Bismillahi Rahmani Rahim
Bayan kwana biyu abubuwa dama sun faru ciki har da ƙarin sauyawar Kawu na, ina ƙoƙari sosai wajen gani ya fahimce ni, naje wajen sa sau babu adadi akan ya yaffe mun amma ko kallon arziki ban ishe shi ba.
Laraba
Yau ne na tashi da wani irin ciwon kai mai tsananin, har bana gane wanda ke gaba na, sosai ciwo ke nuƙur-ƙusata cikin wahaltuwa na rarafo na fito tsakar gidan, cikin marainiyar murya nace, "Anty!! Anty! Zan mutu! Ki taimake ni Anty, kai na!" Na ƙarke maganar. . .