Skip to content
Part 2 of 26 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

A hankali cikin natsuwarta take tafe sanye take cikin wani farin wide leg pant, sai wata bakar shirt, wadda ta ɗora mata farar suit a sama, hannunta rike da jakarta wadda ta kasance itama fara, gashin kanta cikin stail din braid (wato kalba) guda ɗaya, wadda ta sauko da ita kan kafaɗarta ta dama, ta saka robber band a karshen kalbar saboda kada ta warware, dan tsabar santsin gashin kan nata, daga karshen gashin nata tai masa kala da brown yayin da saman kuma yake baƙi, ta dora baƙin mayafi a saman kan nata, kamar yadda babu fara’a a fuskarta haka babu kwalliya.

Daga bayan ta kuma Naani din data ɗauka domin kula mata da ɗanta a office dinta ce biye da ta, yayin da take ɗauke da dan nata cikin baby carrier, idan ka kalli uwar ka kalli ɗan, baka buƙatar ƙarin bayani akan ɗanta ne, Saboda tsabar kamar da suke, banbancin su shine shi kalar kwayar idonsu ce, sai kuma farin da ɗan nata ya fita.

Daga ita har ɗan nata kana ganinsu kasan cewa half cast ne, duk da ita hasken fatarta kamar na indiyawa yake, dan nata kuma kamar ɗan larabawa.

Ko ina ta wuce a office ɗin sai an gaisheta har ta kai office ɗinta, yayinda naani ɗin kuma ta wuce da yaron zuwa ɗakin data tanada domin renon yaron nata.

Executive chair ɗin dake office ɗin taja ta zauna, sannan ta aje jakarta a kan table ɗin dake gaban kujerar tata, ta janyo ipad dinta ta buɗe domin ta fara duba wasu sabbabin design din dinkuna.

*****

Motarta kirar hybrid take tukawa akan titi, bayan ta tashi daga aiki, yayinda ɗanta sanyin idaniyarta ke zaune a seat ɗin me zaman banza, cikin car seat dinsa.

Jifa-jifa take juyowa tayi masa wasa, a gaba ɗayan rayuwarya bata da wani abu me mihimmanci bayan wannan dan nata da kuma mahaifin ta, su kaɗai tasan tana da su, ba ta jin tana san kanta kamar yanda take sansu.

Yau ta kama ranar zagayowar haihuwarta, bayan mahaifin ta da baya gari babu wanda ya kirata ya tayata murna, kuma dama hakance ta saba faruwa da ita a duk shekara, wattanin baya ita kaɗai ko ita da mahaifinta suka shagalin murnar zagayowar ranar haihuwartata, gashi kuma yau mahaifin nata baya gari, dan haka ta yanke shawarar yin shagalin daga ita sai ɗanta.

Dan haka ta parker motar tata a gaban chedi plaza shopping mall, ta ciro dan nata daga cikin car seat din dayake ciki, ta daukeshi a hannu ta nufi cikin mall ɗin. Bayan dan wani lokaci ta fito daga mall din hannunta rike da leda me dauke da tambarin mall din, wanda aka sako mata dan karamin cake din data siya a ciki ( bento cake), ta dawo ta zaunar da yaron a seat dinsa ita kuma ta zagaya ta shiga driver seat ta ci gaba da tuki.

A gaban maƙararen gidan nasu ta tsayar da motar ta danna horn cikin salonta, wanda bayan ita da me gidan kansa babu wanda yake irin wannan horn ɗin, hakan tasa me gadin nasu buɗewa gate ɗin cikin sauri, dan ya gane cewa itace, saboda me gidan baya gari.

Shigowa tayi da motar tata, tayi parking a parking lot, ta fito daga motar ta ɗauki yaronta haɗi da jakarsa da kuma tata sai ta ledar cake ɗin data siyo.

A babban parlon gidan nasu ta samu kowa na gidan, tun daga iyayen yaran har yaran, bata ko kalli inda suke ba ta haye tagwayen benin dake parlon domin shiga ɗakinta

“Mtswww! Aikin banza, wallahi na tsani ganin yarinyar nan, idan na ganta ji nake kamar na bita na shake mata wuya ita da wannan shegen ɗan nata”

Cak ta tsaya daga tafiyar da take, ta juyo a hankali ta kalli babban yayanta kamal dake wannan batu, a hankali ta aje jakukunan hannunta a kasan tiles ɗin dake saman stairs ɗin, dan har ta kai ƙarahe, sauƙowa ta farayi tana tunkarar cikin parlon

“Ya Kamal gata nan fa zuwa” ƙanwarsa na’ima ta faɗi tana kallonta, mahaifiyarsu hajiya mero ce ta buga uban tsaki “sai me kuma idan ta zo ? Ko dukansa za tayi?”

Gabansa tazo ta tsaya, shima ganin hakan yasa ya miƙe tsaye, harma da kowa na parlon “Kamal kake ko wa? Ka da ka ƙara jifan ɗana da kalmar nan ta shege!, ɗana yanada uwa kuma yanada uba, kuma duka nice, dan haka ɗana ba shege bane, ka riƙa kula da kalamanka, idan har a kaina zasu tsaya ba zan tanka maka ba, amma idan har suka ƙetara layi zuwa kan ɗana” tayi wani murmushi me ciwo “zan koya maka hankali kaida wannan uwar taka da bata gabana, bana shiga sabgar kowa, dan haka bana buƙatar kowa a tawa sabgar, ɗana ɗanane, babu wani wanda keda iko dashi, ka fita sabgarsa” “Ke! Dan tsabar baki da mutinci akan wannan sheg…”

Bai samu damar karasawa ba, sakamakon marin data sakar masa a kumatumsa na hagu, ya dafe wajen idanunsa waje yana kallonta, bama shi kaɗai ba, kowa dake parlon saida ya kama baki yana kallonsu su duka, cikin mamaki, a da idan sun maga abu bata kula su sam, amma gashi yanzu harda mari “ke Hanam dan baki da hankali shine zaki mari ya kamal?” Kanwar kamal ɗin rahina wadda suke uwa daya ta faɗi “na mareshi ɗin, ko akwai me rama masa ?… Kai kuma” Ta faɗi tana juyowa kan kamal ɗin dake dafe da kunci yana kallonta da tsananin mamaki “na faɗa maka cewa ka fita sabgar ɗana, dani kake faɗa ba dashi ba, kuma ɗana ba shege bane, nice ubansa mark my words”

Tana kaiwa nan ta bar wajen a fusace, ta bar kowa da baki a sake yana kallonta, dama sun saba mata cin kashi, babu kalar baƙar maganar da basa faɗa mata, tanayin haƙuri ta shanye, amma yau sun kaita bango.

*****

Zaune suke a haɗaɗɗen dakin ɗan nata, wanda bai cika girma sosai ba, saide cike yake da kayan wasa kala-kala, yaron na zaune cikin floor seat, yana wasa da rattle ɗinsa (kacar-kacar), sanye yake cikin onesie (over rall)baka.

Yayin da Hanam ke zaune a gefensa cikin Wata linen tunic dress, rigar dama ta zaman gidace, bento cake ɗin nan ta dauko ta buɗeshi daga cikin take away ɗin da aka saka shi ‘HAPPY BIRTHDAY’ shinr abinda aka rubuta a jikin cake ɗin “Aryaan, yau mummy take birthday, let’s cut the cake” Ta faɗi tana kallon yaron, kamar wani babba  aka take magana dashi, dan hatta dariyarta da mutane suka dena gani cikin wannan shekarar toshi tana masa, karamar wuka ta dauka ta yanka cake ɗin tana wakar happy birthday, cake ɗin ta yanko ta kaiwa yaron baki, yaron ya buɗe ya karba yana ci, itama ta yanko ta saka a nata bakin, tana masa wasa ta dauki tisseu ta goge hannunta sannan tana kallon yaron ta fara cewa “Abu Ummuh  nas bi ƙulu innak ibn gair shar’i, bas ummak bita’arif innak shar’i, li’anna hiya yalli wulidtak, wa rabaitak, wa ɗaitak killil hub, ya ibn hayyi duniya yalli nahni fiyya annas ma bihibbul kil, bihibbu nafsun wa bas, bas saddiƙni ana kitir bihibbaka, wa ana ba’arif innaka bta’arif hasshi sah?”

(Baban mamansa mutane suna cewa wai kai shegene, amma mamanka tasan cewa kai ba shege bane, Saboda mamanka ita ta haifeka, ta reneka, kuma ta baka kowace iriyar soyyayarta, ɗana wannan duniyar da muke ciki ba kowa ke san wani ba, kansu kawai suke so, amma ka yarda dani dan ni ina sanka sosai kuma nasan kaima kasan hakan ko?) “Abu ummu ta’al ila huna (baban mamansa zo nan)” Tayi maganar tana daukansa ta rungume shi a kirjinta tana pecking kansa “ni bazan taba guduwa na barka ba, kamar yanda tawa mahaifiyar ta gudu ta barni”.

Maryam Pov.

Zaune suke gaba dayansu akan babbar tabarma, ita da Maamu da muhsin suna cin jallof ɗin taliya da waken da Maryam ɗin tai musu da daddare, yayinda Hussain da Hassan suma suke cin nasu daban, Hussain sai zabga santi yake, dan idan batun girki ne to Maryam ba daga baya ba “Kinsan allah yaya, ni ji nake na kamar akawai kifi a ciki ” Maryam da Maamu suka masa dariya, banda muhsin dake shirgawa cikinsa abinci, da kuma Hassan da dama shi can miskili ne “au dariya na baku ?”

“Eh mana, Muhsin ɗauko pillow nai masa waigi, dan naga ƙiris ya rage ya faɗi…” Sallamar mahaifin suce ta tsayar da hirar, ya shigo cikin gidan yana musu kallon ɗai-ɗaya, wanda hasken fitilar da suka kunna ya bashi damar ganin fuskokinsu, sigarinsi yake busawa kamar kullum, Maryam, Hussain da muhsin suka masa sannu da zuwa, yayinda Maamu da Hassan ko takansa basu bi ba, kuma kamar yanda ya saba babu wanda ya kula a cikinsu, idan da sabo sun saba, amma kuma kullum basa fasa gaidashi “Ina abincina ?” Hassan ya zaburo za ice, ya basu kuɗin abincin ne ?, Hussain ya riƙe hannunsa yana girgiza masa kai, Hassan yaji kamar ya saka ihu dan tsabar takaici, Hussain ya juya ya kalli Maryam. Yaya ki zubawa Abba abinci”Maryam ta miƙe ta nufi rumfar da suke girki, Maamu taji wani malolon takaci ya tsaye mata a maƙoshi, kamar yanda ya saba maƙale mata a duk sanda zata kalli tijjani a matsayin mijinta.

Sam bata san ta riƙa sa’insa dashi a gaban ƴanƴansa, dan sam bata san su renashi kamar yanda Hassan ya rainashi, shi kullum babu ruwansa da ya suka tashi?, yaya suke?, shin suna cikin halin bukata? ko aa, babu ruwansa da cinsu, shansu, sitirarsu, kula da lafiyarsu, duka bai damu ba. Maryam ta dawo hannunta rike da wani ƙaramin food flask ta tsugunna ta mika masa, a wulaƙance ya kar6a sannan ya juya ya fice daga gidan, da alama yau bazai kwana a gidan ba.

Maamu taji wata kwallar baƙin ciki na shirin sauko mata, amma sai ta dake, ta hana kanta yin hakan, domin sam ko kaɗan bata san yaranta su karaya, tasan da cewa itace kwarin guwarsu, idan har ita ta gwada rauni, to su yaya zasuyi ? “Manmu dan allah”

Maryam ta faɗi a sigar roƙo tana gargiza mata kai, Maamu tayi murmushin takaici, tana kawar da kai “Maryam kenan, aini na jima da hana hawayena zubowa, idan de har akan tijjani ne, to bazan ƙara kuka ba”

Gaba ɗaya yaran nata sai jikinsu yayi sanyi, sun san halin mahaifinsu sun kuma san irin abinda yake a waje.

*****

Maryam ce kwance a ɗakinta, cikin gidan sauro ita da muhsin, shegen tsoronta ya hanata kwana ita ɗaya, Allah ya hallito ta da wani irin bala’in tsoro, yanzu hakama fitsari take ji, kuma gashi tana tsoron fita ita kaɗai, dan tsabar tsoranta ko horro film bata iya kalla, hannu ta kai ta dan daddaki muhsin, ya miƙe zaune cikin magagin bacci “mu je mu yi fitsari auta” “Uhum”

Muhsin ya amsa cikin magagin bacci, net ɗin ta ɗage a hankali, gudun kada ta ɗuro musu sauro, ita ta fara fita sannan shima ta fito dashi, aƙƙalla idan da muhsin ɗin ba za ta ji tsoron sosai ba, lokacin suna kwana da anti fati itace take rakata idan fitar dare ta kamata.

Tafida Pov

A hankali ya shiga ƙif-ƙifta idonsa bayan rana ta ratso ta cikin katangar glass ɗin dake ɗakin, miƙewa yayi zaune yanata waige-waige, shi tun bayan daya dawo daga masallaci baisanma bacci ya kwashe shi haka ba.

Miƙewa tsaye yayi yana miƙa, yau monday dan haka dole yaje aiki, gashi kuma yanajin jikinsa babu daɗi, and so weak, dan haka ya nufi kofar toilet ɗin ɗakin, ya buɗe da hannunsa tunma kafin ya ƙarasa jikin kofar, ta hanyar nuni da handle ɗin kofar.

Bayan jimawar wani lokaci sai gashi ya fito, a gurguje ya shirya dan ya kusa makara, wata bluen shadda ya saka ya dora hula dara itama blue, ya saka flat takalma.

Ya sauko ƙasa da sauri, kitchen ya faɗa ba zai iya jira yayi girki da kansa ba, dan haka yayi amfani da ƙarfin dayake dashi ya hada girkin ya saka launch box, dan sam bashi da lokacin da zai zauna yaci.

A gurguje ya shige office ɗinsa bayan ya kai asibitin “Tafida ya akayi ka makara yau ?”

Khabir ya faɗi bayan ya biyoshi cikin office ɗin “kaide bari, wallahi yau banajin daɗine, kaga ko abinci ban samu naci ba”

Tafeedan ya bashi amsa yana saka lap coat ɗinsa “to Allah kyauta, madam tana gaishe ka” Tafida Ya yi murmushi “A ce nima ina gaisheta” “Yauwa HELEEN ta zo jiya, tace wai na sanar maka cewa zatayi tafiya, bata da ishasshen lokaci da taje gidan naka ta same ki” Tafida ya yi masa banza, yana jan keyboard din desktop dinsa, khabir yayi murmushi yana jijjiga kai, dama yasan ko ya masa maganar ba zai kula ba, dan yasan Tafidah, ya kuma san waye shi.

Wayarsa ce ta ɗau ringing dan haka ya ɗauke hannunsa daga kan keyboard ɗin, ya kai hannunsa da sauri yana ɗaukan kiran ganin wanda ya kira ‘MUMZZY FULANI’.

Da sallama a bakinsa ya ɗaga wayar, yana murmushi, cike da girmamawa yake gaida wadda yake magana da ita a wayar “Yaushe zaka shigo ne?”

Muryar matar me cike da ƙasaita da kuma kamewa ta fito daga cikin wayar “yaushe ne wai bikin ?” Sai da ta ɗanyi jimm, ba wai dan ta rasa abinda za ta ce masa ba, sai dan ƙasaita sannan ta bashi amsa “saura kwana biyar” “Watakila gobe na shigo” “ Allah ya kawo ka lafiya” “Allah Ya ƙara girma”

Daga haka kuma wayar ta ƙare, khabir dake zaune a kujerar dake fuskantar Tafida yace “ina za ka je ?” Yana ci gaba da danna desktop ɗin ya furta “Hadejia”.

<< Yadda Kaddara Ta So 1Yadda Kaddara Ta So 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×