Skip to content
Part 23 of 25 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Yau tana cikin farin ciki, idan ya faɗi abinda yake son faɗi to wannan farin cikin nata zai wargaje ne rugu-rugu, amma ya zeyi ?, dole ya faɗa mata tunda ya zama dole.

Kiran sallah aka ƙwalla, Maryam ta shiga kokarin tashi hannunta na dana riƙe da chocolate tana faɗin.

“An kira sallah, bari naje na sha ruwa…”

Hannunta da Tafida ya riƙe ne yasa ta kasa gama faɗin abinda take shirin fadi, jikinta ya shiga karb’ar irin yanayin da ta saba ji a duk sanda zai tab’ata.

A hankali ya janyo hannun nata ta zauna, wannan karon kusa dashi, kusa dashi sosai, dan har suna gogar juna, wata iska ta maƙalewa maryam a maƙoshi ta juyo tana kallo jar ƙwayar idonsa da har yanzu bata koma blue ba, kasa jurewa tayi dan haka ta kawar da kan nata.

Tafida ya saki hannunta, ya dawo dashi ya riƙe fuskarta ya raba yatsunsa a tsakanin kunnuwanta,maryam ta lumshe idanuwanta ta buɗe, wai ina Fidar yara yake so ya kaita ne?

“Miriam”

Ya kira sunanta cikin irin muryar da ta saka jikin maryam rawa.

“Nayi magana da Mustapha, ilham zata zo ta riƙa taya ki kwana, sbd zan tafi Abuja gobe, kuma kwana biyu zanyi, zanje wani meeting na W.H.O (world health organization) da St. Nicholas suka turani na wakilce su…”

Chocolate ɗin dake riƙe a hannun Maryam ta sub’uce ta faɗi ƙasa.

HANAM POV.

“Wai yanzu ke miye mafitar auran nan ?”

Falaq ƙawarta ta tambaya, Suna zaune ne a office ɗin falaq ɗin, ita mawaƙiyace kuma yar kasuwa. Hanam ta gyara riƙon Arya dake hannunta sannan tace.

“Ban sani ba Falaq, ban sani ba, tun bayan faruwar auren nan ban ƙara samun damar magana da Abba ba, bamu samu wani zama ba”.

“Ai kuwa ya kamata ace kije ki sameshi kuyi magana, dan bazai iyu ba, taya za’ayi ki ci gaba da zama da auren Cristian, yau kusan wata ɗaya fa!”

“Hakane, ba matsala zanje na same shi ɗin, amma kinsan me Falaq?, da ace Uche musulmi ne da ya morewa rayuwa”

Falaq ta gyara zama tana faɗin

“A’a fa Hanam, karfa ki faɗa, tam”

Hanam ta watsa mata harara

“Ban gane kar na faɗa ba, kinji nace ina sansa ?, kawai halayensa masu kyau ne suke burgeni, he is very kind wallahi”

Falaq ta gyaɗa kai.

“Gaskiya kam dama Uchenna ba daga nan ba, kinga fa tun muna makaranta yafi mazan class ɗinmu amma ya mayar dasu abokai, kuma sam bashi da abokin faɗa”

“Falaq bari na tashi na tafi, gobe zanje na yi magana da Abba”

Ta ƙarashe maganar tana miƙewa, itama Falaq ɗin miƙewar ta yi, suna hira har suka fita daga ƙaton mall ɗin falaq ɗin.

Bayan ta koma gida ta yiwa Arya wanka sannan itama ta yi, ta kawo shi parlo ta aje sannan ta koma kitchen dan ta samamusu abin da zasu ci, har yanzu bata fara girki da Uche ba, amma kuma Aryaan ya kama abinci a kwanakin nan.

Tana ɗora tukunya akan stove ɗin gas taji Arya ya ƙwalla ƙara, ko gas ɗin bata samu damar kunnawa ba ta futo a ruɗe, ta sameshi zaune kusa da socket ya ɗaga hannunsa sama yana kuka, hakan ke tabbatar mata wuta ce ta ja shi.

Da sauri ta ƙarasa inda yake a zaune ta ɗauƙeshi tana rarrashin sa, amma yaƙi hin shiru.

“Me kika masa ne ?”

Taji muryar Uche daga bayanta, ta juya bakin ƙofar ta kalleshi, kallo ɗaya zaka masa kasan cewa ya gaji, dan dawowarsa daga aiki kenan.

“Wuta ce ta ja shi”

Wata uwar zabura Uche ya yi sai ganinsa ta yi a gabanta, briefcase ɗin ma daya shigo da ita ya cillar a bakin ƙofa, yanda yake jin ɗan nan a ransa Allah ne kaɗai ya sani.

Kuma tun da ma yana san yaron bare yanzu da suka haɗa gida ɗaya. Wuta ya ja yaron amma shine take wani ce masa wai wuta ta ja shi, babu ma wata damuwa a tare da ita.

Fincike yaron ya yi a hannunta ya shiga dudduba jikinsa yana faɗin

“To wai duk kina me kika bari wuta ta ja shi ?!”

Cikin faɗa-faɗa yake maganar ga kukan Aryaan na tashi kamar da ake zigashi, Hanam ta tsaya tana kallonsa ganin duk yanda ya ruɗe, ko ita bata ruɗe haka ba, har wata zufar tashin hankali yake.

“Mstwwww, asibiti zamu tafi”

kuma yana kaiwa nan bai tsaya jiranta ba ya fice.

Kitchen ta koma taci gaba da girkinta, a kai-akai take murmushi, tana jin daɗin yanda Uche yake kula da su ita da ɗanta, yana nuna dumuwarsa a kansu, wani abu da ya yi ƙaranci a rayuwarsu ita da Aryaan ɗin, bayan Abba da Baabaa ko Baba bata jin akwai wani me san su bayan shi.

Tana parlo tana cin jallof ɗin taliyar data dafa ta ji ƙarar tsaiwar motar Uche, tana zaune a gun suka shigo, ta juya ta kallesu ba tare da ta amsa sallamar Uche ba.

Mutumin da aka fita dashi yana kuka wiwi shine ya dawo hannunsa rike da chocolate ga wasu kayan wasa a hannunsa se dariya yake.

Uche ya ƙaraso ya miƙa mata Arya sannan ya zube akan kujera yana meda numafashi, Allah ya sani yau ba ƙaramar gajiya ya yi ba, ga yunwar da yake ji, kamar daga sama ya ji muryar Hanam.

“Kaje kitchen ka ɗauki abincin ka”

Wani abu da be tab’a faruwa ba a zamansa da ita gaba ɗaya, yau sun kusa wata ɗaya da aure amma bata tab’a dafa abinci da shi ba sai yau, ɗagowa da kansa ya yi ya kalleta, ba shi take kallo ba, Arya ma take cirewa riga, yasan de ba za tayi wa Arya magana haka ba, kenan dashi take.

“To na gode”

Miƙewa ya yi ya tafi ɗakinsa saida ya yi wanka sannan ya sauƙo ya ɗauko abincin ya ci, wani abu sabo, wanda bai tab’a samu ba a zamansa da Hanam.

MARYAM POV.

Kallonsa kawai take, yayinda suke tsaye a kan balcony ɗin kofar parlon gidan, idanuwanta sun ciko da ƙwalla, dan tun jiya da ya faɗa mata bata samu nutsuwa ba, ko buɗa bakin ma ba ta yi shi cikin daɗin rai ba, haka ta kwana maƙale da teddy bear ɗin nan, gashi kuma yanzu ya gama shiryawa zai tafi.

Kamar yanda take kallonsa shima haka yake kallon nata, karara yake ganin damuwa a idonta, yasan bazata so tafiyarsa ba, dan bata saba zama ita kaɗai ba, duk da yayi magana da Mustapha kan ilham zata dinga zuwa tana taya ta kwana, amma yasan duk da haka bata so ba.

Sab’anin kullum yau sanye yake da suit baƙa, jakarsa kuma wadda ya saka kayansa riƙe a hannunsa, yana ci gaba da kallonta.

“Miriam”

Maryam ta sauƙe kanta ƙasa, a sannan hawayen da take riƙewa suka silalo, ta cije lebenta na ƙasa, har ga Allah bata so ya tafi, sam bata so ya tafi ya barta, amma ya za ta yi?.

“Na tsefe kaina tun last week, zan tambayi Maman Ilham inda take zuwa kitso, zanje amin…..”

Muryarta ta fito cikin rauni, kamar tana daf da fashewa da kuka, kuma har yanzu kanta a sunkuye yake tana wasa da hannayenta.

“Bana san kitso Wifey, kar ki yi…..”

Yanzu ma bata ɗago ta kalleshi ba, duk da maganar ta bata mamaki, shima kuma ganin bata dago ɗin ba yasa yaci gaba.

“Na fiso a bar gashi a tsefe dan yafi kyau, dan haka ma da nake son na auri ba’indiya, ki bari indan na dawo akwai inda zan kaiki a miki gyaran kai”

Kai ta gyaɗa masa, kuma har yanzu kan nata a ƙasa yake, taƙi yarda su haɗa ido.

“Daasoooo!”

“Um”

Ta amsa still kanta a ƙasa, jakar hannunsa ya aje, sannan ya kai hannunsa ya kamo fuskarta da duka hannayensa biyu, ya ɗago da kanta tana kallonsa, hawayen ya share mata da hannayensa sannan ya yi pecking goshinta, Maryam ta lumshe ido wasu hawayen na ƙara zubo mata.

“Bye wifey, take care of yourself”

Muryarsa ta fito bayan ya saki fuskarta, jakarsa ya ɗauka sannan ya juya ya fara taku domin fita daga gidan, Maryam ta ji kamar ta bishi, kuma kamar ta riƙe shi ta hana shi tafiya, tace kar ya tafi ya barta ita ɗaya, dan Allah ya dawo.

Tana wajen har ya fice daga gidan, dan devid ne zai sauƙe shi a airport, kuma devid ɗin yana waje.

Hadejia Emirates

“Hajiya Turai ina ga abin nan fa baya cin Tafida”

Muryar Fulani Sadiya ta fito cikin wani irin shakku, wayece kare a kunnenta yayinda take zaune kan ɗaya daga cikin lintsima-lintsiman kujerun parlon ta.

Daga cikin wayar aminyarta hajiya Turai tace.

“To ke ya akayi kika san da hakan ?, bayan shi bama ya garin”

Fulani Sadiya ta gyara zama.

“Bazaki gane ba ai, wato da ace asirin ya cishi dole zamu sani, sbd bazai iyu ba ace yana ciwo me martaba be sani ba”

“Kuma hakane, to amma yaya kenan ?”

“Wata ƙila yan uwan uwarsa ne suka tsafa shi yasa asiri baya cinsa, kinsan indiyawa da tsafin bala’i”

“Kina da gaskiya, to amma yanzu miye mafita ?”

Fulani Sadiya ta gyara zama hadi da sauyawa wayar riƙo zuwa kunnenta na hagu.

“Ke nifa yanzu ba dumuwar Tafida ce a gabana ba, damuwar Galadima ce”

Muryarta ta fito cikin tsantsar damuwa.

“Galadima kuma ?, me ya same shi ?”

“Kede bari Turai, na kasa gane kan yaron nan wallahi, kullum ina nuna masa da ya zama na kirki amma shi kullum yana kara kauce hanya, yanzu kinga kowa yasan halin rashin mutuncin sa har ƴan uwan me martaba, dan suma ba ƙyale su ya yi ba, Mairama ce kaɗai take iya taka masa birki, kuma kin san yanda suke san Tafida dan shi yana musu biyyaya sosai, kinga ko auren da suka masa be yi musu ba ya karb’a, duk kuwa da baya san auren, yanzu dan Allah idan aka ci gaba da tafiya a haka ba mune a ruwa ba ?”.

tana iya jiyo ajiyar zuciyar da Hajiya Turai ta yi kafin ta ji tace.

“To gaskiya ya kamata ace an nemi mafita, bai kamata a ce an ci gaba da zama a haka ba, yanzu de abu ɗaya ya kamata ki yi”

“Faɗamin me ya kamata na yi ?”

“Ki ƙara tura jakadiyarki wajen Galli-Galli, ki ce ke so ki ke a nakasar dashi, kuma wannan karon kice aiki me ƙarfi ki ke so a yi wanda bazai karye ba, ko da sama da ƙasa zata haɗe kada a tab’a karya aikin, kinga idan kika zauna kika yi sake, to wallahi Fulani Khadija ba shiru za ta yi ba, kinga de ita bata haifa ba, kuma ita ta reni Tafida, to duk yanda za ta yi, za ta yi taga an ɗora Tafida akan mulkin nan bayan babu Me Martaba, kinga koda shi Galadima yaci gaba da abinda yake idan shi Tafidan ya nakashe babu wanda za’a ɗora sai Galadima, ko ana so ko ba’a so”.

Fulani ta yi wata kasaitacciyar dariya, abinda ya taru a ranta na damuwa na washewa, me yasa to ita ba ta yi wannan tunanin ba.

“Na gode Turai, kuma da yardar Allah hakan za’ayi”.

Daga haka sukayi sallama ta aje wayar ranta fes, ai babu kuma abinda zata ƙara jira, yanzu-yanzu zata aika jakadiya wajen Galli-Galli, wato bokansu.

MARYAM POV.

Gaba ɗaya kwanaki biyun da Maryam ta yi a gidan jin su take kamar shekaru biyu, duk da da safe zataje makaranta, bayan ta dawo Ilham za ta zo su zauna har dare ta kwana sannan itama ta koma gida sbd tata makarantar, amma sam Maryam bata jin daɗin gidan, ashe idan babu shi gidan lami ne, kullum cikin murza goben hannunta take, kuma sai bayan tafiyarsa ta tuna cewar itafa bata da lambarsa ma.

*****

Yau bayan ta taso daga makaranta ta zauna a parlo tana abinda ta saba a kwana biyun, wato tunani, ta dafa abinciccika kala-kala, tunda yau take sa ran dawowar Tafida.

Wayarta ta buɗe ta shiga tiktok, kwana biyun sam ba ta yi posting ba, dan me mata editing baya nan, sai kawai ta shiga buɗe comments tana replying, yawanci tambayoyine ake mata akan me yasa ba ta yi update ba, domin kullum sai ta ɗora vedios biyu, safe da rana.

Ji ta yi kamar ana tab’a ƙofa, a ranta tace wata ƙila ilham ce, saide ta ɗago ta kalli ƙofar, a lokacin da aka turo ƙofar, ta yi arba da wanda ke tsaye a bakin ƙofar.

Bata san sanda ta miƙe tsaye ba, ta ƙarasa bakin ƙofar da sauri, idanuwanta cike da murna fal, sai kuma taja ta tsaya tana kallonsa, kewarsa da ta yi na tsawon kwanaki ta gushe, tunda yau de gashi a gabanta yana mata wannan murmushin nasa me sace zuciya ya sakata a kwalba ya rufe.

Sai kawai ta saya ta ci gaba da kallon nasa yayinda shima kyawawan blue eyes ɗinsa ke kanta, jakar hannunsa ya saki a ƙasa sannan ya ƙarasa shigowa cikin parlon ya tsaya a gabanta, kuma ba tare da tunanin komai ba, ya jata jikinsa ya yi hugging nata, Maryam ta lumshe ido hawayene masu ɗumi sauƙo mata.

“You miss me this bad ?”.

Abinda ya faɗi kenan yana gyara rikon da ya mata.

*****

<< Yadda Kaddara Ta So 22Yadda Kaddara Ta So 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×