Skip to content
Part 4 of 10 in the Series Waye Zabin Munibat? by Husaina B. Abubakar

Bismllahir Rahmanir Rahim

Ban sake sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi, naga Anty da sauran mak’otan mu sai sannu ake min, ni dai ido kawai nake rabawa ina k’ok’arin tuno abunda ya faru, da sauri na koma cikin d’aki ina dubawa, babu mama na babu dalilin ta, anan na zauna ina ta faman kuka mutane na bani hak’uri inda  Anty ta saka ni a gaba da bani baki akan nayi shiru yanzu mama na addu’a ta take buk’ata ba kuka ba. A gaskiya nayi babban rashi a rayuwa ta domin sai bayan ba ran Mama na, na gane cewa ita ce jigo na!

Bayan k’wana bakwai an yi sadaka an watse, d’aga baba na sai kawu na a zaune a k’ofar gida, cikin mutuntawa da jimami kawu yace” malam ina so na rok’i alfarma a wajen ka, me zai hana tunda Allah yayi ma Rabi’atu rasuwa duba da yanda kai ba  mazaunin gida bane, inaga kamar zaman gidan zai mata zafi da tsananin maraici, shine nace ko za’a bani Mama na ta dawo wajen mu da zama.. har muga yanda abin zai k’asance..?” ya fad’a cikin ladabi.

Baba na ya gyara zaman shi da kyau babu kunya ko kawaici yace, “Naji dadi sosai da nuna k’aunar ka ga y’ata. Amma maganar  d’aya ce a yanzu kaf duniyar nan bani da tamkar ta, bani da wanda zan duba nace wannan jinina ne, to maganar gaskiya bazan iya bada ita rik’o ba, zan zauna na kula da abata in muna da rai da lafiya har na aurar da ita, maganar zaman kad’aici kuma bai taso ba tunda tana tare dani, a yanzu maraici ya zame mana dole daga ni har ita, mu  ajiye wannan maganar ma sam bata da amfani.”

“To shikenan Allah Ya zab’a abinda yafi alhairin, amin.” Babana yace.

A ranar su ka koma garin su inda suka bar ni ni d’aya tal a cikin gidan mu, sai mahaifina dake k’ofar gida, nan na fara ganewa cewa lallai ina ganin rayuwa.. kula da kai na da karatu na ga begen Mama na da ya cika min zuciya, kullum sai nayi kuka..  na koma makaranta sabida na sawa raina damuwa sai hakan ya fara tab’a karatu na, malamai na sun san halin da nake ciki, sune suka cigaba da rarrashi na suna bani kula da karatu cikin hikima a haka har na ha’kura na mik’a lamari na ga rabil’izatti.

Kawu na yana sintirin zuwa duba ni, haka zai kawo min kaya masu yawa  in yazo yai ta nan dani, duk dan nayi farin ciki, gaskiya kawu na zan iya cewa shine mutun na farko da ya fara koya min yanda ake so, ya nuna min tatali da soyayya ya fifitani akan y’a’yansa, gashi duk ranar da yazo waje na to sai ya biya gidan shi,  in yaje gaban Anty tamkar an kunna rediyo haka yake bata labari na da irin siyayyar da yayi min, ya fad’a mata ina farin ciki sosai.

Babban kuskuren  da aka tafka kenan, Anty na ta tsane ni sosai a zuciyar ta, musamma yanzu da take ji tamkar tazo ta k’arfi ta k’wace ni ko abinda yake min  zai dawo k’ark’ashin ikon ta, ta shiga zuga shi akan ya amso ni a had’ani da y’an uwa muyi rayuwa akan wannan zaman da nake ni kad’ai, kada tsautsayi ya fad’o min tunda an san gidan ba kowa wata rana azo a cutar dani, kullum suka had’u had’ubar da take mai kenan ko gajiya ba tayi, wani lokaci har da hawayen ta in ya tambaya sai tace mai wai tana  tausayi na ne.

*****

Tunda Mamana, ta rasu Baba na yake ciwo a tsatsaye, damuwa na cin sa a hankali har ya zame mai hawan jini ba tare da kowa ya sani ba, sannu a hankali ya fara ramewa walwalar sa na raguwa, da ya dawo daga kasuwa baya komai sai barci, wanda baya ba  haka yake ba, sai ya tambaye ni lafiya ta da kuma abinda akayi mana a makaranta, kamar yanda mama na take min lokacin da take raye, ganin canji a wajen sa ba k’aramar damuwa na shiga ba, na saka shi a gaba da kuka har ya amince muka wuce asibiti gwajin farko da akayi mai sakamakon ya fito suka ce jinin sa ya hau sosai, ya rage damuwa. Nan suka rubuta mana magani kafin mu baro cikin asibitin sai da muka siyi magani, sannan muka dawo gida a gajiye.

Na mayar da hankali na sosai akan baba na ina dafa mai duk abinda aka lisafo man, na kiyayye kuma shima muna k’ok’ari sosai, damuwa ce kawai yanzu ta rage kuma yak’i dainawa, yau ciwon cikin dare ya tasar mai duk inda tashin hankali yake na shige sa, haka na saka shi a gaba ina ta kuka, cikin kukan nake fad’in” Baba yanzu baza ka iya cire wannan damuwar dake ranka ba? kafi kowa sani kana da matsala.. yanzu kai ma inka tafi ka barni ina zanje? wa zan na gani zuciya tayi sanyi? dan Allah Baba kar ka mutu ka barni kaima zuciyata zata fashe nima zan biyo ku ne, domin rayuwata ta tashi a aiki.”

Cikin azabar ciwo ya dubi ne atsanake murya can kasan mak’oshi, yace” kul Mama na! kar na sake jin kinyi irin wanna furucin, dama ita rayuwa ai haka take yau in mune gobe ba mu bane, ko da ace na mutu a yanzu ki k’asance me hak’uri da  juriya, Allah yana son bawan sa me hak’uri, ki k’asance me rama Alkhairi ga sharri, ki rik’e mutunciki kin ji..domin a yanzu shine abin d’ogaron ki, ko da wasa karki aikata abinda Allah zaiyi fushi dake duk ko irin rayuwar da zaki shiga, a  k’ark’ashin duk wanda  zaki tsinci kan ki, ina so ki k’asance me biyayya, tabbas zakiyi nasara, Mama na Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari, ya kare ki da karewar sa, bana so ki sawa kan ki damuwa kin ji! kiyi karatunki da kyau wata rana zaki zama wani abu…”  Haka baba na yayi tai min nasiha me ratsa jiki, tun ina kuka har nayi shiru jikina yayi sanyi ‘kalau.

Bayan k’wana biyu kamar ko yaushe kawu na ya kawo min ziyara, yazo ya tarar ina fama da jinyar Baba na, sosai ya tausaya min, shi ya zauna damu har na tsahon sati guda, ranar juma’a bayan su dawo daga  masallaci, kawuna shirin tafiya Allah yayi ma Baba na rasuwa.

*****

Mutuwa kenan me raba d’a da mahaifi, me shiga tsakanin masoya, na shiga tashin hankali sosai naga rayuwa, nayi rashin lafiya kamar bazan tashi ba, na sha jinya a  asibiti sosai, lokacin da aka sallamo ni na tare kawu na da Anty su had’e min kaya na waje guda, ko basu fad’a min na san inda zanje aiko na sha kuka kamar zan mutu, ina ji ina gani suka taho dani garin Kano,  na sha lallab’a da tarairaya a wajen Anty da kawu, a haka har na samu sati daya inda ya nema min makaranta, cikin sa’a kuma makarantar mu d’aya da Aysha k’awa ta a kano, naji dadi sosai lokacin da muka had’u da ita, na fara zuwa sannu a hankali na fara gane wasu abubuwa, damuwa ta tana raguwa sabida Aysha da NAFEESAT suna d’ibe min kewa, Nafeesa y’ar masu kud’i ce sosai, ban san dalilin da yasa iyayen ta suka saka ta a makarantar mu ba, domin makaranta ce ta kowa da kowa, kana dashi ko baka dashi zaka iya zuwa cikin ta tana da sauki sosai.

Kawu na bai koma wajen aikin sa ba sai da ya tabbatar na samu nutsuwa a sannan ne shima ya koma bakin aikin sa, zuciyarsa na waje na, shi kad’ai ne ya rad’a min suna sanyin idaniya ta.

A hankali Anty ta fara gwada min halin ta, sannu sannu ta shiga k’untata min a b’oye, ta yanda ko yaran ta baza su fahimta ba, ni kad’ai na san azabar da nake ci a wajen ta bata fasa yawon ta, haka aikin gida ya dawo kai na gaba d’aya nice kula da yara kula da gida wankin kayan su, wanke-wanke shara, girki, komai na gida nan ni nakeyin sa, zuwa lokacin mun shak’u da Aysha sosai, duk wani hali da zan shiga ta sani idan Anty ta fice ita ke zuwa ta tayani hira, muyi aiki tare irin sha’kuwar da mukayi da ita yasa hatta yan gidan su sun sani.

Aysha su biyu ne a wajen iyayen su, ita ce auta sai yayan ta me tsananin k’aunar ta jameelu, zan iya cewa tunda nake ban tab’a gani yan uwan juna kamar su ba, abin na bani sha’awa sosai musamma in naga yanda yake mata a hankali suka fara jana cikin rayuwar su har na shige cikin ta tsumd’um, mama ta zamo tamkar uwa ta, abinda zatayi wa Aysha shi take min, basu da wani hali domin ko abincin da zasu ci wani lokaci sai jameelu yaje ya dawo zai kawo a dafa ko Baba, haka suke rayuwar su gwanin ban sha’awa.

*****

Like, comment and share.

Mrs Abubakar ce

<< Waye Zabin Munibat? 3Waye Zabin Munibat? 5 >>

1 thought on “Waye Zabin Munibat? 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×