Skip to content
Part 25 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Hadejia Emirates

Da Misalin Karfe  09:30pm

Galadima ne zaune a Parlon ɗakinsa yana ɗaga kwalbar giya yana tittilawa a bakinsa.

Bai san wata masiface ta same shi ba, a wattanninan kuma giya yake sha’awar sha, ya kasa gane dalilin da yasa duk asirin da za’ayiwa Tafida baya kamashi, me makon ma ya kama Tafidan sai de shi ya yana aikata abinda akayiwa Tafidan asiri a kai.

Kuma har yau ya kasa faɗawa Fulani cewa asirinta fa baya cin Tafida, shi ya ke ci, sbd yana jin daɗin abun, shi yasa baya so ya faɗa mata bare ta dena.

Kansa ya ji yana masa ciwo kaɗan-kaɗan, sai ya aje kwalbar, a hankali a hankali ciwon yake ƙaruwa, kansa ya dafe sai kuma yaji ƙashin hayansa ya amsa.

Wata iryar ƙara ya saki yana riƙe bayan, sai kuma bakinsa ya gurɗe ya koma gefe, harshensa ya karye, ƙafafuwansa suka malkwaɗe masa, ihun ma ya kasa yi sbd bakinsa daya koma gefe harshensa ya harɗe, hannayensa ne suma suka shanye nan take, ya dawo kamar lagwani.

Fulani Sadiya na zauna a parlo tana duba wasu kaya a waya, ta ji ƙarar Galadima, A kiɗime ta mike ta yi b’angaren da ɗakin nasa yake, tafiya take sauri-sauri, gudu-gudu.

Da haka har ta iso ƙofar parlonsa hannu ta kai ta buɗe ƙofar, abinda ta fara arba dashi shine, Galadima ne yashe a ƙasa, kansa a langwab’e a gefe, bakinsa ya goce, yawu na zuba ta gefen bakin nasa, hannayensa a shanye, ga ƙafafunsa sun malkwaɗe kamar wani alkaki.

Wata razananniyar ƙara ta saki haɗi da salati hannunta a ka, sai kuma ta yanke jiki ta fadi.

(Ta mance cewa Allah ne me komai da kowa sai yanzu dan taga ɗan da cikin wani hali ta ambato sunansa,hmmm Allah ya fishemu).

MARYAM POV.

Ta juya a gaban mirror yafi sau goma, chickankari(pakistan) ɗin da ta saka ya bala’in mata kyau, gashi ya karb’i jikinta kamar da aka gwada da ita, waje ta samu ta zauna akan stool ɗin gaban dressing mirror, tana bin kayan kwalliyar da suke kai da kallo.

Tunda tazo lagos kusan wata biyu bata tab’a yin kwalliya ba ko sau ɗaya, duk da ko sanda tana Haɗejia ma ba yi take ba, saukaƙƙaƙiyar kwaliya ta yi a fuskarta, gashin kanta da take ganinsa kamar ba nata ba sbd laushin da ya yi ta saka masa ribbom kawai ta fakeshi a baya.

Ɗan gashin dake gaba-gaban bashi da laushin da zai kwanta kamar na bayan, dan haka ta saka gell, ta kawo sea green ɗin mayafin ta ɗora a kanta, sannan ta ɗauki sea green ta kalmi da jaka a cikin na kayan aurenta ta saka takalmin ta riƙe jakar a hannunta.

Zata iya kirga lokutan da ta tab’a saka gyale a ratuwarta, bata cika saka gyalen ba amma yau ta saka, sbd tsabar daɗin da take ji zata fita daga Alaro city, ko ba komai zata ga gari, kuma ita tun da Allah ya yi fa da san fita.

Ta fesa turare me sanyi sannan ta ɗauki wayarta ta saka a cikin jakar ta fito.

TAFIDAH POV.

Zaune yake akan kujerar parlon gidansa, Maryam yake jira dan shi ya jima da shiryawa.

Sanye yake da farar plane hoodie, sai farin chinos trouser hatta da canvas ɗin dake ƙafarsa farine, ya kawo denim jacket baƙa ya ɗora akan hoodie ɗin wadda kalarta ta haɗu da gashin kansa, wanda ya ƙara tsayi sbd rashin aski, amma kuma kamar kullum a cikin tsari me kyau sai sheƙi yake.

Taku yaji daga kan stairs hakan ke nuna masa cewar Maryam ta gama shiryawa, a hankali ya ɗago da kansa ya kalleta.

Tunda yake bazaice bai tab’a ganin mace wadda ta yi kyau kamarta ba, ya gani ya ga wanda sukafita ma, amma kuma nata kyan na da ban ne, yau ta masa kyau fiye da kullum, kuma babu abinda ya ƙara mata kyau a idonsa irin kayan al’adarsa da ta saka, ya ƙara mata kyau sosai, masam cewarsa mutum me san al’adu.

Maryam ɗin ma kallonsa take, ba zatace bata tab’a ganinsa da ƙananun kaya ba, dan yana sakawa idan yana gida, amma idan zai fita ne bata tab’a gani ba, bata tab’a ganin ya saka ƙananun kaya ba idan zai fita, sai de idan filin cricket zaije, kuma shima jersey yake sakawa da wandonta.

Shi baya buƙatar ace ya yi kyau, kullum cikin kyansa yake, sai de ya ƙara wani abun. Miƙewa ya yi sannan yace.

“Shall we ?”

Ya ƙarashe yana miƙa mata hannu, Maryam ta sunkuyar da kanta ƙasa tana murmushi kunya na kamata, ko rannan ma da ya yi hugging ɗinta Allah kaɗai yasan yanda ta ji kunyarsa. Tana jin sautin murmushinsa.

Kafin ta ji yana takowa inda take, kuma beyi tunanin komai ba ya kai hannunsa ya kama nata wanda bata riƙe jakar da shi ba.

Maryam ta ji abinda ta saba ji a duk sanda zai riketa, na ratsawa tun daga kanta har kafafunta.

A tare suka fita kuma hannunsa na cikin nata, har suka shiga cikin mota.

Maryam tana ta kallon unguwar tasu yadda ta mata kyau a cikin yammacin, wasu ma’aikata ne sun dawo daga aiki, wasu ƴan kasuwa, wasu school kowa de yana harkarsa.

Lokacin da suka fita daga babban gate ɗin Alaro city har wata ajiyar zuciya ta sauƙe, taci gaba da kallon gari har suka yi wata doguwar tafiya kamar masu barin gari, amma ba garin suke bari cikin garin ma suke shiga. Tana ganin ana ta kiran wayarsa amma bai kula ba.

Ƙofar wani waje taga sun shiga, wanda a symbol ɗin sa aka rubuta ‘LANDMARK BEACH’.

Hakan ke nuna mata cewa wajen beach ne, a parking lot ya yi parking sannan suka fito a tare, shi da kansa ya zagayo inda take yana ƙoƙarin kama hannunta ta janye, ganin wajen akwai mutan.

“Me ya faru ?”

Muryarsa me zurfi ta tambaya.

“Akwai mutane a wajen”

Ya ɗan juyo ya kalleta kaɗan.

“Ko goyonki zanyi anan babu me kallon mu bare ya mana magana”

Maryam ta kawar da kanta gefe, kunya na ƙara kamata, ya yi murmushi yana sauraron bugun zuciyarta.

“Muje to”

Ya faɗi yana nuna mata hanya, suka shiga tafiya a tare, duk inda suka ratsa sai an kallesu, kuma Maryam tasan kallom ba nata bane, na Tafida ne, dan yawanci ƴan mata ne suke kallonsa.

Taji wani abu na maƙale mata a maƙoshi, ta daure ta haɗiye har suka shiga wani restaurant da a samansa aka rubuta ‘SHIRO LAGOS’.

Babu kai kawon mutane sosai a wajen, saida taga sun zagaya baya wurin taga a wajen ma babu kowa sai wasu mata da maza dake zaune a kan wasu dogayen sofa.

Mutanen dake zaune a wajen basu haura shida ba, mata uku maza uku, suma mutanen suna ganinsu suka miƙe.

“Finally dai yau munga Mrs Tafida”

Taji wani ya faɗi a lokacin da suke ƙarasawa wurin, kuma tanada tabbacin bahaushene, duk da ba kayan hausawan ke a jiknsa ba.

“Ai kuwa tunda ba’a gayyace mu biki ba”

Matar dake tare da shi ta furta tana murmushi, hannu taga Tafida ya bawa mazan suna gaisawa, ita kuma ta gaisa da matan dan taga ɗaya ce kawai ba bahaushiya ba.

A kujera ɗaya suka zauna ita da Tafida duk da kujerar nada tsayi sosai.

“Tafida matarka ta yi kyau, amma de yace kinyi kyau ko ?”

Wata daga cikin matan itama ta faɗi, tana zaune a kusa da wani wanda da alama mijinta ne.

A hankali Maryam ta juya ta kalli Tafida, kamar shine zai bata amsar, sai kuma ta girgiza mata kai.

“This is not fair wallahi, ya za’ayi ta yi kyau haka baka faɗa mata ba”

Maryam ta sunkuyar da kai.

“Ai babe rabu da wannan, bai iya soyyaya ba kwata-kwata bari zan saka shi a makaranta yaje a koya masa”

Gaba daya suka yi dariya harda shi Tafidan

“Yanzu de dan Allah ka faɗa mata ta yi kyau”

Tafida ya dan juya ya kalli Maryam.

“Miriam”

Ta juyo tana kallonsa.

“You look gorgeous, and you look very attractive and cute, you look very pretty to the extant that i can’t take my eyes off you, wifey you have looks to die for, i think you are stunning, you are so adorable wifey”

Duk abinda ya faɗi a bakinsa ya fito ne daga ƙasan zuciyarsa, da gaske yake furta hakan har cikin ransa

Maryam ta sunkuyar da kai saboda kunya, bata sani ba wataƙila ya faɗi abinda ya faɗi saboda an nemi da ya faɗa, ko kuma ya faɗi hakan ne kawai dan yana san faɗar, amma ba dan ta kai matsayin ba, ita bata kai haka ba sam.

“Babe kace bai iya ba, wannan kalamai haka, ai ko kai sai dai ya koya maka”

suka yi dariya.

“Dr. Eshaan ai ya kamata a gabatar da mu ko ?”

“Hakane, Miriam wannan shine Dr. Khabir, wannan kuma Dr. Abubakar, sai Dr. Ola gaba ɗayansu abokan aikina ne, muna aiki tare a St. Nicholas Hospital. Waɗanan kuma matansu ne, Hajara, Fatima da Comport”

Dukansu Maryam saida ta sake gaisawa dasu. Dr. Ola ne ya fara jawabi.

“Kamar de yanda na sanarwa da kowanmen ku, mun haɗa wanna zamane domin mu samu wani abinyi a wannan watan, kullum muna cikin aiki, bamu da abinyi sai shi, ba kuma ma hutawa sai weekend, wani lokacin ma a weekend ɗin bama hutawa, dan haka yau muka shirya wannan fita dan musamu mu miƙe ƙafa mu kuma ƙara sanin juna”.

Yayi jawabin ne a cikin harshen turanci, Dr.Abubakar ne ya yiwa waiter magana, waitern ne ya kawo abinci kala-kala da suka yi oder aka zube musu shi akan dogon teburin dake aje a gabansu.

*****

Maryam ce tsaye a jikin balcony ɗin dake wajen cin abincin, daddaɗar iskar dake busowa daga tekun dake tsallaken balcony ɗin take shaƙa, tana kallon yanda ruwan ke kai komo, ga fitilun wajen da suka fara haske sbd ƙuratowar magariba, ga mutane na wucewa akai-akai.

Ko a mafarki bata tab’a zaton rayuwarta zata sauya kamar haka ba, bata tab’a zaton zata wayi gari ta tsinci kanta a cikin irin wannan rayuwar ba, iskar wajen dake kaɗawa ce ke tuno mata da rayuwarta ta baya da kuma waddama take ciki a yanzu.

“Maryamu Daaso!”

Ta juya a hankali ta kalleshi, duk da tasan shiɗin ne, domin koda a bacci za’a tasheta ta ji muryar sa zata gane muryar tasa, shi ɗin ne tsaye a bayanta, hannunsa sanye cikin aljihun chinos trouser ɗin dake jikinsa, ga wani dan gajeren murmushi dake playing akan lebensa.

Kamar wani jarumin film ɗin india wanda director ɗin yasa shi yayi irin tsaiwar, itama ɗan guntun murmushin tai masa tana juyawa taci gaba da kallon tekun, sakamakon takowa da yake zuwa gareta.

“Baki jin sanyi ?”

Muryarsa me cike da kamewa da aji ta tambaya, yayinda ya ƙarasa kusa da ita ya tsaya, shima yana kallon wajen.

“Babu sanyi, view ɗin akwai kyau”

Kansa ya gyada mata a hankali, kuma ba tare da ya kalleta ba.

“Ko inama a lagos yana da kyau wifey, akwai wajaje masu kyau sosai, ki bari wata rana zamu zaga gari”.

Tayi murmushi me sauti tana sauƙe kanta ƙasa sannan ta ɗago.

“Muje magariba ta kusa”

Ta gyaɗa masa kai a hankali, sannan suka juya a tare.

<< Yadda Kaddara Ta So 24Yadda Kaddara Ta So 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×