Skip to content

Waye Zabin Munibat? | Babi Na Biyu

5
(1)

<< Previous

Bismillahir Rahmanir Rahim

Washe gari da sasafe, sai ga Aysha ta shigo gidan mu fuskar ta cike murmushi, lokaci ina d’urk’ushe a gidin murho ina fama da itace yak’i kamawa, cikin murna na taso hannun ta na kama na jata zuwa bakin zauren gida mu, murya ta k’asa-k’asa nace” lafiya Aysha na ganki a irin wannan lokacin…?” na fad’a ina waigawa baya na tamkar b’arauniya.

Har yanzu murmushin ta bai gushe a kan fuskar ta ba, tace” matsoraciya kawai, zuwa nayi nayi miki albushir Monday in Allah ya kai mu tare zamu koma makaran ta, yanzu nan Mama ta gama gaya min yanda sukayi da Baban mu, yace zaizo ya same Abban ki in anjima.”

Dam gaba na yayi wata irin mumunar fad’uwar, cikin sark’ewar murya nace” me kike ce Aysha? ni dai dan Allah kije kiyi ma Mama bayani muddin Abba ya samu labarin nan wallahi k’ashi na ya bushe a wajen Anty, domin ko bata kasheni ba  zan sha bak’ar azaba, ni dai kawai a maidani makaranta ta ba lallai sai an gaya mai ba, tunda nima ya biya min ita ta hana kud’in har aka gaji aka k’oroni, kin fa san komai Aysha dan Allah kije kiyi musu bayani bana so na sake shiga matsala a yanzu, Abba ko sati bazai k’ara a cikin garin nan ba zai wuce zata iya komai inta ga babu idon sa…” na kai k’arshen zance hawaye na bin k’uncina.

Aysha ta b’ata fuska tana turo baki gaba kamar yanda muka saba tace” kin gani ko? ni matsala ta dake kenan d’an k’aramin abu sai ki kama mai kuka, kwantar da hankalin ki haka ma baza ta faru, na san Baba sare zanyi mai bayani da kai na kuma zai fuskace ni, amma dole Mama zata zo tayi ma Anty wayo kin ji…” ta fad’a tana share min k’wallar.

A haka muka rabu da ita zuciyoyin mu cike da murna, b’angare d’aya kuma cike da tsoron Anty, wajen aiki na na koma cikin sa’a kuma sai naga wutar ta kama,  d’akin mu na wuce na fara tashin yaran d’aga barci mu hud’u ne d’aya ne na miji a cikin mu, kuma yaro ne sosai dan ko  shekara biyar bai gama rufawa ba, cikin sa’a na fara da Bishira kayan ta na tub’e mata duk tana ta magagin barci a haka na fito da ita tsakar gidan lokacin ruwan yayi zafi, wanka nayi mata cikin sauri sabida sanyi da ake, ina gamawa da ita sai ga fiddusi ta fito, tana ta turo baki kamar dole a kai na ta tsaya cikin rashin d’a’a tace” malama ni kiyi sauri sanyi nake ji.”

Niko bani da lokacin magana a yanzu dan haka, kamar yanda tace sama-sama nayi mata wanka ta wuce ita abin ta, a haka sai da na wanke su tas sannan nima na d’auki nawa ruwa na shige bayi, bayan na fito na koma ciki, a zaune na same su babu wanda ya shafa mai a cikin su, baya babu wace bazata iya shirya kan ta ba, har ta taimaki dan uwanta, cikin jin haushin su nace” Bishira ke dai kinji kuny’a wallahi yanzu ki shafa man ne bazaki iya ba  har sai kun jira ni nazo wato ga baiwar ku ko?…” na fad’a ina cigaba da aika masu harara, babu wace ta tanka min a cikin su dan sun san bugu zasu sha.

*****

“Yaya wallahi da gaske nake abinda na fad’a maka, d’azu da sasafe naje gidan kuma nayi  sa’a ita kad’ai na samu a waje, shine take fad’a min yanzu taimakon ka nake nema ta yanda Baba zan fahimce ni…” ta fad’a cikin marairaice wa.

“To karki damu ‘yar gatan Yaya zan samu Baba da batun in ya fito a jima duk yanda mu kayi zakiji, haka yayi miki…?” Cikin murna ta d’aga ka sama alamar Eh fuskar ta cike da murna.

*****

Mun shirya tsaf damu, nayi mana abinci muci mun k’oshi, na had’a k’wanun ka da muka b’ata a gaba na saka Bishira ina wankewa tana d’aurayewa, Allah ya taimake ni har maka gama Anty da Abba basu fito ba, na killace musu nasu abin k’arin yanda in sun tashi zasu same shi da zafi, litattafe na boko na d’auko na shiga duba cikin farin ciki, k’anne na suka koma barci  inda Bishira ta tasani a gaba kamar video tana kallo na, gajiya nayi da kallo na d’ago fuska a had’e nace” ke bana so mugun kallo fa! tashi kije ki kwanta kema.” na fad’a ina zare mata ido.

Murmushi tayi kana tace, “Anty Muni, gaskiya ke kyakykyawa ce har kin mafi Anty Aysha kyau, kinga kina magana k’umatunki na lotsawa, me yasa Umma mu take ce miki me kama da aljanu?”

Ni dariya ma ta bani, na dake jin furicin ta na k’arshe sai na had’e fuska nace” ina wasa dake ne? wuce ki kwanta…”  ina zare nata ido, ba musu ta kwanta amma fa  kamar meya haka ta kafeni da ido, bazan iya da rigimar bata sai na juya mata baya, cikin murya ta tace” nima in na k’ara girma na kamoki a tsaye, haka zanyi ma su fiddusi lokacin ma na fiki kyau…” Ta fad’a cike da jin haushi na.

Dariyace ta sub’uce min a lokacin da ban shirya ba, na ci gaba da abinda nake ban juyo ba, ita ko ta cigaba da k’unk’unen.

*****

“Momy wallahi yau Daddah ta mugun b’ata min rai, fisabililahi sai tana jijib’o mutanen da bata sani ba, wai lallai sai an taimaka musu, baki ga wata bagidajiyar yarinya ba d’azu a bakin get wai taimako tazo nema, kallo d’aya nayi mata nagane karya take domin babu alamar wahala a tare da ita, tsabar iya karya da maula.” ya fad’a yana sakin tsaki muryar nan tashi a sanyaye.

Murmushi tayi tana gyara zaman ta cikin manyace da nuna ita wata ce tace” Hajiya rigima, ni dai har kullum bazan gaji da fad’a muku, ita mahaifiyar Baban kuce bana so kuna sab’a mata, ku kasance masu biyayya a gare ta, in ba haka ba kuma ai ka san sauran, a cikin ku Big man, ne kawai ya iya mata ni da kuyi k’ok’ari faran ta mata ko zata fahimceni a nan gaba.”  Ta fad’a cikin sadukarwa.

AN’NUWAR ya shagwab’a fuska cikin sakalci yace.” to Mommy ya zanyi mata dan Allah? ni bana son talaka ko kad’ai haka bana fatan ko da wasa wata rana numfashi na dana su ya gauraya waje guda, amma Daddah bata ganewa kullum cikin jayo mana su take.”

Babu k’wab’a ko harara sai zallar murmushin jin dadi da tayi mai kana tace” yaro na ka k’ara hak’uri lokaci kawai nake jira daddyn ku ya amince mu bar k’asar nan ma gaba d’aya mu huta, haka yayi maka?”

Cikin jin dadi yace” sosai Mommy da bazan tab’a gajiya da fad’a miki kalamar nan ba Love you sweet Mommy…” Ya fad’a yana manna mata kissing a k’umatu.

****

“Daddah yaushe za muje k’auyen ne?” Ta fad’a a shagwab’ance.

Cikin jin dadi Daddah ta dubi ta tace” kwantar da hankalin ki tak’wara ta yaron nan kawai nake jira ya dawo, gaba d’ayan ku za muje da ku babu wanda zamu bari a gidan, har wan can bahon yayan naki…” Ta fad’a tana yatsina fuska kamar ta ga k’ashi.

Auta ta gyara kwanciyar ta akan cinyar k’ak’ar ta tace, “Wai Ya AN’NUWAR?”

“Eh shi fa d’azu ba kiga yanda ya kusa taka wata k’aramar yarinya da mota ba, sabida kawai ya bata sadaka kud’in da baika ya kayo ba, tswww…” Ta saki tsaki d’aga k’arshe.

“Daddah kin san Addu’ar da nake mai kullum? fatana Allah yasa in ya tashi aure ya rasa mata a cikin masu kud’in da yake maradi, ya samu irin yar talakawar nan usil dinnan naga ta tsiyar shi.”

Dariya tayi har da tafa hannuwa cikin jin dadi tace” Ameen tak’wara ta autar daddyn ta, Allah ya baki miji na gari.”

Haka ya shigo ya same su fuskokin su cike da an’nuri waje ya samu ya zauna yana kallon su, fuskar nan tashi kamar kullum yace” My tsohowa sannu da hutawa wace wainar ake toyawa ne nima ayi dani.”

Da sauri Auta ta mik’e zaune cikin girmamawa tace” sannu da zuwa Big man, ya hany’a da karatu.” 

Cikin kulawa yace, “Alhamdulillahi ya naki karatun? ina Yayin ki? Da Mommy nagan ku kad’ai a nan…?”  Ya fad’a yana kama hannun ta.

Cikin sakalci tace, “Ai ka san Mommy da Yaya AN’NUWAR basa zama a nan suna can shashinta, aboki na kuma ya fita bai dawo ba.”

Murmushi yayi cikin jin dadi yace” lallai ko ki shirya bugu idan ya dawo sai na gaya mai wai aboki kike ce mai..” ya fad’a cikin zolaya.

Aiko ta narke fuska zata fasa ihu tace, “Daddah kin gan shi ko?”

Daddah tayi dariyar su irin ta manya tace” yaron nan bana san tada zaune tsaye, tashi maza kaje karka hargitsi min gida d’aga zuwan ka.”

Yana dariyar sa cikin k’asaita ya mik’e ya fice, dan zuwan shi kenan ya wuto wajen ta.

Kamar yanda na fad’awa Aysha haka akayi Baba bai gaya wa kowa ba, yaje ya biya min kud’in makaranta, ya siya min sababin litattafe da biro, ga sabon takalmin na da aka siyo min duk a cikin kud’i na, da baiwar Allahn nan ta bani lokacin dana ga kayan har da kukan dadi nayi, inda na shiga zumud’i da mararin Monday tayi na koma makaranta, dan gaskiya ak’wai ni da son karatu.

Lokacin da Mama ta samu Anty da maganar makaranta ta babu kunya ba tsoran Allah tace” dama Abban su ne bai ba da kud’in nawa ba, lokacin bai dashi amma tunda suyi ta gode sosai, da yake tafi kowa iya makirci har gida taje ta sake musu godiya, mamakin ta da alajab’in ta ya sake kama su Mama inda Baba ya fara tunanin ko dai sharri nake mata.”

Wannan kenan.

Wacece Munibbat?

Su waye Aysha da iyayen ta?

Menene matsayin Anty a wajen Munibbat?

Waye an’nuwar da mommyn sa?

Ya sunan wannan big man din ne shin shima baya k’aunar talakawan ne kamar dan uwan sa?

Ina iyayen Munibbat ne?

Mrs Abubakar ce

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×