Skip to content
Part 26 of 28 in the Series Waye Zabin Munibat? by Husaina B. Abubakar

Na sake riƙe shi da kyau, idanu na fal ƙwalla tsananin soyayyar sa tana ribata ta…

Cikin hikima ya zame hannun shi daga nawa, a hankali ya sulale ya bar falon, wani irin kuka ya ƙuɓuce mun…

ANNUWAR ban san yanda suka ƙare da mutanen gidan ba, amma da dukn alamu sun hukunta shi domin yanzu ko ganin sa ban cika yi ba…

 A cikin wata biyu da suka wuce abubuwa da dama sun faru, masu daɗi da akasin haka…

Gaba ɗaya yanzu bana ganin mazan gidan, babu abinda yafi ɗaga min hankali samu da rashin MAN a tare dani, Anty na ta sauko amma ba kamar yanda na santa ba…

Ƙwance nake akan cinyar Daddah, muna hira tamkar ana jeho shi daga bakin baka, ya faɗo ɗakin fuskar shi babu wani annuri yace” Daddah ina wuni?…”

Ciki-ciki ta amsa da lafiya..

“” Dama zan faɗa miki ne  na kai ƙuɗin aure na kuma sati biyu nace ina so aka saka…”

” Dariya tayi tana mai kallo mashirmaci tace” ka kyautawa rayuwar ka a’i, waye ubanta to?…”

Ya saki wani ƙyasaitacen murmushi kana yace” ita ba ƴar kowan kowa bace, face ƴar matsiyata! bata da wani gata domin ko mariƙanta ma sun garara riƙeta, Daddah ba kowa bace face yarinyar dai dana faɗa miki ƙwanaki zan taimaka mata!…”

Kamar yanda ya sunƙuyo da face d’in sa yana magana, haka ta wanke sa da wani mugun mari, kafin yayi wani yunƙuri nima ‘na sakar mai nawa marin zuciya ta na tafasa, cikin tsakanin baƙin ciki da matsananciyar damuwa, nace” kai waye!??? da me kake taƙama ne? duk duƙiyar da ba kai ka tara ta da kan ka ba suna ta ohho! domin kuɗin magadane! akwai babban matsiyaci ma irinka wanda zuciyar sa ta mutu akan abinda bashi da iko akai! kullum maganar ka akan ƙuɗi, kuɗi dai ko? bazan san kai me kuɗi ba ne har sai ka tashi ka nema da kan ka, me mataciyar zuciya kawai!!…”

Tsananin mamaki na da tsana ta shi ya hana shi aiwatar da komai, kallo na yake cikin matsananciyar kiyayya ta, ‘na juya zan wuce ya wani fizgoni gaba sa kafin ‘na daidaita tsawa ta, shima ya zuba mun wani ingarmar mari me hawa ka.

Bai gama sauke hannun sa ba, shima yaji saukar wani bahagon mari me tsakanin ƙara da zafi…

ANTY CE a tsaye akan shi, zuciyar ta ‘na tafasa ta buɗe baki za tayi magana.   itama taji saukar nata marin cikin mutuƙar mamaki da mutuwar tsaye gaba ɗaya mu muka juya, idanun mu a waje…

Tsananin tsorone ya saka ‘na saki wayar nima, mamaki al’ajabi ƙarar a fuskanta.

Jamaa waye zaiyi wannan aika aikar ‘dan Allah? 

*****

Mommy ce tana huce tamkar baƙin kumurci, ta nuna Anty da yatsa cikin zallar masifa tace” ko da wasa karki sake gigin taɓa mun yaro! domin yafi ƙarfin ƙazamin hannun naki! ki godewa Allah ba akusa zuciyata take ba da wallahi sai na yanke miki hannu!…”

Kauu tass tass! Daddah ta zuba mata wasu marika masu mutuƙar azabar zafi da raɗaɗi, cikin ƙaukausar murya tace” kinyi ‘na farko kinyi na ƙarshe muddin ina raye a cikin gida nan ke baki isa kin wulaƙanta mun yarinyar ba, shigowarki kenan da abinda zaki saka mana kenan? wannan itace godeyar ? shin kin fara bin ba’asin dalilin hukunta shi? wato ke aimaka uwar ƴan ƴaƴa shine kika ware hannu kika zafgawa ƴata mari ko? ke tsaya m’a tafiyar da kikayi bai koya miki hankali acan ba dama?…”

Mommy riƙe da kunci take duban daddah zuciyar ta babu daɗi, wasu hawayen baƙin ciki suna zubo mata, babban ɓacin ranta shine a gaban kishiyar ta Daddah ta mare ta ga ɗan ta dake tsaye shima yana muzure…

” Daddah! nice ‘fa! yanzu sabida nayi hukunci akan wannan abar shine kika mareni a gaba yaro na da ita?..”

” shitttt! Amina ki ɓace min a gani kafin nayi kasa-kasa dake!…” cewar

Daddah da ranta ya gama ɓaci…

Anuwar ya kamo kafaɗar Mommy domin ya kula bata ‘da niyar tafiya, Daddah kuma tsaf yasan zata aikata abinda yafi wannan, cikin sanyin jiki yace” pls Mommy muje!..” ya faɗa yana tura ta, akan dole ta bishi ba dan ranta yaso ba…

Ni kam tunda aka mari Anty wani irin tsoro ya kamani ban jira komaiba, na gudu bayan kujera warwas nayi a kasa tamkar babu rai a tare dani…

Suna shiga shashinta, tayi maza ta juyo dashi cike da masifa ta zafga mai mari cikin ƙunar zuciya tace” uba me ka aikata musu da zafi haka? Antyn ku baza ta taɓa saka hannu ta dake ka haka kurum ba, dole sai da babban laifi! maza faɗa mun ko na sauya maka kamannin?…”

Ya gigice sosai zuciyar sa ta shiga soya, wata irin tsana ta yake ji kamar yaje ya shaƙeni ‘na mutu, ya daure cikin biyayya yace” kiyi haƙuri Mommy zanyi miki bayani a tsanake yanzu ki hutu zuwa anjima zan shigo, amma ki yarda dani banyi musu komai ba, har yanzu My son dinki yana nan yanda kika sani magance akan wata matsiyaciyar yarinya, Mommy bana son talaka ko kaɗan…” cike da shagwaɓa yayi maganar…

Zuciyar ta tayi mata sanyi ta dube shi cike da ladamar hukunta shi, ta kallen hannun ta a hankali ta sauke ajiyar zuciya kana tace” bana son daukar magana Son ka kiyayyeni kaje zan kira ka!…”

” Mommy!!..” Ya faɗa a sangarce.. cike da soyayyar sa ta dube shi, da ido yayi mata nunin abinda yake so, babu gardama ta ware mai hannuwa ya taso da sauri suka rungume juna, cike da ƙewa…

ANTY ta wuce shashin ta, zuciyar ta babu daɗi, Daddah ma ɗakin ta wuce zuciyar ta a jagule…

Shirun da naji wajen yayi ne yasa na taso a hankali, kamar ɓarauniya na gudu  ɗaki na…

Duk wannan badaƙalar da ake DADDYN su bai sani ba, haka MAN DA NAFISATU…

Daddy kai tsaye ɗakin Anty ya taho, cike da ƙewar matar sa sauƙi ɗaya ma suna video call, ANTY kuwa zuwan ta ɗ’aki ba sanya ta tsaya ba uban ado taci na kece raini tamkar ba abinda ya faru, ko ina na ɗ’aki sai tashin ƙ’amshi yake, gaskiya ANTY na yar gayuce gashi ta iya shanye damuwa, a haka ta shigo ɗakina fuskar ta a sake tace” Baby! Baby! wai har kinyi barci?…” ta faɗa tana juyoni, ɓata fuska tayi gani hawaye shaɓe-shaɓe a face dinna…

” Meye haka kuma?..”

Rungume ta nayi ina kuka me sauti, cikin raunin murya nace” kiyi haƙuri dan girman Allah ANTY!? ki yafe min na san nice sanadin komai, dan Allah kiyi haƙ’uri! ni gaba ɗ’aya ma na rabu dasu!…”

Dariya tayi kana tace” ke sakeni karki bata mun ƙwalliya na, ki tashi ki shirya daddyn ku ya dawo ɗaga yau duk wani kayan sawarki suna ɗakina, ƙwalliya ta zama dole a gareki dokar gidan nan ce Auta zata koya miki komai, tashi maza ki shirya yanzu zan shigo kizo ku gaisa basai na kiraki ba…”

Ajiye mun kayan tayi ita kuma ta fice da sauri, da ido na rakata zuciyata duk babu daɗi, gaba ɗaya na zargi kaina waani kaɗai ma na kasa sakewa, ji nake kamar na bar gidan, da wannan tunanin na shiga bayi domin shiryawa kamar yanda tace…

Tana fitowa Daddy na shigowa, tsallen daɗi ANTY ta daka haɗi da rungume mijinta, shima tsam ya rungume abarsa zuciyar sa nayi ma zullo…

Ɗakin ta suka shige kowa yana nuna tsantsar ƙewar sa ga abin ƙaunar sa….

Kallo ɗaya tayi masa ta kawar da kanta gefe, cikin jimami tace” MAN wai me yake damunka haka? baka ganin yanda na dawo naga ɗan uwanka gwanin sha’awa, idanun ka kawai ma kalla na san zuciyar ka bata jin daɗi matso ka gaya min damuwar ka ɗan albarka!…”  Allah sarki uwa kenan…

A hankali ya matso inda take, cike da ƙewar ta ya ƙwantar da kan shi a bisa cinyar ta, muryar sa a sanyaye yace” missing you so much MY Mom!…” ya laumshe idanun sa..

Ita ma kissing ɗinshi tayi a k’uncin sa, cikin tsananin ƙewar su tace” ina fatan duk na sameku lafiya?…”

” Mommy shine kika tafi kika ƙi dawowa ko? munyi fushi to!..” ya faɗa yana noƙe kafaɗa..

Dariya tayi cikin jin daɗi tace” sorry MAN yanzu ai gani na dawo, duk da bana tare daku amma kuna raina kullum tunanin ku nake ai!..” ta faɗ’a tana ja mai kunne..

Auta dake tsaye akan su ta saki murmushi me sauti kana tace” Ya MAN wato ni ba’ayi missing ɗinna ba ko?..” cikin turo baki ta ƙarke zancen…

Da hannu ya yafito ta tana zuwa ya rungume ta amma ba fa bai tashi daga cinyar Mommy ba, gaba ɗ’aya ta haɗa su a jikinta ita ma tana faɗin Allah ya albarkaci rayuwar ku yaran Mommy…”

Ameen sukace suna dariya…

Gaskiya uwa daban take a duniya, ko menene halinta kuwa uwa uwace, ita ce ƙarshe a jin dadi…

To kamar yanda ANTY tace min na shirya tsaf dani, na sha hijabi har kasa cikin mutuƙar biyayya na nufi palon ta bakina ɗauke da sallama, daga ciki aka amsa mun kaina a kasa na shiga ɗ’akin, ban ɗ’ago kai ba har na zube a k’asa murya ta a raunane nace” Daddy ina wuni! ya hanƴa da aiki, an dawo lafiya?…” A nutse nayi maganar…

Murmushi ya sakar mu cikin jin dadi yace” zo nan ƴata!.. dube ANTY da take ta murmushi yace” itace yarinyar tamu?..”

” _Eh yarinyar yaya na ba!..”_

Da sauri na ɗago ina duban ta, ko inda nake bata kalla ba, a hankali naji ” Daddy yace” Allahu akubar Allah ya jikan sa da rahama Allah yasa ya huta, mu kuma Allah ya taya mu roƙ’o, MUNIBBAT ko?..”

Har yanzu ANTY nake kallo da ta ɗaure fuska taƙi kallo inda nake…

” MUNI kinje ki gaida Mommy ɗin ku ko?..”

Dam gaba na ya faɗ’i na dube shi, a tsorace nace” a’a yanzu dai zanje…”

” Ok yayi kyau kije ku gaisa, Auta ta samu kawa!..” ya faɗa yana murmushi haɗi da shafa mun fuska…

Jikina a sanyaye na tashi, har yanzu ANTY taƙi kallo na, karo na biyu kenan da naji ta faɗi wannan kalmar gashi na kasa tambayar ta…

Shashin Daddah na wuce zuciya ta na zulime, to a nan ne na sake shan mamaki gani Nafisatu a zaune jikin Daddah sai shagwaɓa take zubawa, rabewa nayi a gefe domin da farko bata ganeni ba sai ɗ’aga baya, munyi murnar ganin junan mu sosai Daddah kam sai murmushi take mana,  cike da zumuɗi Nafisatu tace” zo muje wajen Mommy na! dama kullum ina basu labarin ki yau zata ganki!…”

Ni sam banji daɗin maganar ta ba ila tsoro da ya sake gigitani, nayi murmushin yake cikin inda inda nace” Nafisatu bari ANTY ta fito sai muje gaba ɗaya!..”

Daddah tace” MUNI tashi kije mana!..”

Idanuna suka ciciko da ƙwalla, da ido Daddah tayi nunin kar na damu muje kawai, jikina a sanyaye muka tafi…

Su uku ne a falon kallo ɗ’aya nayi musu nayi saurin yin ƙasa da kaina, domin wata irin fargaba ce ta ratsani gaba ɗaya su sun kaffeni da idanu, Mommy ta haɗe girar sama da ta kasa bata ko motsin kirki take duba na….

Bani da abinda zan baki na saka miki, tabbas ke maƙociyar arzikice kin cancanci yabo ta ko wanne gefe, ‘na gode na gode sosai Allah ya biya miki buƙatunkin ‘na alkhairi, dan Allah ina neman alfarmar ku duk wanda yake b’in wannan novel dinnawa ya tayani godeya wajen MAMAN IMAN OR ALMAN, AND BASHIR ALLAH ya kara danƙon zumumci na gode…

Nayi kasa da kai na gabana yana tsananta faɗuwa, Nafisat tace” mommy ga ƙawa ta munibbat  wace nake baki labarin ta kafin muje wurin daddy! Munibbat ga mommy na!…”

Tsuru-tsuru nayi da idanu cikin rawar murya nace” Hajiya ina wuni! kun sauka lafiya?..”

Shiru tayi tana so ta tuna fuska ta amma abun ya gagara, siririn tsaki tayi kana tace” lafiya kalau! ya akayi kika san zata dawo yau? dama kin taɓa zuwa nan ne?..”

Ciki na ya ƙulle, zufa ta shiga karyo min har ga Allah tsoron matar nan nake kamar me!!..

” Mommy!!!..” cewar Nafisat cike da shagwaɓa…

Kallon tayi da alamar tambaya kana tace” Munibbat ko? Ƴar waye ke, ma’ana waye baban ki?…”

” Mommy! marainiya ce fa! a hannun Kawun  ta taso!..” Nafisat ta faɗa gudun kar a wulaƙanta mata ƙawa…

” Shi Kawun nata waye shi to?…”

” Mommy! pls!!!, Munibbat kinga wannan shine BIG MAN din mu! kinyi mamaki ko ? Malam Haidar yaya na ne! sai Ya ANUWAR! dama duk sun san da zamaki ganin ki ne kawai basu taɓa ganin ki ba sai yau! Mommy ita fa ƴar wan Antyce!…”

Ta faɗa tana duban Mommy da ta kafe ta ido jin abinda tace, dariyar MAN muka ji cike da nishaɗi yace” Auta banda  shirme irin naki, ai mun santa mu ta jima a gidan nan sosai!…”

Na zuba mai ido ina duban sa soyayyar sa nayi min wani irin suka a zuciya, nayi murmushi nace” ni zan koma can Nafisat!..” cikin sanyi nayi maganar…

Cikin siririyar muryar sa fuskar nan a shagwaɓe yace” Mommy karya ne ba wani ƴar wanta mahaukaciyar nan ce fa!!…”

Dum gaba na ya faɗi, na daure ban tsaya ba har ‘na kai ƙofar fita naji muryar Mommy na cewa” kallon sani nake mata! amma wannan batayi kama da wace na bari ba…”

Man ya sauke wata nauyayiyar ajiyar zuciya kana yace” Mommy bari na shiga ciki!..”

Dai-dai fuskar ta ya sunkuyo kana ta sakar me kissing a goshi, haɗi da cewa” Allah yayi maka albarka babban mutun…”

<< Waye Zabin Munibat? 23Waye Zabin Munibat? 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×