Skip to content
Part 13 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Tunawa da tayi ba tayi sallar magriba da ake ba yasa ta koma cikin ɗakin da sauri, sai kuma ta shiga toilet, duk jikinta a gajiye take jinsa dan haka ta yanke cewar harda wanka zata yi.

A yau ta godewa Allah, social media da novels da take karanatawa, dan badan su ba, ba zata iya tabuka komai ba, a ranta ta tuno da cewar da ace wata daga area ɗinsu aka kawo wannan gidan, wai da anga ƙauyanci, tayi murmushi a bayyane tana buɗe kofar shower stall ɗin.

Wankan tayi sannan ta fito tayi alwala ta maida kayan da ta cire ta fito, jakarta data zo da ita ta buɗe ta ɗauki hijabi ta saka, taji wani daɗi na ratsata, dan tayi kewar hijabinta, abayar ma ta yarda ta saka ta ne sbd tana da faɗi.

Sallar ta gabatar, sannan kamar yadda ta saba ta zauna tayi addu’o’inta ta shafa, sai kuma ta miƙe ta cire hijjabin ta ninke, jakarta ta kuma biɗewa ta ɗauki wata sabuwar dark navy midi prom dress wadda Anti Fatice ta bata, rigar bata da nauyi kuma hannun rigarma ba wani dogo bane.

Ta sakata sannan ta miƙe ta shiga bubbuɗe lokokin data tarar a ɗakin, bata samu komai a ciki ba, har ta buɗe doguwar drawer ɗin dake manne da wani bango, kuma wardrove ɗin yar bangoce, amma kuma kamar closet dan sai kayi taki ɗaya biyu.

Sannan zata tarar da inda zaka jera kaya a cikinta, nan ɗinma babu komai.

Goge lokar da tayi sbd ƴar kurar data gani a ciki, ta dawo kan akwatunanta ta shiga buɗewa, mamaki kawai take da ta’a jibin abinda take gani, gaba ɗaya kayan atamfofine da lesuka kuma duka an ɗiɗɗinka.

Wani abu daya ƙara bata mamaki shine data gwada su a jikinta duka daidai itane, daga tsayin har faɗi, akwati hud’u na tsaddadun kayan sakawa ne ɗinkakku sai abayas, sauran biyun kuma data buɗe ɗaya daga cikinsu takalma ne da jakukuna a ciki, ita kuma ɗayar kayan kwalliyane harda jewelleries.

Maryam ta rasa ma abunyi, data gaji da kallon kayan ta miƙe ta shiga naɗewa tana jerasu a wardrobe ɗin, har ta gama jeresu kaf, takalma da jakukunan kuma gabaɗaya ta jeresu a lokokin kasa, wani ƙaramin flat kawai ta bari a cikinsu wanda zata dinga sakawa na zaman gida, tana shiryasu tana mamakin kayan, ga shi kuma harda gyalulluka, kuma ita ba ma’abkciyar saka gyale bace, duk da gyalullukan na matan aure ne, dan suna da girma sosai, daga can gefe ta jere wanda tazo dasu, har ta gama shirya kayan wardrobe ɗin bata cika ba, kuma batayi mamakin hakan ba, dan wardrobe ɗin ta kusa cinye faɗin bangon da take jiki.

Gaban drassing mirror ta dawo wanda babu komai a kai, ta jere kayan kwalliyar sannan ta dawo ta zauna a bakin gadon ta ɗauko hand bag din data zo da ita ta fito da qur’an ɗin dake ciki ta saka shi a bed side drawer, ta ɗauko wayarta da ear piece ɗinta harda charger ɗinta, sai kawai ta shiga jujjuya wayar a hannunta, gaba ɗaya screen ɗin wayar ya fashe daga sama, duk bata lura da hakan ba sai yau da safe.

Wayar ta kunna taga babu chargy, gashi tana san ƙiran Anti Fati ko Badar, dan a gidansu babu me waya, su Hussain dama basu da waya, dan dokace maanmu ta kafa musu akan bazasu tab’a riƙe waya ba sai sun gama secondary.

Kuma tun kan Anti Fati har zuwa kanta basu riƙe wayar ba sai da suka yi candyn, jiki a sab’ule ta miƙe ta saka wayar a chargy jikin wani socket dake kusa da bed side drawer, bata san lokaci ya ja ba sai da taji ana kiran sallar isha, ta riƙe alwalarta dan haka kawai ta miƙe ta saka hijjabin data cire ɗazu ta gabatar da sallar ishar sannan ta zauna tana addu’o’in ta.

Ƙofa taji an ƙwanƙwasa dan haka tayi saurin shafa addu’ar ta miƙe a hankali ta buɗe kofar gabanta na wani irin bugu, sai de bataga kowa ba, har zata juya ciki idonta ya sauƙa a kan wasu ledoji guda biyu, ta tsugguna ta ɗauka sannan ta me da ƙofar ta rufe.

Tana ta mamaki, duk da tasan dai babu me mata hakan sai shi, shi ɗin da a yanzu yake amsa sunan mijinta, mijinta ?!! Sunan ya maimaita kansa a ranta, shekaran jiya take faɗin cewa batada niyyar yin aure kwana kusa, amma cikin kwana ɗaya komai ya sauya, rayuwarta ta juya up side down, tana kaikawo a kan siraɗin rayuwa.

Ledar farko ta buɗe, kuma tun kafin ta gama buɗe take a way ɗin da taga a ciki ƙamshin wani abu da ɗumin abin ciki ya daki hancinta da fatarta, wani gasashen cat fish ne da kuma fried potatoes tun kafin ta kai abincin bakinta yawunta ya tsinke, ta ɗauko wata roba da itama take cikin ledar ita kuma tun kafin ta buɗe taga abin ciki kasan cewar rober is transparent, wani haɗin cake parfait ne a ciki, maryam ta aje shi shima gefe, ta buɗe ɗayar ledar kuma ita drinks ne a ciki.

Ƙasan carpet ta dawo ta zauna ta baje kayan abincin, sannan ta shiga toilet ta wanko hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin abincin, tabbas tasan ta iya girki, amma kuma bata saba cin irin wannan abincin ba idan har ba Badar ce ta kawo mata girki ba, ko kuma taje gidan Anti Fati ta tayata girki, amma a gidansu babu irin wannan cimakar.

Cikinta ta bawa hakkinsa sosai, dan bata ci abincin ranaba, rabonta da abinci tun na safe data ɗan caccakala, sannan ta rage wanda ta rage ta naɗe shi ta aje sai kuma da safe hannunta ta shiga toilet ta wanke.

Sannan ta ɗauro sabuwar alwala ta dawo ta kwanta akan lallausan gadon da zatace kusan a irinsa ta kwana jiya, duk da bata samu tayi wani baccin arziƙiba jiyan, dan tunani ne fal ranta.

Sai kuma ta kasa baccin, sbd wata sabuwar kewar gida da ta kamata, Allah ya sani tana kewarsu tun jiya, hannu ta kai ta kashe wuta amma kuma sai ta kasa kwanciya sbd wani tsoro daya kamata, dan haka ta kashe wasu ta bar wasu a kunne, tana tasbihi a ranta har bacci yayi gaba da ita.

Hanam Pov.

Tashi tayi yau Arya baya jin daɗi dan haka saida ta kaishi asibi sannan taje wajen aiki, kuma a wajen aikin ne aka kawo musu kwangilar ɗinkin atamfofi na wani biki da za’ayi a villa.

Ita kuma ma’aikatanta basa ɗinka atamfofi, wanda yake ɗin ma baya gari, dan haka tana buƙatar wanda zai ɗinka mata atamfofin, da wannan tunanin ta dawo gida, yau ji tayi bazata iya zaman ɗaki ba, ai itama gidan gidan ubanta ne, dan haka zata iya zama a ko ina taso.

Dan haka bayan taje tayi wanka tayiwa Arya ma sai suka sauƙo parlon ƙasa, bata sakawa Arya riga ba sai ta barshi daga shi sai diapers, ta fito da system ɗinta dan akwai aikin da zatayi, ta zaunar da Arya a cikin baby floor seat ɗinsa, dan yanzu ya fara wayo ga ta’adi a cikinsa.

Ta tafi kitchen taje ta zubo abinci sannan ta dawo ta zauna kusa dashi a ƙasan, ta ɗora laptop dinta akan coffee table, farar shinkaface da Stew wadda taji naman sa, sai coslow, data tashi sai take bashi shinkafar da coslow ɗin kawai, dan tana so ya fara cin abinci tun yanzu, dan ya kusa shekara, kuma a yanda ta yanke yana cika shekara zata yayeshi.

Tana ci tana bashi tana masa wasa har suka cinye tas, sai ta kira ɗaya daga cikin masu aikinsu tazo ta kwashe plates ɗin, sannan ta cireshi daga cikin floor seat ɗin, ta koma kan kujera tana dudduba aikin nata.

Arya ya kama kujera ya miƙe ya fara rirriƙe kujerar yana tafiya.

“Um um ka ce sai munyi tafiya zamu yi magana”

Ta faɗi tana masa dariya, ya juyo ya kalleta shima yana dariyar, sai kuma ya saki kujera ya koma rarrafe a tsakiyar parlon, duk inda yayi tana binsa da kallo.

Nabila ƴar Mero ce ta sauƙo, babbar mara kunya cikin ƴaƴan mero, ta sauƙo tana wani taunar chewing gum, sai wani kallon tara saura kwata take bin Hanam da shi.

Arya ya kai wajen da aka aje wasu kaya a leda Hanam bata lura dashi ba ya shiga janyo ledar daga ƙarƙashin kujera.

“Kai !! Dan uwarka zaka yi da ledar da kake janyowa?”

Ta ɗura masa ashar ɗin tana finciko shi daga gaban kayan, tsawar da tai masa yasa Aryaan fasa kuka, ‘dan ya tsorata, ta wancakalar dashi a gefe har ya kusa faɗuwa, duk abinda take Hanam na binta da kallo, sai kuma tazo ta tsaya a gaban Hanam tana wani girgiza irin ta tashen balagar nan.

“Ki jawa shegen ɗanki kunne, babu ruwansa da kayan mu a cikin gidan nan”

A hankali Hanam ta kai hannu ta aje system ɗin a gefen inda take zaune, ta miƙe tsaye kuma ba tayi wata-wata ba ta ɗauke Nabila da maruka har uku ƙwarara.

“Naga kamar ranar da na yiwa uwarki da yayanki warning akan ɗana ba kyanan, to kema ga naki warning ɗin, a da kunyi min rashin kunya na jure, kun zageni na jure, but now baku isa ba, kuma har yanzu idan rashin mutuncin ku akaina zai tsaya bazan ce muku komai ba, but if you dare touch my son, hmmm hmmm”

Ta yi wani irin murmushi, tuni matan gidan suka fito sbd kukan da Nabila ta saka, Mero ta kamota tana faɗin.

“Ke de Hanam wallahi baki da mutunci, ki tab’a uwa ki tab’a ƴaƴanta, wannan ai wulaƙanci ne, dama ai barewa baza tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba, haka uwarki ma take”

Hanam ta ba banza ajiyarsu, ta kamo ɗanta ta shiga bashi mama, sannan ta ci gaba da aikinta.

Bayan Abba ya dawo Mero ta same shi da ƙorafi akan Hanam kamar kullum, shima sai ya bata haƙuri kamar kullum ɗin, sannan kuma ya ƙira Hanam ɗin ya yi mata nasiha, bayan ya gama ne ta ce.

“Abba an kawo mana kwangila na ɗinka atamfa daga villah, to kasan musa ya tafi garinsu, su kuma sauran ba iya ɗinka atamfa sukayi ba, shine nake so ka duba min wanda ya iya ɗinki”

Abba yayi shiru yana Nazari.

“Akwai amma ki bari sai nayi magana dashi gobe duk yadda muka yi zaki ji”

“To Abba Allah ya kaimu”.

Abba Ya shiga yiwa Arya dake kan cinyarsa wasa, Hanam ta tsaya kawai tana kallonsu, wani abu na yawata a ƙwaƙwalwarta.

Duk duniya bata da wani farin ciki bayan wannan abu biyun, sune rayuwarta, domin su take farin ciki, bata da komai bata da kowa sai su, a da tana addu’ar Allah ya ƙara bata wani sabon fata, sai kuma ta samu Arya a lokacin, sai ta ɗauki Arya a matsayin wannan sabon fata.

Alaro City.

Da misalin ƙarfe 09:00am.

Dogayen yatsun hannun Tafida suka ƙwanƙwasa kofar ɗakin da Maryam ke ciki, yau lahadi amma dole yaje aiki, saboda kwanakin da yayi baije ba, duk da yana buƙatar ya huta, dan jiya bai samu yayi wani baccin arziƙi ba.

Dan yana aje mata kayan nan suka fita shida drivern nan, ya aike shi yaje ya siyo musu abinci, daga nan kuma ya wuce masallacin block ɗinsu, kuma bai dawo gidan ba sai bayan isha, dan ya tsaya sunyi magana da maƙocinsa wanda shima ya kasance bahaushe ɗan arewa.

A lokacin daya dawo gidan har drivern ya dawo ya karb’i aiken da ya masa ya ware wanda zai bata sannan ya nufi ƙofar ɗakinta.

Kuma tun kafin ya ƙwanƙwasa ƙofar yaji bugun zuciyarta, yana buga ƙofar bugun zuciyar ta ya sauya, wani irin sauti dayafi na ainahin yanda zuciyar tata take bugawa daɗin saurare, idan zuciyarta tana bugawa a tsorace sautin yafi daɗin saurare.

“Ya Rab!!”

Shine abinda ya furta a lokacin, sai kuma yayi sauri ya aje mata ledar cikin wani irin sauri daya zarce na normal ɗan adam ya shige ɗakinsa.

Bai samu yayi bacci da wuri ba sbd bugun zuciyar tata dayaci gaba da saurare. Kuma yau da safe daya fita masallaci yaga wutar ɗakinta a kunne, alamun ta tashi, bayan ya dawo kuma bai fito ba sai yanzu, shine yake san ya sanar mata da zaije aiki.

Kamar kullum jama’a, ina miƙo godiya sinƙi-sinƙi, sannan gaisuwa ta musamman zuwa ga Mrs Zak’s, naga saƙonki, Maryam tana zuba ido.

<< Yadda Kaddara Ta So 12Yadda Kaddara Ta So 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×