Skip to content
Part 14 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Tunaninsa ya katse a sanda Maryam ta buɗe ƙofar, abu na farko daya fara shiga ƙofofin kunnuwansa shine wannan bugun zuciyar, kuma a tsorace yake bugawa, kenan tsoransa take, tana tsoransa a matsayinsa na haka ina ga idan tasan waye shi, ainahin shi.

Sai kuma ya kalleta, hijabi ne a jikinta har ƙasa, hannunta da fuskarta ne kawai a bayyane, idonta ya kalla, wani abu da yafi komai kyau a fuskarta.

Maryam na haɗa ido dashi ta sunkuyar da kai, dan bata tab’a sanin haka kalar idonsa take blue ba sai yau, cikin tsoro da rawar murya ta sunkuya ƙasa tace,

“Ina kwana”

“Lafiya”

Ya amsa mata cikin muryarsa me zurfi, kuma sautin muryar tasa kamar akwai gajiya a ciki, Maryam ta miƙe kuma har yanzu kanta a ƙasa zuciyarta na tsere a ƙirjinta.

Shi kuma ya kasa kunnensa sai sauraren bugun zuciyarta yake, ko da wuƙa za a ɗora masa a wuya a tambaye shi me yake ji a bugun zuciyar tata ba zai iya faɗar komai ba, dan bai san me yasa yake san sauraren sautin ba.

Kawai dai yana jin kamar akwai wani abu a cikin sautin bugun zuciyar tata na musamman, kamar yadda fuskarta take very Innocent hakama zuciyar tata ke bugawa, musamman ma idan tana bugawa da sauri.

“Zanje aiki ne, shine nace bari na faɗa miki, akwai kitchen a ƙasa, zaki iya shiga ki girka abinda zaki ci, ko idan na fita na aiko miki ?”

Ya bata zab’i biyu ne dan be san me ya kamata yayi a cikin biyun ba, idan yace sai ya fita ne lokaci zai ƙure, kuma bai sani ba ko bata makara wajen cin abinci, idan kuma yace ta girka watakila bata iya girkin ba, dan haka ya ya tambayeta.

Kamar Maryam zata ce masa ta rage abincin jiya kuma shi zata ci sai kawai ta fasa tace.

“A’a zan girki”

Muryarta ta fito da irin innocent dinta, a hankali ya gyada mata kai.

“Sai na dawo”

“Allah Ya tsare, Allah Ya kiyaye hanya”

Maryam ta faɗi bayan ya juya, maganar tasa Tafida ɗan dakatawa da tafiyar da yake, addu’ar ta dake shi sosai. A hankali yaci gaba da tafiya cikin takunsa na izza da ƙasaita, tausayin yarinyar na ƙara kama zuciyarsa.

Maryam tabi bayansa da kallo, tana kare masa kallon da bata samu damar masa ba jiya, bata san cewa dogo bane sai yanzu data tsaya a gabansa, kuma wani abu data lura dashi shine yana da rukon al’ada, dan daga jiya har yau duka kayan hausawa take ga yana sakawa, amma ita a ganinta sai take ga kamar kayan basu wani karb’e shi ba, da a ce zai saka kayan indiyawa sai yafi karb’arsa, dan gabaɗaya kamar indiyawa ce dashi.

Ɗakinta ta koma ta cire hijabin jikinta dan dama saboda ya kwankwasa kofar ne yasa ta saka, wajen data saka wayarta a chargy ta koma ta cire wayar.

Da ƙyar ta samu ta lalubo lambar Anti Fati, dan wayar bata dannuwa da kyau, alamun taci sensor, gaisawa suka yi sannan ta tambayeta ya su Maamu suke, Anti Fati ta ƙara mata nasiha, sannan sukayi sallama, ta nemo lambar Badar za ta kirata amma sai aka sannar da ita bata da isasshen kati.

Tayi tsaki sannan ta aje wayar miƙewa tayi ta ƙara saka hijabin data cire sannan ta fita daga ɗakin, ta tsaya a ƙofar ɗakin tana kallon corridor ɗin dakunan, daga karshen corridorn daga dama kuma balcony ne, wanda yake facin kofar gidan.

A hankali take takawa zuwa wurin, balcony ɗin yana da faɗi sosai, ga wasu flower vase da aka jera daga ƙasa, ga grass carpet shimfiɗe a kasan wurin, ga kuma wani lilo a wajen, sai wasu flower vase din rataye a sama.

Daga jikin bango ma wasu ne jere kala-kala, karfen balcony ɗin an masa ado da ne on strip light, hakama wasu daga cikin flower vase ɗin, Maryam har ta hango yadda wajen zeyi kyau da daddare idan aka kumma neon strip light ɗin, daga ɗan sama kuma kejin aku ne kuma akwai akun a ciki.

Maryam taji wani abu na farinciki na ratsa mata zuciya, sai kuma ta kalli sauran gidajen dake tsallaken nasu da ma na kusa da su, ko wani gini iri ɗaya ne hatta da fenti, view ɗin kasan akwai ban sha’awa. Ta koma wajen Akun nan, tana kallonta, can tace.

“Barka”

Akun ma ta maimaita.

“Barka”

Dariyar farin ciki ta sub’uce daga bakin Maryam, gabaɗaya wajen ya gama burgeta.

Fita tayi daga wurin ta ci gaba da tafiya a corridor ɗin, bata buɗe dakin da taga ya shiga jiya ba, dan bisa ga dukkan alamu nasa ne, sai ta bud’e na kusa dashi, shi ma kamar nata yake, amma kuma babu gado sai katifa kawai, kuma komai na dakin an lillibe da kyalle alamun ba’a amfani dashi, ta jawo ƙofar ta rufe.

Amma kuma sai taji tana san taga ya nasa ɗakin yake, dan haka ta koma da baya ta bud’e kofar, “Wow”.

Kawai ta iya furtawa da tayi arba da ɗakin, tsarin ɗakin kamar nata yake amma kuma yafi nata girma, a hankali ƙafafunta sukaci gaba da takawa zuwa cikin ɗakin, tana ta santin kyan ɗakin a zuciyarta.

Ta kalli inda yake aje cricket kit bag dinsa, ga Jersey dinsa rataye a saman jakar, a ranta tace ashe ɗan wasan cricket ne, dubanta yakai kan wani bango a ɗakin wanda yake cike taf da hotuna, kafafunta sukayo kwana zuwa jikin bangon, ta tsaya tana bin hotunan da kallo ɗaya bayan ɗaya, duka hotunansa ne, tun na yarinta har zuwa girmansa.

Idonta ya tsaya akan wani hoto guda ɗaya, kuma wanda yafi kowani hoto girma a cikinsu, wani baƙin fatane ɗan africa sanye cikin suit irin tasu ta lokacin, sai kuma wata ba’indiya fara tas da ita, sanye cikin sari hannun ta riƙe da wani yaro da ba zai wuce 3 yrs ba.

Abu ɗaya ne ya faɗo a tunaninta, tabbas wannan iyayensa ne, kenan babarsa ce ba indiya ? Ga zahiri kinga tunda kamarsu ɗaya da matar, wani sashi na zuciyarta ya amsa mata, Fulani ta faɗa mata cewa iyayensa sun rasu.

Sai kawai tayi musu addu’ar Allah gafarta musu, ta ci gaba da bin hotunan tana kalla, tun yana ƙarami suke hoto da wata budurwa itama kuma ba’indiyace, kode kanwarsa ce ? To amma kuma ai bashi da ƙanwa a wannan hoton, watakila yar uwarsace, dan suna kama hatta da kalar idonta irin nasa ne, amma ita nata idon ba light blue bane, nata dark blue ne, kuma duk da kasancewarta mace yafi ta kyau.

Ya samu gata sosai, ta faɗi a zuciyarta, sakamakon hotunansa da take gani na celebrating birthdays dinsa.

Saida ta gama masa tsurku akan hotunan nasa sannan ta bar ɗakin, ta sauƙo ƙasa.

Kamar jiya, yauma ta tsaya tana ta kallon tsaruwar parlon, ƙofar farko da idonta ya sauƙa a kai ta fara shiga.

Sai taga store ne na a jiyar kayan amfanin gida, akwai irin su wheelbarrow, watering can, spade (shebur), hose (tiyo din ruwa), vacuum cleaner, pruner (abun yankan ciyawa), spenner, hammer, broom ɗinma wata doguwa ce, bucket, dustpan, squeegee mop(mofar goge glass), mop (mofa), scrubbing brush da dai sauransu.

Wasu abubuwan ma bata sansu ba, kuma komai a killace yake, akan kantoci, daga ƙarshen ɗakin kuma washing machine ne har guda biyu, wata chest drawer ta gani a gefen washing machine ɗin, ta bud’eta sai taga laundry detergent, bleach, pegs ( clips ɗin shanya ), ta mayar da rufe, sannan ta fita daga wurin.

Sai kuma ta shiga ɗayar ƙofar shi kuma bashi da girma dan guga kawai ake a ciki, daga ironing board sai wasu lokoki, ta shiga ta bubbuɗe lokokin, wasu kayane a ciki ba’a goge ba, wasu kuma an goge amma ba’a ɗauke ba, sai wasu iron guda biyu babba da ƙarami.

Ta fito daga ɗakin ta buɗe ɗayar ƙofar dake a tsalleken dakunan, shi kuma data buɗe gym ne kawai, katangu biyu da suka zagaye wajen gaba ɗayansu ɗauke suke da mirror, batama shiga ba taja ƙofar, dan a ganinta babu abinda za tayi a wani gym.

Ƴar wata kwana dake bayan ƙofar gym ɗin tayi, taja ta tsaya baki buɗe tana kallon danning table ɗin dake wurin, danning ɗin ya burgeta fiye da misali.

Ƙofar dake kusa da wajen tayi saboda ko tantama ba tayi ƙofar kitchen ce, abinda take ɗaukin gani kenan a gidan, kusan sumewa Maryam tayi, bayan tayi arba da kitchen ɗin.

A rayuwarta tana san kyakyawan kitchen, wasu lokutan kawai sai ta tafi gidan Anti Fati saboda kitchen ɗin gidan, yau sai gashi idonta na gane mata kitchen ɗin daya ninka na gidan Anti Fati girma da kyau, kuma wai na gidan mutumin da ake kira da mijinta ne, wani abu yazo ya tsaya mata a zuciya na murna, taji kamar tana yawo a gajimari, ita da ganin kitchen irin wannan sai a film, ko a social media.

kalar cabinet din kitchen din ash ne, ga wani kitchen island wanda aka kewaye shi da kujeru guda hudu, biyu daga kowani b’angare, wani abu da ya ɗauki zuciyar Maryam ya jefa a cikin ruwan sanyi shine.

Daga tsakiyar cabinet ɗin sama da na ƙasa wanda yake setin inda gas cooker take glass ne a wurin, a bayan wajen kuma garden din gidan ne, ga wasu flower vase da aka jera akan wajen, ga haske a cikin kitchen ɗin ta ko ina, kuma daga ƙasan cabinet ɗin sama akwai wasu led strip light dake haska kan cabinet ɗin ƙasan.

Maryam ta rasa ina zata saka kanta dan murna, a hankali ƙafafunta da babu takalmi suka shiga taka tiles ɗin kitchen ɗin, babu inda zuciyarta ke raya mata ta fara zuwa sai wurin glass ɗin nan.

Ta kai hannu ta zuge glass din zuwa gefe, daddaɗar iskar da bishiyoyin garden ɗin ke bayarwa ce ta silalo zuwa cikin kitchen ɗin, a hankali ta lumshe idonta, sannan ta buɗe, sai kuma tabi vase ɗin dake laye a wajen, green leafy vegetables ne dangin mint, coriander, rapini da dai sauransu, Maryam ta maida dogon glass ɗin ta rufe.

Sai kuma ta dawo ta shiga bud’e cabinet ɗin, gaba ɗaya dangin kayan aikin girki babu wanda bata gani ba, spoon, fork, knife , pot har set biyu kuma duka non stick ne, juicer, tray, tongs, bottle opener, blender, ladle, pestel and morter, choping board, plastic containers dama wadan da bata taba gani ba.

idonta sai ƙyallin murna ya ke, gabaɗaya kayan sauƙaƙawa mutum wajen aikin girki akwai a kitchen ɗin, tun daga toaster, coffee maker, oven har guda biyu, mixer, deep fryer, dish washer, microwave oven, hand blender hatta da dishwasher akwai.

Maryam kamar ta taka rawa dan daɗi, saboda wasu kayan ma ba a ko buɗe su a ledar su ba, sabbabi dal, hakan ya nuna mata cewar ba sosai yake girki a kitchen ɗin ba, ta buɗe fridge ta ganshi cike da fruits da veggies, ga kayan miya ga kuma drinks amma komai a hargitse yake a ciki ga wasu kayan rober, shi kuma tasa kalar ƙazantar kenan?

Wata ƙofa ta gani a kusa da fridge ɗin ta buɗe ƙofar ta shiga taga store ne, kuma akwai kayan abinci amma ba da yawa ba, ta shiga cikin store ɗin ta shiga dudduba kayan ko zata ga abinda zata iya ci.

Aiko tayi kyakyawan gani, wata rice stick wadda tun sanda ta ganta a wani recipe na tiktok ta shiga santin taliyar, yau sai gata ga taliyar, a da kullum bata da zance saina idan tayi aure zata ce mijinta kullum ya dinga siyo mata ita, sosai taliyar ta tafi da ita, saboda a ido idan ka ganta kafin a dafata sai kace zarene ba taliya ba.

Maryam ta kai hannu tana ɗauko taliyar yayin da idonta ke cika da kwallar murna, sai kuma ta tuno gida, nan take murmushin fuskarta ya ɗauke, ko me suka dafa yau ? Ko waye yayi musu girki ?.

Sai kuma ta tuno makarantar ta, yanzu shikenan babu ita ba makaranta ? Lalle rayuwarta ta sauya sosai a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ta samu abubuwa da dama kuma ta rasa abubuwa da dama.

A hankali wata ƙwalla ta sulalo mata, ta daure ta share, sannan ta dawo cikin Kitchen ɗin, ta shiga ƙoƙarin dafa taliyar rice stick ɗin.

Saida ta haɗa komai sannan ranta ya raya mata me zai hana ta duba garden ɗin ma, sai ta rage wutar gas ɗin.

Sannan ta buɗe ɗayar ƙofar kitchen ɗin wadda take da tabbacin garden ɗin zata kaita. Ƙam, ta ƙame tana kallon yanda wajen ya bala’in tsaruwa, shuke shuke ne fal wajen, ga wani water falls wanda aka kewaye shi da stones.

Maryam taji kamar ta nitse a gun dan daɗi, wajen ya haɗu, ya haɗu karshen haɗuwa, wata rumfa dake tsakiyar wurin ta shiga, wadda ke ɗauke da kujeru da kuma table a tsakiya, kamar de balcony ɗin saman nan, shima nan wajen akwai wannaan neon strip light ɗin, an ƙawata wurin dashi, shima dai nan ɗin kamar can ta hasaso yanda zeyi kyau da addare, aiko zata zo ta duba shi da daddaren.

Wani stairs ta gani wanda zai kaita can saman rufin gidan, a hankali ta juya zuwa wajen, tana takawa har ta kai saman gidan, nanma haɗuwarsa ba’a magana, kuma saman ma akwai jerin kujerun zama ga grass carpet ga iska me daɗi dake kaɗawa a wurin, ta shiga duba gidajen dake kusa da nasu dama wanda ke nesa da nasu, ita kam yau ta rasa abunyi dan murna.

Tunawa da tayi ta bar girki yasa ta koma ƙasan ta shiga kitchen ɗin bayan ta leka wani lungu da tagan shi a bayan kitchen ɗin, taga ya b’ulla gaban gidan ne.

Taliyar tata ta sauƙe ta haɗata da kayan haɗin da ta mata sannan ta komo kitchen din ta zauna ta saka taliyar a gaba tana kallo, sai kuma tayi bisimilla sannan ta kai bakinta, wasu lokutan burika na cika a gaske ba mafarki ba, yau gashi tana cin taliyar da take burin ci. Allah abun godiya.

Tafida Pov.

Har ya kai ST NICHOLAS HOSPITAL, bai daina tunanin addu’ar da tayi masa ba, anya kuwa idan yaci gaba da zama da ita bai cuceta ba ? Anya kuwa ba zai zama me san kai ba ? Da haka ya fito daga motarsa har ya shiga floor na farko kuma kamar kullum yana gaisawa da mutane, a ƙofar elevator ya haɗu da Khabir.

“Ango, Ango”.

Itace kalmar da khabir ɗin ya fara faɗi suna gaisawa, Tafida ya yi murmushi, amma baice komai ba, suka shiga elevator ɗin zuwa hawa na 5 dan a nan office ɗinsu su dukan yake.

Khabir sai tambayarsa yake akan auren nasa amma Tafida yaƙi cewa komai sai da suka shiga har office ɗin Tafidan sannan ya bashi amsa.

“Khabir, yanzu bani da abin cewa akan auren nan, ka bari akwai wata waya da nake jira, daga baya sai muyi magana”

Kamar Khabir ɗin zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru.

“Allah kyauta, bari naje”

Tafida ya gyaɗa masa kai, wayarsa ce ta fara ringing tun kafin ya zauna, zaman yayi kamar yanda yayi niyya, ya cire hular dake kansa sannan ya daga kiran, suka gaisa da Muktar sannan dalilin kiran ya taso.

“Me ka samo ?”

Muryar tasa ta fito cikin wannan ajin nasa da kasaita, yanayi yana tura sumarsa baya, muryar Muktar ta fito daga cikin wayar yayinda yake faɗin.

“Komai ma na samo, sunanta Maryam Tijjani Muhammad, haifaffiyar hadejia unguwar garko, tana da yan uwa huɗu, babbar yayarta itace Fati matar Habib, nasan ka sanshi ai gidansa ma kusa da gidan ka ne”

Idanun Tafida a lumshe ya gyada kai, kuma shima Muktar ɗin kamar da yasan ya gyaɗa masa kan sai ya ci gaba.

“Tana da ƙanne uku, Hassan da Hussain sai autansu Muhsin. Wato Tafida abun mamakin shine ƙannen nata ƴan biyu a secondary school suke, kuma sune suke ciyar da gidan nasu, and a shekaru ba za su wuce 18 ba”

Da sauri Tafida ya buɗe idonsa

“Me? But ina babansu ? Ko ya rasu ?”

Ya jerowa Muktar tambayoyin, cikin wata iriyar murya da ba zaka iya gano halin da yake ciki ba.

“Wallahi yana nan da ransa, da drivern tilera ne, ya riƙi kuɗi a da, amma kuma yana bin mata kasan shi kuma ƙarfe ba a haɗashi da kazanta, sai me motar ma ya kwace kayarsa, daga nan kuma sai ya talauce, sai yake ganin kamar wai matarsa mahaifiyar su kenan itace me farar ƙafa, sai ya fara mata cin mutinci baya kula da ita da yaranta, wani yayanta ne wai Usman, shine yake kula da ita har yaran suka taso sannan suka fara aiki a wani gareji, kuma har yanzu sune suke kula da gidan, and Baban kuma har yanzu bai dai na halin banzansa ba, ni wani labari da naji ma ance kuɗin auren Maryam ɗin da aka bashi zaije yayi aure dashi, abun dai abun tausayi”.

“Umhm ina jinka”.

Tafida ya faɗi hannunsa akan bakinsa.

“Shi wanna kawun nasu yayan maman tasu shine yake ɗaukar nauyin karatun Maryam ɗin, dan poly take ma, ta gama level one zata fara level two, kuma kasan wani abu? Wallahi yarinyar akwai kamun kai, ga tarbiyya bata da matsala ko kaɗan, ko saurayi ba ta da shi sai wani wai shi sanata, kuma shima ba kulashi take ba, dan yadda naji labari ma ance wai daga karshe ce masa tayi ita yanzu bata da ra’ayin aure, gaskiya kayi dace”

Ya sauke hannunsa daga kan bakinsa.

“Gaskiya kam na yi dace, na yi dace da su Fulani suka aura min ita, dan nasan idan ba ita bace ba lalle na karb’eta ba, sai dai kuma ita ba ta yi dacen ba, su Fulani sun hargitsa rayuwarta da suka aura mata ni, amma babu komai, zan nema mata gun karatu a nan polytechnic din Alaro, sai ta ci gaba kawai kaje poly din ka karbo min takardunta ka aiko min please”

“Tafida yanzu baza kayi haƙuri da auren nan ba?”

“Yaya zanyi Muktar ?, nesanta kaina da zanyi da ita shine babban gatan da zan mata, idan har naci gaba da kusantar ta zan iya cutar da ita, and if that happens bazan tab’a yafewa kaina ba, bana san na zama silar rasa innocent soul kamarta”

Yana iya jiyo ajiyar zuciyar da Muktar yayi.

“Kuma hakane, Allah ya mana me kyau kawai”

“Ina asibiti idan ka karb’o takardun just let me know”

“Inshallah”

Daga haka kuma wayar ta ƙare, ya ƙira drivern sa ya aike shi siyyaya, sannan ya fara aikin da yake jiransa.

Uchenna Pov.

Dariya yayi bayan Abba ya gama roƙonsa akan wai yana so yayi aiki a ƙarƙashin ƴarsa, to shi a duniya me Abba zaice ya yayi,kuma ya masa musu, shi kuma Abba ganin yana dariya yasa yace.

“Kaga zan saka ta baka albashi fiye da wanda ake baka a nan…”

“Haba mana Abba, nifa bance komai ba, ni yanda kake roƙonane yake bani dariya, abba babu abinda zaka nema nayi maka naƙi, komai kake so wallahi ni me maka ne”

Ran Abba yayi tas, a kullum idan ya kalli Uchenna wani alfaharine ke cika zuciyarsa, yana jin inama ace dansa ne, dan ya fiye masa Kamal sau dubu.

“Haris…”

Sai kuma yayi shiru.

“Na’am Abbana”

“God bless you”

“Abba God has already bless me, tunda ya bani kai a matsayin uba”

Abba ya miƙe daga kan executive chair ɗin da yake kai, ya zagaya zuwa tsallaken teburin nasa ya zauna a kujerar fake facing ta Uchenna.

“I am so proud of you Haris, Uchenna Franklin”

Uchenna na murmushin da baya rabuwa da fuskarsa ya kamo hannayen Abba.

“Abba i am the one that will be proud of you, because you changed my life, Abba ka bani abinda babu wanda ya bani, ka bani kyakyawar rayuwa, Allah ya raya mana kai, Hanam ƙanwatace, zan je nayi mata aiki kyauta, ɗinki baiwata ce, laifine dan na baje basirar ɗinkina domin ƙanwata?”.

Abba Ya shafa kansa, kalamansa sun ƙare, dan babu abinda zai iya cewa.

“Yaushe zan fara zuwa ?”

“Gobe”

“Allah Ya kaimu”

Yana san yaje ya ga wannan ƙanwar tasa da a kullum Abba bashi da magana da ta wuce tata.

Tafida Pov.

Tare suka dawo gidan shida drivern sa, amma bai shiga gidan ba sai da suka zagaya ta baya yasa drivern ya jibge kayan da suka yi shopping, kuma tun daga kitchen ɗin yaga sauyin gidan, dan ko ina a gyare yake tsaf, dama shi baya bawa kitchen ɗin muhimanci idan ba girki zeyi ba, wasu kayanma ba tab’a amfani da su yayi ba.

Saida ya dawo ta kofar gidan ya sallami drivern sannan ya nufi gidan. Curtains ɗin falon wanda ke jikin katangar glass ɗin nan a sauƙe suke, dan haka bai samu damar ganin komai ba.

Abu na farko da idonsa ya fara gane masa a parlon bayan ya buɗe kofar shine, Maryam kwance a kan kujerar parlorn, tayi ɗai-ɗai, amma kuma lullub’e cikin hijabi, daga ganinta ba bacci take ba, duk da idonta a rufe yake, saboda ga wani guntun murmushi a leb’enta, sai kawai ya motsa kunnensa.

Abu na farko daya fara saurara shine wannan sautin, wannan sautin daya sauya duniyarsa a kwanakin nan, ya shiga cikin irin yanayin da ya saba shiga idan yana sauraren bugun zuciyar tata, kamar igiyar ruwa na kaɗawa, kamar iska me daɗi wadda take busowa daga bishiyoyin garden ɗin gidan sa.

A tare da bugun zuciyar tata kuma sai ya tsinkayo wani abu, haka kamar magana, sai ya kara takowa cikin parlon, har ya kawo jikin kujerar da take kwance, sai a lokacin ya samu damar sauraren abinda itama take saurare.

Wato earpiece ta saka tana sauraren novels na ji. Yaji tausayinta ya ƙara cika zuciyarsa, nishaɗinta take hankali kwance, ba tare da tasan halin da rayuwarta ke ciki ba.

Kuma bisa ga dukkan alamu littafin na mata daɗi, a hasaso ya indonsa yanda zata tsorata idan ya tahseta, daga jiya zuwa yau ya fuskanci cewa tana da tsoro, kuma shi yafi jin dadin sauraron bugun zuciyar tata idan tana a tsorace.

****

Yau maryam yini tayi cikin nishaɗi, dan ko ina ta kalla a gidan wani daɗi ne ke lullub’eta, tanajin inama zata dawwama a haka, gidan ya mata fiye da zatonta, kyakyawan kitchen, kyakyawan ɗaki, ga kyakyawan garden.

Komai ma na gidan me kyau ne, haka ta yini ita kaɗai a gidan, amma kuma kaɗaicin bai dameta ba, dan akwai TV, ga kuma kitchen.

Haka ta shiga tayi abincin rana ma sannan tayi na dare dan harda shi ta dafa, bata sani ba wataƙila zai ci.

Har tayi sallar la’asar amma babu alamar dawowar Ficar yara, to wai ita inama ya tafi ne ?, yace mata de aiki za shi, to wani aiki yake?, ta yiwa kanta tambayar lokacin da take banɗaki tana wanka, sai kuma kwakwalwarta ta nuno mata hoto ɗaya daga cikin hotunansa da ta gani ɗazu, hotonsa sanye da lap cort, da kuma wani award da ta gani akan wata chest drawer.

Wato likita ne, bayan ta gama wankan ta fito ta zab’o wata riga ɗaya daga cikin kayan da tazo dasu, dan kayan da Fulani ta bata tace ba na sakawarta yanzu bane, sai ko idan fita ta kamata, fita ?, sai ta bawa kanta dariya, ko waye zai dauki mummuna yar ƙauye kamarta ya fita yawo da ita, kuma ma wai Tafida, Tafida fa?.

Da saƙe-saƙenta ta saka hijabi ta dauki wayarta ta sauƙo ƙasa, dama bata saba kwalliya ba, shi yasa ba tayi ba, kuma bawai dan bata iya ba, ta iya kwalliyar kawai de ba tayi ne.

A kan kujera ta zauna, sai taji tana san kwanciya, amma kuma ta san cewa baccin la’asar ba kyau, dan haka kawai ta yanke shawarar ƙarasa jin littafin wani gari da ta fara, dan haka ta saka ear piece ɗinta ta kamo na inda ta tsaya, dan tana ƙaunar littafi, na karantawa ko naji.

Tayi nisa a abinda take bata ko san mutum ya shigo ba, bare ta san sanda ya tsaya a kanta, sai ji tayi an ɗan bigi kujerar da take kwance akai.

A firgice ta mike zaune, tana dube-dube, sai ganin mutum tayi tsaye a kanta yana kallonta, kuma dai kamar yanda ta sanshi fuskarsa babu fara’a bare a kasinta sai kawai ta sa hannu ta zare ear piece ɗin ta cikin hijabinta, ta tsugunna ƙasa.

“Ba…barka…da da zuwa”

Ta furta muryar ta na rawa, kamar wadda ta yi wa sarki ƙarya, gaba ɗaya ta tsorata jikinta har wata rawa yake, dama ita gata sarkin tsoro kamar farar kura, kanta sunkuye a ƙasa, ga kamshin turaren sa na barazanar fasa mata kai.

Tunda zuciyarta ta buga sau ɗaya yaji wani abu na ratsa shi tun daga saman kansa har tafukan kafarsa, yaji daɗin sautin ma ya fi na waƙar da ya ke saurare, ji ya ke kamar ya taka rawa dan dama shi gwaninta ne.

Wannan ladabin da take masa na ƙara burgeshi da ita, alƙawari yake ɗaukarwa kansa, na har Allah ya karb’i ransa ba zai tab’a cutar da wannan innocent soul ɗin ba, zai yi duk abinda zai yi ganin ya kyautata mata, ya sakata farin ciki, zai tabbatar bata nemi komai ta rasa ba, magana can ƙasan maƙoshi ya amsa sannu da zuwan da take masa, ta shiga ƙoƙarin miƙewa zata bar parlon.

“Maryam…”

Maryam taji wani abu tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafukan kafarta, idanuwanta ta runtse zuciyarta na tsere a kirjinta, sunanta ya kira, cikin wata iriyar murya, ashe dama ya san sunanta?, gaba ɗaya ilahirin jikinta rawa yake har yanzu, ita bata ci gaba da tafiyar ba, kuma ita bata juyo ba.

“I want to talk to you”

Gabanta ya kuma bugawa, saida ya lumshe idanunsa a wannan karon.

‘Hai fagban!’

(oh god)

ya fadi a zuciyarsa kuma cikin harshen indianci, A hankali ta juyo kuma har yanzu kanta a ƙasa, ya zauna a kan kujerar da ta tashi, ita kuma sai ta zauna a ƙasa, idanta a ƙasan tana kallon carpet, amma kuma sai idonta ya kai kan kafarsa ta dama, daga idon sawunsa, taga wani baƙin zare ɗaure a wurin, irin dai zaren da ta saba gani a ƙafar indians a filma, ashe de da gaske ma suna sakawa.

Shi kuma yayi shiru yana sauraren abinda ya zame masa kamar dole, can kuma sai yayi gyaran murya.

Ya fara magana cike da kasaita da kuma nutsuwa.

“Maryam nida ke gabadaya mun samu kanmu a cikin wata alaƙa me suna aure, kuma dagani harke ba tare da mun shirya ma sa ba, saide kuma dole mu karb’i hakan da hannu biyu, domin haka KADDARA TA SO, babu wanda ya isa ya ja da ita, sai dai dolene aurenmu ba zai kasance kamar auren kowa ba, bawai dan ban karb’eki a matsayin mata ba, sai dan wani dalili, Maryam dolene ni da ke mu nisanci juna, domin ni annoba ne, bai kamata ace wani ya rab’eni ba, gashi an aura miki ni, kina rayuwarki aka rabaki da kowa naki aka sakaki a cikin wannan alaƙar, alaƙar da zata iya cutar da ke, Maryam da ace ina da iko da na hutar dake daga wannan auren kinje kinci gabada da rayuwar da ki ka fara, amma hakan bazata samu ba, nayi bincike akanki, kuma an sanarmin da kina karatu dan haka na saka a karb’o min takardunki na can Binyaminu Usman Poly, inaso kiyi join a nan dan akwai polytechnic a cikin estate ɗin nan, inaso kici gaba da rayuwarki kamar yanda kika saba, duk da nasan kin rasa wasu abubuwan a rayuwarki, but i will try my best to make sure that baki rasa komai ba anan gaba, and one more thing, kullum da daddare ki riƙa kulle ƙofar ɗakinki, duk abinda za kiji kada ki kuskura ki fito ko ki buɗe ƙofar, ki yi haƙuri ki jure, ina san ki ɗauki zama dani a matsayin ƙaddara, Maryam”

Ya kira sunanta, Maryam da kalamansa suka saka zuicyarta a cikin wani irin yanayi mara fassara ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai ganin shima kallonta yake, sam ta kasa gane inda zancen nasa ya dosa, farin ciki za ta yi ne ? Ko kuwa, ta rasa ma ƙwaƙƙwaran tunanin da za ta yi a kanta.

“Saboda ni…”

Ya nuna kansa da ɗan yatsa

“Maryam i am a monster, i am a beast so, stay away from me…”

Second daya…Biyu…Uku…

<< Yadda Kaddara Ta So 13Yadda Kaddara Ta So 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×