Skip to content
Part 15 of 22 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Hanam Pov.

Zaune take a office tana dudduba wasu yadika, yau Naani ɗin Arya bata zo ba, wai bata jin daɗi.

Dan haka ta saka aka ɗauko masa castle tent ɗinsa daga ɗakin da ake renon nasa zuwa office ɗin nata, ta saka shi a ciki, ta haɗa shi da wasu teddies da kayan wasa, saima ta manta dashi a office ɗin, dan sabgarsa yake, shi idan da kayan wasa babu ruwansa da kowa.

Sanye take da farin cargo pants, sai wata peach sweat shirt a jikinta, gashin kanta ta ɗaure shi a bayanta, ta saka masa farin bow ribbon clip, daga ƙasa kuma ta sakeshi ya baje a bayanta, duk da gashin nata ba wani tsayine dashi na tashin hankali ba, kuma kamar kullum daga ƙasansa tai masa kalar brown.

Haka zalika amar kullum fuskarta babu kwalliya, ko kwalli bata saka ba bare aje ga hoda da sauran kayan kwalliya, ta sofara pen a bayan kunnenta, wata ɗabi’a wadda tun tana makaranta take yinta, sofara biro a bayan kunne, kunneta karamar barima ce kawai.

A hankali take kaɗa ƙafarta ta dama ta na yi tana duba yadikan, kasan cewar kanta a ƙasa yake yasa bata lura da wanda yake tahowa daga waje ba, dan katangar office ɗin nata glass ne, saiji tayi ana ƙwanƙwasa ƙofar,kuma ba tareda ta ɗagoba ta bada izinin shigowa.

Shigowar yayi ta bashi damar zama, ya zauna a kan kujerar, ta aje ipad ɗin hannunta ta ɗago, ta ɗora idonta akansa, Damm!, Gabansa ya faɗi da ganinta, tunainsa ya ɗauke shi can shekarun baya.

2016, NEW PRIME ACADAMY, ABUJA

Ɗaliban SS3 ke hayaniya sbd test ɗin da ake raba musu, kowa sai haƙilan samun tasa yake daga hannun ifeanyi, wanda ya kasance shine montan ajin nasu. Saida aka gama rabawa kowa ya koma seat ɗinsa ya zauna, sannan malamin geography ɗinsu, Uncle Bala ya ce.

“Kowa ya samu tasa ?”

Suka amsa masa da eh

“To ɗalibai, kowa yayi ƙoari, kuma kun bani mamaki sosai, gaba ɗaya cikinku naga babu wanda ya samu ƙasa da 10, dan haka wanna abun alfaharine, but their is only one person who score below 10…”

Gabaɗaya kowa yayi shiru yana jiran wa za’a ce, duk da sun riga da sun san ko wa za’a kira dan gaba ɗaya ajin ansan waye baya focusing kwata-kwata, kuma kamar yanda suka zata hakance ta kasance.

“Uchenna Franklin, stand up!”

Duka suka saka masa dariya, yana daga seat ɗin baya kansa a ƙasa ya miƙe tsaye, kallo ɗaya zaka masa ka gane cewa yafi duka yaran ajin a haife, dan da gani ba sa’ansu ba ne, a hakan da ya ke ma zai iya kaiwa 24.

“Shut up my friend!!”

Ɗif!, dariyar ta ɗauke, Uncle Bala ya kalli uchenna, wanda kansa yake ƙasa rai a haɗe kamar bai san wata kalma wai ita dariya ba, bayan inde barkwanci ne Uche yafi kowa iya shi a ajin.

“Kafi kowa girma amma kafi kowa koma baya, why Uchenna?, yanzu fa kuna second term ne, before you know zaka ga har kun kai third term, kuma kasan cewa a third term ake zana neco da waec, haba Uchenna, ya kamata ace ka gyara, yanzu kai baka jin haushin yanda yara kannenka suke maka dariya ?, kaf nan nasan babu wanda bakafi a haife ba, ya kamata ace ka gyara”.

Da kyar ya gyaɗawa Uncle ɗin kai, yana kawar da kai gefe, Uncle ɗin bai san me Yake tunani bane shi yasa, bai san miye yake hanashi karatu ba shi yasa, kuma shi yanzu Hanam Muhammad Hakuɗau ce ba ya so taji ana masa faɗan shi yasa yake basarwa, kyakkyawar balarabiyar ajinsu.

Kaf yaran ajinsu babu wadda ke burgeshi sai Hanam, saide kuma ita bata ma nuna ta san shi, bata nuna akwai kalarsa a ajin, bama shi kaɗai takewa hakan ba, kusan kowa takewa hakan, ƙawayenta biyu kaf ajin, daga Salma Sa’ad Gashuwa, wadda Suke kira Falaq, sai Iqra Muhammad Ilyas Raja, sukenan ƙawayenta.

Dubansa ya kai inda take zaune, ta kama kanta kamar bata san ana wani abu a ajin ba, ya ɗan cije leb’ensa a hankali, ya ƙudiri cewa yau-yau ɗin nan zai faɗa mata saƙon zuciyar sa.

Hakan kuwa aka yi, bayan sun tashi break ya sameta zaune ita da ƙawayenta biyu, kallonsu kawai yayi suka watse, duk da ita iqran bata tsoransa, dan jinin sojane ke yawo a jikinta, mahaifiyarta soja ce, Hanam ta bishi da kallo har yazo ya zauna kusa da ita.

Juyowa tayi ta kalleshi, ita bata tab’a masa kallon kullira ba ma sai yau, Baƙine amma kyakyawa, dan Uche bashi da muni sam, ga tsafta kamar ba Cristian ba, komai tsaf-tsaf, itama ɗin saide ta faɗa masa farin fata, amma ba kyau ba.

“What ?”

“Au haka ma zaki ce ?, to shikenan let’s go straight to the point, ina sanki Hanam, shine abinda nazo na faɗa miki, kuma ina fatan zaki karb’eni”.

Wani irin kallo na baka da hankali ta masa sannan ta miƙe tsaye.

“So you think we are joking ?”

Shima sai ya miƙe tsaye, ta ɗan ɗaga kanta ta kalli fuskarsa dan Uche akwai tsayi ba laifi.

“What do you mean Haman ?”

“I mean ni da kai bazamu tab’a zama ɗaya ba, hanyoyunmu mabanbanta ne, ba addininmu ɗaya ba, muna da banbanci Uche, tun ba yau ba nasan cewa sona kake, amma kayi haƙuri soyyaya tsakaninmu abune mara yiwuwa, dan bazamu tab’a zama ɗaya ba”

Tana kaiwa nan ta tafi ta barshi a wajen.

*****

Har yanzu bai manta ranar ba, dan daga ranar bai sake ganinta ba sai yau, to yama za’ayi ya manata ranar, nan take wani abu da ya daɗe da mantawa da shi ya dawo masa, wani hoto da yaso yayi deleting ɗinsa daga kwakwalwarsa ya dawo, yan da mahaiyarsa ke kuka a ranar

“Na tsaneka Uche, Allah ya tsine maka”

Sai kuma tsinuwar ta shiga dawo masa tunaninsa, yanda yake tsine masa a mabanbanta lokuta.

“Kai tsinanne ne”

“sai ya Allah tsine maka”

“Ba zaka tab’a ganin daidai ba a rayuwarka”

“Tsinuwata ce za tayi ta bin ka”

*****

“Hello!!”

Firgigit ya dawo daga tunanin, kamar wanda lantarki ta kama.

“Are you okay ?”

Muryarta ce ta tambaya, shekaru kusan bakwai kenan, amma kammaninta na nan yadda suke, bata sauya komai ba sai girman da ta ƙara, to amma me yasa bai gane cewa Abba shine mahaifin ta ba ?, ko ta sunansa ya kamata ace ya gano hakan ? Shi yanzu ta tuna da shima ma ? Ba lalle ace ta tuna dashi ba, wata ƙilama tayi aure abinta.

Shi kuma tun bayan ita bai kara san ko wace yarinya ba, duk da ƴan mata da yawa sun sha kawo kansu gareshi amma baya kulawa, Hanam kawai ya so, kuma baya jin zai sake san wata bayan ta.

“Yeah i am okay”

Muryar tasa ta fito cikin wani irin sauti wanda bazaka fahimci komai a cikinsa ba.

“Mr. Uchenna Franklin right ?”

A hankali ya gyaɗa mata kai, Hanam ta shiga nazarinsa, tabbas ta gane shi, shine Uche wanda sukayi makaranta tare, wanda giyar yarinta tasa yazo yace yana santa, dan ita a ganinta kawai wannan yarinta ce ba komai ba, duk da ya sauya ya ƙara girma kammaninsa sun ɗan sauya kaɗan, amma ta gane shi.

Sai dai kuma ba wannan ne abun da yasa take nazarinsa ba, tana nazarinsa ne sbd muryarsa ta yanzu, kamar ta tab’a jin muryar a wani wuri, saide ta kawar da tunanin.

“Ok tam da fatan Abba ya yi maka bayani ?”

“Eh ya yi min bayani, yaushe zamu fara dinkin ?”

“Zuwa gobe, yau zan sa a kaika ka zagaya fashion house ɗin kafin ka fara aiki”

“To…”

Kafin ya faɗi wani abun, yaji wani dan karamin hannu ya riƙo ƙafarsa ta ƙasa, a hankali ya sunkuya ya kalleshi, Damm! Wani bangaren na glashi ya fado a zuciyarsa, ganin wani yaro me tsantsar kama da matar dake zaune a gabansa, babu ta yadda za a yi ka kalli yaron kace ba jininta bane. Yaron kamashi yayi yana jan kafarsa, a hankali ya kai hannu ya ɗauko yaron ya ɗora akan cinyarsa.

“Yaron ki ne ?”

Ya faɗi yana masa wasa.

“Eh, yaro nane”

“Shine na farko ko na uku?”

Ta ɗanyi wani gajeren murmushi, har yanzu Uche bai sauya ba.

“Shine na biyar”

“Miye sunansa ?”

“Muhammad Aryaan, Arya”.

“Wow what a wonderful name”

Arya ya kama gemun Uchenna yana ja.

“Kai! Kai! Bari, wannan me tsada ne, hala Babanka baya dashi, shi yasa kake tab’a min nawa”

Ya faɗi yana kama dan karami hannunsa.

A karo na farko zuciyar Hanam ta motsa akan maganar mahaifin Aryaan, kowa kallon shege yake masa, babu wani wanda ya tab’a magana akan mahaifinsa kamar haka, wata ƙila shima Uchen dan bai sani ba ne.

Yana kallon reaction ɗinta, kuma nan take ya fuskanci cewa akwai matsala game da yaron, ko dai mahaifinsa ya rasu, ko kuma dai akwai wata a ƙasa.

“Baabaa”

Daga Hanam har Uchenna kallon Aryaan suke da tsantsar mamaki, Hanam bata tab’aji yayi magana haka ba, saide gwaranci amma baya magana haka, ko Mama bai iya cewa ba amma gashi yana kiran wani Baba, Baba?.

“Baba?, ko dai ina kama da Babanka ne ?”

“Khalisa zata zo ta zaga da kai, thanks for concern”

Hanam ta faɗi dan ta dakatar da bugawar da zuciyarta ke shirin yi, sai Uche yayi murmushi, ya miƙe ya zagaya inda take ya bata Aryaan ɗin, sannan ya shafa sumar kansa me taushi.

“God bless you my boy”

Daga haka kuma ya fice, Hanam tayi wata iriyar ajiyar zuciya tana dafe kirjinta.

“Ya’ani inta manak zau’u, bit ɗalla’a ala hada garib wa tuƙullu Baba, badal ma tafda’a ma’a ismi ana”

(Gaskiya kaikam baka da kirki, kawai sai ka kalli mutum ka kirashi Baba, maimakon ka fara da kiran sunan).

Kamar wani Babba idan yayi abu haka take masa faɗa, harda wata harara, sai kuma ya bata dariya ganin yanda yayi lamoo yana kallonta, shima tanayin dariyar ya bangale nasa wawulon bakin, Hanam ta aje shi akan table ɗin kayan aikinta sannan tayi pecking kansa tana shafa sumar kan nasa.

”Abu ummu inti galiz”

(Baban mama baka jin magana)

A hankali ta rungumeshi.

Maryam Pov.

Ba ta ankara ba har famfon sink ɗin ya cika robar dake hannunta har yana zuba, saurin kai hannu tayi tana kashe kan famfon, a hankakali ta juya ta kalli kitchen island ɗin, wanda ta cika shi da kayan kitchen ɗin, dan so take ta sauyawa komai ma’aji, amma gaba ɗaya ta kasa, tunani ne fal ranta, tayama zata iyayin wani ƙwaƙƙwaran aiki ?.

Ta tuna abinda yace mata jiya, dan second daya… biyu…

A na ukun ne wayarsa dake kan coffee table tayi ringing, kusan tare suka kalli screen ɗin wayar, ‘NEHA’ shine abinda aka rubuta, a gaban sunan kuma akwai heart emoji, gaban Maryam yaci gaba da buga a lokacin, wayar ya ɗauka ya miƙe, har ya kai kan stairs sai ya juyo ya kalleta a inda ya barta.

“An kawo kayan abinci, suna kitchen kije ki duba ki gani, idan akwai abinda babu sai ki faɗamin”

Cikin karfin hali Maryam ta gyaɗa masa kai.

Tana jin ya ja kofar ɗakinsa itama ta miƙe harda gudu ta shiga kitchen ta ɗauki abuncin ta data dafa na dare, ta koma ɗaki ta kulle.

Sai kuma ta tsunduma duniyar tunanin cakuɗɗaɗun zatukansa, wanda babu abu ɗaya data tsinta a ciki, gabaɗaya zantukan nasa sun ɗaure mata kai, wai me yake nufi da shi annoba ne? Me yasa zai kira kansa da monster? Kuma beast? Dama mutum yakan zama dodo ? Ko dai yayi hakan ne dan ta nisance shi ? To amma Fulani ta faɗa mata makamancin hakan.

Ko dai dan yana so ya auro wannan Neha ɗin ne yasa ya ce mata haka ? Kai ba ma haka bane, koma dai mi ya ye shi ya sani, amma kuma a can ƙasan zuciyarta a tsorace take, dan Maryam gwanar tsoro ce, sai dai tunanin zata koma makaranta, da na kayan abincin daya ƙara cika store ɗin da shi sai ya kore wannan tunanin, tunda dai har yace ta nisance shi, kuma yace ta riƙa kulle kofa ai shikenan.

Amma kuma duk da haka abincin data ɗauka bata samu ta ci ba, bacci ma da ƙyar tayi, daga ta ɗanji motsi zata farka, da haka har gari ya waye, kuma taji sanda ya fita masallaci, sai a lokacin ta sauƙo kasa ta mayar da abincin kitchen ɗin.

Sannan ta shiga store ɗin aje kayan amfani na gidan, ta ɗauko broom da squeegee da mop ta koma saman, ta share ko ina a ɗakinta ta goge, ta wanke toilet ma, haka balcony, ta buɗe curtains ɗin tana kallon yadda hasken rana ke baza duniya.

Ga tsirarin mutane na kai kawo, sannan ta dawo cikin ɗakin, kuma bata fita ba saida taji ya dawo daga masallaci, sannan ta fito, ta share corridor ɗin nan tayi moping sannan ta saka squeegee ɗin nan ta goge glass ɗin balcony ɗin.

A wajen taga abincin akun nan ta zuba mata harda ruwa, sannan ta ɗauko watering can, tayiwa flowers ɗin dake wajen bayi, kana ta sauƙo ƙasa, parlon ma ta gyarashi sosai harda wajen daning, dama store da ironing room, sannan ta shiga kitchen, kuma shi har yanzu bata gyara shi ba saboda so take sai ta gama shirya kayan cikinsa kafin ta gyara shi.

Da wannan tunanin ta ƙaraso island ɗin, ta ɗauko wasu gajerun kwalabe na glass wanda tasan cewa na species ne, ta riƙa juye kayan species ɗin har saida ta gama, sannan ta janyo wata cabinet guda haka ta jerusu.

Sai kuma ta dawo kan glass cups da smoothie jars da kuma mugs, suma ta jeresu a loka guda, tana yin aikin zuciyarta na washewa da farin ciki, plate da bowls ma nasu wajen da ban, sai kayan stainless steel cooking utensil set, ta aje su kusa da stove, oil containers din data zuba mai a cikima ta aje su kusa da set din.

Knife set ma a wajen ta aje shi, sai frying pan, work, set ɗin tukunya duka ta aje su a waje guda cikin wata cabinet, blender, greater da juicers suma tai musu ma’aji, kayan shayima su bournvita da su lipton ta sauya musu mazubi zuwa wasu containers na glass.

Sai da ta tabbatar da komai a killace yake sannan ta shiga share kitchen ɗin, kayan fridge ɗin ta barsu sai ta gama sharar.

Bayan ta gama sharar ta goge ko ina, sai kuma ta tsaya tana bin ko ina da kallo, wai ita zata nayin girki a wannan kitchen din, abun is un believable.

Fridge ɗin ta buɗe ta fitar da gabadaya tarkacen ciki duka har karafen fridge ɗin, ta wanke su sannan ta mai da su ciki. Ta ware kayan fruits ta saka su a cikin wata roba wadda ta gani a cikin fridge ɗin, kayan ganyema ta ware musu gu.

Ta ɗauko ma’ajin ƙwai, duka ƙwan da aka kawo wajen cret biyu haka ta jere shi a wajen sai taga harda space, kayan miya ma ta ware su da ban, kayan drinks kuma su ta fara sakawa a sama, su miones, bread gesha da dai sauransu duk ta killace komai.

Sannan ta rufe fridge ɗin, ta koma store ɗin, tana duba gabadaya kayan girkin, albasa, doya da dankali dama tun da farko saida ta ɗebo ƙasa a garden ɗin ta zuba a ƙasa sannan ta saka su a kai.

Ta san cewa zai je aiki, dan haka ya kamata ace tayi masa girki, dan haka tayi niyyar dafa masa wani abun me sauƙi idan har zai iya cin abincin data girka.

Sai kawai tayi niyyar yin sandwich da pancake, babu b’ata lokaci ta shiga aikin, tana ganin abun kamar mafarki, girki na ɗaya daga cikin abinda take so kuma yake bata nishaɗi, dan haka gaba ɗaya ko wace damuwa ta nemeta ta rasa.

Ta mai da hankali sosai akan aikinta, sandwich ɗinma a sandwich maker tayi, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta gama komai, saboda akwai kayan aiki.

Tana haɗa hot chocolate taji alamun ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Gabanta ya faɗi, dan tasan ba kowa bane face shi, dan haka ta juyo da sauri, a dai-dai lokacin da shima ya buɗe ƙofar yana kallonta.

Kamar jiya sanye take da hijabi, kuma tun daga ƙofar kitchen ɗin ya soma sauraron abinda ya zame masa wajibi, bugun zuciyarta, yasan cewa tabbas yanzu bata da abin tsoro daya wuce shi, tunda har ya faɗa mata waye shi.

Bai damu da tunanin da zatayi akan sa ba, amma yasan abinda yayi shine dai-dai, dan ya zama dole ya faɗa mata gaskiya.

Kuma jiya bayan wayarsa tayi ringing ya ɗauka ya koma dakinsa ya daga, kanwarsa ce Neha, wadda take da aure a Abuja. Sun jima suna waya har ya faɗa mata cewa yayi aure itama ta gama masa ƙorafi na yayi aure bai sanar musu ba, ya bata haƙuri kafin tace wai ya bawa matar tasa waya su gaisa, shi kuma yasan a lokacin ba lalle ta iya tsayawa a gabansa ba, wata ƙilama idan ta ganshi zuciyarta ta buga gaba ɗaya kowa ya huta, dan haka sai yace mata tayi bacci ta bari sai gobe zai haɗa su.

Bayan ta kashe kuma saiga kiran Daadi, kakarsa wadda ta haifi mahaifiyarsa kuma ita tana zaune ne a india, ita kuma faɗama ta shiga masa, kuma bama shi kaɗai ba harda me martaba take haɗawa.

Tana faɗin ai shine ya masa auren, dan bai basu muhimanci ba shi yasa bai faɗa musu ba, dan kar su aura masa ƴarsu shi yasa su suka aura masa tasu yar.

Saida ya fahimtar da ita cewa auren ya farune cikin gaggawa sannan ta kwantar da hankalinta, amma tace masa dole yazo india, ya faɗa mata cewa yana da aiyyuka da yawa, tace masa kada ya kuskura ayi bikin holi ba tare da yazo india ba, ya rantse tare da mata alkawari, kuma tace sai ya nuna mata alkawarin nasa, shi kuma yace zai tabbatar mata ta hanyar tara gashi a kansa bazai yi aski ba sai ranar daya zo india, da haka hankalinta ya kwanta, har tace ya gaida matar tasa daga haka wayar ta ƙare, kuma yayi mamaki daya ga wutar ɗakinta a kunne, dan kusan kwana yayi yana sauraron rabin ransa.

Kuma yauma da safe yaga wutar ɗakin nata a kunne, yana jin sanda take moping corridorn ma, yanzun ma ya fito ne cikin shirinsa na zuwa aiki, kuma shi bai iya riƙe yunwa ba.

Dan haka ya fito dan yaci abinci, a nan ne yaga ko ina na gidan ƙal ta share ta goge. Sai kuma gashi ya ganta a kitchen.

“Ina kwana”

Muryarta ta fito cikin sanyinta, kuma haka kamar da tsoro a ciki, ya fara takowa cikin kitchen ɗin yana amsawa da

“Lafiya, fatan kin tashi lafiya ”

Muryar tasa ta fito da wani irin sauti fayau, ba za ka tsinci komai a ciki ba, Maryam ta miƙe tana faɗin.

“Lafiya”

Store taga ya nufa, jim kaɗan ya fito sai ta ganshi da kayan girki, kenan abincin zai dafa, da ƙyar tayi ƙarfin halin faɗin.

“Ga abinci fa na girka maka”

Cak ya tsaya da kunna wutar da yake, a hankali ya juyo ya kalleta yayin da ita take tsaye a jikin island tana hada hot chocolate a cikin wata jar, ya kalli plate ɗin dake kan island ɗin, abinci ta dafa masa? Shi ta dafawa abinci ? Wata kulawa da baya samunta sai idan yana india, amma a nigeria kam sai dai idan Abuja yaje, dan tun yana yaro koda sau ɗaya Fulani bata tab’a masa girki da kanta ba, sai dai ta sa bayi su masa.

“Ke da kanki kika yi?”

Yayi tambayar ba tare da shi kansa yasan ya yi ta ba, kanta a ƙasa ta gyaɗa masa kai, sai ya fara takowa zuwa island ɗin, gaba ɗaya kamshin turaren sa ya cika mata hanci, kuma yauma kamar kullum sanye cikin kayan hausawa yake.

Wata shaddace a jikinsa Kansa kuma babu hula, wannan kyakyawar sumar tasa tare a kansa, saida ya kai hannu ya shafa sumar tasa yana kallon abincin, ashe a ƴan area irin tasu akwai wayyayu kamarta ? Gaskiya ta fita da ban.

“Na gode”.

Ya faɗi yana zama akan ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da island ɗin, Maryam ta kasa gaskata abinda take ji, godiya fa yake mata, gaskiya wannan abun azimun ne, kai kawai ta gyaɗa masa, bayan ta haɗa hot chocolate ɗin ta miƙa masa.

Sai yanzu ya kai hannu ya ɗauki sandwich ɗin ya kai bakinsa, saida ya lumshe ido, sannan yaci gaba da taunawa, daɗin abinci mara misaltuwa ne, ta iya girki sosai, ya cinye na hannunsa tas.

A lokacin ita kuma ta ɗauki nata ta bar masa kitchen ɗin bayan ta jere kayan da tayi amfani da shi a dish washer, dan bazata iya zama ga ta ga shi ba, yace su nisanci juna, to hakan take ƙoƙarin yi.

Tafida bai san ya cinye abinci ba sai da yaga plate ɗin babu komai, sai kuma ya dawo kan hot chocolate ɗin, shima ya shanye tas, bai cika cin abinci da yawa ba, amma yau yaci sosai, ya miƙe ya buɗe dish washer ɗin sannan ya saka plate da jar ɗin a ciki.

Ya buɗe freezer zai dauki ruwa, ya tsaya yana kallon komai a tsare, a ransa yace gyara da daɗi, dan shi ba wani bi takan kitchen ɗin yake ba, ya ɗauki ruwan ya sha sannan ya rufe.

Fita ya yi, ya koma ɗakinsa ya ɗauki wayoyinsa da hularsa da key ɗinsa ya dawo ƙofar ɗakinta ya ƙwanƙwasa.

Maryam na cin abinci ta miƙe ta saka hijabinta ta buɗe masa ƙofar, kuma kamar kullum gabanta na bugu.

“Zanje asibiti ne”

Shine kawai abinda ya faɗi bayan kofar ta bude Maryam ta bayyana a gabansa, kamar zata tambaye shi me zai je yi asibiti sai ta tuna ashe likita ne.

“A dawo lafiya, Allah Ya tsare”.

“Ameen, thanks for the meal”

Ya faɗi yana juyawa, kamar jiya yau ma Maryam tabi bayansa da kallo, tana gode masa itama a ranta.

<< Yadda Kaddara Ta So 14Yadda Kaddara Ta So 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×