a me gaskiyarki dana sani…” cikin sanyi yake min maganar, jikina yayi bala’in sanyi na gagara cewa komai..
A hankali na d’ago kaina, a raunane nace” me yasa Kawu na? shin dama akwai ranar da zaka badani ga mutane da baka san ko su suwaye ba? kamar yanda ka saba tafiya ka barni haka kuma ka dawo ka tarar dani lafiya kalau, a yanzu Ina me neman alfarma a wajen da ka barni a cikin gidan nan, bana son zuwa ko ina Kawu na!..”
“Kin ha’kura da (A&M) dinki? shin zaki iya rayuwa ba tare dashi ba?..”
Cikin mutu’kar razani na d’ago, idanuna sun ciciko da k’wallar bakin ciki….
Cikin mutu’kar razani nake kallon sa, shima kallo na yake babu ko kifftawa, a hankali nayi kasa da kai na, ” eh dama tun asali ban san shi ba, bare kuma yanzu na daurawa kaina aiki, ni dai ka barni a nan!..” cikin shagwab’a na k’arasa maganar…
” to ke yanzu banda abunki, wanne ubane zai bar yarsa a cikin gida irin wannan ita kad’ai tayi rayuwa ba tare da manya a ciki ba? ki bar ganin Ina nan nima a gobe zanje ganin gida kuma bazan dawo ba har sai ranar da zai dawo, gara ma ki ta tare ki bisu Allah yasa a dace shine fatana a gareki, in na samu lokaci zan na lekoki!..” ta fad’a game da shafa min kumatu…
Na bata fuska sosai, cikin turo baki gaba nace” a’a ni dai ba zani ko ina ba!..” to nan fa na burkice musu duk abinda sukace nima sai na kawo tawa hujar, gani zan bata musu lokaci yasa Kawu na dakatar dani ta hanyar daka min tsawa, akan na tashi na bashi waje baya son shirme, akan dole na koma d’aki na zuciya ta babu dadi, ni ba wai son komawa ne banayi ba a’a yanda zanyi da soyayyar MAN nake tunani…
Cikin daren Kawu na, yazo ya lalashi ni d’aga k’arshe ya bani duk wasu sauran takardu dake hannun sa, ya kwantar min da hankali sosai, ya sake min nasiha me ratsa jiki.
*****
Tunda ya fara maganar nake kukan rabuwa dashi, domin na san babu shaka Kawu na ba wasa yake min ba, lokacin da ya fita ya bar ni na fara duba saƙonin da MAN ya aiko min, tsatsar soyayya da zallar ƙauna na gani, nayi kuka kamar bazan ɗaina ba, wata irin soyayyar sa nake ji tana ruɗ’a ta, gaba ɗ’aya barci ya ƙaura cewa idanu na, banda hawaye babu abinda nake, a gaskiya ina mutuƙar ƙ’aunar MAN har cikin zuciya ta…
Cike da nuna kulawa Daddah tace”” Nusaiba kin san me nake so dake yanzu..”
” A’A hajiyar mu!..”
” Gobe in Allah ya kai mu, ki gyara min ɗ’akin baby zanyi baƙuwa, duk abinda ya kamata a sake ki tabbatar ana saka shi kinji!…”
cikin biyayya tace” insha Allah! Hajiya, su Auta zasu dawo kenan?..”
Murmushi tayi marar sauti kana tace” a’a halan kin manta su da alhaji zasu dawo? wannan baƙuwa tace zata zo..” kafin ANTY ta sake magana har Daddah ta fice a ɗakin…
ɗaki na ANTY ta shiga, jikin ta a sanyaye take duban komai na ɗakin, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, cikin murya me rauni tace” yaushe zaki dawo gareni baby na!?..” ta jima a zaune tana tunani na, daga bisani ta fice a ɗakin…
Washe gari, da sasafe na fice a gidan mu, kai tsaye gidan su Aysha na nufa zuciya ta na zafi, sai da na tsaya a zauren gidan naci kuka na na gode Allah sanan na ida shiga ciki, ita kaɗai na samu a tsakar gida, da alama yanzu ta tashi, ganin ta da nayi a yanzu take naji zuciyata na tafasa, ji nake kamar na fasa gaya mata, amma dana tuna halacin da tayi min sai na ɗ’anne zuciya ta, nace” AYSHA!…”
Da sauri ta ɗ’ago, fuskar ta cike da an’nuri tace” MUNIBBAT kece da sasafe haka?…” ta faɗ’a tana wani duban baya na kamar wace bata yarda dani ba…
Hannun ta na kamo, cikin ƙarfin hali nace” zo kiji..” ba musu ta biyo ni har zaure, na ma rasa ta ina zan fara gaya mata, gani shirun yayi yawa yasa tace” MUNI lafiya dai ko?..”
” Eh lafiya kalau, dama ehm dama..” wallahi na gaza faɗa mata…
A hankali ta dafa kafaɗa ta cikin sigar rarashi tace” me yake damuki kawa ta? ko ANTY CE?…”
” Za muyi tafiya ne, kuma ban san ranar dawo war mu, shine nazo nayi muku sallama, ina Yaya Jameel?..”
Shiru tayi na yan mints sannan tace” amma shine kika tashi hankalin ki haka, anya gaskiya kika gaya min kuwa?..”
Murmushi nayi nace” tunda nake dake na taɓ miki karya? Allah tafiya zanyi yau din nan!…”
” To naji me ya samu idanuki suka kumbura, ni gani nake ma kamar baki samu isha-ishan barci ba?..”
Tausayi ta bani gani yanda take bani kulawa ta musamma, again murmushi na sake saki, kana nace” gulma kawai me ya shafeki da idanuna! ni dai ina Yaya Jameel yake?..”
Ita ma murmushi tayi kana tace” kamar kin san jiya sai da muka raba dare dashi muna hirar ki, shi a lallai sai na fara faɗa miki, amma bari na taso shi waƙ’a a bakin me ita tafi daɗi…”
Ban kawo komai a raina ba, har ta wuce ciki babu jimawa ta dawo, hirar makaran ta muka fara, a nan ne na samu damar tambayar ta, cewa” Aysha niko ya soyayyar ki da Mal Haidar kuwa? kin samu ci gaba ko kuwa?..”
Take an’nurin fuskar ta ya ɗ’auke damuwa ta maye gurbin sa, cikin tsaki tace” wallahi MUNI kin taɓo min inda yake min ƙyaƙƙayi, mutumin nan ya mayar dani wata sha-sha, tunda nake dashi bai tab min kallon so ba, bare na sa ran nan gaba zai furta min kalamar so, kullum ni kaɗ’ai nake hauka na, gashi ke da NAFESATU yanzu duk ba zuwa kuke ba, na ma rasa ta yanda zan bullowa lamarin, sam zuciyata bata kyau ta min ba, please ki bani shawara ya zanyi ya so ni dan Allah!??…” ta faɗ’a tana kama hannu na cikin wani yanayi na buƙatuwa…
” Ki cire shi a ranki Aysha! zan so ace shi ne nuna miki so kafin ke, bana so ki wahala akan soyayyar da bata da riba, wato makauniya soyayya, kiyi haƙuri dashi shine mafi alhairi!..”
Zare hannun ta tayi ɗaga nawa, idanun ta har sun kawo ruwa, tace” hmm kin ɗauka soyayya ta a gare shi wasan yarace? a’a MUNI dan baki san zafin so bane kawai, shi yasa zakice na rabu dashi, ina masa san so! soyayya da babu irin ta, har yanzu ke yarinya ce a fagen soyayya, ina mutuwar ƙaunar HAIDAR duk da shi bai san ina yi ba, Allah yasa shi rabu na ne!…” wasu hawaye masu zafi ne suka zubo mata, ta sake duba na cikin karaya tace” muddin kin san ba addu’a zakiyi min akan na samu cikar buri na ba, karki sake magana akan mal Dan ALLAH!..”
Na kasa magana sai aukin kukan zuci da nake, tausayin Aysha ya gama cika min zuciya, ga tausayin rayuwar da nake ciki, zuciyata taki bani cewa da gaske Aysha yake aikowa da saƙ’onin sa, to in ba ita bace WACECE? gaba ɗ’aya kai na ya ƙulle, tabbas Aysha baza tayi min karya ba…
*Yanzu waye zaɓi na a cikin su?…”*
Zanyi magana kenan sai ga Jameel ya fito, fuskar sa cike da farin ciki, sam bai kula da yanayi da muke ciki ba…
” My kanwa ta! ashe ko da gaske take ke kike kira na…”
Kallo ɗaya nayi mai na gane cewar wanka yayi da safiyar nan, da ƙyar na iya ƙaƙalu murmushin yake, nace” barka da safiya Ya Jameel?..”
” Yauwa barka dai, ina fatan kanwar tawa tashi cikin ƙoshin lafiya?..”
” Lafiya kalau..”
“Aysha ta isar miki da saƙo na kuwa?..”
a gajiye nace” a’a ta dai sheda min, gaisuwar ka amma ban da wanna banji komai ba!..”
Ya wani rage murya, haɗi da kashe min ido, cikin wata murya da ban san shi da ita ba yace” MUNIBBAT tun ba yau ba, tun kan kika haka, nake jin wani baƙwan yanayi a tare dake, a kawai wani babban sirri dake cin raina, kullum ƙwana duniya dashi nake tashi, dashi nake ƙwana, ban sani ba ko kema kina jin irin abinda nake ji?..”
Gaba ɗaya ban fahimci inda ya dosa ba, hankali na yana ga kanwar sa, a gajiye nace” bana jin komai a raina ni kam kamar yanda Aysha take nima haka na ɗ’auki kai na a wajen ka…”
” Ɗ’aga yanzu ki cireni a wannan matsayin, ki ɗ’auki kan ki ke kyakykyawar kaddar tace, “`MUNIBBAT INA SONKI, INA ƘAUNAR KI, KIN AMINCE ZAKI AURE NI“`…”
Cikin sigar soyayya ya faɗ’i maganar, yana wani langwabar da kai gefe…
Cikin tsananin tashin hankali nake kallon sa, gaba ɗaya jikina ya ɗ’auki rawa, idanu na sun firfito waje na shiga girgiza kai na tamkar wata ƙyadangaruwa, wasu hawaye masu dumi suka zubo min, na juya zan gudu Aysha tayi saurin shan gaba na, idanun ta fas akai na…
” A’a MUNI, dan Allah karki zamo sanadin tarwatsiwar farin cikin gidan mu, na amince zan amshe k’addara ta ta rashi sa’a a soyayya da hannu bibiyu, zan jure bakin ciki na, dan Allah karki sa na fara tunanin rashin sa’ar mu a jini yake! YAYA yana mutuƙar ƙaunar ki, tun farko zuwanki rayuwar mu, a ta dalilin ki ya dawo zama cikin anguwa, dan Allah ki amince dashi, na san bazaki watsa mana kasa a ido ba!..”
Tabbas Aysha tafi kowa sani, in na shiga ruɗani bana iya magana, amma yau sai ta gaza fahim ta ta…
A hankali ya dafa kafaɗar ƙanwar sa, alama yayi mata da ido akan ta bani waje na wuce, babu musu ta matsa min, tamkar jira nake na fice da gudu ɗ’aga gidan ko Umma banyi wa sallama ba, ina shigowa gida na tarar da Kawu na, a tsaye a bakin ƙofa ta ban iya cewa ba komai ba ila rungume shi da nayi, sai a sannan na samu damar fashewa da wani irin kuka, cikin hargowa nace” *YA ZANYI NE? YA ZANYI WAI!!!*…”
” Shittt!! yarinyar kirki, addu’a zakiyi shine kawai mafita!…” ya faɗ’a yana shafa min bayana a hankali…
*****
Yau tun farar safe Daddah ta saka kowa a gaba sai da taga ya kimtsa tamkar za’ayi wani dan ƙ’aramin biki, babu wanda baiyi mamaki ba, amma ba halin tambaya ita kaɗai ta fice yau ko mutun ɗaya bata nemi ayi mata rakiya ba, an gyara ɗaki na sosai yayi kyau komai an saka sabo, picture din na kuwa an mamaye su a jikin bangon dakin, wanna duk umarni Daddah ne, ANTY na kam kishi ya hana ta sake shiga ɗ’akin tunda bani zan zauna a ciki ba, shi yasa bata san wainar da ake toya ba…
Ina shiryawa Kawu na yana haɗa min kaya na, har ya gama shirya kayan ban gama shirya kai na ba, da na ɗ’ago mun haɗa ido dashi sai na fashe da kuka, shi da kan shi ya shirya ni tsaf, har wata ƙwalliya yayi min abun gwanin ban sha’awa, zan so ace masu karatu kuna wajen lokacin da Kawu na yake min ƙwalliya, sai shagwaɓa nake zuba mai yana biye min, duk abinda na nuna shi yake min, gaskiya ina haukar son Kawu na! haka shima yana masifar so na, naga gata iya gata, ba laifi Anty ma ta nuna min so, sai wani nan suke dani take, suna gama shirya ni tsaf sai ga sallamar Hajiya Daddah nan har cikin ɗ’aki na ta shigo, sai a sannan ne idanu ya sake rinewa da kukan rabuwa da SANYIN IDANIYATA, shima cikin dabara da wayo yake goge nashi hawayen, har mota suka rako ni ko wannen su na ɗ’ago min hannu, a haka har muka bar layin….
Babbar tarba na samu ɗaga ahalin gidan, Anty na tana ciki taki fitowa, har sai da Daddah ta shigo ɗ’akin da kanta, cikin murmushi ta dube ta kana tace” ƴata me kike a ɗ’aki ban ganki wajen tarbar bakuwar mu ba? ta buɗe baki zatayi magana Daddah tayi saurin cewa” cuff!! na san duk wannan abun da kike akan baby ne ko? ƙwantar da hankalin ki, za muyi maganar amma kafin nan zo kiga wani abu!…” hannun ANTY ta roƙo har bakin ƙofar palon inda ta barni, kuma ta hanani buɗe fuska ta…