Skip to content
Part 10 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Washegari, Juma’a. Titin Barikin Sarki, Hadejia Emirates.

Da misalin 10:00am.

Ga duk wanda yasan bayan tsohuwar firsin, daidan kan titin bariki yasan cewa wajen zaman ƴan cacane, mutane masu shekaru harda waɗanda suka fara furfura ne ke zaune a wajen ana calander, ga kuma masu buga karta, sai hayaniya suke ga warin sigari na tashi a wajen dan ɗaiɗaiku ne basa busa hayaƙin a wajen, cikin masu busa hayaƙin harda Tijjani Direba ne.

“Tijjani ba ni kuɗina!”

A hankali Tijjani ya ɗago da kansa ya kalli Wasila, ƴar daba da ta kai sa’ar yarsa ta biyu a haife ba, amma kalli yanda take wani ƙifi-ƙifi da ido dan tsabar rashin kunya, kuma babu wani baba gatsal ta kira sunansa.

“Haba ƴar wasil-wasil, kinsan idan na sam…”

“Wallahi ba ka isa ba, kuɗina zaka bani yanzu”

Ta katse shi tun kafin ya ƙarasa maganar, Tijjani ya miƙe ya shiga bata haƙuri, harde ya samu ya kashe bakinta da nera ɗari ta haƙuri ta koma rumfar da take saida abincinta tana aiko masa harara.

Kafin ya zauna wata mota tazo tayi parking a daidai inda suka, gaba ɗayan su suka bi motar da kallo, dogarai suka ga sun fito daga motar har su Uku, gaba ɗaya kowa ya miƙe yana kwasar gaisuwa, dan da gani babu tambaya kasan cewa daga fada suke

“Waye Tijjani anan?”

Wani dogari ya tambaya cikin wata garjejiyar murya, cikin Tijjani ya tsure ƴan hanjinsa suka kaɗa, kadafa ace sarki ya yiwa laifi.

“Gashi nan”

Muryar Lautai ta fito yana nuna shi, abokin cin mushen nasa, Tijjani yayi tsilli-tsilli da ido yana binsu da kallo.

“Zaka biyo mu muje fada, sarki yana nemanka”

Cikin Tijjani ya ƙara kadawa, har ɗan wani guntun fitsari na suɓuce masa, shiko me zaisa sarki ya nemeshi ?

“Ko baka ji bane! Ance kada mu maka dole, dan haka salin alin ka biyo mu”.

“Lautai bari naje na dawo”.

Tijjani ya faɗi yana kallon su Lautai, suka gyaɗa masa kai, haka Tijjani ya nufi motar, suka buɗe masa gidan baya ya shiga, ɗaya dogarin ma ya shiga ya zauna, ɗaya ya zauna a mazaunin driver ɗaya kuma yana gefen drivern.

Suka tada motar suka miƙi titi ɗoɗar dan daga wajen da suke zaune zuwa fada wani dogon titine ya haɗa, babu ko kwana ɗaya har suka iso ƙofar fada.

*****

Tijjani direba ne durƙushe gaban, Turaki, Ciroma da sarki, dukansu sun kasance ƴaƴan sarkin haɗejia Abubakar Masu na da, kuma sarki Abdullahi shine babba a cikinsu, kaf ƴaƴan sarki abubakar ɗin Tafida da Mairama ne kawai babu a ciki, kasan cewar shi Tafida ya rasu, ita kuma Mairama macace, dan wannan maganar bata mata bace.

Tijjani sai juya maganar da Ciroma ya faɗa masa yake, to tayama akayi suka ga ƴar tasa?, kuma me yasa suke san aurawa ɗansu ita ?, kuma wai a yau, yau ɗin nan fa ?, duk waɗannan tambayoyin kansa yakewa, dan bai isa ya furta musu ba.

“Malam Tijjani ka yi shiru?”

Tijjani ya ƙara gyara zamansa, ya kuma durkusawa kamar zai yi musu sujjada sannan ya furta abinda ya zama sanadin sauyawar rayuwar mutum biyu.

“Shi ke nan Malam Tijjani, ga wasu kuɗaɗe nan, tunda an saka lokacin auren a ƙurarren lokaci sai ayiwa yarinya abinda ya kamata”.

Da rarrafe Tijjani ya isa ga Turaki ya karɓi kuɗin, sannan Ciroma ya faɗa masa daidai lokacin da zaizo masallaci.

Haka ya tashi ya fice suna binsa da kallo.

“Yanzu mai martaba kana ga wannan ita kaɗaice mafita ?”

Mai martaba da tun zuwan Tijjani beyi magana ba sai yanxu ya kalli turaki

“Ita kaɗaice mafita Turaki, ita kaɗaice hanyar da zan iya ceto rayuwar ɗan ɗan uwana”

“Hakane, to yanxu shi Tafida yasan halin da ake ciki ?”.

Tafida Pov.

“Eshaan”, muryar ta fito cikin dariyarta, fiskokinta daya saba gani a kullum sune suke giftawa a hankali, a hankali kuma cikin mabanbantan lokuta. Sai kuma hoton wani lokaci da sam baima san ya auku ba, wata mota ƙirar honda civic ta wancan zamani tana juyawa akan titi, tareda wasu mutum biyu a ciki mace da na miji.

“Eshaan”, ita ce kalma ta ƙarshe da ta fita daga bakin macen, har ranta ya fita daga gangar jikinta. Daga can wani kogo kuma wani mutum ne, kansa duk ya tara gashi ga wani farin gari zane a gaoshinsa da ɗugon ja a tsakiya yana ta watsa wani abu a cikin wutar dake ci a gabansa.

Sai kuma fuskarta ta dawo tana dariya tareda faɗin “Eshaan”.

“Maa!!, Maa!!!”

Sai kuma ya buɗe idonsa, ya kalli inda yake, a cikin ɗakinsa ne na turakar Fulani Khadija, kamar dai kullum mafarkine kamar yanda ya saba, a hankali ya fara ƙoƙarin miƙewa, sai yaji wuyansa ya ƙage, hannu ya kai zai taba wuyan nasa, sai yaga wutar nan, daya saba gani a kullum tana ci a tafin hannunsa, hannun ya dunƙule sannan ya buɗe nan take wutar ta b’ace k’arasa miƙewa yayi, dan yashe yake a tsakar ɗakin, yabi ɗakin da kallo.

Gabaɗaya yau ɗakin a hargitse yake, wasu kayan ma sun farfashe, mikewa tsaye yayi sannan ya ɗaga hannayensa ya shiga mai da kayansu da suka faɗo ma ajinsu kuma ba tareda ya ta6a komai a cikinsu ba, yana amfani da ƙarfinsa ne, har ya maida komai inda yake sannan yaje gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa, sumar kansa duka ta sauƙo kan goshinsa ta barbaje, gabrigar jikinsa duk ta faffarke, ga raunikan dake jikinsa, hannu ya kai ya cire rigar, a hankali ya lumshe idonsa, gaba ɗaya raunukan dake jikinsa suka fara haɗewa da kansu, kamar bai taba rauniba, sai kuma ya buɗe idonsa, wani abun mamaki yau idonsa beyi ja ba yana nan a blue ɗinsa.

Banɗaki ya shiga yayi wanka haɗi da alwala ya fito yayi sallah sannan ya samu ya sauya kaya, yau juma’a kuma yau za’a ɗaura aure, dan haka ya saka wata farar shadda ƙal, kuma sabuwace dan bai ta6a sakawa ba, ya kawo falmara zabuni maroon color ya ɗora rigar an mata aiki da milk ɗin zare, ya saka hula dara itama maroon, ya saka wani farin takalmi halp cover, ya fito a ainahinsa na jinin sarauta, ya feshi jikinsa da turare, ya tsaya yana kallon kansa, kamar shine angon, sai kuma yaji gabansa ya faɗi, amma me yasa ?, kai ba wannan zancen, wani bangare na zuciyarsa ya ayyana ma sa, ya ɗaura digital watch ɗinsa sannan ya ɗauki wayoyinsa ya fita.

A parlo na biyu ya iske Fulani tana tsaye tana bada umarnin yanda za’a gyara mata parlon, sai kace itace take auren ƴar ba Fulani sadiya ba, ya ayyana hakan a ransa, ƙarasawa yayi ya gaisheta ta amsa tana masa ya jiki, dan Nadra ta faɗa mata komai.

“Baki za ki yi ne?”

“Ba biki muke a gidan ba?”

Ya gyaɗa kansa a hankali.

“Hakane”

Ta ɗan juyo tana kallonsa, a kullum Tafida ƙara girma yake haɗi da kyau, ga wani kwarjini da yake ƙarawa sai ai kuma a bayan wannan kyan, girman da kwarjinin akwai wata fuska, fuskar da babu wanda ya santa sai makusantasa, idanta ne ya kai kan wani rauni dake gefen kansa.

“Akwai rauni a gefen kan ka”

Ta faɗi a hankali kamar ba ita tayi maganar ba, kuma yaji ɗin, dan a zuciya ne kawai mutum zeyi magana in har kana kusa da shi bai ji ba, a hankali ya lumshe idonsa, nan take raunin ya haɗe jikinsa, kamar wajen bai taba fashewa ba, dama haka yake inde har yaji rauni lokacin da baƙin ruhin ke jikinsa to da zarar ya dawo hayyacinsa yana haɗewa inde har rauni bai haɗe ba a jikinsa to ainahin jikinsa ne yaji raunin.

“Ina zaka je baka ci abinci ba? ”

“Asibiti, zanci a can”

Ta gyaɗa kanta…

“Kada ka makara saboda ɗaurin auren da za ayi”

Bai san dalili ba, amma tana maganar auren gabansa ya faɗi, hakan yasa ya ɗigawa maganar auren ayar tambaya amma sai ya gyaɗa mata kai, ya kaɗa kai ya fice bayin dake wajen sai gaisheshi suke yana amsawa.

Kamar yadda ya faɗi ɗin asibitin ya tafi yaje sukayi abinda za suyi shida Muktar sannan suka haɗu gaba ɗaya suka wuce babban masallacin juma’a na garin haɗejia, dan duka ƴaƴan sarki a nan ake ɗaura musu aure.

Tsabar cikar da masallacin yayi kwata-kwata basu samu damar shiga ciki ba, a waje suka samu, can kusa da tsohuwar kotu a nan sukayi sallar juma’ar tasu kafin aka sannar da cewa za’a ɗaura auren, sai suka koma kan motocinsu, suna ɗan hira shida Muktar jifa-jifa samari na wucewa suna miƙo gaisuwa, dan Tafida akwaI farin jini matasa.

An ɗaura aure na farko, wanda ya kasance shine auren Amina Abdullahi Abubakar da angonta Adam Isma’il, su Tafida sun samu sunji sanarwar ɗaurin auren ta hanyar lasifikokin dake manne a kowani b’angare na titin masallacin.

Sai kuma akace akwai wani na gaba, kowa ya kasa kunne yana jiran yaji wani aure za’a ɗaura.

Sunan da aka sanar shine ya saka kowa a shock, an ɗaura auren Eshaan Auwal Tafida da amaryarsa Maryam Tijjani Muhammad.

Damm!, gaban Tafida ya faɗi, a hankali ya sauƙo daga kan motar da yake, wasu abubuwa na masa yawo a akai, shifa kansa ya kulle, kamar ma baya ji da kyau, kuma kamar ya kurmance, aure ?, wai aure aka ɗaura masa ?, to waima da wa aka ɗura masa auren ?.

Maryam Pov.

Yau suka tashi da abun mamaki, dan da wajejen ƙarfe sha ɗaya saiga Abba ya dawo, yazo yana ta wata fara’a da suka kasa gane mata, yau rabonsa da kwana a gidan wajen kwana huɗu kenan.

Ya shiga ɗakinsa ya ɗauko kaya yayi wanka ya saka kayan daya sama ɗin rabonsa da ya saka su tun auren Fati, farar shaddace hadda babbar riga (malum-malum), Maanmu da Maryam dai kawai binsa suke da kallo har ya gama ya fice. Har maanmu na zaton kode aure zai ƙara to in ba baka b me zaisa yana wannan abubuwan ?.

Bayan fitarsa sai ga Hassan da Hussain sun dawo tareda Muhsin ɗin da suka kaɗo shi a waje yana wasa, suma shiryawa sukayi har Maanmu na basu labarin Abbansu yazo ya fita, suma shirin zuwa masallacin juma’a su kayi, kasan cewar babu nisa sosai daga unguwarsu zuwa masallacin fada, domin titine kawai ya taba fadar da masallacin.

Bayan an sauƙo daga masallaci Maryam na alwalal sallar azhar, yayin da Maanmu ke zaune a rumfar gidan nasu tanajin radio, dan ana rahotone na musanman akan bikin ƴar me martaba, Maryam ta gama alwalar ta zo zata shiga ɗaki Maanmu ta tambayeta ƙarfe nawa, ta tsaya ta ɗauki wayar tata akan window tana faɗo mata lokacin sai wani magana da ake a radio ya ɗauki hankalinta, dan haka tayi shuru tana saurare.

“Bayan an ɗaura auren gimbiya Amina da angonta Adam sai kuma aka ɗaura wani aure me ban mamaki, saurayin da ƴan matan haɗejia ke ribibi, samarin haɗejia ke ƙaunarsa an ɗaura masa aure a yau ɗin nan bayan na ƴar uwarsa, a da mutane suna tunanin auren ɗaya za’a ɗaura amma kuma sai gashi an ɗaura biyu, haƙiƙa wannan aure ya bawa mutane da yawa mamaki, wannan aure de ba kowani aure bane face auren Eshaan Auwal Tafida, wanda akafi sani da Tafida, ɗa a wajen tsohon Tafidan Hadejia, da amaryarsa Maryam Tijjani Muhammad, ƴa a wajen Tijjani driver…

Iyaka abinda ta iya tsinkayi kenan, wayar hannunta ta sub’uce ta faɗo a dandaryar ƙasa, sabon screen gard ɗin da Hassan ya sako mata ya fashe har screen din wayar ma.

<< Yadda Kaddara Ta So 9Yadda Kaddara Ta So 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×