Bismllahir Rahmanir Rahim
Cikin d’acin rai ta fito banyi aune ba sai ganin ta nayi a tsaye akai na.
Cike da tsoro na ja da baya, ina ta raba ido, muryar ta a hautsine tace” menene kike buga min k’ofar da sassafe?”
Take jikina ya d’auki rawa cike da tsoro nace” zan wuce ne shine nake so na fad’a miki in bazaki sa mu damar zuwa ba ki bani na kai…” cikin ladabi nayi maganar.
Kawai sai ta shiga tafa hannuwa tana rik’e baki, can tace” lallai yarinyar nan, yanzu tsabar rashin kunyar ki har kin san ki kalle cikin ido na kice wai na baki kud’in ki in bazan je ba, ehh lallai nayi sake da yawa to kije ki turo duk uban da ya tsaya miki, kud’i ne na ciye bazan bayar ba, naga me k’watar miki fitsarariya.
Na fashe da kuka ina zubewa gaban ta cikin magiya nace” Anty kiyi wa Allah dan zattin sa, ba dan ni ba ki taimake ni ki biya min kud’in makarantar nan wallahi in ban kai yau ba kora ta za’ayi, ni kuma bana son duk abinda zan tab’a min karatu na…”
“Makira uwar makiraru, ni zakiyi wa ‘kalar tausayi wallahi in baki b’ace min a gani ba sai na illata ki a nan wajen munafika.” Ta juya zata shige d’aki.
Nayi maza na kamo hannu ta ina kuka nace” Anty karki manta ni marainiya ce, bani da wanda suka fiye min ku a duniya a yanzu in baku bani wazai bani ina zan kama?, karatun nan dashi na dogara kuma shine burin rayuwa ta, dan girman Allah da mazan sa, ki taimake ni kar na rasa dama ta Anty nima naga ‘yar ki ce fa!”
K’wace hannu ta tayi da sauri tana aika min da wani mugun kallo, da dukan alamu maganar dana fad’a ta tab’a mata zuciya, kawai sai ta shige d’aki ta barni zaune a tsakar gida, ina ta faman kuka ni kad’ai.”
A ranar duk wannan d’au kin da nake banje makarantar ba wuni nayi ina aikin kuka, yau bata je ko ina ba ita ma haka kuma bata sakani aiki ba, duk wani abu da nake na aikin gida ita tayi kayan ta, tanayi tana ‘yan wak’e-waken ta, gani kukan bazai k’areni da komai ba sai da na bari lokacin tashimu a makaranta yayi sai na fice na wuce gidan su Aysha a waje mu ka had’u da ita, cikin b’ata fuska tace” yanzu nake shirin shigowa naji dalili k’in zuwan ki, me ya hanaki zuwa makaranta? ko dan kinga yau kowa da Baban shi zaije ko Yayan sa, shine kike makyale a gida..” ta fad’a tana aika min da harara.
Take naji wasu sababin hawaye suna bin k’uncin na, nayi saurin gogewa ina cewa” nima yanzu haka da kika gani gidan ku zanje.”
“Ok to mu k’arasa mana.”
*****
Mun gaisa da Mama da Ya jameelu, inda yanke ta tsokana ta da cewa” ‘yar farar k’anwa ta, yau kuma a nan aka yada zango?”
Gaskiya ina jin kunyar sa sosai nayi kasa da kai na ina wasa da yatsun hannu na, cike da kunya.
Mama tace” zaka fara ko? ka bar min yarinya ta huta d’aga dawowar ta zaka sakota a gaba..” ta fad’a cike da wasa.
D’akin muka shige ina ta sunna kan kasa, Aysha tana dariya take cire kayan ta take cewa” malam wai me ya hanaki zuwa makaranta yau.”
“Humm Aysha akwai matsala fa..” fasa cire wandan tayi tazo gaba na ta zauna cikin jimami tace” wace irin matsala me ya faru?.”
“Aysha kin san jiya kawu na ya koma ko?”
Ta ce. “eh na san wannan.”
Nan na kwashe yanda abin ya kasance na fad’a mata, cikin jimami ta ce, “To yanzu shikenan ta cinye kud’in baza ta bayar ba kenan? kuma gara da baki je ba yau dan wallahi anyi kora sosai.”
Nan muka shiga tataunawa da ita, tana bani baki da shawarwari, ko Allah zai sa tayi hak’uri tabani nayi na’am da duk shawarar da ta bani, nan mu kayi salama da ita na koma gida zuciya ta cike da fargaba.
Wasa-wasa sai da nayi k’wana biyu ina rok’on Anty, amma tayi banza dani, naji haushi sosai sai na dai mata aiki nima na koma zaman d’aki wani lokacin nayi kuka sosai musamma in na tuno da iyaye na.
Dadi na ma d’aya Aysha tana zuwa har gida tayi min bayani abinda akayi a makarantar, amma ni wannan ba ya gamsar dani nafi buk’atar naji d’aga bakin malaman.
Lokacin ya ja na dawo zama gida, yaran ta ma yanzu kullum a makare suke zuwa makaranta dama nike shirya su har suje akan lokaci to yanzu na dai na, wani lokaci har hana su shiga akeyi haka zasu dawo gida.
A hankali canza war da nayi ya fara damun Anty, gani shirun da take min bai da amfani, yaran ta zasu rasa karatun su akan sakacin ta, ga aiki da yayi mata yawa a yanzu kawai sa ta shiga cin ubana kafin tace ma na tashi nayi, cikin han zari nake komai, kwatsam sai ta dawo da batun maula duk ran da ban samo ba me rabani da ita sai Allah gashi ta hanin kuka, ga damuwa karatuna da nake ta asara fiye da sati biyu, ga yawo da take aika ni na babu gaira babu dalili, nayi bak’i na lalace Yar kibar nan da nayi gaba d’aya ta kama kan ta, wani lokacin a gidan su Aysha nake yada zango, in Allah ya taimake ni Ya jameelu ya bani in yana dashi wata rana Baba, har Mama ta sha bani dari , dari biyun ina kai wa Anty duk dan a zauna lafiya.
Wannan ba hanani ma’amula da mutane ba musamma Jameelu da mukayi wata irin shak’u dashi, wani lokaci har mamaki yake bani in yana min wani abu, duk kun cin da nake ciki muddin zamu had’u dashi to fa sai ya sani farin ciki sanna muke rabuwa, a na shi b’angaren ba k’aramin so yake min ba amma halin da nake ciki ya hana shi furta min, kullum da tausayi na yake k’wana yake dashi yake tashi.
A yau ne na tashi da masifar anty, domin jiya dana fita ban samo komai ba, bata dake ni ba amma ta hanni abinci.
Da wuri na fita yau din na zagaye ko ina ban samo ba, har yamma tayi min likisi shine na kamo hanyar koma wa gida, na biyo ta bayan layin mu silar had’uwa ta da su Hajiya Daddah suka taimaka min kenan.
Matar Ahaji Abdulazizi ta biyu me suna Nusaiba, macece me hak’uri da sanin ya kama ta, bata da matsala ko kad’ai ko girman kai, ga taimakon na kasa da ita wanna dalilin ne yasa ta samu shiga a wajen Hajiya, kuma har yanzu bata samu haihuwa ba, a can garin Abuja ya ajiye ta, kamar yanda ya zubawa Hajiya Amina masu aiki ita ma haka ya zuba mata.
Hajiya Amina akwai ta da kishin bala’i dalilin da yasa bai had’e su ba kenan, a yanzu kuma Hajiyar sa ta kafa fitina akan sai ya dawo da ita cikin gidan su zauna tare, sam bai so haka ba sabida shi mutune ne me hak’uri da gudun fitina a tsakani iyalin sa, gashi me biyayya bazai iyawa Hajiya gardama ba, a take ya amince mata, tai ta zuba mai albarka.
Lokacin da Mommy taji wannan batun haukacewa tayi a gidan, dan sosai tayi mai bori.
Ya shiga damuwa sosai, amma sai yayi banza da ita, ya cigaba da shirya-shiryan dawowar matar sa kusa dashi.
*****
Like, comment and share.
Sannan ku biyo ni a babi na bakwai don ci gaban labarin.
Mrs Abubakar ce