Titin Kauyen Hakuɗau.
Da misalin 05:30pm.
Motoci ne guda biyar suka gangaro daga titin Auyo suka hau kan jan b'irjin da zai kai ka har zuwa cikin ƙauyen hakuɗau, tun daga kan hanya yara ke binsu har suka yi parking a ƙofar wani gida me ginin bulo irin ginin zamani.
Gidan kamar ba a ƙauye ba, hatta da fentin sa sabo ne, ƙofar gidan ma gate ne.
Yara da manya duka a ka firfito ana kallonsu, duk da ba wannan bane zuwansu na farko, suna zuwa lokaci-lokaci, sai dai kowa yasan cewa idan dai Alhaji. . .