A haka muka cigaba da tafiya da rayuwar mu, babu ranar bazan sai na rubar da hawaye, tuni a ANTY na ta fahimci me nake nufi da kuma abinda nafi k’auna, tana bala’i k’ok’ari wajen bani kulawa, ko da yaushe ita ke rarashi na, da nuna min hanya, duk zaman da za muyi da ita to insha Allah sai ta nuna min MAN shine yafi cancanta da soyayya ta…
A halin da ake ciki a yanzu shi kan shi ANNUWAR ya fahimci akwai wani abu boyayen sirri tsakani na da MAN, duk sanda muke hira dashi, da zarar naga MAN tofa shikenan maganar ta yanke, haka zan kafeshi da ido babu ko kifftawa, shima nashi bangaren haka ne, ko a wajen cin abinci hakace take kasancewa, sau tari sai yayi min magana nake ci, ANNUWAR kuwa ko ta kan shi bana bi…
Kawu na sau biyu yana zuwa gani na, sosai yaji dadi ganin yanda na sauya, na dawo wata k’aramar Hajiya, ga kyau dana kara, shima yayi fass dashi kamar ba Kawu na me shekaru da yawa ba, mun jima sosai dashi d’aga bisani mukayi salama ya wuce ni kuma na shiga ciki…
Zaune yake a gaban Daddah cikin biyayya yace” Hajiya dama nazo ne muyi magana akan MUNIBBAT, ni da ita mun yarda da juna, shine nake so ki shige mun gaba har ta zamo mallakina!…”
A wani gatsine take duban sa fuskar ta sam babu alamar farin ciki, zuwa can tace” ANNUWAR yarinyar fa Yar talakawa ce, masu warin talauci, har yaushe ka fara tunani irin wannan,? ita fa ba yar kowan kowa bace, yanzu har ta kai matsayin da zaka zauna da ita? cewa fa kayi in ma ta mutu ba damuwar ka bane tunda su talakawa basu da galihu, shin me ya sauya maka ra’ayi? _ki kwantar da hankalin ki Mommy inda ina raye sai na auro miki yarinyar da kaf garin nan babu me irin kudin ubanta, ki rabu dasu shirme kawai suke,_ ko ba haka kace mata ba? yanzu ka fasa cika mata burin nata ne? bazan shige maka gaba akan auren yar talakawa ba, kar uwarka tazo tace na lalata mata yara, kajira ta dawo sai ta nema maka irin macen da take so, amma ba MUNIBBAT ba domin ita din ba sa’ar aurenka bace…”” a wulak’ace take mai maganar..
Ranshi in yayi duba ya baci, cikin jin haushi yace” Daddah yanzu ba lokacin tuna baya bane, tunda nace zan aure ta kawai kiyi min abinda nake so, har yanzu ba wai na sauya a buri na bane, ina nan yanda kika sani zan aure tane kawai dan na taimaka mata, kamar yanda kika fidota a ranar kika kawo ta innuwa, ba wai auren soyayya zanyi da ita ba auren taimako ne, wallahi ban tab’a son ta ba, kuma bazan taba sonta har abada, domin ita mumunar k’addara tace, ban dani bana jin akwai wanda zai iya wanna jahadin ya aure ta!…”
” To naji ubana! MUNIBBAT bata buk’atar taimakon kowa sai na Allah, kaje kaji da mumunan burinka, amma ko zaka mutu bazan yarda na aura maka yarinyar mutane ba, ka sani ita din ba ajikan bace, matar manya ce ka rubuta ka ajiye zata auri wanda zai rik’e ta bisa amana, ba shasha irinka ba, alk’awari nayi wa kai na zabin ranta zan bata ko waye a cikin garin nan…”
” _Ni kuma nayi miki alk’awari nine wanda zata zab’a sai naga yanda zakiy_….”
Tauuu tauu tauu!!!
A jere ta zuba mai wasu maruka masu mutu’kar gigita tunani da lisafi, cikin kunar zuciya ta nuna shi da yatsa idanun ta suyi jawur tace” _ko ubanka bai isa ina fad’a yana fad’a ba balle kuma kai!! in kuma kana takama da uwarka ne ko ita bata isheni kallo ba, dan uwarka!!_…” ta ingiza shi zuciyar ta nayi mata zafi domin ya kai ta k’arshe…”
ANNUWAR tsananin zugin mari da raradi, ga tsoron da ya dalsu a zuciyar sa, na gani yanda tayi masa yasa shi saurin barin shashin nata, a hankali yake jin wani tsana ta na taso mai, tun daga ranar dana shigo rayuwar su na sauya komai, a ta dalili na sau biyo kenan yana shan mari a hannun Daddah, ko da wasa bai tab’a jin sona a zuciyar sa ba, yayi haka ne kawai dan ya ci min mutunci, ya nuna min ni ban isa na shigo cikin ahalin su ba, sai gashi Daddah na shirin bashi matsala a karo na biyu, ni ban isa na shigo cikin rayuwar sa na fita haka ba, har yau bai daina min kallon kazamar talaka ba, a baiyya ya furta “” “`NA TSANE KI NA TSANE KI
MUNIBBAT, KUMA SAI KIN GANE BAKI DA WAYO“`
Take ya rikid’e ya dawo ainahin ANNUWAR din sa, idanun sa sun kada sunyi jawur, a sanyaye yace ” I missing you Mommy!!…”
Tsaf ta gama shirya kayan ta yau, zata kai wa aminiyar umma ziyara, sai murna take yau za’a barta taje gidan ANTY…
Kallo tayi fuskar ta cike da murmushi tace” y’ata yau insha Allah muna da bakuwa yarinyar aminiya ta tazo, kinga kin samu kawar hira na kwana biyu, duk da bazan hada ku a d’aki d’aya ba…”
Gani tana farin ciki da bakuwar tane yasa nace” ANTY in ba damuwa ki bari mu zauna a d’aki d’aya mana, ita ma ai kamar yace ko!..”
Murmushi ta sake sakar min tace” k’ware kuwa, bana so a takurawa baby na shi yasa, dole a d’akin baki zata zauna kinji!…” shiru nayi ban sake cewa komai, jin gabana yana fad’uwa sosai a hankali na fara ambaton sunan Allah…
Kamar yanda akan kwatanta mata, haka tabi har zuwa bakin get din, gida ne na gani na fad’a galala ta tsaya kallo bakin ta a bude, murna fal ranta da yake akwai ilimi tayi saurin dakewa, zuciyar ta nayi mata zullo, a haka ta ida shiga cikin gidan…
Har na kwanta wata zuciyar ta raya min zuwa shashin Daddah hira, cikin nutsuwa nake tafiya har zan shiga naji karar kofa alamar ana buk’atar budewa….
AYSHA ta sake gyara tsawar ta zuciyar ta fass, tana zumudin shiga wanna dankareren gidan…
Da salama na shiga shashin nata, shiru babu motsin kowa a palo, cikin na shiga dan na san bazata gaza nan ɗin ba, zaune ta a gefen gado daga gani ta jima a haka domin ta lula duniyar tunani me zurfi, a hankali na zauna a kusa da ita cikin biyayya na kamo hannun ta duk biyu, fuskata cike da murmushi nace” Daddah! tunanin me kike haka?…”
Murmushi ta sakar min tamkar ba abinda ya same ta tace” yaushe kika shigo yar amana ta!?…”
” Kin gani ko Daddah, bama ki san lokacin da na shigo ba, gaskiya ki cire tunani a ranki domin in muka rasaki shikenan mu ganta kan mu…”
Dariya tayi kana tace” babu wanda ya isa ya wuce lokacin sa, in lokaci na yayi ba wanda ya isa ya tsayar dani, abinda nake so daku shine ku k’asance masu mana addu’a, MUNIBBAT!..” ta kira sunan cikin wani yanayi…
Na gyara zama haɗi da ɗaura kai na bisa cinyar ta, kana nace” Na’am Daddah!..”
“” Ina so ki faɗ’a min tsakani ki da Allah, menene alakarki da Aliyu?..”
Shiru nayi babu ko ƙwaƙwaran motsi, zuwa can nace” Daddah yace miki wani abu ne?..”
” Ba tambaya ta nake buƙata ba amsa nake son ji…”
“” _Yana so na Daddah!!_ _nima ina son shi sosai_ sai dai akwai matsalar dake damuna game dashi, Daddah ina mutu’ƙar ƙ’aunar MAN har zuciya ta, amma bazan iya auren shi ba saboda shine burin Kawa ta, AYSHA tana son Mal Haidar so me tsananin, in na shiga tsakanin su tamkar na raba soyayya ne, Daddah muddin MAN zai kasance cikin farin ciki to ba makawa zan iya sadaukar mai da nawa farin ciki, Aysha tafi ni gaskiya Daddah ita ta fara son shi, tun kan na san waye shi take tare dashi, ni take gaya wa damuwar ta a duk lokacin da ciwan sa shi ya motsa mata, tayi kuka akan shi sau babu adadi, me yasa zan rabata da abinda take ƙ’auna? a ranar da zan dawo gidan nan take sheda min irin son da take mai, tayi min musali me girma, Daddah a gaban ta Yayan ta yake baiyya na min irin ƙaunar da yake mun, ga ANNUWAR shi ma yana kan nuna min so! a cikin su waye zaɓi na?…”
Cikin kuka na dakata da maganar ba wai dan raina yaso ba, na so na faɗi duk abinda yake damu na ko hakan zai sa na samu sausaucin a zuciya ta…
ANTY da tun farƙon zancen take tsaye jikin ƙofa, jikin ta yayi bala’in sanyi a hankali ta shigo ɗ’akin, ita ma kusa da Dadda ta zauna ta yanda bazan iya hango ta ba…
Daddah ta shiga shafa min kaina alamar rarashi, har sai da ta tabbatar nayi shiru kana tace” au ke saboda wannan ƙaramin dalilin zaki cutar da zuciyar ki akan abinda take buƙata? shin a tunaninki in kikayi haka MAN din naki zai yafe miki? ko ana gaya miki haka ake sadaukarwa? MUNI MAN fa ke yake so ba Aysha ba, hasali ma bai san tanayi ba, kema kuma kina son MAN to in baki faɗawa Aysha gaskiyar zance ba, kika sadaukar mata da SOYAYYAR ki domin tayi farin ciki har abada baza ta taɓ’a tunanin kinyi ne domin ta ba, tunda bata san abinda ya faru ba, musali in ke kince bakya son shi, kinyi ne domin Aysha ta samu shiga ko ba haka ba? to shi kuma Aysha ba tsarin sa bace kina tunanin zai so tane har ya aure ta? duk da ke kin rabu dashi ne domin ta! ba yanda za’ayi ya aure ta tunda bai san tayi ba, yarinya ta yana da kyau ki nutsu ki sauya tunanin tun wuri, MAN shine yake miki son gaskia, MUNI ko da wasa karkiyi wasa da soyayyar MAN a gareki domin nan gaba zaki gane abinda nake nufi, yana miki son so! shine wanda ya san ciwan ki, shine wanda zai riƙe miki maraicinki, ki bawa zuciyar ki zabin ranki karki bari wani bazan tunani ya haramta miki farin cikin ki, ba wai ina gaya miki haka ne dan ki aure jikana ba a’a iya gaskiyar nake faɗ’a miki a matsayi na na kaka a gareki, kije kiyi tunani wataƙila ki gano gaskiyar!…”
Jiki na yayi mutu’ƙar yin sanyi da kalaman ta, tabbas Aysha bata san akwai wata halaƙ a tsakani na da MAN ba, to in haka ne ni nake damuwa da damuwar ta ba tare da ta sani ba, kawai zan amince dashi in yaso daga baya sai na sanar dashi AYSHA tana son shi, in da rabo sai ya aure ta shikenan kowa ya samu cikar burin sa, amma ta yaya? bazan iya zaman kishi da AYSHA ba, tana da zafin kishi haka nima bana ƙaunar naga ko wace mace a tare dashi matsawar ba mahaifiyar sa ba, to ya zanyi yanzu? Me zan ce mata game da yayan ta da yake dakon soyayya ta? me zan cewa ANNUWAR in ya san abinda yake faruwa?…”
” Yarinya ta karki wahalar da kan ki fa, amsar a baiyyane take ki so me sanki tsakani da ALLAH, karkiyi ruwan ido kinji!…” Cewar ANTY na, ƙunya ta kamani a dan ƙunyace nace” yaushe kika shigo ANTY?…”
Ta harareni cikin wasa tace” kina can kina aikin kuka taya zaki sani, to yau dai abinda ake boye min na sani!, Daddah baƙuwar ta iso shine nazo na faɗ’a miki yanzu zan saka a rakota, ta gaidaki…”
Murmushi tayi kana tace”” to ba damuwa, memakon ki taho da ita kawai…”
” Tashi muje to!..” ta faɗa min tana mikewa tsaye…
Daddah ta harari ANTY cike da tsokana tace” au yau naga wariyar launin fata, wato na shawo miki kan yarinyar ki shine zaki ɗauke ta ko? to ke MUNI tashi kibi maman ki tunda bata son zamanki dani…”
A ƙunyace ANTY ta fice a ɗakin, nan Daddah ta cigaba da rarashi na, da nuna min ilar abinda zanyi, d’aga ƙarshe na shiga bayin ɗ’akin ta domin kimtsa kaina, ita kuma ta fice falo…
A takance dai haka muka ringa samun sabani da AYSHA bamu haɗ’u ba, gashi ANTY ta cika ta da labarin Baby, ta matsu sosai taga Baby sai dai kashi duk lokacin da zamu haɗu da ita, to koni na bar wajen ko ita ta bar wajen, a haka har ta shafe sati a gidan, ko MAN bata taɓa gani ba amma tun shigowar ta taci karo da mayan picture din su a babban falon gidan, kullum fatan ta shi ne ta ganshi ko taga baby…
Muna zaune tare dashi, duk lokacin sa zai ambata mun kalmar so ji nake kamar ba dani yake ba, gani nake tamkar karya yake domin duk abinda yake cewa bana ganin sa a tare dashi, ya kalleni a ɗan gayen ce yace” ina so ko daddah ta tambayeki waye zaɓinki kice mata nine kinji!..”
” To insha Allah…”
” Yauwa tawan tashi muje ciki lokacin cin abinci yayi..”
Gaba ɗaya jama’ar gidan su haɗu ciki har da Aysha daga zauna a kujerar dake kallon ta MAN, sai wani rawar kai yake…
” Oyoyo dear! tun dazu nake baza ido banga shigowar ki, ina kuka tsaya?..” cewar ANTY..
Cikin sauri Aysha ta ɗago d’aga kallon ƙurillar da take mawa MAN, muna haɗa ido da ita na sakar mata wata muguwar harara, ta buɗe bakin ta galala tana duba na, cikin matsanancin mamaki, tace” MUNIBBAT! me kike a nan kuma?…”
Ban kula ta ba ila zama da nayi, kusa da ANTY cikin shagwaɓ’a nace” ANTY!!! yunwa nake ji!…”
Murmushi tayi haɗi da turo min na gaban ta, tana cewa” to BISMILLA ci mana BABY na!…”
MAN ya taso shima, haɗ’i da turo min nashi yana murmushi, muryar sa a rausaye yace” MY HAPPINESS nima ga nawa nan ki haɗa duk ki cinye!!..”
Na fiddo ido waje zanyi magana sai ga Daddah ma ta turo nata, ai ban san lokacin da na fashe da dariya ba, inayi ina nuna su da hannu ɗaya bayan ɗaya, suma dariya suke abin gwani ban birgewa, AYSHA ta zuba min ido babu ko kifftawa…
ANNUWAR tun da ya kalle Aysha sau ɗ’aya bai sake kallon inda take ba, haushi ya cika mai zuciya musamma da yaga ina dariya shi baiga abin dariya a nan ba, ya saki tsaki a baiyyane…
” Ɗibi naka ka tashi mana, ko munci dole sai ka zauna…” Cewar Daddah dake zafga mai harara a wayance…
Shiru yayi kamar bazaice komai ba, sai zuwa can kuma yace” na fara gajiya wallahi, kun dai san har yanzu bamu gama yarda da abinda kuka ɗ’auko ba, yanzu kuma gashi na sake ganin wata ƙazamar talaka a cikin mu, har waye ma ya bata damar zama a inda muke cin abinci? Allah ya dawo min da Mommy wallahi duk sai kun gane…” A fusace yayi maganar…
MAN ya miƙe zuciyar sa babu daɗi yace” ANNUWAR! su waye zasu gane? menene aka ɗ’auko wanda baku gama yarda dashi ba? wacece ƙazama a nan? kana da hankali kuwa? dama har yanzu wannan muguwar ɗabi’ar baka barta ba? me kake nufi ne ANNUWAR?…”
ya ida zance da cafko ma kafaɗa yana matseta da ƙarfi…
To kun dai sai mutumin na ku dan hutu ne, cikin alamar yatse fuska da gajiyawa yace” MAN bana son irin wanna ka sake nace! dama nace na sauya ne wallahi bana ƙaunar talaka kuma bazan taɓ’a son ba har abada!..”
shima ƙ’arfin sa ya saka ya ture MAN din ya wuce abin sa…
Daddah ta dafe goshi game da cewa” MAN ka rabu dashi please, inaga ya fara samun matsala a kan sa gaskiya…”
Aysha gaba ɗaya sai taji gidan ya gundire ta, ta taƙure a waje ɗaya sai jujuya abincin take, a hankali na juya wajen ta cikin kulawa nace” karki ji komai akan Yaya na zan fahimtar dashi kinji, ba wai dake yake ba shi din na daban ne…”
kallo tayi bata sake cewa komai ba har mutane suka fara tashi, aka bar mu dagani sai ita da MAN, Allah Allah nake ya tashi a wajen kar ya ɓaromin aiki…
“” Baby Ina son magana dake yanxu kinji?..”
Murmushin ƙarfin hali nayi kana nace” to ba damuwa amma bari zuwa anjima yanzu na gaji sosai Ya MAN!…”
Cikin kulawa yace” yawo yai tai min dake ko?..””
Ban kula shi ba ila tashi da nayi, dai-dai kunnen Aysha na sunƙ’uyar cikin raɗ’a nace” to yau fa gaki ga MAN, sai ki baiyyana mai abinda ke ranki ko zaa dace!…” duk da zuciya ta sam batayi min daɗi ba haka na ɗaure na furta dan na fita a zargi a wajenta…
MAN ya tsareni da ido haka nima, ji nake kamar na fashe da kuka amma babu hali, Aysha tazo a lokacin da nake so na manta da soyayyar ta ga MAN, shikenan komai ya watse…
” Daddah ita ce fa kawar tawa, AYSHA da nake gaya miki, yanzu haka na bar su da MAN zata baiyyana me sirrin ta…”
” Sannu sarki hankali kin kyauta ai sarauniyar tausayi, tashi ki bani waje shasha kawai…” ta faɗa cike da jin haushi na, zan sake magana ta d’agatar dani ta hanyar ɗaga min hannu, jikina a sanyaye na fice a sashin ta, gani na rasa mafita a karo na farko kenan…
Ina tafiya MAN ya mik’e zai wuce Aysha tayi saurin cewa” am Mal, sai kuma tayi shiru can kuma tace” nayi mamaki sosai da naga nan gidan ku ne, gaskia kun burgeni sosai dama kun haɗa wata alaƙa da MUNIBBAT ?…”
” To AYSHA mun gode, “`Eh ita ce matar da zan aura ina fatan zaki tsaya har bikin mu“`?..”
Cak ta makyale a waje guda, zuciyar ta nayi mata zullo wata irin zufa na karyo mata, hankali a tashe tace” MUNIIBAT fa Mal?..”
*” Eh Ita fa, ko akwai matsala ne?…”*
Ko kallon shi bata sake ba tayo ciki zuciyar ta nayi mata suya, a hargitsi take raɗa min kira, Ina kan ciyar ANTY bayan na gama gaya mata wacece AYSHA a waje na, jikin ta yayi sanyi har ta kasa ce mun komai, sai kuma ga kiran AYSHA…
Na mike da sauri tana zuwa ta kafe ni da ido, wasu hawaye masu zafi suna zubo mata, a haka har ta iso gaba na cikin kuka tace” kin kyau ta MUNI! na zaɓeki a matsayiƙ me rokon amana da alƙawari, na faɗ’a miki damuwa ta dan ina gani zan samu kulawa a gareki, na ɓata lokaci na domin muguwar shawarar ki, Ashe duk kina yin haka ne domin cikar burinki! kin shiga tsakani dashi, kin rabani da masoyi na na gaskiya a ƙ’arshe kin zagayi zaki aure shi, wato ni na zauna zaman jiran gawar shanu ko? me yasa kika sauya a yanda na san ki MUNI? yaushe kika dawo mayaudariya ne? kin cuce ni MUNI kin rabani da abinda nafi kauna, kullum kina cewa _ƙawata zan so ya fara furta miki kafin ke ki fara,_ Ashe duk cutace kika shirya ban sani ba, kin zalinci zuciyar da ta jima da matowa akan maradin ta…”
Gaba ɗaya kaina ya kule hankali na ya tashi, cikin rashin fahimta nace” Aysha tsaya ki ji, har abada bazan ci amanar ki ba!…”
” Karya kike karya ne wallahi, munafika kawai me tausayin munafirci, kin gama dani MUNI, sai yanzu na gano dalilin ƙin amicewar ki ga Ya jameel, yanzu na fahimci komai kina so ki aure MAN dan abinda yake dashi ko?…”
” Aysha wace irin magana kike haka ne? sanin kanki ne kuɗ’i basa gaba na!..”
” Karya kike! kina son shi ne domin wannan dukiyar da kike hange, haka ne mana in ba haka ba yaushe kika san su? nafi kowa sanin wacece ke, duk duniya baki da wasu yan uwa ko dangi da ya wuce Kawu da matar sa, me yasa kika dawo nan gidan da zama? kinyi haka ne duk sabida kudi! Eh amasar kenan MUNI, son abun duniya ya mayar dake wanda yayi miki domin Allah bashi kike gani da daraja ba, kin fifita kuɗi akan komai _sabida baki gada ba! rudin zuciya da nuna ƙulafici yasa kika kwaso jiki, kika taho gidan masu kuɗi munafika kawai wace bata gaji arziki b_…” Kauuu kauuu kauuu shuuuu taji ƙunne ta ya ɗauka, idanun ta suka lumshe jinta da ganin ta suka ɗauke na wucen gadi….
MUNIBBAT ta zare ido gani irin aika-aikar da kayi…” *Ita din yata ce Eh yata ce nace miki! kin ɗauka bata da kowa a duniya? ko an gaya miki bata da gata ne? ba ita take soyayya dan kuɗi ba kece kika haukace domin kuɗi, tun wuri ki kauce a hanya ta, ko uwarki bata isa tayi abinda kikayi ban hukunta taba, alaƙar mu da MUNI ta jini ce ba wai irin taki ba ta ƙawar uwa, shashar yarinyar kawai akan wata bazan soyayyarki da bai san kinayi ba zaki zo kina ɗaga mutane murya wai kenan me masoyi!, kin san yanda muke fama da ita akan shi kuwa tana ƙi? tana son MAN fiye da yanda kike son shi amma taƙi yarda dashi sabida ke! wallahi azeemin da na san kece Aysha da kike saka min yarinyar a damuwa, da ko hanyar gidan nan bazaki sani ba bare ki shigo shi…”*
Kuka nake sosai maganganun ANTY na dawo mun cikin kai, *yata ce alaƙar mu da ita ta jinii ce*
Aysha ta gigice, da irin huƙuncin da ANTY ta yanke mata, maganganu ANTY sun sosa mata zuciya sosai, ta runtsi idanun ta hawaye na zuba a hankali ta zube akan gwiwoyin ta, cikin mutuƙar dana sani tace” kiyi haƙuri ANTY, banyi haka dan na bata miki raiba! na kasa jurewa!…”
Tausayin ta ya kamani, cikin ƙarfin hali nace” kiyi haƙuri ANTY dan…”
” Ki min shiru baby! bana so ki sake cewa komai a nan!…”
Da gudu nayi ɗaki na, kuka na yana kara tsanan ta, tabbas tun da nake a duniya babu wanda ya taɓ’a gaya min magana me zafi da ciwo irin ta AYSHA ba, na shiga rera kuka kamar me waƙa…
Aysha ta ringayiwa ANTY naci akan sai tayi haƙ’uri, har sai da ta sauko a tsanake ANTY tayi mata bayani halin da ake ciki yanzu, ta kara dacewa” MUNI ƴata ce ta ciki na, domin yarinyar Yaya nace ita, ita kadai ce damu ko ita bata san alaƙar mu da ita ba, duk kan mu nan MAN muke so ta aura, ita ma shine zaɓin ta gobe insha Allah zaa kawo ƙ’arshen wannan matsalar ki shirya kayan ki yau zaki komai gidan ku…” tana rufe bakin ta ta mike ko a jikin ta…
Aysha tayi kuka kamar zata mutu ganin babu sarki sai Allah yasa tayi shiru ta shiga bawa zuciyar ta haƙuri, amma taji daɗi yanda MUNI ta nuna mata ƙauna duk da basa tare, gashi ita kuma ta ci mata mutunci…
” Kiyi haƙ’uri ƙawata ni sam ban san halin da ake ciki ba, ANTY ta gaya min komai kiyi haƙ’uri kinji!..” cewar Aysha dake tsaye akai na..
Na share ƙ’walla ta cikin muryar kuka nace” ba kiyi min komai ba Aysha, duk wani abu da kikayi kinyi ne akan abinda kike so, to ni banga laifinki ba, ki ƙwantar da hankalin ki gobe insha Allah MAN zai zamo naki haka yayi miki?…”
Ta sauke ajiyar zuciya tace” a’a MUNI ni yau zan tafi, na sani MAN shine mafarkin ki, me yasa kike so ki sadaukar min da farin cikin ki? shine zaɓ’in maman ki kaka Daddah, haka shima ke yake so, to me yasa ni da ba’a san inayi ba zan shige tsakani, a’a MUNI bazan raba ku ba nima Allah ya bani nawa!…”
Tausayi ta bani nace” Ina so ki jira zuwa gobe kinji ƙawata! bana so ki sake cewa komai, na fi kowa sani kina mutuƙar ƙ’aunar MAN ki bani zuwa gobe…”
MUNIBBAT da kan ta roƙi ANTY ta bar AYSHA zuwa gobe…
Washe gari, gaba ɗ’aya kowa na gidan yana zaune a cikin tanƙameme palo, babu wanda yayi ƙ’aramar shiga ko ka kalla ba baya ba, Daddah da kowa ita yake sauraro ta dube MAN da manya idanun ta, cikin isa tace”” MAN kai muke sauraro!!..”
Ya saki murmushi yana sosa kya a ƙunyace, yace” a’a Daddah ni a shirye nake da duk abinda aka yanke, fatana ɗaya shine a tambayi yarinyar abinda take so!…”
Daddah ta ƙura mun ido har sai da na tsora ta kana tace”” MUNIBBAT! ke muke jira!..” da sauri na kalle AYSHA dake kallo na cikin tararabi, ANNUWAR yayi gyaran murya nayi saurin kallon sa…
ANTY tace” baby! dake fa ake!…”
Rintse ido na nayi abubuwan da suka faru dani a baya suka shiga dawo min tamkar yanzu akeyi, a hankali na furta”” *kuyi haƙuri da abinda zan ce, tabbas ina mutuƙar ƙaunar jarime na, domin shine cikar burina, ina son shi sosai bana ji ko nan gaba akwai wanda zan so sama dashi, na kalle MAN ido cikin ido nace kana sona kamar yanda nake son ka? zaka iya sadaukar min da soyayyar ka? kana jin abinda nake ji a zuciya ta MAN?…”*
ANNUWAR ya zuba mana idanu cikin ƙunar zuciya da mamaki abinda muke, domin shi sam bai san akwai wata alaƙa tsakani na da dan uwan shi ba…
” “`Ina son ki!! ina kaunar ki, ina ji a jikina bazan iya rayuwa ba tare dake ba MUNI, ina miki son so! naji dadi sosai yau a gaba jamaa kike baiyya na min abinda na jima ina son ji daga gareki, amincewar ki kawai nake jira shin zaki aure ni!?..”“`
A hankali na miƙe tsaye hawaye na zubo min, na share cikin ƙarfin hali nace” ina so kayi mun alfharma ɗ’aya tak MAN! *Ka manta ka taɓ’a son wata me suna MUNIBBAT a rayuwar ka, ma’ana ka manta dani!..”*
Dumm gaba jama’ar waje Ya faɗi zuciyoyin su sukayi baƙi, ran su ya ɓaci MAN ya mik’e a zuciye…