Da sauri ta dubeni a yanzu a yanda nake mata maganar tabbas ta san zan iya abinda yafi wanda na faɗ’a domin cikin zafi nake mata maganar…
Har na fice a ɗakin bata ce komai ba, illa kura min ido da tai…
Kamar yanda yace lokacin tafiyar mu nayi Musa yazo muka ɗ’auki hanya gaba ɗ’aya mu mu shida, yara sai murna suke yau zasu ga Maman su tausayin su da na kai na ya kamani, shiru nayi ina ƙoƙarin mayar da ƙwalla ta…
Babban gida ne na zamani ba laifi ko baa faɗa ba dagani suna da arzikin su dai-dai gwar-gwado, muna tsayawa yara suka shiga ciki da gudu ko wanne yana ƙalawa Maman shi kira, jikina yayi sanyi na fito amma na tsaya ban motsa ba, hannu naji an kama na ɗ’ago da sauri Bishira ce ta sakar min murmushi haɗi da cewa” karki damu babu abinda zai faru ANTY!…”
Kamar wace ƙwai ya fashe min a ciki haka na ringa binta, a hankali mu na tafiya har muka shigo cikin gidan, a tsaya muka tarar da ANTY sai murna take tana d’aga yaran nata d’aya bayan d’aya tana saukewa…
Bishira ta tsareta da ido cikin kewar juna tsakanin ɗa da mahaifi, a hankali ta buɗe mata hannu aiko ta sakeni ta wuce wajen Mamanta a suƙwane, nima nima na samu irin wannan a wajen ta ko da sau ɗaya ne a rayuwa ta na ajiye tarihi, shine tunanin da zuciya ta tafi…
Gani ma kamar sun manta dani yasa na juya jikina a sanyaye….
*****
” Mama ANTY MUNIB ce ta kawo mu!..” cewar Bishar..
A hankali ta ɗago ta fuskar ta har yanzu akwai murmushi tace” tana ina yaushe ta dawo?..”
Har na kai kofar fita najiyo murya ANTY tace” MUNIBBAT!..”
Cak na tsaya ina me goge hawayen fuska ta, a hankali na juyo kai na a ƙasa, naƙi bari mu haɗa ido ta saki murmushi me sauti jikin ta yayi bala’in sanyi ganin yanda na sauya na ƙara kyau da zama cikakiyar mace, cikin sanyin murya tace” a karo na farko kenan a rayuwa ta kinyi min abinda bazan manta dashi ba, na gode sanyin idaniyar Kawun ta!..”
Da sauri na dube ta jin yau ANTY ke min godeya, na sake goge hawayen fuska ta da kyau, ina murmushin jin dadi…
Hannuna ta kama har cikin ɗakin ta, ba lefi akwai komai najin dadin rayuwa, sai nan-nan take damu yara kam ko wanne ya haye mata jiki, gaskiya uwa daban take a duniya…
Kayan da muka zo dashi ta aika wasu yara ƙanwa ta, suka shigo dasu bayan komai ya lafa maman su ta shigo muka gaisa, mu danyi hira da ita kaɗai a maganar tane na gane ANTY tayi sanyi irin sosai dinan, cikin maganar ta manya taka take bani haƙ’uri a fakaice, na gane me take nufi amma nayi kamar basan inda ta dosa ba, bayan fitar tane ANTY tace” MUNIBBA yaushe kika dawo?..”
Cikin biyayya yanda ta sanin dashi nace” jiya nazo, munyi hutu ne shine bangaki ba, dana tambayi Kawu yace min kinyi tafiya ne, shine muka zo na gaisheki…”
Dadi taji har cikin ranta, gani duk ukubar data gana min ban manta da ita ba, tace” za kuyi min ƙwana biyu ko?..”
Kallon ta nayi a yanzu sai ta bani tausayi, nace” amma bamu tambayi Kawu bs kina ganin bazaiyi faɗa ba?..”
” Kina tunanin a irin soyayyar da yake miki akwai abinda zakiyi a yanzu yayi miki faɗ’a, tunda nazo gida yarana basu sake kwana a inda nake ba dan Allah kice mai zaku ƙwana biyu!..?”
Wani irin dadi nee ya sake kamani jin yau ni ANTY take roƙa, na gaza boye jin dadi na da murmushi akan fuska ta nace” ba komai ANTY zan gaya mai!…”
” Yauwa, MUNIB ina fatan gidan da kike bakya samun wata matsala ko?..”
Take yanayi fuskata ya sauya zuwa damuwa, Ina shirin yin magana waya ta ɗauki ruri cikin sauri na ciro ta Mama nace! murmushi nayi game da tashi d’aga wurin ina komawa gefe domin ganawa da ita…
Nan ta bini da ido gani na fara waya, sai ta koma kan yaran ta da tambayar lafiyar su, ko wanne su karar ANTY Rabi yake kawo mata, d’aga wannan yace tayi masa kaza sai me cewa baiyi komai ba ta dake shi, kuma a gaban Abba…
Haka dai ranta ya ɓaci amma sai ta ɗaure tuna abinda tai ne ake ramawa akan nata yaran, danasani ya taru ya cushe mata zuciya, Bishira ta matso kusa da ita murya can kasa tace”” Mama ki nemin yafiyar to ko zamu sakewa a gidan mu, kin ma san yau ANTY tayi faɗ’a akan mu, tacewa matar baba dole ta bar mu mu sake a gidan ubanmu in ba hakaba kuma ta hana ta sakatt! Mama shiru tai bata iya bawa ANTY amsa ba..”
Ƙare mata kallo tai kana tace” d’aga yau kar na sake jin kinyiwa wasu laɓe ko kin dauko zance da baa tambayeki ba kin faɗawa wani, zan ɓata miki rai mutuƙa akan wannan halin da kika d’auko sabo!..” cikin faɗ’a tai mata maganar…
Jikin Bishira yayi sanyi ta koma gefe kamar munasira, tace” kiyi haƙuri Mama..”
Lokacin dana gama wayar ANTY ta bar wajen, dan haka na nemin gurbin zama hankali na akwance, sai kuma kewar Mama na da nakeji a kwana ɗ’aya kawai tana mita na dawo inaga nayi aure na bar gidan kuma, na saki murmushi me sauti…”
To kamar yanda nayi tsamani Kawu bai kirani ba haka kuma bai turo Musa ba, aiko muka baje abun mu a gida hankalin mu a kwance babu kyara bare hantara, gaskiya yanzu ANTY ta sauko domin har hira take dani in muka zauna a tare ko barci nake sai ta tasheni, ni wallahi tausayi take bani ganin yanda ta dawo salahar ƙarfi da yaji…”
A karshin zuciyar ANTY akwai soyayya ta sosai, ko a baya ɗannewa kawai take yanzu kuma lokaci yayi da ya kamata ta nuna min, ɗ’aki ɗ’aya muka ƙwana da ita a gado ɗaya mu uku, duk a takure nake domin ni yanzu na manta da rayuwar matsatsi, haka nayi haƙ’uri cikin dare Anty ta fahimci bana jin dadin ƙwanciya tashi tayi ta komai kasa duk ko da irin sanyi da ake…
“`Ruwa ake kamar da bakin ƙwarya gari ya ɗ’auki sanyi irin sosai dinnan, gani tayi na ƙwance a takure waje guda alamar sanyi nake ji, ranta ya ɓaci aiko ta d’auko ruwa ta sheƙ’a min a jikina d’aga ni har maƙwacin nawa muka jike jagwab, na miki a firgice Ina zazare ido _kiyi hak’uri ANTY_ shine abinda nace budar baki na duk da banyi mata lefin komai ba“`
Da sauri ta mike zaune tana sauke a jiyar zuciya haɗi da duban inda nake kwance a hankali ta miki zuwa gaba na, ganin yanda nake barci na a sake sai ta saki murmushi k’walla fal idanun ta tace” ki yafe mun marainiyar Allah? haƙiƙa na wutaƙantar dake na zalince ki, na wulaƙantaki a lokacin da kike buƙ’atar kulawa, na banzatar da rayuwar ki a lokacin da kika rasa wani gata na iyaye, sam ni ban cancaci yafiya a gareki ba domin ni kaɗai na san irin zalincin da nayi miki, duk wani abu da yake faru dani a rayuwa ta a yanzu alhaƙin ne MUNI, da banyi miki abinda nayi ba da har yanzu Ina nan zaune lafiya kalai da miji na bai kara aure ba, da ban zamo sanadin korarki a gidan ba da har yanzu nima igiyoyin aure basu girgiza ba, an rabani da yarana ta ƙarfin tsiya, bayan komai ina yine domin su sabida su samu gata a wajen uba wanda yafi naki na tsaneki, ina da kishi, ina da kishi marar amfani, bana jin dadin komai ni yanxu!…” Cikin shasheƙa kuka ta ida zancen…
Kukan ta da maganganu ta ne suka tashe ni, amma ba bude idona ba, sosai take kukan ladama tamkar ance mata na mutu, kwana tai a haka gashi naki bude ido na amma zuciya ta fal take da farin ciki da kuma taikaici na barin su da zan sakeyi a nan gaba, ban san yanda ta kasance ba barci barawo ya saceni, ta sakar mun kissing a kuncina lokacin da taji ana fara kira-kirayen sallahr asuba, tayi saurin ficewa a hankali nima na mike zaune baki na d’auke da addu’a, shafa wajen nayi ina murmushin dadi kamar ya kashe ni…
Ku san kullum sai ANTY tazo min cikin dare tana kuka da bani haƙk’uri akan abinda ya faru, a tunanin ta bana jin ta nan ko Ina jin duk wani abu da take cewa da zarar dare ya rabane nake barci abu na…
Satin mu ɗ’aya yau yawanci yan uwan ANTY duk mun gaisa dasu, a wayace suke bani hak’uri a cewar su k’addara ce, abinda na fahimta duk ANTY ce take aiko su ɗaya bayan ɗaya, nima amsa ta ɗayace a zamana da ita batayi min komai ba….
To dare nai muna ta shirin kwanciya barci sai ga kiran Kawu na, jikina a sanyaye na ɗ’auki wayar,
” Asalam alaikum..” shine abinda nace..
Amasawa yayi haɗi da cewa” ku fito mu wuce!..”
Da sauri na tashi zaune ina cewa” ina Kawu?..”
ANTY ma ta mike zaune tana duba na, ” ba tambaya nace ki tsaya yi min ba fito waje yanzu..” yana gama faɗar haka ya kashe wayar sa…
Ajiye wayar nai haɗi da mikewa tsaye, ANTY tayi saurin cewa” ya akayi ne MUNI?..”
” Kawu ne yace muzo mu wuce yanzu, amma yace yana waje inaga da kan shi yazo!..”
Da sauri ta mike fuskar ta sake fadaɗa farar ta ciken tsananin nishaɗi tace” da gaske? Shafi’u ne yazo kofar gidan mu yau?..” ai bama ta bari na bata amsa ba ta fice abin ta, tausayi ta bani jima na shirya a gagauce na fice..
A zaure na tarar da ita sai leƙe take ta makafar get din su, har zan wuce tayi saurin dawo dani baya murya kasa kasa tace” please MUNI kice ya fito waje kinji?..”
Da kai na amsa mata na fice, d’aga waje na tsaya haɗi da turo baki gaba alamar nayi fushi, dariya yayi shima kana ya fito gaba d’aya yana kallo na yace” to ya akayi ne yarinyar Kawu? waya taɓa min ke ?..”
” Bayan bakayi missing dinna ba, tunda na tafi baka kirani ba ko sau ɗ’aya!..” cikin shagwaɓ’a nake maganar kuma abin yayi masifar yi min kyau..
Dariya yayi yace” wato ke da lefi shine zaki wani waske ko? to na ganoki gajiya nayi da fushin tunda naga ke bashi san zuruba nace bari nazo da kai na, Ina kannan naki na ganki ke kadai?…”
Kuka na saki cikin sangarata nace” mu bazamu koma ko ina ba sai da tare da ANTY na!…”
A yanzu kam da sauri ya dubeni, yana sake ware idanun sa akai na yace” ohh abinda aka kitsa miki kenan ko?..”
Shiru nayi banyi magana ba sai kuka da nake, gani bilhaki kuka nake ya rage muryar sa cikin rarashi yace” kiyi shiru to! ANTYnki ta aiko ki ko? itama tace miki tana son dawowa ne?..”
” A’a ni nake so ta dawo Kawu, wannan ANTY Rabi ta cika faɗa ga saurin hannu, duk su Bishira basa sakewa sabida ita, Kawu na! bazan so ƙanena suyi irin rayuwar da nayi a baya ba, Ina san su sosai Ina jin su har cikin raina, mahaifiyar su itace farin cikin su nutsuwar su da walwalar su, ko da ace ni bazanyi farin ciki ba su Ina buƙ’atar ƙaunar su, dan Allah Kawu kayi magana adai na ta kura musu, nima inda nake babu wanda yake takura mun, na sake a can tamkar gidan mu ai ka gani Kawu, suma dan Allah ka kwatar musu ƴancin su, na san kanayi komai domina ne to indai nice na yafe mata duniya da lahira, na San zakayi mamaki ya akayi na san bakwa tare da ANTY, fahima tayi Kawu dan girman Allah ka dawo da ita?…” Cikin kuka nayi maganar ina zubewa akan gwiwoyina…
Runtsi idanun sa yayi har cikin zuciyar sa yaji dadin yanda na nunawa yara sa kulawa, ko ba komai shima zai dawo da sahibar sa ne ai bazaiƙi wannan tayin nawa ba, a hankali ya kamo ni zuwa jikin sa yace” kiyi shiru yarinyar kirki, indai haka yayi miki to kije na wakiltaki kiyo mun bikon ta!…”
Dadi ne ya kamani ina murmushin Ina komai nace” na gode na gode Allah yasaka a aljanan fiddusi I love you so much Abbanmu!…”
Kud’i ya bani masu yawan gaske mu kayi sallama ya wuce ni kuma na dawo ciki, banga ANTY a zaure ba sai ban kawo komai a raina ba na wuce d’akin mu, zuciya ta fal farin ciki….