Skip to content
Part 11 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Bayan Shuɗewar Awa ɗaya.

Malam Tijjani yayi sallama a ƙofar gidansa, kuma ba tareda ya jira an amsa masa ba ya sa kai. Da kallo yabisu ɗaya bayan ɗaya, Maanmu ce sai hassan da hussain da suka zo suka ƙara tabbatar musu da gaskiyar batun ɗaurin auren.

Maanmu ta ɗaga kai ta kalleshi, hannunsa riƙe da huhun goro da kwalin alawa a kai, tunda Maanmu taga haka ta san cewa Shikenan, ta faru ta ƙare. Hawayen da ba ta samu tayi ɗazuba sune suka sulalo mata, alawa da goron ya aje sannan yace.

“Ku shiryata, anjima za’a zo a ɗauketa, kuma gobe zasu wuce lagos”.

“Wai dan Allah malam me kake nema ? Anya ma kuwa kaine ka haifemu?, me yasa zaka siyar mana da ƴar uwar mu ?, dan na tabbatar da siyara mana da ita kayi, dan wannan sunansa kasuwanci ba aure ba, kum…”

“Ya isa Hassan!”

Tsawar da Maanmu ta daka masa ce tasa yayi shiru da maganar da yake, sai aka koma kallon-kallon tsakaninsa da mahaifin nasu, hussain ne ya miƙe shima ya ja hannunsa zuwa ɗakinsu, dan yana ganin hakan itace mafita, dan idan ba hakan yayi ba a yanda hussain yake ji zai iya kaiwa abban nasu duka.

Maanmu ta tsaya tana kallon cikin idon Tijjani.

“Allah Ba azzalumin sarki bane, ka riƙe wannan Tijjani”

Tana kaiwa nan ta shige dakinta, shime rigarsa ya kaɗe ya fice daga cikin gidan, ai yau ganima ta samu.

Maryam da ke zaune a ɗaki itada Anti Fati wadda bayan an ɗaura auren kai tsaye mijinta ya wuce gida ya sanar mata kuma bata jira komai ba ta taho gidan ta rushe da kuka, Anti Fati ta riƙota.

“Maryam wai miye na kukan ?, inde har Tafidan da kowa ya sani ne to bakya bina bashin rantsuwa kan zai kula dake, Tafida ba irin ko wani na miji bane, kawai kiyi haƙuri ki ɗau haka a matsayin Yadda Kaddara Ta So.”

Maryam taja hanci, daga ɗazu zuwa yanzu har idonta yayi ja tsabar kukan da ta sha.

“Anti Fati ba wannan bane abunda ke damuna, taya za’ayi a aura maka mijin da baka sanshi ba?, wanda baka tab’a ganinsa ba, kuma Anti Fati ko kaffara bazanyi ba kan kuɗi suka bawa Abba ya aura musu ni, Anti Fati me yasa Abba zai min haka ? Me yasa ?”

Ta faɗi tana nuna kanta, cikin muryar kuka, sai kuma ta share hawayen dake zubo mata.

“Anti Fati kinsan de yadda gidan sarauta yake, yanzu daga na shiga gidan ganina zasu dingayi da wannan tabon da Abba yayi min, zasu dinga min kallo ƙasƙanci, above all ƴan matan dake Haɗejia sai ni?, Anti Fati why me ?, why ?, shikenan rayuwata ta zo ƙarshe anti fati, garinma zan bari zan bar kowa nawa na bar karatuna na barku, mutafi can ta yanda zaiji daɗin min gori”

Anti Fati ta rungume ƙanwar tata, ta san Maryam kamar yunwar cikinta, Maryam tanada haƙuri da kuma b’oye abinda ke ranta, tunda kuwa take faɗin hakan lalle abin ya kai ta ƙarshe.

“Ina imanin ki ya tafi Maryam ?, kiyi haƙuri ki ɗau hakan a matsayin ƙaddara…”

Guɗarn Badarce ta tsayar da Anti Fati daga ban bakin da take ma Maryam ɗin, ta shigo ɗakin sai wani fara’a take kamar itace amaryar.

“Iskanci, miye na wani kuka ?, ai ƙawata farin ciki zakiyi ba kuka ba, Tafida ?, hmmm Tafida fa kika aura Maryam”

Ta ƙarasa shigowa ɗakin tana wannan batu, batun da ya ƙara karyar da zuciyar Maryam ta fashe da wani sabon kuka, hakan yasa Badar ta fuskanci cewa abun ba na wasa bane, dan haka ta zauna itama aka ɗora sabon shafin rarrashin da ita.

Kan kace kwabo har gidan ya cika da ƴan uwan Maanmu dana Abba, Anti Fati ce ta saka Badar ta tsefe mata kai, ira kuma ta mata kitso, zuwa lokacin ta dai na kuka dan taga koma me zatayi ba fasa auren za’ayi ba, tunda an riga an ɗaura, wai itace ta auri Tafida, abun ya tsaya mata a rai. Gaba ɗaya ta rasa takamemen tunanin da za tayi.

Hadejia Emirates.

“Wai Tafida yayi aure ?”

Muryar Fulani ta fito cikin wani irin nishaɗi da bazaka iya musaltawa ba, ƴaƴanta ne biyu zaune a gabanta cikin dakinta da babu wanda yake shiga sai ita da yaran nata, Galadima da Maimun, Galadima yayi murmushi.

“Ai ni abun ya min daɗi, duk irin wannan so da ƙauna da ake nuna masa amma haka akayi aurensa lami”

“To ni so nakema na san dalilin yin auren” cewar Maimun

“Zai wuce so suke su halaka ƴar mutane, yau in ba haka ba sa aura mata Dodo”

Gaba ɗayansu suka saka dariya, Fulani Sadiya tana cikin farin ciki domin yau an ɗaura auren ƴarta ga kuma maƙiyin ɗanta anyi masa aure irin wanda ba kowani ɗan sarauta za’ayiwa ba.

A daidai wannan lokacin da suke wannan dariyar a wani b’angare na fadar, Tafida ne zaune a ƙasan lallausan carpet ɗin dake falon Me Martaba, wanda yake ganawa da iyalansa, a zaune akan kujera kuma Sarki ne, da Turaki, Ciroma da kuma Mairama sai Fulani Khadija.

“Eshaan”

Ciroma ya kira sunansa, chikakken sunansa, a hankali ya ɗago da kansa ya kalli iyayen nasa, sannan ya amsa.

“Na’am”

Gaba ɗaya ya sauya a cikin yinin nan kawai, ya cire zabunin dake jikinsa ɗazu, kansa babu hula gaba ɗaya gashin kansa ya sauƙo ya baje a goshinsa dan har ya rufe girarsa sai idonsa kawai ake gani.

“Munsan cewa mun isa da kai, shiyasa ma muka yanke wannan hukuncin ba tareda munji ra’ayinka ba, munsan cewa kanada hankali da kuma biyyaya, munsan cewa kai ba kamar ɗan uwanka Habibu kake ba, kana mana biyyaya a koda wani lokaci, bamu tab’a aje kara munce kada ka tsallaka ka tsallaka ba, kana binmu sauda ƙafa, to dan hakama a wannan karon muna so kayi mana biyyaya kamar yanda ka saba, muna so ka kakarb’i auren nan hannu bibbiyu, ka riƙe yarinyar nan da amana, munsan ka san cewa aure ba abun wasa bane, inshaallah idan kayi biyyaya a gaba sai kayi alfahari da wannan auren, ka ɗauki wannan auren a matsayin YADDA ƘADDARA TA SO ”.

A lokacin shi kaɗai yasan abinda yake ji, sam ya kasa wani tunani me kyau, ya rasa a wani matsayi zai saka wannan auren.

“Inshaallah zaku sameni a matsayin me bin umarninku kamar yanda na saba”.

Masomin kaddarar kenan, Daga haka aka soma.

*Da misalin 09:00pm*

Tafida ne zaune a parlon gidansa, tunanuka barkatai a kansa, shi ya rasa inda kansa yake, baya gane komai tun bayan da amace an daura musa aure.

“Me yasa baka san auren nan ?”

Muryar Muktar ta tambaya, wanda yake zaune a gefensa, Tafida ya gyara zamansa, tareda kai hannu ya tura sumar kansa baya, dan yau ta sauƙo masa kan goshi.

“Muktar su Me Martaba sun tafka babban kuskura, ni sam ban cancanci zama da kowa ba, kaɗaici shine abinda ya kamaceni, bai kamata ace ina rayuwa da wani a kusa dani ba, yarinya tana can tana rayuwarta suka rabota da danginta da farin cikinta suka aura mata ni, ni bancanci zama da kowa ba Muktar, sun lalata rayuwar ƴar mutane a banza”.

“A’a Tafida ba haka bane, tunda de har kaga hakan ta faru to tabbas akwai abinda Allah ya hukunta a ciki, kuma Tafida duk wadda ta sameka a matsayin miji itace tayi sa’a ba kai ba”.

Tafida yayi wani bussashen murmushi yana tura sumar kansa baya, sai kuma ya dawo da hannun nasa ya dunƙule ya ɗora a bakinsa.

“Inaso ka nemo min bayanai akan yariyar me suna Maryam ”

“Me yasa ?”

Sai ya ɗago ya kalli Muktar

“A tsarin gidanmu babu saki da na saketa taci gaba da rayuwarta kamar yanda ta saba, amma tunda har hakan ba zata samuba zan yi yanda zanyi na temaki rayuwarta bazan bari wani ya cutu sbd ni ba”.

Maryam Pov.

Zaune take a bakin makeken gadon da aka bata, babu abinda take tunawa sai yanda aka rabota da gida, tana kuka tana komai, wani abu daya tsaya mata a rai shine maganar da sukayi da Maanmu ta ƙarshe.

“Maryam, bance kada kiyiwa mijinki biyyaya ba, kiyi masa biyyaya iyaka bakin iyawarki, ni misalice a wajenki, kinga yanda naci tarin baƙin cikin mahaifinki, kada ki duba sigar da aurenki ya faru kawai kiyiwa mijinki biyyaya, wannan shine kaɗai abinda zan iya faɗa miki”

Sai taji wata sabuwar kwalla na zubo mata, daga wannan magana ta Maanmu wasu manyan mata da aka aiko daga fada wanda suka shiryata cikin alkyabba suka fita da ita daga gidan, suka sakata a cikin mota suka kawota fadar haɗejia, tunda take a rayuwarta bata tab’a shigowa cikin fada ba, dan bataga dalilin da zaisa ta shiga fadar ba, kuma suna kawota ne kaitsaye akayi turakar Fulani da ita, duk da tanajin fadar babu hayaniya sosai alamun ƴan wancan bikin suna gidan dinner, kuma tunda aka kawota bangaren da take ciki kai tsaye wannan ɗakin da take ciki aka kawota, daga ita sai jakar kayanta guda ɗaya, kuma yawancin kayan ciki Anti Fati da Badar ne suka bata shi, dan gaba ɗaya nata cewa sukayi bazata tafi da suba, hijabanta kawai suka bar mata.

Tunda tayi sallar isha har yanzu hawaye bai yanke a idonta ba.

Jin kamar ana motsa kofar ɗakin ne yasa gabanta yayi wata wawuyar yankewa ya faɗi, ta tsirawa kofar ido sai taga Fulani ta shigo, a sirrance ta sauƙe a jiyar zuciya, Fulani na mata murmushi ta ƙaraso har cikin ɗakin tana zama a kusa da ita, Maryam ta zabura zata sauƙa kasa Fulani tayi saurin riƙota tana girgiza mata kai.

“Haba! Haba! Maryam ai yanzu kin zama ƴar gida”

Maryam ta share hawaye tana zama amma a ɗarare ta zauna sai kama jikinta take, zama kusa da matar sarki ai abun azimun ne.

“Maryam, inasan nayi miki magana a matsayina na uwa wadda take fatan samawa ɗanta lafiya, ba a matsayin Fulani Khadija matar sarki ba”

Sai Maryam taji abun banbarkwai, itafa dama tasan cewa dole dai wanna auren na manufa akayi, in ba haka ba taya za’ayi a zab’ota ita ɗaya kaf cikin tarin ƴaƴan masu kuɗi da mulki na garin nan ace sai ita, ita kaɗai, Fulani ta kamo hannayen Maryam.

“Maryam, Tafida ya taso ne cikin wata hautsinnaniyar rayuwa, tun yana yaro ya rasa iyayensa, Raruwarsa gaba ɗaya lillub’e take da wani baƙin duhu, Kuma a yanda aka sanar mana babu me iya kawar da wannan duhun na rayuwarsa sai ke”.

Sai kuma tayi shiru, hawayen da Maryam taga a idonta shi yafi ruɗata fiye da maganganun da ta faɗi.

“Ina me roƙonki Maryam, dan Allah ki temaki ɗana, ki ceto shi daga cikin wannan kogin da yake ciki, Nasan zakimin kallon me san kai, amma ina roƙonki dan Allah….”

Maryam ta shiga girgiza mata kai, ita bakinta ma ya kulle, ta kasa cewa komai, maganganun sunwa ƙwaƙwalwata nauyi. Ta masa fahimtar maganganun nata gaba daya, da kyar ta iya lalubo muryarta.

“Ni ban isa na warkar da kowa ba, Allah shine me waraka, kuma shine me warkar da kowa”.

<< Yadda Kaddara Ta So 10Yadda Kaddara Ta So 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.