Juyo dani tayi cike da jin haushi na, ta wanke min fuska da mari, tana hawaye take cewa” kina hauka ne MUNI? kin san me kike cewa kuwa? MAN fa! buluci zakiyi musu? shine fa wanda yayi jinyarki a lokacin da baki san inda kan ki yake ba, shine wanda yayi sadaukarwar jinin sa har kika samu damar ci gaba da rayuwa! wannan shine sakayyar da zakiyi masa kenan? shine mutumin da yaso ki a lokacin da baki da wata nutsuwa! ya so ki tsakani da Allah! ya ƙauna ce ki, shine JARRIME da kikewa kuka a ko wanne dare! yaushe tunanin ki ya sauya? saboda ni zakiyi toshewa kanki makafar farin cikin ki? Kul kul MUNIBBAT in dai nice daga rana irin ta yau bazan sake tuna cewa na taɓ’a son wani abu me kama da MAN ba har abada! insha Allah! K…”
Cikin sauri na toshe mata baki ina me girgiza mata kai alamar tayi shiru, cikin zubar da hawaye nace” me yasa zaki cutar da kanki ta wannan hanƴar? na sani duk wannan kalaman naki iyaka fatar baki ne kawai, bai kai zuci ba! MAN kike so ko ba haka ba?…”
” A’A ban taɓa son shi ba!..”
” Aysha meyasa zakiyi min haka!..”
” Sabida tafiki sani hallaci MUNI, tafiki sani alhairi! ita labari kawai na bata amma ta san ya kamata ba kamar ke da abin ya faru dake ba, tunda har bakya jin shawara kiyi abinda kikafi gani ɗai-ɗai ne bazan sake miki magana akan wannna ba!…” cewar ANTY kafin nayi wani yunƙuri tuni ta bar falon…
ANNUWAR ya miƙ’e gani tashi damar tazo mai a sauƙaƙe, cike da yauƙi iri na shi yazo gaba na cikin taushin murya yace” MUNI ta! tabbas kin san hallaci, ke cikakiyar aminiyace, har naji na ƙara sonki fiyye da baya, ni sam ban san akwai wani abu tsakani ki da YA MAN ba, ina sonki sosai bazan iya rabu dake ba, na san ɗan uwa ‘na, yana san abinda nake so, kamar yanda kika nemi alfarma a wajen sa ki tayani neman tawa duk sa na san har abada bazai taɓ’a ƙin amincewa ba ko dan nayi farin ciki, ya barini tare dake ko farin ciki na zai ɗ’aure dan Allah Ya MAN!???…”
Daddah ta yunƙura a fusace za tayi magana MAN yayi saurin tare ta, ya kalle ANNUWAR cike da tausayin sa yace” bana ji a duniya akwai wani abu da zaka nema a waje na, na gagarayi maka shi har abada bazan zamu sanadiyar raba ka da farin cikin ka ba, ANNU muddin zaka iya auren MUNIBBAT, kuma ka kula min da ita fiyye da zato na na amince na bar maka ita, kaje ka gwada taka basirar ko zaka dace, amma ka sani _itace farin ciki na, mafarki na maradin zuciya ta, bana jin akwai wata mace da zan sake so kamar ta, ina son ta fiyye da zaton ka, zan barta ne kawai sabida ka nuna min kafi ni son ta, ka riƙ’e ta amana ANNU dan Allah karka cutar mun da ita!…_”
Ya juyo gareni, idanun sa jajir cikin dake wa da jin zafi na, yace” haka yayi miki ko? haka kike so ko? naji na amince na ƙware a soyayyar ki, a karo na farƙo a rayuwa ta banyi nasara ba, amma ba komai na amshi wannan a matsayin kaddara, alfharma da kike nema kiyi haƙuri bazan iya ba, a tsarin rayuwa ta Aysha ba ita ce a gaba na ba, dama can ina da wace zan aura, na barki lafiya amaryar ANNU!…”
Cikin sauri ya ɓace a wajen, kuka nake tamkar zan sheɗi tsananin danasani ne yake nuƙurƙusa ta, Daddah ta mike tana aikawa da ANNU wani mumunan kallo, kana ta ɓace a wajen, shima ko ta kai na bai bi ba ya wuce abin sa, AYSHA ta zuba mun ido na wani lokaci kana tace” gashi nan kin tashi a biyu babu, kin ɓ’atawa kowa rai sabida wani banzan tunaninki, wallahi ni sam baki birgeni ba, a ƙwayar idanun sa kwai na hango tsatsar kiyayyar ki, banaji mutumin sonki yake tsakani da Allah, amma tunda kin amince mai ke kika sani, hakin bawan Allah nan ma kawai ya ishe ki…” ta wuce abin ta…
A ranar Aysha ta bar gidan, ko ganina bata sake tsayawa yi ba, ANTY Kam sosai ta ɗ’auki fushi dani, a wajen Daddah ne kawai nake samu nutsuwa, dan ko kaɗ’ai bata sauya min ba, ta kanyi min nasiha da nuna min abinda ya dace ni, duk cikar gida nan babu wanda ya gaya min MAN dinna bashi da lafiya, har ya ƙwantar dashi a asibiti abinda na lura dashi kawai ANTY yanzu bata cika zaman gida ba, haka Daddah wani lokaci ni kaɗai ake bari kamar mayya, wasa-wasa har aka shafe sati biyu..
Tsakani na da ANNU kuwa tunda daga ranar ban sake ganin sa ba ko a falo bama haɗ’u dashi…
Katsema aka shiga gyaran gidan ta ko ina, cikin sati biyu cif aka kamala komai, sauki na ɗaya ma ina zuwa makaranta kuma wuni nake, in na dawo kuma zan samu Daddah, ANTY ma na rabu da ganin ta, duk abin duniya ya ishe ni ga tunanin MAN dake narke a zuciya ta, ga rashin kulawar da bana samu a wajen ANTY, take ƙewar Kawu na ya dawo mun sabo dal, nan da nan tunani ya kwantar dani, ban gaya wa kowa bana jin dadi ba, abinda na sani duk daren duniya bana iya barci sai tunanin yanda za’ayi na gyara ƙ’usƙure na nake, bazan iya cewa ga adadin kukan da nayi ba, abinda na sani a yanzu hawaye shine adon fuska ta, idanu na sun ƙanƙance ko magana muke da Daddah kai na yana kasa bana bari tana kallon fuska ta…
Zaune yake a falo yana ta latse-latse a wayar sa, kallo ɗ’aya nayi masa na san yana jin dadi chat din da yake, na zaune nesa dashi cikin girmamawa nace” barka da yamma Ya ANNU!…”
A hankali ya ajiye wayar sa daga gefe, fuskar sa babu an’nuri ko kaɗai yace” barka da yamma kuma? gaishe ni ne bazaki iya ba ko tsantsar rashin tarbiyar ne kika fara nuna mun?…”
Mamakin kalaman sa ya san na gaza magana, zuciya tayi mun wani nauyi…
” Ke ba magana nake miki? tukuna ma waya baki izinin zama a inda nake? kina yar matsiyata dake wace baki san menene arziki ba, har kin isa ina zaune kizo ki zaune da wannan ƙazamin jikin naki!…”
A yanzu hawaye sun gama jike mun fuska , na ɗ’aure cike da ƙarfin hali nace” ANNU anyya kana cikin hankalin ka kuwa? nice fa MUNIBBAT dinka! nice fa wace ka nemin alfharma akan soyayyar ta, me kake cewa haka? ina ga akwai wanda ya ɓata maka rai, kar fushi wani ya shafeni dan…”
Ɗauke ni yayi da wani ingarman mari, yana huce kamar wani bakin kumurci yace” ke har kin isa ina magana kina magana! ke wacece waye ubanki? me kike dashi? a cikin tsarin rayuwa ta babu irin ku a cikin ta, bari kiji ki kuma sani wallahi azeemin ban taɓa sonki na, na tsaneki na tsaneki bana ƙaunar ganin ki ko kaɗai, kuma bana jin akwai ranar da zan fara sonki a duniya, a sanadiyarki rayuwa mu ta sauya, kece kika shiga tsakani na da Daddah, ke ba alhairi bace a cikin rayuwar mu! kuma nayi rantsuwa sai kin fita a cikin ahalin mu! Mayya kawai!!!…
Na firgice iya firgita, na tsora ta iyakar tsoro, zuciya ta ta karaya na gama gigicewa, komai nawa ya tsaya cak Ina ji ina gani ya ɗauki wayar sa, sai da yazo gaf dani ya tofa mun meyau din baki sa a hankali ya furta mun” ƴar matseya ta, mayya kawai!…”
Nafi awa a tsaye a wajen, sai da naji ina neman faɗuwa, sannan na zauna sai a lokacin wasu hawaye masu zafin tsiya suka zubu mun, na fashe da wani mugun kuka me mutuƙar cin rai, a hankali nace” nayi ƙusƙure! nayi ƙusƙure nima!…”
” Eh nayi ƙusƙure na amince ni nayi ƙusƙure, amma me yasa zai mun haka? dama duk karya ce?…” A haka ANTY ta same ni, har zuciyata tanaji tausayi na kamar bala’i, amma ta ɗaure cikin ɗaure fuska tace” MUNIBBAT me kikeyi a nan ke kaɗai, tashi ki koma ciki…”
” A’A ba inda zani! sai kin gaya mun gaskia kema ba so na kike ba ko?…”
Harɗe hannuwan ta tayi a ƙirjin tana kallo na, fuska ta babu alamar wasa..
Nace” Eh ya faɗa mun ni mayya ce da gaske ni din mayya ce ANTY? ni nayi komai ne domin aminiya ta, amma me saya baza ku fahimceni ba? bashi kaɗai ba nima ina haukar san shi amma ANNU ya gaya min duk *baso bane cuta ce* sau biyu kenan a gaba ki ana cewa ni matsiya ce babu abinda kikayi a kai! yace bai taɓ’a so na ba, ya tsane ni baya ƙ’aunar gani na, me yasa kuka rabani da Kawu na? MAN a gaban ku yace ya rabu dani kuma kun san karya yake amma bakuce komai ba, kema kin ɗaina kulani kin ɗaina mun dariya, na rabu da ganin ki na wani lokaci, to wai me na tsare muku ne? na yarda na amince a yanzu ni *banyi dace ba* eh zan komai inda na fito na gaji!…”
” Kin gama? shikenan abinda ke bakin ki? dan dai ƴar wanna maganar? tsaya ma kafin shi ya furta waya fara furtawa? gara shi ɗan uwan sa ya barwa ba kamar ke da kika raina soyayya sa ba kika bawa ƙawarki! duk abinda zaki ce kin jima baki ce ba, wawuyar yarinyar kawai…” tana ida zance ta wuce abin ta…
” Na shiga uku, ya zanyi ne wai? ina zan kama ne?…”
Na sake faɗuwa a wajen ina kuka, da sauri ANTY ta karasa barin falon gudun kar zuciyar ta karaya…
Shi kuwa ANNU cikin mutuƙar farin ciki ya bar falon, kai tsaye gidan su Hafsat ya nufa…
ANTY tana shiga daki ANNU ta fara kira, kamar zata tashi sama amma a banza yaƙi ɗauka, gajiya tayi ta haƙura…
Shi kam yana kallon Kiran ta yaƙi ɗagawa, ƙarshe ma ya ƙashe wayar gaba ɗ’aya…
Nima na ƙauracewa kowa, bana hira da kowa tsakani da su sai gaisuwa, abinci ma sai naji yunwa zata ƙasheni nake ci…
To matsala kam tsakani na da ANNU kullum cikin jifana yake da kalamai masu zafi da ƙaushi, in nayi magana na sha mari…
MAN gaba ɗaya ya ɓace a gidan, tunda aka sallamo sa ya rabu da zaman gida, kullum yana yawo wuraran shaƙatawa ko hankalin sa zai ƙwanta, baya bari mu haɗu dashi ko kaɗ’ai, amma duk ƙwanan duniya sai ya gani hankalin sa yake kwanciya, video call suke da ANTY cikin wayo da dabara take haskeni ya gani ta kashe wayar ta…
To yau iskacin sa yafi na kullum, ya mayar dani wata ƴar aiki komai yake so sai yace ni, cikin gadara yace na haɗo mai coffee, ban kawo komai a raina ba na miƙe, ko da na haɗa sai na tafi ɗaki na, gaba ɗaya sai na sha’afa da abinda ya sani, sai zuwa can na tuno yama gama hucewa, cikin sauri na ɗauka jikina yana rawa na taho falon, coffee na gani a hannun sa yana sha, gabana ya faɗ’i na ɗaure, nace” yallaɓ’e gashi!..” kamar yanda ya ingaya min kar nake ce masa Yaya domin yafi ƙarfi na…
Ajiye na hannun sa yayi, da yake dan bala’i ne sai yace” matso dashi to!…”
Jikina har rawa yake wajen miƙo mai, ƙ’arewa coffee din kallo yayi yaga yana ta turiri, hankalin sa ƙwance yace” me kike tsayayi har kawo wannan lokacin?…”
” Kayi haƙ’uri mantawa nayi!..” cikin rawar murya nayi maganar domin har ga Allah yanzu tsoran sa nake kamar raina…
” Daga yau bazan sake sakaki aiki ki manta ba…”
Na dago da sauri, lokacin MAN ya kawo kai zai shigo, Daddah ta fito kallo ita ma, ANNUWAR ya daga cop din tae din dake turiri ya watsa mun a fuska, wani irin zugi da radadi ne ya ratsani na saki wata kara me hawa kai…”
Daddah ta zaro ido waje, cikin mutuƙar razani, MAN yayi wata muguwar sufa cikin kaɗ’uwa, ya damƙeni a jikin sa baiyi wani jinkiri ba, wajen cire rigar sa ya shiga goge mun fuska, hankali a tashe…
ANNUWAR ko a jikin sa, sai ma wani yauki yake yana kara batsewa…
Gaba ɗ’aya MAN ya gama haukacewa, yama rasa wanna irin taimako zai bani, ruwa me sanyi Daddah ta miƙo me aiko ya shiga danna min a fuska ta, yana ta jera mun sannu, jina da nayi a jikin sa hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba, zuciya tayi sanyi na nemin ciwon narasa, sai kukan shagwaɓa da nake fitarwa a hankali, ga wani ruwan sanyi da yake danna mun a face din ya haɗ’u ya sake bada wata ma’ana daban…
A hankali ya furta””” _MUNIBBAT! bude idon ki na gani! kalle ni nan! ya ɗaina mike zafi! kalle ni Mana._..” cikin wani salo yake maganar..
Aiko na sake narƙewa, cikin kuka da turo baki na nuna gefen fuska ta ina kuka kasa-kasa…
Yana taɓawa nayi saurin cewa” Ashe!!..” alamar zafi, shima yamutsa fuska cike da tausayi na, ji yake tamkar ya cire ciwon ya dawo kan shi, wani irin so mukewa junan mu me ma’ana, wata irin soyayyatace take fuzgar sa, a hankali ya miƙ’e zai wuce nayi saurin riƙo hannun sa, ya juyo a fusce, na buɗe ido na a hankali da sukayi jajir nace” I LOVE YOU SO MUCH HUBBY…”
DA SAURI YA KAWAR DA KAN SHI GEFE…