Abinda na fahimta yanzu ANTY bata cika zama muyi hira tare da ita ba, ko da yaushe tana d’akin ta, maganar komawar ta gidan Kawu na, ban gaya mata yanda mukayi dashi ba amma maman ta ta san komai itace ta hanani gaya mata, shirye-shirye muke tayi a tsakanin mu tamkar za’ayi bikin wata budurwa, kullum mune yawan cin kasuwa…
B’angare MAN kuwa ya shiga damuwa sosai rashi na a tare dasu, haka ma Mama na kullum sune kirana a waya sai mu bata lokaci muna abu d’aya dasu, abun mamaki wai har Dady cewa yake na dawo gida sunyi kewa ta, in muna waya dasu na kan shiga nishadi sosai babu wanda bana tambayar lafiyar sa a cikin a halin su, wannan karamamci nawa yake sake d’aga darajata a idanun kowa na gidan su MAN, kamar yanda muka saba yau ma waya muke dasu da yake a amsakowa suke sakani kowa yaji abinda zan fad’i, Mommy na zaune cikin izzar ta da isar ta gaba d’aya haushin su take ji ganin yanda suka wani zagaye waya guda kamar wata jinin su…
Bayan mun gaisa da kowa nayi kasa da murya cikin yanayin tausayi nace” please my family ku gaida mun da Mommy sosai dan Allah, ina me sake bata hak’uri a karo na babu adadi, tabbas ni me lefice a gareta na amince da wannan amma dan Allah ta amsheni a matsayin ya ko da na rana d’aya ne a rayuwa ta, ina buk’atar kulawar ta itama Ina so naga tana min murmushi tamkar yanda take ma Auta! dan Allah ku tayani bata hak’uri!…”
Shiru! wajen ya dauka sai numfashin su dake tashi a hankali, ko wa kallon Mommy yake ganin me za tace a hankali ta mike tamkar zata aikata wani abu, har inda suke tazo wayar ta dauka tana kallon kowa daya d’aya kana ta kashe wayar gaba d’aya cikin bacin rai tace” har abada bazata zamo wani shashi na cikin zuri’ata ba, ko muryar ta bana son jin bare kallon fuskar ta, amma da yake doluwace murmushi na take buk’ata, aikin banza!!!..” ta saki wayar a k’asa tayi gaba abinta…
Babu wanda ya tanka mata har ta fice a falon, takaici yasa Dady lumshe idanun sa…
Nikam jin an kashe wayar ban kawo komai a raina ba, na mike duk da zuciya bata min dadi tunanin d’aya ya za’ayi yanzu Mommy ta soni ita kadaice ta rage min a yanzu!..
Washe gari MAN ya matsa min da waya dole ta sa nayi masa kwatancen inda nake yazo, abun mamaki shima har da kayan sa wai sai ranar da zan koma shima zai tafi, ANTY ta amshe shi hannu bibiyu tunda zuwa yanzu ta san matsayin da yake dashi a wajena…
Muna shirin komawar ANTY ga soyayya muna zuwa ba tamkar bazaa mutu ba, gaskiya MAN dan soyayya ne na k’arshe, nima baa barni a baya ba wajan nuna mai k’auna soyayya ce me tsafata da daraja juna…
Cikin sati biyu akayi komai aka gama, matan Kawu sunyi mutu’kar mamaki ganin dawowar ANTY ko wace ta shiga taitayin ta, Kawu na ya dawo tamkar wani basarake ko wace na nuna mai iyakar k’aunar sun shagwab’a min Kawu na sosai, duk da haka yana bamu lokaci nida MAN dinna da muka zama tamkar tagwayen juna, yanzu har kaya iri d’aya muke sakawa abun gwanin ban sha’awa…
Duk wani iskaci da shashanci sai da ANTY RABI ta sauke shi, shima ta sanadiya ta domin sai da na matsa mata iya matsawa, ya zamana itace take shakar fitowa bamu ba, Kawu na ya goya min baya dari bisa dari…
Zaune nake a gaba ANTY kamar yanda ta buk’ata cikin biyayya nace” ANTY gani!..”
Kallo tai idanun ta cike da k’walla tace” ban san ta yanda zaki amshi magana ta ba Muni tabbas na zalinceki, na cutar dake sosai amma a yanzu zuciya ta cike take tsantsar ladama danasani, akwai wata alfarma danake nema guda d’aya a wajenki duk na san abune me mutu’kar wahala na sameta…”
Ta zame kasa bisa gwiwoyin ta cikin zubar da hawaya tace” sautari Kawunki yana min hangan wannan ranar, amma tushewar basira yasa na kasa fahimtar abinda yake nufi, DAN ALLAH DAN ANNABIN RAHAM, IN KINAYI WA IYAYENKI DAN GIRMAN ZATTI MUNIBBAT KI YAFE MIN DAN GIRMAN ALLAH!?…” cikin kuka sosai take maganar..
Mamaki da alajab’i ya hanani magana ba abinda nake face zazare ido Ina kallon ikon Allah, kukan da take har cikin raina nake jin sa, nima wata k’walla me zafi tazo bu min koba komai ANTY ta ri’keni kuma tayi min gata ta wani bangaren, a yanzu bana ganin lefin ta sam…
Gani har yanzu bance komai ba yasa ANTY mikewa tsaye cikin kuka tace” ni dama na sani abune me wuya kiyi yafe min abinda na aikata miki, amma ki sani zuciya ta bazata taba samun salama ba har sai ranar da kikace kin yafe mata, bazan sake farin ciki ba har sai ranar da kika shirya amsa ta a matsayin uwa MUNI, kiyi hak’uri na saki tuno abinda ya wuce!..”
Tana rufe bakin ta tai waje da sauri, ni gaba daya tausayin ta ne ya hanani magana ba wai wani abu ba, ina ji ina gani har ta fice ban iya tsayar da ita ba…
Bishira ta karasa shigowa d’akin itama tana kuka tace” ANTY MUNI tabbas mamana ta aikata miki babban lefi wanda zaiyi wuya ki iya mantawa dashi cikin sauki, tun kan nayi wayo na fahimci wacece ke a cikin gidan mu, amma hakan bai sa na rainaki ba nima ina me rokar wa mahaifiyar mu alfharma d’aya Dan Allah kiyi hak’uri ki yafe mata ko muma ma samu kwanciyar hankali da nutsuwa a gidan nan, hakin kine yake shafar mu ANTY dan Allah ki yafe mata ba dan halin mu?…
Nima cikin muryar kuka nace” me yasa kuke rokona ne? ban tab’a ganin abinda ANTY take min ba a matsayin mugun abu, har kullum ina gani tamkar gyara take min a rayuwa ta, ta sanadin ta na samu mahafiya ta, niko me zance mata da ya wuce Allah ya biya ta, ban tab’a rike ANTY a zuciya ta ba dai-dai da rana d’aya, kullum burina shine nima naga tana kula dani tamkar yanda take muku, Alhamdulillahi na samu cikar burina a wajen ta, me kuma tai min yanzu? sam ni ban riketa a zuciya ta ba…”
” Duk mun fahimci haka ANTY burinmu a yanzu shine ki furta da bakin ki!..”
” Furtawa ta kawai kuke da bukata?..”
” Eh!..”
Tunda mukayi haka da ANTY ta shige daki, shiru taki fitowa gashi yamma har ta doso kai, ko abinci safe bata ciba wanda na ajiye mata ma yana wajen baa taba shi ba, na shiga damuwa sosai amma sai na d’aure na dauka ko barci take, ranar girkin ta ne mu mukayi komai har Kawu na ya dawo ANTY bata fito ba, babu irin bugun da baayi mata ba amma shiru babu amsa, tuni cikin mu ya gama kulewa tun Kawu na d’aukar abin wasa har yazo ya zarce tunanin sa, duk wata dabara anayi amma shiru Anty taki bude k’ofar room din ta, a ranar kowa haka ya kwana da tararabi a zuciyar sa amma shiru babu alamar zata bude sabida tashin hankali gaba d’aya a falon muka kwana, cikin dare kuwa muka daura da buga kofar ko Allah zaisa ta bude MAN ne yayi mana k’ok’ari wajen kirana masu irin wannan harkar aka zo aka bude k’ofar, sama bata cikin dakin mamaki da alajab’i ya kama jama’a da dama, kowa yana jimammi kamar ance na tura bayin ta, Ina turawa naji kofar tarike gam na sake turawa da k’arfi a hankali ta bude amma mutun bazai iya shiga ba, MAN ne ya taimaka min har muka bude gaba d’aya kwance take a wajen cikin mutu’kar galabaita fuskar ta ya yamushe, da dukan alama cikin ruwa ta shiga domin gashi nan jikin ta ya nuna hakan, na makyale a waje daya cikin azabar razana idanuna a waje…
Kawu ya matso da sauri ganin yanda muke mane a jikin bango dan tsoro, bai ce mana kalla ba illa daukar matarsa da yayi ya fice a bayin, sai a lokacin na sauke ajiyar zuciya game da firta “” ANTY!…” Hankalina a tashe…
Kafar ta ya shiga murzawa a gagauce, ganin abinda yake nima na kama hannun ta ina hawaye ina murzawa, Bishira ta rik’e d’aya hannun inda fiddusi ta kama k’afa daya, dan danan hannuwan mu suka dauke zafi, bango ne kwato MAN ya dauko ya shinfida mata shi a jikin ta, gaba d’aya waje muka fito Kawu ya cire mata kayan dake jikin ta ya saka mata wani masu nauyin, kafin mu shiga doctor yazo tare da kayan aikin sa, d’aga shi sai Kawu a d’aki aka bari basu dauki lokaci me tsaho ba doctor ya fito ya wuce abin sa, zaune muka tarar da Kawu ya daura hannu a kan ga ANTY dake kwance a gefe tamkar mataciya, cikin sauri na Isa gaban shi har rigi rigin tambayar sa muke ” ABBA me doctor yace!.??…”
Yana dagowa na hangin wasu hawaye masu mutu’kar gigita tunani na shirin zubo mai, nayi saurin yin kasa da kaina gaba na yana tsanenta fad’uwa, a hankali ya mik’e game da cewa” a yanzu addu’ar ku take buk’ata ba kuka ba yarana!…” Gaba d’aya kallon shi muke cikin hautsinewar tunani…
Wani irin zullo nayi na faɗ’a kanta cikin wani bahagon kuka, ina jijiga ta nake cewa” me yasa? me yasa zakiyi min haka? a lokacin da nake buƙ’atar ki a lokacin dazaki gudu ki barni! ya kike so nayi da raina ne ANTY? dan ALLAH ki tashi karki tafi ki barni dan ALLAH!…” Gaba ɗ’aya na dawo abar tausayi, kuka nake kamar zuciya ta zata fito a kirjina…
Bishira ta sunkuyo fuskarta jiƙe da hawaye cikin muryar kuka tace” menene lefin da tai miki haka MUNIBBAT da kika kasa furta mata kalmar yafiya? kukan me kike yanzu ? kamata yayi kiyi farin ciki tunda burinki ya cika, kece matun na ƙarshe wanda Mama tai magana da ita kafin ta samu kanta a cikin wannan halin, bakin cikin ki ne ya kashe min Mama na, bazan taɓ’a daina ganin ki da wannan tabon ba, a yanzu matsayin ki darajarki kimarki….”
Maganganu zafi suke min tamkar wace take watsa min tafashashen ruwa, cikin zafin nama da ƙwarin gwiwa na zafga mata mari idanuna cike da hawaye ina nuna ta da yatsana manuniya nace” kul dinki Bishira! karki ƙusƙura ki ɗaura min lefin kisan kai! ki bar ganin ba ita ce ta haifeni ba, amma a matsayin mahafiya na ɗauke ta, ke haifarki kawai tai amma nakifi ki jinta a raina! kina tunanin wannan daliline zai sa ta kashe kanta? kin ɗauka ni kaɗai ce damuwar ta? in kika sake buɗe bakin ki a kai na da nufin faɗar kalma marar dadi zan saɓa miki wallahi!…” cikin izza nayi mata woning…
Shiru tai dafe da kunci tana kuka, Kawu ya matso a hankali yana duba kana yace” da gaske ta neme yafiyar ki kafin faruwar lamarin?..”
Ba tare da nayi tunanin komai nace” Eh! Amma bata tsaya taji abinda zan faɗa na ta wuce ɗ’aki..”
Kan ANTY na koma na ci gaba da kuka na ina rarashin ta, cikin kuka na kwanta a bisa kirjin ta a hankali nace” innalillahi ANTY yanzu a kai na dama zaki iya kashe kan ki? tun ba yanzu ba na jima da yafe miki ANTY, tun dana bar gidan nake miki addu’a har kama I yanxu, ban taɓ’a ganin lefinki ba ANTY na sake yafeki miki tun a gidan ku da kike zuwa min cikin dare kina kuka, na sake yafe miki a karo na uku lokacin da kika rungume ni a kirjin ki da zan faɗi a shashin ANTY Rabi, to me kuma kika sake nema ANTY? inda domin na furta miki ne kinaji na to ki saurareni ANTY *na yafe miki na yafe miki duniya da lahira, na yafe miki har ƙarshen rayuwa ta* dan Allah ki tashi ki cireni a zargin da ake shirin jefani….”
Kawu na ya dafani cike da damuwa yace” wa ya gaya miki ANTYnki ta mutu ne MUNIBBAT?…”
Soror nai Ina kallon shi baki na a bude, nace” kana nufin tana jina?..”
” Eh amma a halin da take ciki bazata iya magana ba sai nan da awa hudu, yayi mata allure ne sanadiyar bugawa tai a kai shine yayi silar faɗawar ta ruwa, gashi jikin ta babu ƙwari na rashi. abinci da bata ci ba kwana biyu, a yanzu tana buƙ’atar hutu!…”
Dariya nake me haɗe da kuka, na sake kallon ANTY sai yanzu naga alamar numfashin ta amma kadan-kadan! Nace” Kawu mu tafi asibiti mana d’aga gani tana jin jiki!..”
Murmushi kawai yayi ya wuce abin sa, Bisha ta dubeni da nufin nayi mata murmushi aiko na haɗe fuska tammau, jikin ta a sanyaye ta fice a d’akin…
MAN ya sakani a gaba da tsokana, tun abun na bani haushi na ya fara bani dariya, kamar ba jinya na zauna ba sai gamu muna ta guje-guje a cikin ɗakin har tsallake ANTY nake ina dariya, shima haka!…
Gaba ɗaya zuciyar ta ajagule take, cikin takaici tace” yanzu dan Allah honey bani da iko akan yarana bisabilillahi yaron nan da lalacewa tunda ya tafi har yanzu yaki dawowa, kamar wanda yaje dangin uwar sa ni dan Allah ka kyaleni naje har gidan na ci mai mutunci tunda bai da hankali…”
Kare mata kallo yayi cike da jin zafin ta yace” Amina zo nan!…” d’aga yanayin da yayi magana ta san abune me mahimmaci cikin dauriya ta zauna kusa dashi haɗi da cewa” gani!…”
” Iya zamana dake ban taɓ’a tunanin zaki sauya halinki gaba ɗ’aya cikin ƙanƙanin lokaci irin haka ba, tunani na ko da ace babu aure tsakani na dake to zan iya tsawatar miki kibi zan kuma iya saka doka shima dole kibi, mahaifiya ta tamkar mahaifiya take a wajen ki tunda yayar mahaifiyarki ce, amma ba tun yanzu na fahimci matsayin da kika ajiye mu ba, sanin kanki ne bana ɗaukar rashin nutsuwa a rayuwa ta wallahi tallahi badan ke din kece ba, da wata matar ce daban da bamu kai wanna matakin da ita ba, koni ban sa kin bar gidan nan ba Hajiya da kanta zata saki ki bar shi, Amina na roƙeki a karo na farko ki riƙe mutuncinki da darajarki a idanun surukarki, karki bari ta rainaki tun kafin ta auri ɗ’an naki da kike ikirari, ko da ace MAN bai aure yarinyar nan ba to wallahi ke zaa bari da jinya domin a yanda yake mata tsananin soyayyar tsaf zaki rasa shi, kinga kin tashi biyu babu kiyi haƙ’uri ki rugume auren nan da zuciya ɗaya insha Allah nan gaba zaki ga alfanun hakan, kin sa yanzu Hajiya nayi miki wani kallo na daban, kin ɗauki muguwar ɗ’abi’a kin daurawa kanki wahala, badan Hajiya ba da tunin kin manta kin taɓa auren miji me suna Abdulazizi a rayuwarki, shin baki mamakin yanda nake zuba miki ido kike duk abinda kika ga dama? , duk Hajiya ce take hanani tsawatar miki a cewar ta ke marainiyace bazaa ta kuraki ba kina buƙ’atar rarashi, kin san dalilin ya da sa take son MUNIB din? duk dan sabida ita ma marainiyace kamar ke tana so kema ki iya tausayin na kasa dake ko da baki taba ganin shi ba, burinta shine ki dae na kyamar talaka da talaucin kanshi, amma kin kasa ganewa ina jiye miki ranar da talakan da kike rainawa wata rana shi zaki roka taimako, ko ya taimake ki Amina ki shiga hankalinki tun kafin ayi auren nan domin nan da sati biyar za’ayi komai a gama, in kinga dama ki amshe ta in kinga dama a ranar da aka kawota ki kashe ta!…” Mikewa yayi ko a jikin sa ya wuce ciki abin sa.
Mommy Kam kuka take bilhaƙi da gaskiya, domin taji zafin maganar sa sosai, yanzu duk yanda Hajiya take nuna mata ashe ba iyawa zatayi ba, tabbas tafi kowa sanin Hajiya tana sonta sosai amma me yasa itama bazaa duba nata uzirin ba, ko bai faɗa ba inta matsa gefe tana jijina yanda yake jure rashin ɗaa’ar da take zubawa, Ashe Hajiyar mu ke takamai birki, to yanzu ta Ina zata fara gyara ƙuskƙure ta mijinta me sonta da ƙ’aunar ta yau shine yake gaya mata da tuni ta manta ta taɓ’a auren sa, aiko ta sake fashewa da kuka me mutuƙar cin rai, tunawa tai ai yanzu yana gani ba ita kadai bace dashi dole ne ya faɗi duk abinda ke bakin sa ai, wani kishi yazo ya sake tare mata makoshi, gashi bata jin zata so MUNIB a rayuwar ta ko kad’ai yarinyar ce kawai batai mata ba, gashi yanzu kamar kan yaranta ya fara rabuwa, tunawa tai a baya yanda suke rayuwar gwanin birgewa, ta lumshe idanun ta a baiyyyane tace” zan amince ayi auren shikenan hankalin kowa sai ya kwanta, amma hmmm zata gane bata da wayo…”
Kamar yanda ta niyyata haka ce ta kasance, tana iyakar ƙ’oƙ’arin ta na ganin ta gyara zamantake war ta da kowa, a yanzu ba tayiwa Daddah musu ko gardama musamma akan maganar auren mu, duk abinda zasuce haka nee kawai take binsu dashi, har cikin zuciyar Daddah taji dadi yanda ƴar tata sauya hata Mommy din ta fahimci haka, Hajiya Nusaiba ma ta fahimci sauyarwa Mommy, Dady yaji dadi yanda ta ɗauki maganar sa ba tare da wata fitina ba, bai gaya kowa ba sai ganin tai anzo an ƙwashe kayan ɗakin ta tsaf an zuba mata sababi masu tsadar gaske, duk wanda yake gidan shima sai da d’akin sa ya sha gyara, jin dadin sa kawai Mommy ta shiryu shine yake wannan bishashar, Mommy kuwa a tunanin ta anyi mata ne domin hidimar biki…
Alhamdulillahi jikin ANTY ya warware sosai, abinda ke damunta yanzu kuwa ya rage tsakanin ta da mijinta, domin ni kusan kullum sai tace na yafe mata kamar wata k’aramar yarinya, wani lokaci har dariya take bani, soyayyar mu ke zuwa a gaba kowa yanzu nakan furta mai Ina ƙaunar ka JARRIMA NA, shima haka yake nuna min k’auna…
Yau muka shirya tsaf zamu koma gida, uban kaya masu tsadar gaske Kawu ya siyo min a matsayin tsarabar da zan tafar musu dashi, ga tawa dake akwati guda da yake ya san da maganar aurenmu, zaunar damu yayi ya saka mu a gaba da nasiha tun muna amsawa har mukazo sai ido kawai, ni kam har da kuka na domin ji nai kamar wace in na tafi shikenan, ANTY ma ta nuna min banjinta sosai wajen fitar dani kunya tsaraba kaya har da na kunya, akwatin Mommy daban haka ma ta Daddah na ANTY na yafi na kowa, ba laifi matan Kawu na sunyi masa kara ko wace ta bani 50000k a cewar su na sha ruwa a hanya, gefe na naji Anty Rabi ciki kasa da murya nace” dan Allah kiyi haƙ’uri anty kinji ?..”
Dariya tayi kana tace ” babu komai MUNIBBAT domin halinki na kware ne hakan da kikayi ya sa na gane kina da wata baiwa ta daban a rayuwar ki, Allah ya kiyayye hanya …”
Ameen nace aiko nayo gaba abuna…
Ni da nazo a mota ɗ’aya sai gashi zan koma da biyu, domin wata tsadadiyar mota Kawu na ya siyo mun, a matsayin itace tsarabar sa gareni, a ƙarshe ma ni kuka na saka dan dadin yayi min yawa, babu wanda baya kewa ta ba haka ina ji ina gani muka ɗ’auki hanya, tun ina d’aga musu hannu har na ɓacewa ganin su….