Skip to content
Part 3 of 10 in the Series Waye Zabin Munibat? by Husaina B. Abubakar

Bismillahir Rahmanir Rahim.

MUNIBBAT yarinya ce k’waye d’aya tak da iyayen ta suka mallaka a duniya, mahaifiyar ta me sunan Rabi’atu macece me hak’uri da juriya,  bama su kud’i bane suna  da rufin asirin su dai-dai gwargwad’o, basu rasa cin yau basu rasa sutura ba, domin malan Dahiru yana da sana’ar sa kuma Alhamdulillahi yana samu sosai, kayan miya yake siyar wa a cikin kasuwar  gwarawa, dake cikin hayin rigasa,

yarinya ta taso cikin kulawar uwa da uba, ta samu ingantaciyar tarbiya ta ‘bangaren biyu, tun tana k’arama iyayen mahafin ta suka rasu, sshi kad’ai ne dasu, bashi da wa bare k’anni haka ne yasa ya mayar da duk wata kulawar sa ga matar sa wace ita ma tun tana k’arama Allah ya amshi ran iyayen ta, bata da kowa sai Yayan ta na miji, yana bata kula sosai duk da sunyi ma juna nisa yakan ziyartar ta lokaci bayan lokaci tare da matar sa me sunan SHAFA’ATU, wace Mama na, ke kiran ta da ANTY kasancewar ta matar Yayan ta amma ba wai dan ta girme mata ba.

Tun ina k’arama ta Allah ya d’ura min k’aunar karatu, Allahmdulillahi ina shekara goma cif-cif na sauke alkur’ani me girma, inda Baba na ya taka rawar gani wajen yi min walima dai-dai k’arfin sa, kawu na yazo da matar sa shi ma yayi k’ok’ari domin dinki yayi min har kala biyu, matar sa kuma ta siyo min takalmin me kyan gaske, Anty tana bala’in sona sosai ta kan nuna min k’auna a gaban iyaye na musamma gaban k’awu na, kwanan su biyu suka koma.

Nan na mayar da hankali na akan karatuna na boko da had’ar alkur’ani da muke yanzu a makaran ta , iyayen na suna alfahari dani sosai  shi yasa duk abinda suka samu MUNIBBAT duk da k’arancin shekaru na wani lokaci har tausayi suke bani, ina da shekara goma sha uku cif-cif, Anty ta haihu ta samu ‘yar budurwa, gaba d’ayan mu muje sunan ta kano, inda tun kallon farko na k’walla rai akan yarinyar ranar sunan  aka rad’a mata SUNA BISHIRA abin gwani ban sha’awa, washe gari SUNA muka dawo garin mu kaduna zuciya ta cike da soyayyar Bishira.

*****

Shekara ta goma sha shida yanzu na san koma na san yanda rayuwa take tafiya, na iya duk wani aikin gida kuma haka bai hanani karatuna ba, ina da k’ok’ari a makaranta  a yanzu ina JS3 abu na, hata malaman makarantar suna alfahari dani gaskiya, a lokacin ne ANTY ta sake haihuwa inda ta samu d’a miji murna a wajen iyaye na ba’a cewa komai, lokacin Bishira tana da shekara shida a duniya, har anyi mata k’anwa me suna fiddusi, yanzu kuma ga yaro an sake samu, gaskiya iyaye na suna k’aunar k’awu na da matar sa sosai su kayi musu siyayya ta ban mamaki zuciyoyin su cike da murana a suna saura k’wana biyu da yake ranar alhamisi ta haihu muka d’auki hanya muka tafi, dama mun samu hutu a makaranta.

Anty tayi muryar ganin mu har da kuka lokacin da su Mama na ta bata abinda mu kazo dashi, washe garin suna kamar yanda aka sab’a muka tashi tafiya.

*****

Tunda gari Allah ya waye Anty ke had’e rai, ko yan uwan ta sun kasa gane kan ta bare kuma mu haka bai hana mu fasa shirin mu ba, k’awu ne zaune a gaban Mamana cikin nuna kulawa gare ta, yace ” wai ni kam dole ne sai kin tafi a yau ne?”

Cikin murmushin da bai rabuwa da fuskar tace” to kafi so na zauna a nan na bar mijina a can shi kad’ai a gida..?” ita ma ta fad’a cikin zolaya.

Murmushi yayi yace” a’a ni na isa! kawai haka nan naji bana son tafiyar taki ne me zai hana ki bari zuwa gobe, in yaso sai mu wuce tare tunda duk hanya d’aya ce.”

Cikin girmamawa tace” gaskiya bana jin tafiyar mu za tazo d’aya domin nayi wa malam alk’awari washe garin suna zamu dawo, in yaji shiru ran shi bazai ba mai dadi ba, a yau zan wuce gaskiya…” ta fad’a cike da damuwa.

“To shikenan Allah yasa haka ne mafi alhairi, sannan ina neman wata alfarma a wajenki, tunda naga yanzu anyi hutun makaranta me zai hana ki bar min Mama na tana taya Anty ta aiki, in hutu ya ‘kare sai na dawo miki da ita?” ya fad’a yana duban ta.

Shiru tayi na wani lokaci sai zuwa can tace” gashi kuma ban fad’a wa malam ba, amma ba damuwa in na koma zan man bayani tunda na san bai da damuwa, amma ita Anty ta amince?”

“Eh ita tazo min da batun ma ai, dah na nuna mata k’in amincewa ta akan mahaifin yarinyar bai sani ba shine take fushi tun asuba.”

Murmushi k’arfi hali Mama na tayi kana tace” ba damuwa to Allah ya taimaka…” nan ta fito min da kaya na, ta jiye a gefe, cikin kula ta dube ni tace” zo nan yarinyar kirki… lokacin k’awu ya fita.

A jikin ta na k’wanta, ta b’ata lokaci sosai akai na tana min nasiha da nuna min yanda ribar hak’uri take, tamkar me min bankwana, ta kuma umarce ni dana k’asance me biyayya ga Anty na da kawu na dan bani da tamkar su in basa raye, har kuka ta sakani a irin maganganu ta, naji zafi sosai na rubuwa da uwa ta domin wannan shine k’aro na farko dana tab’a barin ta a rayuwa ta.

Da kuka muka rabu da ita inda k’awu na yake aikin rarashi na.

Bayan k’wana biyu da tafiyar Mama na, nan na fara gane ko wacece Anty macece da sam bata zaman gida, ta cika yawo sosai, duk wani aikin gidan ni nake yin sa, haka zata falle ta bar min yaro me shan nono, yayi ta tsala min kuka wani lokaci nima zama nake yana kuka  inayi, Bishira na gefe na tana taya mu, ga uban aiki.

Wahala kuwa ta sani nayi rama a cikin sati biyu kawai, gashi nayi duhu bana samun kulawa sam, to ta ya zan samu kulawa matar da gari na waye wa take ficewa, kamar wace k’afar ta ke mata k’yak’ayi,  na matsu hutun mu ya k’are na koma garin mu.. a cikin haka ne muka had’u da Aysha yarinya ce me hankali da nutsuwa gata kyakykyawan da ita, sannu a hankali muka saba zata zo gidan mu ta jima zan je gidan su wani lokaci na kwashe yaran mu tafi tare wani lokaci nima na barsu a gida.

Sati uku cif-cif k’awu ya dawo, ya sha mamaki lokacin da ya gani na dawo abar tausayi, nan ya shiga tambaya ta abinda ke damuwa da yake ni din a kwai zurfin ciki, haka nace ba komai ni gida nake son komawa, ya sakani a gaba da rarashi amma fur nak’i nace ni ina gida zan koma,  sam Anty bata ji dadi ba amma ta d’aure a gaban sa tai ta nuna min tatali da so, duk inda zatayi a cikin gidan dani take zuwa kamar wata wawuya.

Satin shi d’aya da dawowa, nayi kyau abu na, domin ya nuna min kulawa fiya da y’ay’an cikin sa,  ko k’ofar gida zaije tare dani yake fita ko k’unya bayaji gansamemeya dani, yanzu tunda yana nan bana aikin komai ita ma bata zuwa ko ina muna tare da ita a gida, abinda na fuskata da ita shine muddin d’aga ni sai ita a gidan to fa babu wannan walwalar bare kulawa, tsakani da ita sai tsawa da hantara, ga sani aiki jefi-jefi, ko me nake da taji sallamar sa  yanzu nan zan ganta a kai na tana min fad’a wai bana jin  magana tace na barshi nak’i.

Shiko hakan yana mai dadi sosai a ran shi, ina lisafe da hutuna ya kusa k’arewa, shima gobe zai koma wajen aikin sa, cikin soyayya da mutunwa na same shi, a cikin nutsuwa nayi mai bayani komai, shima cikin jin dadi ya amince min akan dama yana niyayya gobe zan koma gida, nayi murna sosai a gaban sa ba tare dana bar wajen ba, rawa nake ina fad’i” shikenan zan huta da wahala, zan koma gida mu na ga Baba na da Mama na wayoo dadi dadi!”

A haka na fice a d’akin na barshi a zaune yana min dariya, domin shi bai d’auki abinda na fad’a da mahinmaci ba.

A ranar naje mu kayi sallama da Aysha da Maman ta, zuciyata kar farin ciki, zan koma gidan mu a cikin gidan nan kuwa babu wanda nake tunani zanyi kewarsa kamar k’awu na.

Lokacin da Anty taji zan koma gida dan munafinci har da kuka, wai za’a d’auke mata me taimaka mata, Bishara yarinyar ce k’arama bata iya komai ba, ni wallahi haushi ma ta bani Aiko a gaban idanun ta na tura baki gaba nace” ni gaskiya gidan mu zan koma..”  Tun daga lokacin bata sake magana ba.

Washe gari muka d’auki hany’a sai gani a kaduna, zuciya ta fass da ita na gaji da zaman mota sai nake gani kamar baza mu kai gida ba, k’awu na lura dani sai ya danganta hakan da jimawar danayi banga iyayen nawa ba.

Na dawo na cigaba da karatu na, cikin amincin Allah da kulawar iyaye na, b’angaren d’aya kuma Anty ta damu k’awu akan ya d’auko ni na ci gaba da zama da ita.

Haka rayuwar mu ta cigaba da lafiya cikin amincin Allah, in muka samu hutu k’awu yazo tafiya dani sai na saka mai kuka akan ni ba inda zani, dole ya ha’kura bai sake zuwa da niyar tafiya dani ba.

Bayan shekara guda lokacin na shiga shekara sha bakwai, na san koma girma yazo min ina da samari sosai amma ni ba su ne a gaba na ba, burina nayi karatu na zama wata ko dan na taimaki iyaye na, a hankali   Mama na ta fara wani irin ciwo me wuyar sa’ani, mun sha sintirin zuwa asibiti, ba’a gani komai kawai ciwo ne d’aga Allah, abu ya zame min biyu ga kula da gida da karatuna haka na dage ina k’ok’ari sosai, Mama na, tana iya komai da ya shafe ta amma na hana ta aikin komai a gida.

*****

Dawo ta kenan d’aga makaranta, ina cire hijabi na  fara tashin Mama na dake kwance a k’asa tana barci, cikin zak’uwa nace” Mama na tafi ta kowa, barci ne kuma  ba’a hau kan gado ba aka kwanta a k’asa? ki tashi kinji sakamakona na san zayi farin ciki sosai.”

Na i’da maganar ina tab’a ta, shiru bata motsi ba, na sake magana shiru, sai na sake tab’a ta nan ma shiru, take wani tsoro ya tsarga min, a hankali na kai hannu na kirjin ta, shiru babu numfashi, a haukace na juyo da ita sai naga gaba d’aya tayo jikina shak’wof, Innalillahi na furta a rud’e A hankali cikin wani yanayi nace” Mama na!”  gani na k’asa gane abinda ya hanata motsawa kawai sai na fice da gudu, mak’otan mu na shiga  hankali a tashe, da taimakon dattijuwar gidan muka dawo d’akin, yanda na barta tana nan a wajen, duba tayi da kyau sannan ta jayo zanin dake rataye a kan kyaure ta rufe ta, had’i da fad’in ” Allah ya jikan ji Rabi’atu, Allah yasa kin huta.”

Tun daga lokacin ban sake sani abinda ya faru ba na d’auke.

Like, comment and share.

Mrs Abubakar ce

<< Waye Zabin Munibat? 2Waye Zabin Munibat? 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×