Humm rayuwa kenan wai nice zan tafi ANTY take kukan rabuwa dani, MAN baya kaunar kukana ko kad’ai tun yana rarashi na har sai da ya gaji ya rufe kunnen sa jin kai na ya fara ciwo ga kumbura da idanun sukayi yasa nayi shiru ba dan raina yaso ba…
Abinci aka shirya mana me rai da motsi, kowa yaci uban ado kamar za’ayi wani dan k’aramin biki, bakin get din suka fito ko wanne ya ƙosa yaga shigowar mu, Nafisatu sai kai kawo take Mommy tana ciki bata fito ba, Mama nace da Dadda sarakan zumudin suka fito…
Fitowar Mommy yayi dai-dai da zuwan mu kofar gidan, sabuwar motana ce ta fara danno kai cikin harabar gidan, Mommy ta ware ido domin ta san kudin motar itace abin da take hari nan gaba, ta saki siririn tsaki tace” yara sun mayar damu kamar wasu sa’anin su sai jiran su muke amma shiru!..”
Hango Mommy da nayi a matsayin wace tazo tarar mu wannan abun yayi masifaryi min dadi, har wasu hawayen naji sina neman zubo min…
Ni na fara fitowa cikin nutsuwa da yauki irin na halitta, fuskar tai fayau sabida kukan da nasha, sai wani irin tsantsar kyau na yake baiyyana, na saki wani yaulwatacen murmushi ina duban su ɗaya baya ɗaya, sai ma na rasa Ina zan nufa, Daddah shine abinda zuciya ta raya min aiko nayi wajen ta a sukwane..
Rungume ta nayi cikin jin dadi da kewar juna, na sake ta Man ma yazo ta saka mai albarka, na d’ago kenan muka haɗa ido da Mommy ga mamaki na sai naga ta sakar min murmushi ta bude hannun ta kamar wace take jiran isowa ta, iko na tafi gaba ɗaya na zuciya na sake tsunduma cikin farin ciki….
Abun mamaki ba baifi saura taku uku tsakin mu da ita ba naga MAN yazo ya rungume ta, itana ta rungume abunta har da ajiyar zuciya, cak na tsaya ina me ƙura musu ido, Mama na naji ta rungume ni hadi dacewa” oyoyo yarinyar kirki nayi kewarki sosai!..” jikina a sanyaye nace” nima nayi kewarki Mama na!..” na sake kallon Mommy da har yanzu Man yana kafadar ta… A nan dai muka tatara muka koma ciki, kowa yana jan mu da hira ta yaushe gamo, a sace na kalle Mommy cikin biyyeya na tsuguna a gabanta nace” Mommy ina wani? mun samu ku lafiya?…”
Shiru wajen ya ɗauka kowa yana kallon mu, TA ɗanne zuciyar ta tace” lafiya kalau ya hanƴa da iyayyenki?..”
Daɗi naji sosai yau ta amsa gaisuwa, aiko ‘na saki fara’a kafin nace” suna gaida ki!..” bata sake kula ni ba hankalin ta yana wajen MAN, sai wani dudduba shi take kamar gyada!…
Ma’aikatan gidan ne suka fara shigo da kayan dana zo dashi, kowa mamaki yake yanda kayan suke da yawan gaske, ina jikin Mama na bayan mu gama cin abinci, tana shafa min kai na tace” Baby! wanna kayan duk na menene haka?..”
Mommy tana jin mu amma batace komai, nace” tsaraba ce Kawu na ya siyo min kowa na shi daban, motar da muka zo da ita kuma tawace ya siya min!..”
Mamaki ne ya kama Mommy batace komai ba illa tashi da tai a wajen, kai tsaye ɗakin ta wuce zuciyar ta cike da wasi-wasi a ina iyayena suka samu irin wannan kuɗ’in da sukayi wannan bajintar?..”
Sai da aka gama shigo da komai sannan MAN yazo nashi kad’ai ya dauke, ya gudu ganin yanda Daddah ke shirin bude mai…
A nan aka bar kayan har sai da Dady ya dawo bayan naje na gaida shi, yake ce min” MUNIBBAT ya maganar da mu kayi dake? shin kin amince zaki aure Aliyu ko kina da wanda kike so?..”
Ni wallahi tambayar tashi tazo min a bazata, cikin jin kunya nace” bana jin akwai abinda zaka umarceni dashi na bijire maka, kai ubane a gareni zan k’asance me biyayya a ko da yaushe, na amince da Mal kuma zan zauna dashi da zuciya ɗaya har ƙ’arshen numfashi na…”
” Masha Allah Allah yayi miki albarka, ki gaida min da Kawun naki in kuyi waya, ki masa godeya sosai!…”
A kunyace na bar wajen sa, shi kuma dadi yaji sosai ganin dai karamar yarinyar amma ina aiki da hankali, komai nawa cikin nutsuwa nake yin sa gaskiya Haidar yayi dacen mace ta gari Allah ya bashi ikon riƙe ta bisa a amana…”
Mommy ce zaune a gaban Daddah ance ta raba tsaraba, ta kalle Daddah ranta a haɗe amma haka ta d’aure tace” to ai abu a rabe yake Hajiya, ku kirawo yarinyar tazo ta nuna shine kawai!..”
Dadi sosai Daddah taji yanda Mommy ta amshi zance bata hautsine musu ba, aiko aka kirani banji daunin kowa ba na miƙa mishi tashi tsarabar, hata ANNUWAR da nashi akwatin…
Duk wanda ya bude sai ya rik’e baki ganin irin uban kudin da aka kashe akan kayan…
Bayan kwana biyu biki na sake gabatowa inda aka fara shirye-shirye babu kama hannun yaro, a yanzu Daddah bata bari na na fito ko falo kullum ina cikin ƙuriyar dakinta, da ko ishashen haske babu gyara suke mun na fitina, d’akin kaɗai ka shigo tashin k’amshi yake bare kuma kazo inda nake, na kara kyau jikina ya sake murjewa, ANTY NA ma tazo amma bata kwana ba kayan gyaran jiki ta kawo mun yan uban su, hata waya yanzu sun ƙwace sun hanin dauka a cewar su MAN bazaiji murya ta ba sai bayan aure…
Muna cikin halin damuwa sosai na rashin ganin juna da mukayi na kwana biyu, sautari wani lokaci ba kukan rabuwa dasu nake kuka rashin ganin sa nake, a na shi b’angare kuma Mommy ya saka a gaba da naci lallai sai ta saka an fito dani, wani lokaci ma haushi yake bata ko kula shi batayi…
Hafsat ta samu labarin auren ko irin kishin nan bata ji ba domin ita yanzu ba aure ne a gaban ta ba, a yanda take harsashe in ma aure zatai bazata auri d’an najeriya ba bare kuma wani MAN…
Nafisatu ce taje har gidan su Aysha ta taho min da ita, jameel yayi aure shima ita kuma an kawo kudin nata aure, ko zuwan ta ma sai Daddah ce ta gaya min amma baa barta tazo inda nake ba, da farko nazo dabarar guduwa cikin dare, kamar yanda nake yau ma na kwanta kamar me barci Daddah tazo ta kwanta babu jimawa naji ta fara munshari duk da bashi da k’arfi amma alamar barci ne, na miki a hankali saɗaf saɗaf nake tafiya kamar wata barauniya bata ce min kala ba har sai da na kai bakin kofa sai ji nayi tace” sannu Karishima Kapoor duk nacin ki baza ku haɗu yanzu ba dawo ki kwanta!..”
Jinayi kamar na nutse a k’asa dan kunya jikina a sanyaye na dawo na kwanta, kamar jirana take ta d’aure kafa ta a jikin ta ta, shikenan tun daga ranar da zarar zata kwanta sai ta haɗe kafar mu waje guda ta d’aure…
Dama ance duk wayon amarya sai ansha man, yau sati na uku kenan a kunshe a cikin d’aki ji nake kamar nayi shekara ban fito ba, aike yayo yau ma salama ake tayi shiru ba’a amsa jin dainayi ba’a amsa ba yasa na fito falon, wata iska naji ta d’aki hanci na har cikin zuciya ta naji dadi, tsayar na tarar da yarinyar hannun ta rik’e da wata leda cewa tayi gashi inji ango wai a bawa amaryar ko yau yayi shigar dare!…”
Da sauri na amsa domin kullum maganar sa kenan inaji wani lokaci in Daddah zata kwanta tai ta mitta wai an haɗa ta yara marasa kunya, in yazo sai dai ya sace mu gaba ɗaya ba’a bani ba, na kanyi mamaki in naji kalaman ta…
” Kiyi sauri ki tafi duk wanda kika had’u dashi karki ce mai ni kika bawa, shi kuma kice mai yau amarya ta amshi sakon sa, kuma tana gaida ango!…” Kamar munafika haka nayi kamar gudun kar ajiyo ni…
Da sauri na dawo daki ledar na bude wayace dank’areriya sabuwa fil a kwalinta, cikin sauri na bude ta dadi naji gani akwai caji tamkar jira yake ina bude sakon shi na shigowa, jikina har rawa yake wajen budewa…
*Amincin Allah ya tabbata a gareki haske idaniya ta, ki sani zuciya ta tana cikin tsananin kewar daɗ’an kalaman ki, ki sani idanun sun makance sanadiyar zubar hawayen rashin tozali dake, Ina cikin wani mayuwacin hali na rashinki a tare dani, please ki fito na ganki ko giftawarki ne ko hakan zai sa zuciya ta samu nutsuwa, ki taimake wannan bawan Allah da ya gama matowa a soyayyar ki da bigenki!*…
Rungume wayar nayi a kirjina, zuciya nayi min wani irin sanyi soyayyar sa nayi sake min ƙami ciki kogin zuciya ta…
Sak’onin soyayya iri daban-daban MAN ya ringa an tayo min, tuni nima na shiga mayar da martani cikin matsanancin farin ciki da k’aunar sa…
*Ka sani nima nayi kewar ka irin wace bazaa taɓa musaltuwa ba, na kadara a raina cewa ni zautaciyace akan k’aunar ka, ina haukar sonka MAN ina maka k’aunar da babu irin ta, Ina ji a raina duk ranar dana rasaka shikenan nima tawa ta kare, domin kai ne mukulin rayuwa ta, ina jinka sosai a raina, ka kwantar da hankalin ka zamu haɗ’u haɗuma mafi kyau da tsari wace zaa kafa tarihi marar musaltuwa, haɗuwar da har abada abadina baza’a so a rabu ba, nan da kwananki kaɗai zan zamun mallakin ka ta har abada, ina kaunar ka mijina na gobe!…”*
Nima na tura mai amsa ta zuciya ta cike da farin ciki…
Ya turo kenan zan duba Daddah ta shigo cike da rashin gaskiya na shiga kici-kicin boye wayar kallo rashin yarda tai min kana tace” ke lafiyar ki kalau kuwa? tunda na nufo shashin nan na san kin fito, yanzu MUNIBBAT saurayi yafini kenan? yaushe kika fara koyar kafiyane…?”
” Daddah banje ko ina ba wallahi, iya kata falo shima naji shiru ne shine na leko!…”
” Ohho dago naga idanun ki!..” ta fad’a tana kafeni da ido, ban kawo komai a raina ba na d’ago, aiko muna haɗa ido da ita ta saki sallati tana taffa hannuwa, game da kama baki tace” na shige su ni Nafisatu! yanzu yarinyar nan bin shi kikayi gashi nan har fuskar ki ta nuna! to inda Jan zaki ne kije ki taiyi wata rana da kafarki zaki gudo nan nima a lokacin zan murd’a kanbu na, in kinyi hak’uri saura sati d’aki ki koma inda yake da zama ma gaba ki d’aya sai ku kwaɗa juna ku cinye inga k’arshen soyayya!..”
Tsoro ne ya kamani aiko na saki kuka cikin kuka nace” wallahi ba inda naje Daddah, wata yariyar ce kawai tazo ta kawo min waya, kuma ko kira baiyi ba kika shigo!..”
Mama nace ta shigo hannun ta rik’e da kofi, bata damu da kukan da nake ba sai cewa tai”” ungu maza shanye ki bani cop dinna!..” “
Ni kam dama ba san abinda take dirka min nake ba na shiga rera kuka abuna, ko kallon ta banyi ba, Dadda tace to yanzu ina wayar take?..”
Shiru nayi naki magana dan na san yanzu itama zasu ƙwance, duk yanda suka so nayi magana a lokaci ƙi nayi sai kuka nake babu wanda ya tsaya rarashi ne suma suka wuce abin su, Ina ganin sun fice nayi saurin tashi na wake fuska ta, agogo na duba ganin har yanzu akwai lokaci sai na kwanta abu na barci me dadi ya dauke ni!…
Rayuwa ta ci gaba da tafiya, Mommy har da ɗ’auko me gyaran jiki, yanzu ita take min komai waya kuma tun daga ranar ban sake ganin ta ba ashe Mamace ta d’auke lokacin da zata fita, zaman d’aki yasa na dawo wata katowa fatar jikina tayi wani irin kyau ga gyara da take sha, haske na yanzu har wani yalo yalo take….
Gida ya cika sosai baki ta ko ina, gidan da Mama ta taso suma sun zo da abin arzikin su, tunda satin nan ya kama yanzu Ina ganin jama’a shima jefi-jefi, su Bishira gaba d’ayan su sun sunzo, baki ne suku tarowa kamar me Mommy jamaar ta sun zo suma ko wanne na shi na bangaren sa, biki ake kamar na mutun biyar an tara jama’a sosai….
Duk wani shagali anayi shi, ranar dana fara fitowa kowa kallo na yake cike da mamaki a Ina MAN ya samu balarabeya, dangin Mommy sun yaba da zaɓ’in shi na sha kyautitika a wajen su, duk wace aka kani wajen ta da abinda zata zabani na samu gwala-gwale a wajen su haka ma dangin Mama suma sunyi min ƙ’oƙari, gaskiya ni ƴar gata ce ta ko ina…
Ba lefi ANNUWAR ya sake ba kamar dah ba, ya shigar cikin jamaa shine akan gaba duk wata hidima idan ta taso, MAN kam gaba ɗaya ya matsu a ta tareni a kaini duk da bamu da wani nisa, amma gaba d’ayan sa akan gwiwa yake, kishi na yake sosai musammma abokan sa in suna yabata har fad’a suke dashi…
Duk wani fati da aka shiri da kyar ya bari akayi biyu shima sai da Mommy ta saka baki, a cewar sa shi baya son sa ido an dami matar sa da kallo, ranar jumma’ar aka daura mana aure NI da MAN…
BABBAN tarihi babbar ranar, ana dawo d’aga daurin aure zancen yazo min k’unne da gudu na tafi shashin Mamana rugume ta nayi ina kuka kamar yanzu ne lokacin tafiyar, sosai nake kuka tun tana ture ni ta dauka wasa nee har sai da abun ya zamo gaske, itama ta cire kunya ta shiga rera kuka, manya kawaye ta suka shiga dariya da taffa hannuwa, a k’arshe sai wajen muka bari ANTY tazo da nufin ta rarashe mu itama yanda nake musu magiya dan Allah kar su barni sai gashi tana kuka…
Daki guda muka ware imu-imu bayan sun sakani a gaba nayi sallah suka shiga rarashi ne da nasihohi iri-iri, ko wace da abinda take ce min, ni dai babu baki sai kuka nake har muryata ta dashe, tausayi na ya gama karyar musu da zuciya haka suka d’aure basu barni na zauna haka nan ba, wata babbar macece tazo har d’aki ta wuce dani wajen manya, gaskia na sha fad’a ko wace da abinda take ce min tsofafine amma irin su Daddah ne masu jikin kyau wanda kudi ya zauna musu, duk wace ta gama min fad’a sai ta daura min abu a hannu na bana ganin sosai sabida hawaye matar da muka shigo da ita take daukewa, a haka har muka bar shashin Daddah na Mommy ta kai ni nan ko wace fad’a take min da nuna min ribar hak’uri a k’arshe ta kaini wajen Mommy da kan ta, duk da bana gani sosai amma yau ina so ta gwada min iyaka ta, cikin kuka na shige jikinta abazata ina rik’e ta ciki kuka, shashek’ar kuka na fitar da sauti me kashe jiki, murya kasan makoshi nace” ki yafe min Mommy dan Allah? kiyi hak’uri da duk abinda nai miki a zamu, ki yafe min kinji Mommy!?…” a yanayin da nayi maganar babu me jin me nace sai ita, a yanda nake kuka da zubar da hawaye yasa duk wanda ke wajen sai da na bashi tausayi masu saurin kuka kam har da tayani…
A hankali ta rungumeni sabida idanun mutane tace” ba komai y’ata Allah ya baku zaman lafiya, kiyi ta hak’uri kinji!…” ta fada tana d’ago ni kallon ta nayi ido cikin ido na sake marairaicewa hawaye na gudana a ido na nace” dan Allah fa nace Mommy!…”
Wani irin tausayi na ne ya kama ta a karo na farko kenan a zama na da ita, tunanin tai wata ranar haka Auta zatai itama, sai ta shafa min fuska tana min murmushi tace” na yafe miki yarinya ta!…”
A mota aka d’auke ni sai gidan Kawu na, a jikin sa na kwanta abu na sai kuka nake yana shafa min sumar kai na, sai da ya tabbatar nayi me isata sannan ya shiga min nasiha cikin sanyi, a yanda nake fad’ar falalar auren da yanda zaman takewar take da hakurin da zanyi sai jiki na ya sake yin sanyi, na sake shiga hankali na Mama na gani a gidan duk da ba abin mamaki bane, ashe ita da ANTY suka dawo tausa suke da kalamai masu dadin gaske a yanzu ni kukan ma yaki zuwa sai ajiyar zuciya da nake saukewa akai-akai, kafin dare yayi har nayi rama, nayi nacin duniya su bari sai gobe amma ana idar da sallahr i’sha’i suka shirya ni sai buri nake ina turjewa sai da Mama ta zare min ido sosai sannan nayi hankali nayi shiru, motoci aka kawo na d’aukar amarya ina rike ANTY tana kwacewa aka fito dani, aiko ina ganin Mama na makale ta gam jan duniya akayi min naki sakin ta dole tazo aka shiga motar da ita, wai da baza tazaje ba ai ita ce uwar amarya ce, to ganin bazan sake taba yasa sukace ta shiga mu tafi, Kawu na yana d’aga nesa damu yaki zuwa gudun kar naki tafi, inaji ina kallo suka rabani da gidan mu…
Aure me dadi kenan aure me raba ƴa da uwa, ƴan uwa da dangi, sai dai muce Allah ya kara mana zaman lafiya me daurewa!…
Kawu na ya zuba mun kaya masu bala’in kyau shi yayi min bedroom dinna Mama na tayi min na MAN, Daddah ta zuba min kujeru dady kam bangaren baki shi yayi komai a ciki woni ƴar gata, da yake na samu kayan lefe sosai gashi an dinka musu kamar hauka domin sunfi hamsi, ko ina a gyara yake tsaf a can muka tarar da su Aysha suna zaman jiran mu, ko wace taci uban ado wa yanda suka kawo ni basu jima ba suka tafi abun su mama ta mike cike da dabara naji tace” Aysha Ina nee bayi a nan?..” ban san me sukace mata ba na sake ta miki ta fice a gidan zuciyar ta cike da kewa ta…