Skip to content
Part 12 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Washegari.

Malam Aminu International Airport

Da misalin 10:00am.

Tafida ya fito daga wani shagon snakes, inda ya saba kaiwa ajiyar key kafin Muktar yazo ya karb’a, wasu lokutan ma tare suke tahowa idan ya aje shi sai ya juya da motar, to yau sun taho da wata shi yasa bai biyo shi ba, tun jiyama da sukayi sallama bai ƙara ganinsa ba, kawai de da zasu taho ya kirashi akan zai bayar a aje masa keyn inyaso sai yaje ya karb’i motar.

Inda yasan ya bar Maryam ya dawo, zaune take akan daya daga cikin wasu kujerun dake wajen, ga jakukunansu a kusa da ita, sai yanzu ya samu damar ƙare mata kallo, dan yau da safe da yaje fada sarki ya fara zuwa ya gaisar,sannan yayi masa sallama sai ya fita yaje ya yiwa Fulani sallamar itama, kuma itace tace masa yaje ya jira Maryam ɗin a mota, yana zaune a motar suka ƙaraso ita da Nadra.

Kuma har ta shiga motar bai kalleta ba, gaisuwar da ta masa ma da ƙyar ya samu ya amsa, kuma bai kalleta da kyau ba sai yanzu.

Bata cika fari ba, amma kuma farar ce, bata da wani kyau na tashin hankali, saide bata da muni kyanta daidai ita, kuma bata da jiki duk da abayar dake jikinta tanada faɗi, amma hakan bai hanshi ganin sirirantar ta ba, wani abu dayafi komai kyau game da ita shine idanunta, farare tar, duk da sun ɗanyi ja, alamun tayi kuka, wani irin innocent face gareta, kuma akwai nutsuwa da kamewa a tareda ita, Kuma daga ganinta kasan cewa akwai ƙarancin shekaru a tareda ita, sai yaji tausayinta ya ƙara kamashi.

“Muje ko ?”

A hankali Maryam ta ɗago ta kalleshi, gabanta yayi wata iriyar muguwar faɗuwa, taji kamar tana nitsewa a cikin wani abu, kamar yanda shima bai kalleta ba itama bata kalleshi ba sai yanzu, ta saba jin hirar Tafida a bakin mutane da yawa bata san ashe haka Tafidan yake ba, lalle kuwa Tafida, ai wannan bai dace da wannan sunan na Tafida ba, wannan sunansa Eshaan, dan shine yafi dacewa da shi, ashe duk abunda Badar ke faɗa mata gaskiyane.

Kuma tana kallon fuskar tasa sai maganganun da sukayi da Fulani yau da safe suka faɗo a cikin ƙwaƙwalwarta.

“Maryam, nasan da cewa Allah shine me temakon kowa da komai, amma ke kece sanadiyyar temakon Tafida, akwai wani abu dake damun rayuwarsa da bayasan karatun alqur’ani ko addu’a, nasan cewa ke me ilimice dan haka ki riƙi addu’a, ga wannan qur’an ɗin ki lazimci karantashi a kullum, na tabbatar da Allah zai temakeku, ya kuma baku zaman lafiya, Allah ya miki albarka”

A ɗazun sai ta kar6i qur’an ɗin ta kuma mata godiya, bayan fitar Fulani wata ta shigo wadda ta bayyana mata kanta a matsayin Nadra, ta bata wata brown abaya, kuma itace bayan tayi wanka ta saka dan har yanzu ma itace a jikinta, saida suka fitone taga tarin wasu akwaituna guda shida, Fulani ta sheda mata da kayan aurenta ne da aka mata, a lokacin ma saida tayi hawaye, kuma wasu bayine da Nadra suka rakata har motar da akace Tafida na ciki, suka saka kayan a baya, sannan ita ta shiga motar.

Kuma tun bayan gaishe shi da tayi bata ƙara cewa komai ba, shima kuma baice ɗinba, sannan batayi gigin kallonsa ba har suka iso kano, amma kuma gaba ɗaya a takure take a cikin motar.

Kuma bayan sun zo ne ya saka aka shiga musu da kayansu ciki yace ta zauna ta jirashi yaje ya dawo shine har yanzu yake tsaye a gabanta.

*****

Kamar yadda a mota suka yi tafiyar kurame yanzuma haka ita suke yi, zaune take a gefensa, cikin wani irin kusanci, kusancin ma har yafi na ɗazu, gaba ɗaya sai taji wani iri, ta takura fiye da ɗazu.

A hankali ta ɗan waigo ta kalli fuskarsa, ba ita yake kalloba idonsa na kan wayarsa yana dannawa, ga wani sun glasses wanda yake idonsa tun tahowarsu daga haɗejia, wani abun mamaki ta gani a gefen fuskarsa, ƴar haɗejia ta gani a kusa da sajensa, gefen kunnensa, abun ba ƙaramin mamaki ya bata ba.

Ashe shima yana da ita kamar yadda itama take da? Ai ita tunaninta su basa yin irin wannan abubuwan. Da sauri ta juya ta kalli window domin itace a window seat, wani abu da bata tab’a kawoshi koda a mafarkinta ba, shine hawa jirgi, yau sai gata a cikin jirgi, tana iya hango gajimaren dake ƙasa, abun gwanin ban sha’awa. Hankalinta gaba ɗaya ta maida akan kallon windown, dan yafiye mata alkairi, dan da taci gaba da kallonsa gwara ta kalli windown.

Tunda ta juyo ta kallishi, Tafida ya ankara da ita amma bai ko nuna mata ba, sai kuma wata hira da wasu ƴan mata dake tsallakensu ta dauki hankalinsa.

“Yanzu dan Allah Hafsa idan na samu wannan guy ɗin ban more ba?”

Sai kawai ya motsa kunnensa ta yanda zai samu damar jin abinda suke faɗi da kyau, sai kuma ya tsinto abinda beyi zato ba, wannan bugun zuciyar, bugun zuciyar da yake kwana yake tashi da shi akwana kin nan, wannan bugun zuciyar da yake kwantar masa da hankali ya saka masa nutsuwa.

A hankali ya juya ga inda sautin ke fita, ita ɗince zaune a gefensa gaba ɗaya ta maida hankalinta kan kallon window, iko sai Allah, ashe itace ?, tabbas itace domin sunanta Maryam, amma sam beyi tunanin sake haɗuwa da ita bama, balle har ya sake sauraren bugun zuciyar tata.

“Hello Handsome!”

Maganar ɗaya daga cikin ƴan matan dake tsallaken nasu ta katse masa hanzari, a hankali ya zuyo ya kalleta da idonsa dake cikin sun glasses.

“Ya aka yi?”

Mamaki ya kamata dan ba tayi zaton yanajin hausa ba, ita kallon indian take masa, zuciyar Maryam ta matse a ƙirjinta, itafa shi yasa bata san kyakyawan namiji, yanzu ƴan mata zasuyi caa akansa. Gara taso mummuna duk kuwa muninsa, inde har yana sanya kuma itama tana sansa hakan ya wadatar.

“Ammm… da…dan Allah lambar wayarka zaka bani ”

Amsar da ta fito daga bakinsa ba ƙaramin basu mamaki tayi ba, bama su kaɗai ba, harda Maryam dake zaune a gefensa.

“I am sorry maam, but i am married, kinga matata ma”

Ya ƙarashe yana ɗan kaucewa dan su samu damar ganin Maryam ɗin dake rakub’e a gefensa.

“Oh sorry”

“Never mind”

Maryam ta haɗiye wani abu, ahse har zai iya nunata a waje yace ita matarsa ce ? Kode yayi hakan ne dan ƴan matan su ƙyaleshi ? Itafa tunda ta ɗora idanta akansa wani abu ya zo ya tokare mata maƙoshi.

Tana hango ɗumbun tazarar dake tsakanin ta dashi, sam ko kaɗan basu dace ba, basu dace da juna ba, a da tana neman dalilin da yasa aka aura masa ita, amma bayan maganar da sukayi da Fulani jiya ta samu amsar tambayarta, an aura masa itane sbd itace maganin wani ciwo a rayuwarsa ba dan yana santa ko yana ra’ayinta ba, amma me yasa ?, me yasa rayuwa zata mata haka ?.

Har jirginsu ya sauƙa a lagos Maryam nata saƙe-saƙe a ranta, shi kuma Tafida ya bada himma wajen sauraren bugun zuciyarta ne, shi abun har mamaki yake bashi, ya rasa me yake tsinta a bugun zuciyar tata.

Drivernsa na asibitine yazo ya ɗauke su zuwa ALARO CITY, tunda Maryam tazo duniya gari uku ta taba zuwa bayan Hadejia, daga ƙauyen su Abbansu sai kano sai kuma malam madori da ta tab’a raka Badar wani biki, amma kuma bayan su bata tab’a zuwa ko ina ba.

Ita manyan gine-gine irin wanda take gani a yanzu sai a waya ko a tv, suma ɗin dan ta kasance ma’abociyar kallon finafinan india ne, amma da bazata tab’a sanin akwai kalar wannan abinda take gani ba, kuma irin waɗan nan ɗinma tana ganinsu a tiktok, dan akwai wani a tiktok wanda yake posting kyawawan wurare a nigeria.

Ta tuna yanda suke ta musu itada Badar akan wasu wajejen ba nigeria bace, amma kuma a yau, sai gata a gaban waɗannan manya-manyan gininnikan. Da ace bata san abinda take ba, kuma bata da wayewa da ta zuba ƙauyanci.

Ta lekki link bridge suka wuce, ita batama san akwai ta a nigeria ba, tasan de akwai irinta a mumbai, kuma itama ɗin a waya ko tv take kalla, wato inda ranka ka sha kallo, ta faɗi hakan a ranta.

Mamaki bai cinyeta ba saida suka iso ALARO CITY, wani babban estate me kama da wani garin, a babban symbol ɗin dake manne a saman wajen ta karanta sunan estate ɗin, haka sukayi ta wuce blocks kala-kala, kuma ta lura da kowani block ginin gidajesu iri ɗaya ne.

Maryam taga kamar sun shiga wata duniya ne da ban ba earth ba, abun akwai ban mamaki ga wanda bai taba gani ba, gaba ɗaya tsarin estate ɗin irin ginin ƙasar turai ne.

Block 3, suka shiga, drivern yayi parking a kofar wani gida wanda yake shima gininsa iri ɗaya ne da sauran gidanjen cikin block d’in, ta waya Tafida ya buɗe musu gate ɗin, drivern ya shiga cikin gidan, yayi parking suka fito, ya kalli Maryam.

“Ki shiga ciki”

Ya faɗi cikin wannan muryar tasa me zurfi, da ƙyar maryam ta gyaɗa kai, sannan ta kama hanyar shiga cikin gidan, hannunta riƙe da hand bag ɗinta, hannunta na rawa ta kai ta buɗe kofar gidan, bakinta da sallama ta shiga cikin gidan.

Bazata iya cewa komai ba akan tsaruwar gidan, gidan ya haɗu ta ko wani fanni, shida drivern ne suka shigo ɗauke da jakukunansu, sannan taga sun haura sama, da hannu yayi mata alama da ta biyoshi, haka tabi bayansu har zuwa ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan dake saman, daga inda take tsaye a corridorn ta leƙa ƙasa ta kalli parlon, a ranta tana jinjina girman gidan, shida drivern ne suka fito daga ɗakin da suka shiga sannan yace mata.

“As from today this will be your permanent room”

Her permanent room ? Kenan yana nufin zai zauna da ita har abada ko me ? Itafa ta kasa ganewa, amma sai ta gyaɗa masa kai, ƙasan taga shima yayi yabi bayan drivern yayinda ya bar jakarsa a wajen, batayi gigin tab’a masa ba.

Tasa kai ta shiga ɗakin, Allahu ƙadirun ala man yasha’u, shine abinda Maryam ta ayyana a zuciyarta, bayan da tayi arba da ɗakin, ba wani me girma bane can, amma kuma ya ninka ɗakinta da take kwana na gidansu, gidansu ?, kalmar ta maimaita kanta a ƙwaƙwalwarta, yanzu ita ɗaya zata kwana a wannan katafaren ɗakin ?, ko a wani hali gidan nasu ke ciki ?.

Sai kuma tabi ɗakin da Kallo, komai na cikinsa ja ne da baƙi, babu abinda yafi ɗaukar hankalinta irin kofar balcony ɗin, wadda ta kasance ta glass ce, hand bag dinta ta aje a kan gadon sannan ta taja a hankali zuwa balcony ɗin ta kai hannu ta kawar da curtais ɗin sannan ta zuge kofar glass ɗin, ta taka zuwa balcony ɗin, wata iriyar iska me cike da ni’ima ta bigi ƙofofin hancinta dama na fatarta, kyakyawan garden ɗin gidan dake back yard yayi mata sallama, daga saman da take tana iya hango kyan garden ɗin. Ga wata kujera me kamar lilo a balcony ɗin, sai wasu flower vase masu kyau da aka jera a kasan wurin, wurin ya tafi da imaninta.

<< Yadda Kaddara Ta So 11Yadda Kaddara Ta So 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.