Skip to content
Part 32 of 32 in the Series Waye Zabin Munibat? by Husaina B. Abubakar

Shirun da naji bata dawo bane yasa na gane wayo tai min aiko na shiga rere kuka, Aysha ce kawai take rarashi na amma su Nafisatu da Bishira sarakan shiririta dariya suka ke min, a haka har angoye suka karaso gyara d’akin aka sakeyi kafin su shigo turaran k’amshi ya ci gaba da tashi ta ko ina…

Kamar yanda alada ta tanar anyi addu’oi d’aga bisa su sake mana nasihohi masu ratsa jiki, abinda suka shigo dashi suka ajiye gefe guda komai katan-katan aka siyo kazar ce na hango ta a  hannu MAN loz, babbar rigar ya cire inda ya tafi rakasu ni kuma na tashi na shige cikin d’aki na cigaba da aikin kuka na…

An tafi a barni dagani sai hali a gida na, aure ma fa kenan ba mutuwa tunda shi duk lokacin da kaji kana son fita zaka fita ka sha Iska ka dawo, mutuwa kuma in ka tafi  katafi kenan babu me zuwa maka ziyara ku had’u Allah ka sa mudace….

To maganar Allah azumi zamu shiga, ko wace ta fasalta yanda masoyayyan  nan zasu faranta ran junan su….

Washe gari sosai na tashi da wani irin ciwo, gaba d’aya bana iya ko tashin arziki, duk da MAN yayi min k’ok’ari sosai wajen kula min da jikina amma kafata makalewa take, tunda na idar da sallah nake cikin zuwan zafi da ya salamce sai ya sake sauya min wani a haka har jikina yayi min dama-dama, na shirya tsaf jikin wata doguwar rigar atamfa ta mashi jikina sosai sai wani ƙyale nake abu na, barci muka koma d’aga ni har shi din bamu wani jima ba aka fara buga mana gida, a gajiye ya tashe ran shi bai so ba jallabiya ya saka kana ya wuce yana fita nima na miki da sauri na zan biyo bayan sa babu shiri na koma sharaf dani a gadon kwankwasona kamar ya ɓalle, azabar radaɗin da nake ji ya hanin motsi…

ANNUWAR ne hannun shi d’auke kayan abinci yana turo baki gaba yace” kun tashi lafiya? gashi inji Daddah wannan kuma ance ka bawa amarya…”

Ko amsar shi bai jira ba ya juya abin sa ya tafi, ko bai fad’a mai dalilin fushin nashiba yasa taso shi akayi d’aga barci dan ba yanzu ne time din tashin sa ba, ciki ya dawo a yanzu da sameni sai da gaban shi ya fad’i cikin sauri yazo ” ya haka my happiness?..”

Cikin shashek’a kuka nace” ban sani ba!..”

Dariyar sa ya danne cikin azama yaxo ya taimaka min na gyara har na ci wani abu, d’aga bisani ya bani abinda aka aiko mun dashi, kamar sun san halin da nake ciki tashi nai  a hankali gani tafiyar tawa zata bada matsala yazo ya dauke ni cak sai bayi domin ya fahimci inda zanni, aiko na shiga bugun sa ina cewa” ina kuma zaka kai ni yanzu? sauke ni wallahi bazan yarda ba ni gidan mu zan tafi ma, tunda baka da hak’uri ai sai da nace kayi hakuri kar ka ƙara amma sai da ka ƙara gashi nan ka cinye min lakar kafafuna bana iya tafiya, bilhaƙi nake dukan shin hawaye shaɓ’e-shaɓe gashi babu ikon nayi zullo na fado…

To amfanin da nayi da had’in da Daddah ta aiko min dashi sai naji dama dama, zan iya tafiya amma sai da dabara MAN fa ba k’aramin aiki yayi min ba a daren jiya, gashi da wayon tsiya gari na wayewa ya wanke zanin gadon yaki bari a saka wani yana bushewa ya mayar dashi,  kallon shi kawai nake da mun hada ido sai harara…

Duk wanda ya tashi wucewa sai ya biyo yaga d’akin amarya kana yayi gaba abun sa, ina zaune kamar an dasani duk wanda zo bana tashi Daddah ce tazo da yamma nan ko na saka mata rigima sai na bita, dariya tai me isar ta kana tace” yarinyar me nace miki satin da ya wuce ? ke ba har satar hanya kike kije ba to ba wanda zai d’auke ki d’aga yau bazaki sake ganin kowa ba, ku ta abu d’aya babu sauki!..” 

Kuka na saki cikin jin kunya nace” kuyi hak’uri  dan ALLAH in ba haka zan mutu!…”

Ganin yanda nake kuka ne yasa tai shiru d’aga zulaya ta hadi da cewa” kiyi amfani da abinda ƙaninki ya kawo miki da safe ?…”

Duk da naji tace ƙaninki ban tambaya nace” eh!..”

” To ikon Allah amma har yanzu da zafi bai ragu ba?..”

Kunshe fuskata nayi da hannu na, dariya tai kana tai min nasiha sosai dama jiya banganta ba, ashe gudu tai Daddah har da koya min yan dabarun su na tsofafi…

Kamar yanda tace tun daga ranar ban sake gani kyar kowa ba, duk wanda na kira a waya ma muna gama gaisawa suke kashewa kamar had’in baki….

Gaskiya MAN rigimameni na karshe kafin nayi sati biyu har nayi yar  rama, idanun na yayi zuroro abinka da ba’a saba ba, ni kullum abun a sabo yake zuwa min…

Bayan wata biyu kwance nake a cinyar sa muna wasan mu na soyayya, a yanzu kam nayi kilin abu na bana fargaba sai dan abinda abaa rasa ba,  hira muke wace ta shafi rayuwar mu ta baya  ko wanne yana bayawa abokin sa irin yanda son shi ya wahalar dashi, to a nan ne naji yanda yayi rashin lafiya har na tsahon sati ba tare da na sani ba….

Bayan wata biyar a yanzu kam na fara cire rai da ganin Kawu na a gidana, babu irin kukan da banyi   mai ba, amma yaki zuwa a k’arshe ma cewa yayi sai ranar da yazo ya tarar na haukace shine zaizo!…” Sosai nai kuka na kamar me sai nake gani kamar nayi masa wani lefine…

Mommy har ita da Dady basu zo na, in anyi magana sai suce akwai lokaci, ANNUWAR yana zuwa shida Nafisatu amma yar bazan izzar tashi ce take had’in dashi, d’aga gaisuwa bana sake ce mai komai har ya bar gidan, abinda ban sani ba yana neman kafa dani ne ni kam ban san yanayi ba sosai suke zuba soyayya shi da Bishira tun da suka had’u a wajen biki…

Zaune ta same shi cikin girmamawa tace” barka da hutawa yallab’e!..”

” Yauwa barkan mu dai!..”

” Magana nazo muyi akan auren yaron nan MAN!.”

” UMHH ina jinki!..”

” Dama munyi da kai akan in akayi auren sa da zaɓin ka nima bayan wani lokaci za’ayi da nawa zaɓin shine nake so akayi a wata d’aya ita kuma!…”

Duk maganar da take bai kalle ta, illa gyara kwanciyar sa da yayi yace” to ba damuwa ki samu wakilin shi kuyi magana,  inda buk’atar kud’i  sai kiyi min magana, ki fad’awa hajiyar mu da abokiyar zamanki!…”

Wani irin farin ciki ne ya kama Mommy jin dady ya amince ba tare da ya nuna mata wani jin haushi ba…

Batai tammanin samun haɗin ka Daddah, kaf cikin gidan babu wanda ya bata matsala duk wanda taiwa maganar auren sai ance mata Allah ya sanya alhairi, wanna abun yayi mata dadi sosai, sai take ganin yanzu ta kai matsayin da zatayi komai da kanta, a cewar ta MAN dinma bazata fad’a mai ba sai bayan ana daura auren zatai mai albushir…

Daddah da Mama nee suka zo har gida, mura ta kamani kamar nace me dan dadi, sai hidima nake dasu na kasa zama waje guda duk wani abun da nake dashi motsa baki zuwa nake na d’auko musu,  cikin hikimar zance da dabara Daddah ta ringa yin min nasiha wace na kasa fahimtar dalilin ta, sai da tai me isar ta kana Mama na ta daura itama duk abinda suke cewa da insha Allah nake binsu dashi,  tausayi na suke ji sosai a ran su babu wanda ya gaya min dalilin zuwa su har suka wuce…

Naji dadin zuwan nan da su kayi min musamma da Mama na ta sake min zuwa na biyu…

To MAN ana kira shi sosai su Daddah su kai mai fad’a kamar yanzu ne farkon aure mu, shima da insha Allah ya bisu d’aga bisani ya dawo gida.

A rayuwar auren mu babu wata matsala dake tsakana dashi kullum cikin farantawa  juna rai muke, mu kan samu akasi ta wanin b’angare na halin rayuwa amma cikin sauki muke maganin matsalar mu, na fahimce shi sosai kamar yanda shima ya fahimci halina…

Kamar yanda Mommy take buk’ata haka ce ta kasance, shiryawa sukayi  shiri na ban mamaki an kashe kud’i iya kud’i tamkar wace zaaje d’auko amarya gaba d’aya, ficikar Dady ba tai kuka ba domin cewa tayi a yanzu zabin ta zai aure dole ne ta nunawa duniya zai aure yar gata me cikaken iko,  kanin Dadda sai kanin mahaifin su Dady wanda ya rage musu, neman aure har da Mommy kamar wata d’iyar sarki…

Duk wannan hidimar da Mommy take bata san yarinyar da take burin d’anta ya aure yau nee ake dinna din ta, da wani hamshakin me kud’i wanda ya ke ji da kan shi a kasar Dubai, ya tara abin duniya sosai jin sa yake tamkar wani ƙaruna kallon kowa yake a wulak’ace, domin dan izza ne na bala’i ita kanta Hafsat zai aure ta ne dan wani burin sa ba wai dan ta kai ajin auren sa ba,  a cikin sati gudu yake so ayi komai a gama, kud’i kawai yake turo musu kamar hauka amma har yanzu basu ga keyar sa ba, a yau aka daura auren su a cewar sa baya buk’atar komai sai matar sa kawai kuma a ranar yake so zasu bar kasar, Murjanatu  bata d’auki Mommy a matsayin wata kawar kirki ba shi yasa ko bikin bata ganyace ta ba, hidima suke bana wasa Mommy tazo da mota biyu na kayan alatu, sai dai aka gama bincike kayan tas sannan suka barta ta wuce, manya kawaye Murjanatu ne duk inda ka duba ka san kud’i ya zauna haka Mommy tai ta wuce su zuciyar ta cike da mamakin wannan taron, tsayar da ita akai a wani karamin falo ace war su Hajiya babba tace kar kowa ya shigo tana ganawa da yarinyar ta ne!..

Da yake ta san halin kawar ta bata ji komai ila, zaman jiranta da tai sosai ta b’ata lokaci kafin ta fito hannun ta rik’e dana Hafsat dake ta washe baki kamar gonar audiga, ko kallon Mommy Hafsat batai ba bare ta sa ran gaida ta..

A yanƙwane Murjanatu ta amsa gaisuwar Mommy tana yi tana duban jama’ar dake nesa da ita suna magana a haka, zuciyar Mommy ta soso da irin wulak’acin da akayi mata amma ta jure cikin k’arfin hali tace” kawa ta magana nazo muyi akan wannan alkawarin namu!..”

” Dama akwai wani alk’awari dake tsakanin na dake wanda ban sani ba?…”

Murmushi tai had’in da cewa” eh maganar yara nan namu da muke ce zamu hada su aure! to naga lokaci yayi ne shine nace nari muzo mu tautauna gashi na nazo da wakilan yaron suna wajen maza,  ina so ayi komai a gama nan da wata daya kawai…”

A wulak’ace take duba ta sama da kasa, cikin yauki tace” amma wallahi Amina kin samu matsala, yanzu banda rashin kunya ma irin taki ki dubi wannan zankadeɗiyar yar tawa kice na hada ta aure da wani matsiyaci? banda hauka ma irin naki yarinyata ta miki kama da aure me mata! to in baki sani ba ki sani yau aka daurawa ɗiyata aure da wani hamshakin me kud’i wanda ya kerewa tunanin ki, a yau kuma zai dauki matar sa su wuce dubai a can zatai rayuwar ta, ni wallahi kin bata min rai Amina fiyya da zaton ki, banda wulak’aci ki rasa wanda zaki hada yata aure sai da tsatsonki ku da baku gaji wani arziki ba, malama tun kan raina ya baci na saka a fitar dake cikin kaskanci  ki tashi ki fice min a gida, tunda talauci ya fara zautar dake!…”

Tashin hankali marar musaltuwa, cikin kidima  wani mugun zafi maganganun Murjanatu Mommy ta miki fuskar ta cike da bacin rai take duban ta, tace” Murjanatu ni kike cewa matsiyaciya? yaron nawa ne matsiyaci? ni zaki wulakanta?…”

Tsaki tai ko kallon Mommy ba tai ba, cikin izza ta saka wasu kartin mata su fitar mata da Mommy a cewar ta akai ta waje a jifar kamar wata tsunma!…

Jin haka da Mommy tai bata sake gigin tsewa ba ta fice jikin ta a sanyaye hawaye na bin k’uncin ta, duk rukunin matan da tazo wuce sai su fashe mata da dariya, to iyayen Dady kam Mommy na shiga ciki suma suka tafi ganin yanda ko wa yake harkar gaban sa babu wanda ya amsa musu salamar su bare abasu wajen zama….

Gaba d’ayan su sun falo hira suke cikin kwanciyar hankali, ko wanne ka duba zuciyar sa cike take  annashiwa, da sauri Mommy ta gifta su hawaye na bin k’uncin ta ko sallama batai ba, kai tsaye d’akin ta wuce cikin bakin ciki marar musaltuwa, sai ta k’arewa d’akin ta kallo sai ta saka kuka babu abinda yafi ci mata tuwa a kwarya irin yanda murja ta d’aga murya  a gaba wasu jama’ar tace mata matsiyaci ya, yanzu duk wannan daular da take ciki yau ita aka ciwa mutunci!…  

<< Waye Zabin Munibat? 31

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×