Skip to content
Part 17 of 33 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Hanam ce kwance akan gadonta, daga gefenta kuma Arya ne zaune yana wasa, waya ce kare a kunnenta, tayi shiru tana sauraron matar dake iƙirarin cewa itace mahaifiyarta.

Wai mahaifiyarta? Matar da tun da tasa ƙafa ta bar nigeria kusan shekara ashirin da biyar bata ƙara waiwayowa ba.

Taje ta can ta haɗa wani sabon iyalin, ta manta da ƴarta dake nan cikin wani hali, hatta da date of birth ɗin yarta tata ta manta, tana da jika amma bata sani ba.

Da ta ga hotonsa akan dpn Hanam ɗin ta tambayeta waye? Hanam ɗin tace mata ɗanta ne, kuma bata ƙara cewa komai ba, bata tambayeta ba shin aure tayi ? Tsintar yaron tayi ? Ko kuwa.

Babu ɗaya data tambaya daga ciki. kuma sai tayi shekara bata kirata ba, itama kuma Hanam ɗin bata kiran nata sai dai idan ita tayi niyya ta kira. Dan ta riga ta faɗawa kanta cewar ba ta da mahaifiya.

“Izan shu an shaglik ?”

(To yaya aikin ki ?)

Muryar matar wadda daga muryarta zaka tabbatar dacewa balarabiya ce, ta fito daga cikin wayar, sai da Hanam ta wani jujjuya idonta sannan tace.

“Kullu tamam, kaif Awladik?”

(Lafiya ƙalau, ya yaranki ?)

“kullun mnah, am ya sallumu alaiki”

(Dukansu lafiya, sun cema suna gaisheki) Muryarta ta fito da fara’a, taji daɗi an tambayi yaya lafiyar yaranta, Hanam ta miƙe zaune tana cire wani zare a kan Aryan

“Biya’ar funi shi ?” (Sun sanni ne ?)

Sai da tayi dariya sannan ta amsata

“Hinin biya’arfuki kitir”

(Sun sanki sosai ma kuwa)

Hanam ta gyaɗa kai.

“Ibni bi hajati, salam”

(Ɗana yana buƙa tata, sai anjima)

“Oh ana asfe, kifu ibnik ?”

(Ohbyi haƙuri na manta, yaya ɗan naki yake?)

Ta manta ? Wai ta manta, taya za’ayi uwa ta manta da cewar yarta tana da ɗa? Ko da yake ba wani abun mamaki bane, hakan zata iya faruwa, tunda uwar ɗan ma manta ta ake, ai ba lefi dan an manta ɗan.

“Huwa nih, bitasil ma’ak ba’adain”

(Yana lafiya, zan kiraki daga baya)

Kuma bata jira cewar ta ba ta kashe kiran, kuma bawai dan Aryaan ɗin na bukatarta bane, wayarce ta isheta, komawa tayi ta kwanta tana kallon Aryaan, yana juyowa ya kalleta suka hada ido, his blue eyes ya tuno mata da shi.

Ta kawar da kanta gefe, a lokacin da shima yaron ya ci gaba da buga motar wasan dake hannunsa, kuma jiyowa tayi taci gaba da kallonsa, wani abu na mata yawo a ka, tunanin shekarun baya suka su shiga dawo mata, waɗanan shuɗayen idanuwansu.

Ƙofar ɗakin aka ƙwanƙwasa, dan haka ta miƙe zaune, Abba ne ya buɗe ƙofar ya leƙo da kansa.

Kuma tasan babu me mata hakan sai shi, sai kuma Rafi’a ƴar gidan Hajjo, dan Allah ya haɗa jinin yarinyar da Aryaan, tana shigowa ɗakin idan Hanam ɗin tana gida, kuma itama bata hanata ɗaukarsa.

“Abba”

Ta kira sunansa bacin ya shigo ɗakin

“Na’am, Bannute (Babu girl) ”

Ya faɗi yana kallon su ita da Arya, bayan ya tsaya kusa da su.

“Ki shirya jibine tafiya Hakuɗau”

“Ai kuwa gwara da ka tuna min, dan na manta, tare da sauran yaran gidan za muje ?”

“Eh mana, ba ƴan uwanki bane ?”

“Nima bance komai ba fa, zan tafi da motata ne ”

“To shikenan. Kai ƙatoto baka yi bacci ba ?”

Ya ƙarashe ya nawa Arya wasa, Hanam ta yi dariya, irin wadda take a duk lokacin da ɗaya daga cikin su yake tare da ita.

“Wasa ya ke, ka ce Abba sai ka fara bacci zanyi”

“Idan ya yi magana ai guduwa zanyi“

Yayi maganar yana ɗaukansa, gabaɗaya suka saka dariya.

Tafida Pov.

Ƙofar ɗakin Maryam ya dosa, kuma tun kafin ya ƙwanƙwasa ya tsinkayi muryarta tana karuntun ƙur’an, yaji wani dummm, idonsa yayi duhu, kamar ana so za’a zare masa ruhinsa ne, yaji kamar wani abu ne zai fita daga jikin nasa.

*****

Yayin da a can cikin wani rami, wani baƙin hayaƙi ya shiga yawo a cikin kwalbar, yana girgiza kwalbar.

*****

Gara ya buɗe ƙofar ya dakatar da ita daga karatun kafin ransa ya fita gabaɗaya, irin wannan yanayin yake shiga a duk lokacin da zai yi sallah, daga ya tada kabbarar harama zai ji wani yifff, kamar abu ya faɗo daga jikin nasa.

Sai kuma yayi sallahr cikin nutsuwa, yanajinsa saka yau, yana jin tabbas wannan shine, shine yake controling kansa ba wani ke controling ɗinsa ba, Sannan daga yace assalamu alakum na sallamar da sallah, wannan abun zai faɗo masa a ka.

Sai yaji kamar wani dutsene ya danne shi, kamar an ɗora masa wani abu akan nasa, kamar wani ke controling ɗinsa. Kuma a kullum a cikin irin wannan yanayin yake, sai dai idan sallah zaiyi.

Ya kawar da ko wani tunani dake kansa ya buɗe ƙofar kansa tsaye, shi tunda ta zo gidan bai ƙara shiga ɗakin ba sai yau, bai ganta a cikin ɗakin ba, kuma dama ba daga nan yake jin sautin ta ke fitowa ba.

Yau cike da farin ciki Maryam ta tashi, dama ita bata saba baccin safe ba, dan haka tana tashi ta shiga yin aikace-aikacen ta data saba, ta gyara ko ina.

Sannan tayi girki me sauƙi, taci nata ta aje masa nasa akan danning kamar yanda ta saba, taga launch box har guda biyu a kayan kitchen ɗin, dan haka ta zuba musu cake da meat pie ɗin da ta yi.

Kuɗin daya bata kuma ta saka a cikin wata daga cikin jakukunan da fulani ta bata, saboda idan ta dawo daga makaranta zata tsaya a super market ɗin ta yi siyyaya, yau zata huta da zaman kaɗaici, wataƙila ma sanda zata dawo gida shima ya dawo, dan haka kaɗaici ya ƙare.

Bayan da ta gama duk abinda za ta yi sai tayi wanka ta saka abaya a cikin kayan wajen Fulani, ta dauki ɗaya daga cikin hijabanta ta saka, ta zauna a ɗakinta tana jiransa.

Sai kuma taga da zaman banza ai gwara ta ɗan tab’a tilawa dan ta ɗan jima ba ta yi ba, ga azumin alhamis da litinin da take shima ta dena, ta ɗanyi tsaki kaɗan tana mitar sakacin da ta fara, kuma ta ƙudirce a ranta a cikin satin nan zata dawo da yin aziminta.

Ba taji shigowarsa ba, sai da taji takunsa, da kuma ƙamshin turaren sa, zaune take a balcony akan wannan kejarar me kamada lilo, ta dakatar da karatun a lokacin daya karasa shigowa balcony din.

*****

Kuma a lokacin ne wannan hayaƙin ya kwanta a ƙasa, kwalbar ta daina girgiza.

*****

Miƙewa tsaye tayi tana gyara zaman hijabinta, Allah ya temaketa yasa dashi a jikinta, kanta a ƙasa ta gaisheshi dan ya ce ta dai na tsugunnawa har ƙasa idan zata gaidashi, kuma kwata-kwata basu haɗu ba tun jiya da daddare. Ya amsa mata kadaran kada han, kamar yanda ya saba, fuskarsa babu fara’a bare walwala, ita tarasa meke damunsa haka.

“Kin shirya ?”

Muryar sa me zurfi da taushi ta tambaya.

“Eh na shirya”

Bai ce komai ba ya juya yana tafiya, Maryam tabi bayansa da kallo, kamar yanda ta san shi inde zai fita manyan kaya ne a jikinsa, yau wani yadine me kyau a jikinsa black color, hular kansa ma akwai ratsin baƙi.

Haka takalminsa, ita kam riƙon al’adar mutumin nan na bata mamaki, yanzu waɗanda suke hausawan ma gaba ɗa ba basa riƙe al’ada kamar haka, bare shi da ya kansace ruwa biyu.

Cikin ɗakin itama ta komo ta aje ƙur’anin a kan wata chest drawer, sannan ta ɗauki jakar data saka kuɗin nan a ciki da wayarta, itama ta fita.

A motarsa ƙirar Audi suka fita, Maryam kam yau tana cikin farin ciki, dan tunda tazo garin wajen sati ɗaya da kwanaki bata tab’a fitowa daga block ɗinsu ba sai yau, kuma ba su yi wata doguwar tafiya ba suka isa makarantar.

Komai shi ya mata babu abinda ta yi, kuma taji daɗi, daɗi sosai ta ji, dan hakama tun yanzu take tunanin abinda zata dafa masa idan ta koma gida, duk da ta koma baya abun bai dameta ba, ai dai zataci gaba da karatun.

*****

“Miriam”

Muryar Tafida ta faɗi yana kallon Maryam yayin da suke tsaye a jikin motarsa, dan tafiya zaiyi ita kuma yau zata fara shiga aji, bata amsa ba sai ɗagowa da tayi ta kalleshi.

Kasa jurewa kallon idonsa ta yi saboda sun mata tsauri da yawa.

Shi ma bai san me yasa ya kirata ba, kawai dai yaji baya so su rabu, baya so ta tafi sautin bugun zuciyar tata ya yanke masa. Launch box ɗin hannunta ta miƙa masa.

“Miye wannan ?”

“Meat pie da cake”

Ya tuna yadda ya ɗanɗana na jiya, kuma yasan cewa shine wannan ta zubo masa, sai kawai ya karb’a still yana kallonta.

“Meri aakho ka tara hai tu Miriam”

Kuma yana gama faɗin hakan ya buɗe motar ya shiga ya tafi, Maryam ta tsaya a wajen kalaman na maimaita kansu a kwakwalwar ta, ita bata jin indianci, amma tana kallon fina-finan india, kuma ta ɗan san wasu abubuwan, amma wannan kalaman daya faɗa mata babu ɗaya data gane, sai de ta riƙe su gam a kanta, kuma zata tambayi Google me kalaman suke nufi.

*****

Tafida ya shigo cikin corridorn da zai sada shi da office ɗinsa bayan ya fito daga elevator.

Wasu nurses ne suka gaida shi, ya amsa musu, kuma bayan ya wuce sai yaji suna wata hira data ɗauki hankalinsa, dan haka ya motsa kunnensa yana ci gaba da tafiya.

“Ke naji an ce wai yayi aure”

Ɗayar ta tambaya

“Eh mana, yayi aure kuma ance wai da yaje garinsu aka aura masa ita”

“Kenan itama ba’indiyar ce ?”

“Eh to bana ce ba, tunda ban ganta ba, kuma ai kinga yana saka kayan hausawa, wata ƙila hausace”

“Uhmm, ai ko idan ƴar masifar nan ta sani za’ayi bala’i”

“Wa kenan ?”

“Helen mana, ni bana ganinta ma, ta jima bata zo nemansa ba”

“Eh rannan tazo wai zata masa sallama, ta tafi abuja wani aiki, ke dai bari kawai, Allah ya kawota musha kallo”.

Yayi wani gajeren murmushi yana buɗe ƙofar office ɗinsa, shi sai yanzu ma su ka tuna masa da wata Heleen, ya manta da ita gaba ɗaya. Heleen? Wata mata da zai iya cew…

Ƙofar da khabir ya turo ce ta katse masa tunani.

Gaisawa suka yi kamar kullum kafin Khabir ɗin ya zauna.

“Ka kirani kace nazo”

“Eh, yanzu dama kai yaɗani ka yi ta yi a asibitin nan wai nayi aure?”

Khabir yayi dariya

“To ai abun farin ciki ne, lefine dan na faɗa ? Shine kaɗai dalilin kiran ?”

“A’a ba shi bane, hijabai muke so, kuma manya shine nake so a tambaya min Madam ina zamu samu?”

Yanzu ma Khabir ɗin dariyar ya sake yi

“What’s funny ?”

“A’a wai naga ka zama Maigida ne shi yasa”

Ya ɗanyi murmushi kaɗan

“Shikenan zan tambaya maka ita, though ita bama saka shi take sosai ba”

“To godiya nake”

“Bari na je ”

Khabir ya faɗi yana miƙewa, sannan ya fice.

Bayan wasu mintina wayar Tafida ta yi ringing.

Yana duba wasu files a cikin book shelf, ya ajiye wanda ke hannunsa ya jiyo ya ɗauki wayar. Muktar ne dan haka ya ɗaga ba jira, gaisawa sukayi kamar yanda suka saba kafin Muktar ɗin yace.

“Muna tare da su yanzu haka, godiya suke so su maka”

“Umhm bari ma kira video call”.

Daga haka ya katse kiran, laptop ɗinsa ya buɗe ya aikawa Muktar ɗin kira. Nan take Muktar ya ɗaga kiran, tare da seta wayarsa ga mutum biyun dake zaune a gefensa, Tafida na ganinsu ya tsinci kamarta a fuskarsu, duk da su sun ɗan fita kyau, duka a tare suka gaisheshi, ya amsa musu, ɗaya daga cikinsu ne yace.

“Mun gode sosai Yaya, Allah ƙara girma”

“Nop, kamar yanda kuka ce ni Yayanku ne, idan Yayar ku ta muku abu zaku mata godiya ?” A tare suka girgiza kai.

“Good to nima haka, we are all the same, ba kira nayi dan ku min godiya ba, kira nayi dan na ƙara jaddada muku cewa, ku kula da Mamanku sosai, kuma ku kauɗa kai daga abinda Abbanku yake, kada ku riƙa masa rashin kunya, musamman ma kai Hassan, nasan Hussain yana da haƙuri, amma karinƙa haƙuri kaima, kaga shi mahaifi ne, kuma mahaifa haƙuri ake dasu, dan Allah ku kiyaye”

“Insha Allah Yaya”

“Good boyz, yanzu ina asibiti, zamu yi magana daga baya”

“Dan Allah ka bamu lambar ta Yaya”

Ya ɗanyi jimm, shifa bashi da lambarta ma.

“Kawai ku turomin taku sai na bata”

“To zan turo maka”

Cewar Hassan, daga haka yayi sallama da su ya ci gaba da aikinsa.

<< Yadda Kaddara Ta So 16Yadda Kaddara Ta So 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×