JARRIMME NA tare da ANNUWAR, sunyi bala’in haɗuwa ko wanne su yana bani waje, gaskiya Allah yayi halitta a nan kyau iya kyau, babbancin su a baiyyane yake MAN ya fishi sakin fuska, da ƙwarjini amma shima fa ba baya ba wajen haɗuwa, ta cikin yalolon mayafi na nake hango su, akan MAN idanu na suka tsaya, wata irin soyayyar sa ce take fizzga ta, a hankali nayi kasa da ido haɗe da ɗanne zuciya ta, wasu siraran hawaye na zubo min, Daddah ce ta katsi min kuka nawa da cewa” yarinya ta BISMILLA!…” da idanu tayi wa ANTY alama akan ta buɗe mun fuska, cikin yake da basar wa tace” ANNUWAR zo ka buɗewa baƙuwar mu face din ta…”
Har a zuciyar ta kishi take da wannan baƙuwar, sam ba’a san ranta zata zauna a ɗ’akin babyn ta ba…
Da sauri Daddah tace” No ke nake so ki bude!..”
MAN kam ya kafeni da idanu, haka shima ANNUWAR, a cikin su babu wanda yake ƙwaƙwaran motsi, a hankali ANTY ta matso inda nake, tun daga kasa ta fara kallo na har zuwa saman kai na, cak idanun ta suka tsaya a face din, kirjin ta ya buga da ƙ’arfi cikin sauri ta yaye min mayanin kaina….
Masu karatu kun dai san yanda nake da kyau dama, gashi Kawu na yayi min ratsatsiyar ƙwalliya, da sauri nayi kasa da ido cikin wani salo me ɗ’aukar hankali, iskar na kaɗa min gashin idanun na, gaba ɗaya su ƙamewa su kayi, domin sun ga cikar haiba, kyau me asali da nagarta, ilimi haɗ’e da tarbiya, gaskiya Alhamdulillahi…
Da sauri ANTY ta juya ga Daddah, da ido tayi mata nuni da cewa to ya kika gani?…” a suƙwane Anty ta saki wani mahaukacin murmushi har haƙoranta na baiyyana, ta sake gyara tsawar ta da kyau, cikin sanyin jiki kuma tace”” BABY NA!!!…”””
“” Baby na!! kece da gaske?…” ta ida zancen da ɗago min fuska, muna haɗa ido da ita tayi min wata wawuyar runguma…
MAN gaba ɗ’aya ya kasa cewa ko ƙaza, kawai kallon mu yake, Dadda kam ta haɗe hannuwan ta waje guda sai aukin murmushi take…..
A ranar naga gata, naga yanda ake nuna kulawa, a cikin su ko wanne gwanine wajen nuna min ƙauna….
Kamar yanda suka tsara, duk ranar Monday ANNUWAR ne yake kaini makaranta, in aka tashi MAN yazo sauran ranaku kuma MAN ne yake kaini…
Sabowar rayuwa, saban farin ciki da nutsuwa gaskiya jama’ar gidan su MAN mutanen kirki ne, sun nuna mun gata sun bala’in shagwaɓ’a ni a yanzu ko yatsa na ka taɓa saina saka maka kuka, duk cikar gidan nan sai sun fito wani lokaci na saka dariya, haka zasu ta bina kamar zasu dake ni, amma fa da naje wajen ANTY na! na tsira! ina jin dadi rayuwa dasu sosai….
A ɓangare ɗ’aya kuma ina ƙewar Kawu na kamar me, ganin ba sa son bacin raina yasa nake ɗ’anne wa har sai na kebe waje guda sannan nayi kuka na…
Soyayyar mu da MAN kullum kara haɓ’aka take, mo sa yaushe sa irin kalaman sa yake gaya min, ina jin don shi sosai a raina, amma van taɓa furta mai ba..
Shiru wajen ya ɗauka tamkar babu mutane a cikin sa, cikin wata zazzaƙar murya yace” BEBBY NE!!! har yanzu fa banji kince komai kan soyayyar mu ba, shin kin amince dani a matsayin wanda zaki ƙare rayuwarki dashi? ko har yanzu baki gama tunanin ba?…”
Shiru nayi ina wasa da yatsun hannu na, zuciya ta na saƙamin abubuwa da dama, cikin sarƙewar murya nace” ina so na tambaye ka wani abu! Ahmm dama nace ya kukayi da Aysha?…”
Cikin rashin fahimta yace” wacece haka?..”
” AYSHA Musubahu Aliyu mana ɗalibar ka!…” na faɗa zuciya ta na bugawa, tsorana ɗ’aya kar naji abunda raina yake saka min.”
” Ohh wanna wai? yarinyar tana da kirki sosai, ta taimaka min a lokacin da nake neman gidan ku, duk wani bayyani ɗaga gareta na same shi, gashi yanzu ta fara mayar da hankali akan karatun ta, da farko bana son yarinyar gaskiya, amma sabida ta zamu wani babban sanadi a rayuwa ta, tana dan birgeni amma fa kaɗ’an…”
Lumshe idanu na nayi hadi da ɗ’anne zuciyata da ƙarfin tsiya, a hankali nace” to WACECE AYSHAN DA KAKE AIKOWA DA SAK’ONIN IRIN NA MASOYA!..??”
Wani makirin murmushi ya saki game da shafo sajan sa, kana yace” AYSHA!!! shine suna da muke kiranta dashi lokacin da bata da lafiya, babby kuma shine inkiyar ta, ina fatan yanxu kin gane?…” ya faɗ’a yana waro min idanun sa…
Na kasa jurewa, harshena yayi min nauyi, maƙoragona ya bushe, zuciya ta na tafasa a hankali na mike zan wuce ciki, yayi saurin riko min hannu ido cikin ido yace” baki gane ba ko?…”
Wani irin kishi nakeji a zuciya ta, na sake ɗannewa haɗi da daga mai kai alamar Eh, murmushi yayi min kana yace zauna…”
Ba musu na zauna amma fa kasa nake kallo, cikin hikima da dabara ya shiga bani labari na, da dalilin saka min sunan tamkar a novel haka naringa jin sa,
yace” tun daga ranar da kika shigo rayuwa ta na fara sanki! shin ke bakya jin irin abunda nakeji a raina? ina ji in na rasaki nima tawa rayuwar tazo ƙarshe, Ina miki wani irin so wanda ban taɓ’a ganin wanda yakeyi miki irin sa ba, zan iya sadaukar da rayuwata domin ki, muddin zaki kasance a cikin farin ciki to tabbas zanyi haƙura da nawa farin cikin dominki! karki nauyin baki MUNI in kin san bakya so na tun wuri ki shada mun, kar mu wahalar da juna mu! KINA SO NA MUNIBBAT!!???…”
~KIN DAUKA SOYAYYA TA A GARE SHI WASAN YARACE? INA MASA SON SO, SOYAYYAR DA BABU IRIN TA,INA MUTUWAR KAUNAR HAIDAR DAN ALLAH IN KIN SAN BAZAKI MIN ADDU’A YA ZAMU NAWA BA, KARKI SAKE CEWA KOMAI PLEASE!…~
Maganar Aysha ta dawo min cikin kaina tamkar yanzu take gaya min, a tsorace na kalle shi idanu sun ciciko da ƙwalla, na mike a fusace zan gudu yayi saurin juyo dani gaban sa, ƙoƙari ƙwacewa nake naji yace” _na fahimta MUNI, bakya so na ko? shi kike son gaya mun ko? ba komai ni bazan takura miki ba, abinda kike so shi nake so, amma karki cutar da kanki please!! shi so ba’ayin sa dan dole, na barki lafiya!…_”
Galala na tsaya ina kallon sa zuciya ta nayi min wani irin zugi, na kasa cewa komai illa ƙura mai ido da nayi kawai har ya ɓacewa gani na, a hankali na sulale a wajen sai haki nake kukan ma yaki fitowa bare na samu sausaucin a zuciya ta…
Duk wani abu na fashe wa dake ɗakin sa sai da MAN ya rotsa shi, cikin ƙunar zuciya da azababban kishi, idanun sa sun kaɗa sunyi jawur, ya faɗi a wajen yana dafe saitin zuciyar sa, da ƙarfi ya buga kan shi da jikin garu, ji kuke tauuuu!!!…”
A haka na lalaɓ’a na koma ciki, nayi sa’a ba komai a hanyar na wuce dakina, kye nayi ma ƙofar da kyar na samu na isa kan bedroom dinna, numfashi na yana sama da kasa, jikina ya bani MAN dinna baya cikin hayacin sa a yanzu, na mike tsaye cikin rashin sa’a na zame ban tsaya a ko ina ba sai a ƙ’asa kaina ya bugu da gefen gadon ji kike kauuuu!..
ANTY dake zaune tayi saurin tashi tsaye a hankali tace” MUNIBBAT! Or MAN..?”” ai bata tsaya godon nazari ba tayo ɗaki na, ta tura taji a rufe Aiko ta shiga kirana kamar tashin hankali, tanayi tana bugun ƙofar…
Da kyar na iya juyawa, kaina yana min wani azababban ciwo, ga jini da yake diga ina jan jiki a haka na isa ƙofar, numfashi na sama-sama nace” ANTY!…” gaskiya na sha wahala sosai sannan na samu na buɗe ƙ’ofar room din…
Hankali a tashe ta shigo ɗakin, halin da ta ganni a ciki shi yafi komai birkita mata lisafi, tamkar jirin zuwan ta nake, a jikin ta na ƙwanta murya ta na sarƙewa nace” ANTY MAN DINNA!!!.” na faɗa ina nuna mata hanyar waje da hannu na…
Tana shirin tambaya ta na sume a hannun ta…
Ko nauyi na bata ji ba, haka ta saɓe ni sai shashin Daddah…
Gaskiya ranar anga tashin hankali a gidan, kamar yanda ta kasance dani haka ce ta faru a bangaren MAN, shi kuma Daddah ta shiga duba sa, duk a gida aka zo aka duba mu, sai maguguna da aka bamu…
Tun daga ranar muka shiga wasan yar buya tsakani na dashi, muddin yana waje bana zama, ko magana nake da na hango shi zan koma ciki, tun su Dadda basu fahimta ba har suka gane halin da muke ciki…
Gashi kullum san shi da ƙaunar sa kara ruruwa yake a cikin raina, gashi bama iya haƙ’uri sai muga juna mu hankalin mu yake ƙwanciya…
Ina ƙwance a gado na, na lula duniyar tunani inata karanta wasiƙar jaki, har ban san lokacin da ANTY ta shigo ba, tsaye tayi a kaina tana ƙare min kallo gani bana cikin duniyar yasa ta dafani cikin sigar rarashi tace” Baby! lafiyarki kalau kuwa?..”
Hmmm na sauke ajiyar zuciya, zanyi magana tayi saurin cewa” muddin kin san abinda zaki faɗa min ba gaskiya bane kiyi shiru da bakin ki bana buƙata, ban san wannan irin matsayi nake dashi a zuciyarki ba baby, a tunani na yanda na ɗaukeki ƴ’a haka kika ɗaukeni uwa, ashe abun ba haka bane! shin kina da wanda zaki gayawa damuwarki sama dani a yanzu? kin san halin da nake shiga idan na ganki cikin halin fushi ko rashin walwala? MUNI ina ji a jikina ni uwace a gareki ta jini, zan so ki faɗa mun abinda yake damunki ni kuma muddin baifi karfina ba insha Allah zaki sameshi ko menene? zan gani nakai matsayin da nake tunani ko kuwa!…””
Shiru nayi ina tunani mafita, ta juya zata wuce zuciyar ta babu daɗi nayi saurin cewa” *KE UWACE A GARENI ANTY!!* nima Ina jinki sosai a raina, Ina miki kallon mahaifiya tane, na samu duk wata kulawa da nake buƙ’ata a wajenki, a yanzu kece jigona! ina ƙaunarki ANTY ki fahimceni please!…”
_nima haka ƴ’ata ina sonki_… ta faɗa cikin rauni…
To tun daga ranar fa ANTY ta saka min ido, duk inda take ina zaune a gefen ta, ko MAN ya fito bana samun damar guduwa domin kallo ɗaya take min na nemi wajen zama…
Ɓangaren ANNUWAR kuwa mukayi wata irin shaƙuwa ta ban mamaki, a ɓangaren na bana jin komai akan sa, a nashi ɓangaren kuma wata sabuwar soyayya ta yake ji tana fizgar sa, a hankali a hankali ya fara turamin ra’ayi irin nasa, soyayyar me zafin gaske ta fara shiga ta, dana rufe idanu na shi nake hange sai nayi nisa a tunanin sa katsam kuma sai MAN ya faɗo min, tamkar na tashi a barci haka nake zabura duk lokacin da nayi irin wanna dogon tunanin… JAMEEL, MAN, ANNUWAR
Gaba ɗ’aya yanzu na dawo sai hankali, kullum tunanina shin wa zan zaɓ’a? waye yake min san gaskiya a cikin su? MAN Ina da babban dalili akan sa, tabbas kwayar idanu na kawai zaka kalla ka san abinda nafi maradi, MAN shine zuciya ta, jinin jiki na, buri na, haka shine jarime a cikin birnin zuciya ta, har abada banajin akwai wanda zai kama ƙafa dashi a soyayyar sa, domin shi din na daban ne nima Ina mishi son MUTUWAR!!!…
ANNUWAR kuwa a zahiri ba wata soyayya da nake mai, ina biye mai ne kawai gudun kar a samu matsala, bana so gaba ɗ’aya a ce mazan gidan ta dalilina sun samu matsala, kullum cikin boye halaƙta dashi nake, sai dai kashe abinda ban sani ba wanda nake domin sa ya riga kowa sanin halin da muke ciki, duk wani motsi na akan idon sa nake, yayi kukan bakin ciki sosai lokacin da yaga inda na faɗa, amma yayi farin cikin ta wani bangaren gani ɗan uwan sa yayi dace da mata ta gari, a yanzu picture dinna sune abun kallon sa kullum cikin begena yake, har yanzu bai cire rai da zan ƙasance tashi ba…
Ya sha alwashi kamar yanda yagani da ido sa sai kowa ya san me muke kullawa, muna zaune dashi kamar kullum yana ta gaya min kalaman sa na soyayya, cikin gajiyawa yace” MUNI! wai me yasa kullum ni zan zauna naita gaya miki sirin zuciya ta amma ke ko da wasa ban taɓ’a jin kin gaya min kalama ko ɗaya ba? shin har yanxu zuciyar ki bata gama aminta dani ba ko ko?..”
Murmushi nayi iyaka face din na, kana nace” duk wata mace an san ta da ƙunya, a tsari na duk wani abu da nake so a aikace zai fahimci matsayin sa, kar ka wahalar da kan ka wajen san ji furicin baki na har kullum abinda zuciya ta take sheda min shine _ina ƙaunar sa kawai_ abinda na sani kenan a yanzu, ni zan shiga ciki…”
ban jira cewar sa ba na taso abuna,…
Cak na tsaya ina kallon sa, shima ni din yake kallo fuskar sa babu an’nuri ko kaɗan, zuciya ta na buga da ƙ’arfi nayi saurin yin kasa da kai na, zan wuce ta gaban sa murya ta na rawa nace” ina wuni Ya MAN!!..” ban jira amsar sa ba na wuce ciki da sauri…
Waye wannan me sa’a haka?
Abinda ya iya cewa kenan a zahiri…
ANNUWAR kam a tunani sa shine wanda zuciyar take ambata mata, bai kawo kowa a ranshi ba, amma ya kula da irin kallon da sukewa juna mu in sun haɗu yau ma hakace ta kasance, a dan hanzarce ya bar wajen…
Ina shigo ɗ’akin na, na saki wani marayan kuka cikin raunin zuciya nace” Allah ka taimake ni! Allah ka min zaɓi mafi alhairi a cikin su! Ina son ka sosai, nima Ina ƙaunar ka kamar na mutu!…” na takure waje guda, ANTY dake zaune gefen bed dinna ta ajiye abinda takeyi a hankali, zuciyar ta babu dadi tace” me nake ji haka yarinyar kirki!? ke da waye? ba dai soyayya kika far’a ba?…”
TTiirr Kashi!!!!!…….
” Daddah sai yaushe Mommy zasu dawo ne?..”
” Ka kira ta mana kaji, ai kafi kowa sanin wa take kira ta gayawa…”
” Ok..” shine abinda yace kawai…
” Jan zaki na! ni kam ya maganar MUNIBBAT ne? kun dai-dai yanzu ko?…”
Fuskar sace ta sauya zuwa tsananin damuwa, cikin dauriya yace” ai dama a dai-daice muke da ita, ko akwai wani abu ne?..”
Murmushi tayi cikin jin dadi tace” kace ni kuke jira na tsayar muke da ranar aure?..”
A gajiye ya waigo idanun sa sunyi jawar da zallar kishi, yace” da wa din? a’a ba dai ita ba, ina da me so na nima, sai dai ko ANNUWAR…”
Tsananin mamaki da alajab’i ya hana Daddah cewa komai, sai ido da take bin sa dashi da kyar ta iya ɗanne bacin ranta tace” kun samu matsala ne?..”
Zuciyar sace ta karye tamkar mace, haka ya saki wani marayan kuka…
D’adda ta shiga tafa hannuwa, tana sallati haɗi da matsewa a jikin kujera kana tace” na shiga uku ni Nafisatu, me zan gani haka? zanɗandan dakai kana ɓarka kuka kamar wani na yaye?…”
Jikin ta ya shige yana sake sakin wani wani kuka, itama jikin ta ne yayi sanyi sosai har ta kasa motsi, zuwa can tace” ya isa haka! haba jarimin jarimai, haba Aliyu na Jan gwarzo Jan zaki, ban san ka da saurin karaya ba babban mutun, har ina mazan suke! menene zai baka tsoro akan soyayya, ba tun yau ba na fahimci cewa a kwai matsala a tsakanin ku, to gudun kar ace na cika sa ido yasa na ja baki na na tsuke, gashi yanzu tayi kai har maza sun faɗo kasa…”
” Tace bata so na Daddah! MUNI ANNUWAR take so bani ba, ya zanyi da soyayyar ta yanzu? me yasa tayi min haka? shikenan fa na rasata Daddah, saura kaɗai nima na mutu kowa ya huta!…” da sauri Daddah ta bige mai baki, cikin fushi tace” me zatayi da wanda yayi sanadin ƙwanciyar ta? ko bata faɗa min ba na hango tsatsar ƙ’aunar ka a ƙwayar idanun ta, me yasa zaka wahalar da zuciyar ka akan abunda ta jima da samu, ko shaka bazanyi ba MUNI takace kai d’aya tal! kar ka sake kuka akan mace kar na kuma gani! ka tsayar da zuciyar ka waje guda kaji!…” ta faɗa cikin tsawa…
Sai yanzu ya samu sausauci a zuciyar sa, sai yanzu yaji cewa zai iya yaki da kowa akan maradin zuciyar sa, amma fa banda mutun d’aya…
” Muddin shine maradin ta, ba shaka ni kuma zan barta dashi Daddah, gaba ɗaya su Ina so na gan su cikin farin ciki, bana son ganin bacin ran su…”
Ko kala bata sake cewa ba, har ya fice a d’akin…
” Faɗ’a min su waye kike so?…” ANTY ta faɗ’a cikin daurewar fuska…
Hantar ciki na ta kada ban taɓa sani Ina tsoran ta ba sai yau, gashi ta kafni da idanu nayi saurin goge kwallar face dinna, a dan tsawace tace” ba magana nake miki ba MUNIBBAT!??…”
” Alhaji yana da kyau ka duba lamarin yarinyar nan, a gani na barin ta a kasar nan shi zaisa ta mayar da hankalin ta sosai wajen karatun ta, kai da kan ka kace kaga sauyi cikin rayuwar ta, dan Allah a karo na farko ina neman alfharman haka??..” ta fad’a cikin mutu’kar biyayya!..”
Ya gyara zaman sa, cikin nuna kulawa a gare ta yace” banki ta taki ba ai Ameena! abinda nake so ki gane a nan shine, Hajiyar mu tafi so gaba d’aya mu zauna a waje guda, a gabanki fa akayi komai kina jin abinda tace umarini ta bani ba shawara ba, dole tare da Auta zamu koma najeria, in ta amince shikenan sai ta dawo ai!..”
A hankali Mommy ta mik’e zuciyar ta babu dadi tace” dama na san ni har abada bazance ga abinda nake so na samu a wurin ka ba, shikenan ni zan d’auki nauyi yata…”
tana rufe bakin ta Auta na shigowa, fuskar ta a sake take duban su, a shagwab’e tace” Mommy and Daddy wai yaushe zamu koma gida ne?…”.
” Tambayi daddy din ku, amma ke a nan zamu barki, ANNUWAR zai zo ya zauna dake har ki kammala karatunki!..”
Murmushi tayi me sauti kana tace” a’a Mommy ni bana son zama kasar nan, shikenan fa ni da ku sai dai a waya, a’a wallahi bazan jure ba nima binku zanyi!…” ta fada tana noke kafada…
Dariya abin ya bashi, har ya gaza jurewa yace” to wace akayi domin ta tace bata so, ya kenan yanzu? zo nan Mama na!…” ya fad’a yana d’ago mata hannu….
Haushi ya kama Mommy tayi kofa ta bar wajen…