*****
Kimanin wata biyu kenan shiru Mommy bata sake maganar aure ba, yanzu ko da yaushe tana d’aki abinta, magana bata dame ta ba…
Allah sarki Daddah ita ko wannan saban halin da Mommy ta fito dashi sai duk ta bi ta damu kan ta, kullum cikin leka ta take ta gani ko lafiya, sabuwa ladama ke damun Mommy tunnani take ta ina zata gyara k’usk’ure ta musamma a wajen surukar ta me ladabi, tunda ku san kullum sai na kira ta a waya na gaidata, tun tana kin dauka har ta fara wani lokaci tai shiru ina gamawa ta kashe wayar wani lokaci kuma tace min lafiya d’aga haka babu kari, ita yanzu kunyata take ji sosai shi yasa bata bari muyi wata dogowar magana a tunanin ta na san abinda ya faru, abinda bata sani ba dagani har Man bamu san da maganar wani aure ba, zaman lafiya muke cike da soyayyar juna ga wani karin abin farin ciki Mama na da ciki har na wata biyu, fad’ar irin murnar da wannan ahalin su kayi bata baki ne, hata Kawu yayi farin ciki sosai ku san kullum ina hanyar gidan nice dafa wannan daura wan can…
Gata Mamana take gani kamar wata yarinya, hat Mommy ta cire kishi yanzu zama take su ta tsokanar Mama na, muna cikin haka nima nawa cikin ya kuno kai sai jiyya ta zama biyu domin ni nawa me laulayi ne irin sosai din nan, abinda ban sani ba na jima dashi a jiki na ko su Dadda sun sani shi yasa suke ta nan-nan dani, ganin bai bani wuya yasa basa hanani duk wani aiki da nai niyyar yi, gaba da muka hadu muka tare a gidan naki komawa gidana a cewata yana takura min wanna karan Mommy ce ta tsaya cak akan cewar ba inda zani dole MAN ya ha’kura shima ya dawo gidan gaba d’aya, abinda zai baka dariya kuma ya birge ka sai Dady ya shigo da leda a hannu Man na biye dashi da tashi ledar, ko wanne na Kiran babyn sa yake wani lokaci Daddah guduwa take d’akin ta Mommy ma haka, rayuwar muke cike da farin ciki marar yanke, na samu soyayyar Mommy kamar yanda na fahimci ta dalilin cikin nan ta sauko, abin mamaki Mommy ce yanzu da kan duk ranar da za’ayi sadaka take fita ta raba, ta koya ANNU ma ta k’arfi da yaji da yake yana bala’in tsoronta da jin maganar ta dole ya dawo kirana da ANTY, shima ba lefi yanzu har maka zama dashi muyi hira, a bangaren Aysha kuma tayi aure ta aure wani dan uwan baban su ba lefi yana da abin hannun sa shima…
Cikina yana wata bakwai akayi bikin Bishira da ANNU, gaskiya angi shagali sosai kud’i kuma yayi kuka babu wanda bai halaci wanna taron ba Mommy itace ta tsaya akan komai, mutanan da suka san halin ta da yawa sunyi mamaki yanda ta saki jiki ake biki lafiya, ba tare da ta nuna komai ba Amarya tazo da goshi ita ma domin ANNU cewa yayi a bangaren sa zai zauna MAN ne ya d’auki gyara komai da akayi, Mama na sai yawo take da tikeken cikin ta, duk wanda ya ganta sai yayi mata sannu, duk inda tai Ina biye da ita wasu har dariya suke mana a wani abin ma nafita dauri, ciki kenan…
Bayan shekara biyar
Wasu kyawawan yara na hango ko wanne an ɗanɗasa mai ado na kece raina, farare ne tas dasu ga gashin su da akayi musu ado dashi a tsakiyar kai, ko wannan su ya zauna cikin shirn fita…
MUNIBBAT na hango cikin wata rantsatsiyar shiga ta fitina a hankali take tafiya kamar marar lafiya da sauri na kalle gaba na ta sai na hango wani k’aton ciki tamkar an kifa mata kwarya, da kyar take tafiya yaran nan su uku biyu mata na miji guda suka taso cikin jin dadi ko wanne bakin sa na fadi” Mome!! Sannu da fito…
Murmushi tai cikin jarimta tace” yauwa yaran mome me kuke har yanzu baku fita waje ba!..”
Cikin had’in baki sukace” muna jiran ki ne mome!..”
Murmushi tai tana duban su cikin jin dadi tace” to muje kun san abban ku bayan san jira!..”
Cikin nutsuwa su ka wuce waje kowane ya rike hannun dan uwan shi, zaune yake a cikin motar sa shi ya sha gilas alamar girma ya fara zuwa, hango ta da yayi ta fito ya shi saurin fitowa fuskar su cike da an’nuri mota ya bude yaran suka shige shi kuma ya karaso waje na…
Tsayawa nayi tana turo baki gaba, dariya yayi yana dubana kana yace” kin gan yanda cikin nan yayi miki kyau madam!…”
Bata fuska nayi Ina sake narkewa nace” wannan kyau ni dai gaskiya honey in Allah ya sauke ni lafiya hutawa zanyi haka, haba yara hudu ma ai sun ishe mu!..”
Baice min komai ila daukata da yayi sai mota shi sam baya jin kunyar yaran sa, muna tafiya in mita har muka isa gida, sake daukata yayi bai ajiye ni a ko Ina ba sai a falon Mommy haka kuma bai kulani ba fuskar sa ma bata nuna yaji haushi magana ta ba, ciki ya shiga sai gashi da Mommy sun fita gaskiya Mommy Yar gayuce duk da girma ya kamata amma haka ta ci uban ado, ban san me yace mata ba nan dai ga itama fuskar ta babu faraa…
Bayan yara sun shigo ta gama dasu sun wuce bangaren Mama na, ta sakani a gaba da fad’a ta inda ta shiga ba ta nan take fita, kamar zata dake ni wai kar na sake cewa haka in ba haka kuma zata saka shi ya ƙara aure ni naje nai ta huta na, ita jikoki basu ishe ta ba kuka nai tayi sabida ta fahimce ni amma fafor Mommy taki sauraro na, har da cewa Kawu na zata kira ita ta gaji da wanna karar da ake kawo mata kullum…
Duk inda naje a gidan yau babu sauki fad’a na sha na ɗan uban su, Mama yanzu yaran ta biyu na mijin shine babba sai macen wace bama a yaye ta ba, ni dama yan biyu na haifa duk mata sai na miji guda d’aya me sunan baba na, ga wannan cikin ma da akece yan biyu ne…
To kamar abin arziki haka ya ringa daukata yana kai ni wajen iyaye na d’aya bayan d’aya suna min fad’a kamar zaa dake ni, ANTY ma sosai ta nuna min bacin ranta dole nayi hakuri..
Shima sai muje kwanciya nake rama abinda yayi min dan in nace banji haushi ba nayi karya, Mommy ta ƙwace yara gaba d’aya yanzu d’aga ni sai shi a gidan….
Allah ya sauke ni lafiya na samu Yan biyu duk maza, murna a wajen su Mommy ba’a cewa komai, gidan na koma abu na dan nace bana zama MAN kamar yayi hauka amma nima na shafawa idanuna toka…
Anyi bikin auta biki na Yar gata, wannan karan ni na nunawa Mommy halaci domin komai ni nayi mata shi, taji dadi sosai har godeya tai min, Allah da ikon sa sai gashi auta bata auri me kud’i ba kuma haka bai dame Mommy ba, sai ma fatan samun zaman lafiya da tai musu….
A yanzu yarana suyi wayo sosai soyayya muke zafgawa ni da JARRIMME NA kamar bazaa mutu ba, Allah ya dube ni na samu hutu haihuwar su Hassan sosai domin har fad’a muka fara da MAN ya ji shirun yayi yawa, Mommy ta d’auke min wuta Allah cikin ikon sa yara na suna shekara biyar na sake samun wani cikin..
A wannan karan haihuwar tazo min da matsala, su likitocin da kan su suka bani hutu dole kuma suma sukayi hak’uri, nayi jinya sosai kafin a sallameni…
Bishira ma yanzu yaran ta uku inda Mama take da biyar, Aysha biyu nima shida dan kusan tare muke tafiya da Mama na…
Rayuwa ta dawo min sabuwa kullum cikin samun ci gaba
nake, ANNU har gida yazo ya sake bani hak’uri, muna ZUMUNCI sosai da Yan uwana baki d’aya…
Hafsat kuwa sai bayan aure ta gane mijin nata yana da aure har da yara biyar, da yake matan na shi turawa ne babu abinda suka iya sai sex shine dalilin aurota da yayi tazo ta zame musu yar aiki, wani lokaci yana sex da ita tana aiki in Taki tsayawa kuma ya zanne ta yayi dole ta k’anwar naki take biye mai duk abinda yace, gashi matar sa ta farko shadaniyace da zarar ya fita itama zata shigo tun Hafsat na gudu yanzu har ta saba mutun biyu take mawa amfani mace ta cita na miji ya cita…
Tana fara rashin lafiya ya antaya mata saki uku cif, ya karo ta gida a wukalance, Murjanatu tai kuka kamar me domin suma yanzu gari ya fara gara musu dukiya da ake tun kaho da ita duk ta Kade a banza…
Rayuwa kenan ka shuka alhairi ko ka tsinci abinka a ranar gobe Allah yasa mabiya wannan novel nawa sun fahimci illar zalinci da wulakatan maraya a rayuwa, duk talauci mutun yana da rana a rayuwar sa duk wanda ka gani a duniya yana da nashi amfanin, Alhamdulillahi a nan na kawo k’arshen wanna novel din nawa abinda na rubuta ba dai-dai Allah ya yafe mana baki d’aya, Ina maku barka da shigowa Ramadan Allah yayi Mana maganin wannan anobar…
Alhamdulillahi
Ina muku fatan alhair masoya Na
Nice taku har kullum Usaina Bala Abubakar
Wace kuka fi sani da Mrs Abubakar ce wato sweet bukar dinnan, a nan nake muku sallama..