Skip to content
Part 26 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

UCHENNA POV

“Ya matarka take ?”

Muryar mahaifiyar sa ta tambaya daga cikin wayarsa, ya yi murmushi yana shafa sumar kansa me karfi irin ta sauran Africans.

Yana zaunene a balcony ɗin ƙofar entrance ɗin gidansa.

Matarsa?, abunma ya bashi dariya, matar da babu wani abu na kusanci irin na mata da miji da ya shiga tsakaninsa da ita, ba wata hira suke ta arziki ba, maganarsu biyuce a rana, daga gaisuwa sai sannu da zuwa, sai kuma yanzu da ta fara girki idan ta gama zabtace masa yazo ya ɗauki nasa, bai san me yasa take haka ba, amma ya san cewa Hanam bata sansa, kuma baisan dalili ba.

“Tana lafiya”

“Ka gaida min da ita”

“In sha Allah zata ji”

Daga haka wayar tasu ta ƙare, miƙewa ya yi ya koma cikin gidan, yanzuma bata parlo, sam yau be ji motsinta ba, sau ɗaya ya ji kukan Arya a ɗakinta.

Rashin ganin nata ya ɗarsa masa shakku a zuciyarsa, Hanam ba irin wannan matan bane, tana bawa aikinta muhimanci, koda wasa bata fashin zuwa wajen aiki, sai de idan wani uzurine me ƙarfi ya taso mata, duk yanda akayi ba lafiya ba.

Shawara ya yanke akan zaije ya duba yaga ko lafiya, ɗakin nata ya nufa, saida ya isa ƙofar ɗakin, ya ɗora hannunsa akan handle ɗin, sai kuma ya samu kansa da kasa buɗe ƙofar.

Tunda tazo gidan bai tab’a shiga ɗakinta ba, tun ranar da aka sauya kayan gidan bai ƙara shiga ba.

Sai da ya furzar da wani numfashi sannan ya murɗa handle ɗin, ya tura ƙofar gaba tare da bugawar zuciyarsa, dan baisan me zai tarar ba, ɗakin ya shiga ƙarewa kallo.

Baiga kowa a ciki ba sai Arya dake zaune akan gado yana wasa da teddy, ƙaran zubar ruwan da yaji a banɗaki yasa ya fahimci cewa tana banɗakin.

Ƙarasawa ya yi jikin gadon, ya kai hannu ya ɗauki Arya dake ɗaga masa hannu alamun ya daukeshi, zuwa yanzu ya fara ƙiwa amma kuma shi baya masa, wasu lokutan har idan ya karb’eshi baya yarda ya koma wajen Hanam.

Shi kansa ƙaunarsa da yaron na bashi mamaki, wasa ya shiga masa yana faɗin.

“Yau ina ka shiga ban ganka ba ?”

Ƙaran buɗe ƙofar banɗakince ta dakatar da maganar tasa, ya juya idonsa zuwa ga ƙofar bandakin, ya kalleta.

Sai da zuciyarsa ta dungura fiye da ƙirgensa a lokacin da ya ɗora idonsa akanta, wata pleated maxi dress ce me gajeren hannu jikinta, gashin kanta nannaɗe cikin bun, wanda ta ɗora claw clips a samanta.

Ba shigar jikintace ta haddasa dungurawar zuciyarsa ba, abinda yake gani a fuskarta shine ya haddasa masa bugawar zuciya sau biyu a lokaci guda.

Wani irin yanayi ne ɗauke a fuskar tata, irin yanayin da yake gani a fuskar mom ɗinsa a duk lokacin da babansa ya daketa, irin yanayin da yake gani a fuskar mahaifiyar tasa idan bata da lafiya.

Idanuwanta sun faɗa ciki, kuma sunyi ja, haka kuma yanayin fuskar tata a raunane yake, fuskar tata fayau.

Kallonsa take kamar yanda shima yake kallon nata, a hankali ta fara takowa zuwa wajen da yake. Tun safe ta tashi da zazzab’i, yau ta ɗaura niyyar samun Abba akan batun Uche, dan tun rannan baya gari, ya yi tafiya.

Jiya ya kirata yake faɗa mata ya dawo dan haka zata iya zuwa ta ganshi, kuma tace masa zata zo ta ganshi yau, sai kuma Allah beyi ba, ta tashi da zazzab’in.

Ta saba a duk lokacin da take jinya babu me damuwa da halin da take ciki sai Abba, idan kuma baya gari ko baya gidan saide taci ciwonta ita kaɗai ta cinye, ta saba da hakan tun ba yau ba, dan haka a nan ɗin ma da babu wanda ya leƙota bata damu ba duk da tasan Uche ɗin yana gidan, kuma ba ta yi mamakin ganinsa a ɗakinta ba.

Arya ya aje akan gado yana ci gaba da kallonta, ta ƙaraso har gabansa ta tsaya tana kallonsa da idanunwanta dake nuna cewar bata da lafiya ƙarara. A hankali ya yi yaƙi da abinda yake ji a zuciyarsa yace.

“Baki da lafiya ne ?”

Muryar tasa ta fito cike da kulawa, kulawa irin wadda bata samunta daga wajen kowa sai Abba, Abbanta ne kawai ke mata magana cikin irin wannan kulawar, idanuwanta ta ɗan juya kaɗan, sannan tace.

“Zazzab’ine kawai”

Kansa ya girgiza mata a hankali yanaci gaba da kallonta, a hankali ya ɗago da hannun sa ya yi abinda daga ita harshi ba su yi zato ba, shi da kansa da ya yi abun saida ya bashi mamaki.

Da hannun nasa ya tashi sauƙa, bai sauƙa a ko ina ba sai akan goshinta, Hanam ta riƙe numfashinta da ƙyar, wanda ke shirin zarcewa maƙogwaranta, sbd wani abu daya ratsa tun daga hannunsa har zuwa fatar kanta, wani abu kamar shock ɗin wutar lantarki.

Abinda ya faɗi bayan hakan shine ya ƙara saka zuciyarta kokwanto a kansa.

“Subhannallh, jikin akwai zafi sosai”.

Anya kuwa taji da kyau ?, kamar subhannal taji yace ?, Anya kuwa ba a baibai take kallon Uchenna ba ?, shin da gaske shi Cristian ne kokuwa ?.

*****

Cogrove Estate,st 3, house NO 334

“Malaria ce kawai, amma babu wata damuwa ki tabbatar kinsha waɗanan magungunan, in Allah ya yarda zaki ji sauƙi”

Muryar Dr. Hasina likitan asibitin Cosgrove estate ke korowa Uche da Hanam wannan bayani, bayan Uchenna ya yi amfani da wayar kiran emergency ya kira can asibitin sun turo musu ita.

Hanam dake kwance akan gado rabin jikinta lillib’e da bargo ta gyaɗa mata kai.

“Bani takardar sai inje na siyo mata”

Muryar Uchenna dake tsaye daga baya ta fasi cikin irin wannan kulawar ta ɗazu, riƙe yake da Arya a hannunsa yana kallonsu, Dr. Hasina ta juyo tana masa murmushi.

“Kada ka damu Uche zan siyo sai na aiko maka, ai kai kafi da haka Uche”

Ya ɗanyi murmushi, kirkinsa na saka a masa alfarma a lokauta da dama, dan Uchenna na kowa ne, kowa nasa ne, bashi da abokin faɗa kona gaba, ga haba-haba da kowa, kuma kullum cikin barkwanci ya ke.

“A’a Dr. Ki bari de naje”

“A’a ka zauna da matarka kawai, tana buƙatar ka”

A hankali ya jinjina kai, Dr. ta gama haɗa kayanta sannan tai musu sallama ta fita

“Bari naje na rakata”

ya fice hannunsa riƙe da Aryaan, Hanam tabi bayansa da kallo tunanika iri-iri na yawo akanta, wai meke shirin faruwa ne ? Ya zama dole ta nemi Abba su tattauna.

Jim kaɗan ya dawo, zama ya yi a kusa da ita cike da kulawa irin ta ɗazu yace.

“Me zaki ci ?”

Kai ta girgiza masa a hankali tanaci gaba da kallonsa.

“No you need to eat, how will you take medicine without eating?”

“Baki na nake ji da ɗaci…”

Ta amsa masa a hankali muryarta na fita cikin zafin zazzab’in dake jikinta.

“Duk da haka, ya kamata ace kinci”

Bata san musun, dan haka ta gyaɗa masa kai, dan yawan maganar zai iya saka mata ciwon kai, ita dama can ba me yawan surutu bace, yanayin rayuwane ya sa ta zama me yawan magana.

“Baki da zani na goye shi?”

“Babu zani saide towel”

Kansa ya gyaɗa mata sannan ya shiga bathroom ya ɗauki towel ɗin, bai fito ba saida goyon Arya.

Hanam taji zuciyarta ta motsa, wani abu daga can ƙasan zuciyar tata ya gangara zuwa ƙasa, ƙasa can inda bata san da shi ba.

*****

Alaro city lekki, lagos, B3 house No. 122

Da 10:00am

TAFIDA POV.

“Me kika dafa yau ?”

Muryar Tafida me zurfi ta tambaya, yayinda yake karb’ar wayar da Maryam ke miƙa masa bayan ta fito daga kitchen, yayinda shi yake zaune a parlo bayan ya dawo daga wajen buga cricket.

Maryam ta zauna a ƙarshen kujerar tana amsa masa da.

“Shinkafa da wake”

“Bana cin shinkafa da wake Miriam”

Ta ɗan juyo ta kalleshi, a sannan ne kuma taga abinda bata lura dashi ba ɗazu, gefen fuskarsa ya yi ja da shatin circle, kamar an daki wajen da wani abu.

“Me yasa baka cin shinkafa da wake?”

Ya shafa sumarsa yana ci gaba da danna wayarta sbd yana mata editing vedion da ta yi recording na jiya dana yau, dan bai samu zama ba jiya.

“Haka kawai, dan ban tab’a ci ba, kuma babuma a inda zan ganta bare nace”

Har Maryam za ta yi magana sai kuma ta yi shiru, to a ina kuwa zai ci?, shida yake gidan sarki, sai ta sauya zance da.

“Da wasa nake maka ma, ba ita na yi ba, pancake ne da salad sai fried chicken”

Ya jinjina mata kai kaɗan, yana ƙara godewa Allah da ya sako Maryam a cikin rayuwarsa, kyawawan halayenta sune a kullum suke bata matsugunni me kyau a zuciyarsa.

Bugun zuciyarta ya fara saurare, kafin ransa ya raya masa ya yi abinda zai saka zuciyar tata ta buga da sauri, dan idan zuciyarta na bugawa da sauri sautin yafi masa daɗin saurare.

Karshen kujerar ya kara matsawa sannan ya kwanta, Maryam bata zata ba taji kansa a cinyarta, zuciyarta ta buga da ƙarfi, wani abu ya shiga kaikawo daga zuciyar ta zuwa ƙwaƙwalwarta yana faɗa mata cewar bazata tab’a sabawa da wannan yanayin ba.

Wata busashiyar iska ta haɗiye a maƙogwaronta sannan ta sunkuyar da kanta ta kalleshi, amma kuma shi ba ita yake kallo ba, Wayar dake hannunsa yake kalla yanaci gaba da dannata.

Kafin taga ya ɗago hannunsa ya kamo nata hannun wanda ke ɗauke da guntun jan lallen da ta yi da be koɗe ba. Maryam ta rintse idanunta.

Sakamakon hannunta daya sauka kan lallausa kuma me taushin sumarsa, sai kawai maganar su Aisha ta shiga dawo mata a ƙwaƙwalwarta, ranar da suke faɗin suna so su tab’a sumarsa.

Sumarsa nada laushi da santsi fiye da tata dan shi tasa naturally haka take, ita kuma tata ƴan dabarune akayi ta koma kamar hakan.

Muryarsa ta fito a hankali, cikin wani irin yanayi daya haddasa bugawar zuciyar Maryam sau biyu a lokaci guda.

“Wifey ki sosa min kaina, sumar ta min yawa”

Da ƙyar ta iya lalubo sautin muryar ta, sannan tayi ƙarfin halin furta.

“Ƙaiƙayi take maka ?”

Yanayin yanda muryar tata ta fito, da yanda zuciyarta ta buga saida ya kusa saka shi dariya, amma sai ya dake, dan da gaske yana buƙatar a sosa masa kan nasa, a hankali ya girgiza mata kai, wadda ya haddasa motsawar cinyarta.

“A’a ba ƙaiƙayi take ba, kawai de banajin daɗin yawan sumar dake kan nawa ne”

“To me yasa ba zaka aske ba ?”

“Sbd na yiwa Daadi alƙawarin bazan aske sumata ba sai naje india, kuma dama mun saba haka da ita, idan tana so na zo india sai tace tanaso na tabbatar mata da alƙawarina, ni kuma dan na tabbatar mata da zanzo ɗin sai nace mata zan tara sumar kaina, tasan cewa bana so gashi ya min yawa, shiyasa take yarda dana faɗi hakan, idan ina india kullum ita take min susar kai, dan ina so”

Duk da Maryam bata san wacece Daadi ɗin ba, amma kamar ta fahimci cewa kakarsa ce, dan haka taji indiyawa suna faɗawa kakaninsu a film, Da ƙyar ta iya motsa hannunta a cikin tarin sumar kan nasa, hannunta ya nitse a ciki.

Tafidah ya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya yi kewar hakan sosai ba kadan ba. Dalilan da kam ƙara sakawa yaji Maryam har ransu shine tana sakawa yaji kamar yana india.

A hankali take motsa hannun nata a cikin sumarsa.

“Wai ni Miriam da wani suna kike amfani ne ?”

“Maryam Tijjani Muhammad”

Kansa ya girgiza mata wanda yasa cinyarta motsawa yanzuma.

“Ba’a school ba, a page ɗinki, naga kamar babu suna ma”

Kai ta gyaɗa masa tana motsa hannunta a cikin sumarsa.

“Umm, babu suna, na rasa wani suna zan saka ne”

“Ya kamata ki saka suna”

“Me ya kamata na saka, da ina tunain na rubuta ‘MARYAM’S KITCHEN’”

“A’a ‘DAASO’S KITCHEN’ dai”

Sai ta yi dariya yayinda shi kuma ya yi murmushi.

“Seriously ki saka ‘MRS TAFIDA’”

Yanzuma dariyar ta yi.

“A’a ‘MRS ESHAAN’ dai”

“Ummm yafi kam, bari na rutuba miki to”

“To kuma iyaka Mrs Eshaan ɗin za’a rubuta?”

Ya tambaya a sanda hannunsa ya danna edit account. “MRS ESHAAN’S KITCHEN”

“MEK kenan ?”

“Eh”.

Shiru Ya ratsa parlon, kafin Maryam ta tambayi abinda take san tambaya tun ganinta da shi a yanzun.

“Sultan (King), menene wannan a gefen fuskar ka?”

Tafida ya ɗago da idonsa ya kalleta, tareda lumshe idonsa, sbd yanda ta motsa hannunta a cikin sumar kansa dan ta tab’o har fatar kansa, sai kuma sunan da ta kirashi dashi ‘Sultan’, idon nasa ya buɗe sannan ya kalleta da kyau.

“Joakim ne ya bugomin ball ɗin cricket”

Ya juya idonsa yaci gaba da kallon wayar yana latsawa.

“Baka saka helmet bane ?”

“Mantawa nayi”

“Ai ko gashi wajen yayi ja, harma ya kumbura…”

Wayarsa da ya baro a ɗakinsa tana cahrgy ce ya ji kamar tana ƙara, dan haka ya motsa kunnensa ya tabbatar da ƙaran wayar yake ji.

Kansa ya ɗaga daga cinyar Maryam sannan ya miƙe, kafin yace mata komai aka ƙwanƙwasa ƙofar gidan, a tare suka kalli ƙofar shi da ita.

“Bari na ɗauko wayata, naji tana ringing”.

“Ok to nima bari na duba waye”

Shi ya yi sama ita kuma ta ƙarasa ta buɗe ƙofar.

“Surprise!”.

Abin da muryaryoyi biyu dake tsaye a ƙofar gidan suka faɗi kenan, zuciyar Maryam ta takarkara ta yi tsalle a kirjinta, ta ji kamar zuciyar tata zata fito daga kirjinta ne.

Zara da Aisha ne, ba wai bata san zuwansu gidan bane, bata so suga Tafida ne, dan har yanzu a cikinsu babu wanda yasan cewa ita matarsa ce, kuma har wa yau basu fasa zantuka akansa ba.

Da ƙyar ta lalubo murmushi ta yab’a akan fuskarta. Sannan ta haɗiye wani guntun yawu, ta ƙarasa bud’e ƙofar tana faɗin.

“Ku shigo daga ciki”

Har ranta ba haka ta so ba, duk da ta ji daɗin zuwan nasu, sam bata fatan Tafida ya sauƙo yazo ya iskesu, zama suka yi akan kujera suna ta mata murmushi wanda itama take meda musu martani.

“Wai dama Maryam ke a gidan ma da hijiabi kike zama kullum?”

Maryam bata amsa Zara dake wannan batu ba, sai kawai tace.

“Bari na kawo muku abun sha…”

“Ke bar abun shan nan wallahi”

Maryam ta gyaɗa musu kai kaɗan, a lokacin kuma Tafida ya sauƙo daga sama, hannunsa riɗe da ɗan ƙaramin littafi da kuma pen, sai wayarsa data Maryam a ɗayan hannun nasa.

“Wifey ai wayar taki ba data…”

Zuciyar Maryam ta dungura ta ƙara dungurawa, ta rintse idonta gam, a lokacin da take da tabbacin su Zara sunga Tafida, kuma sunji sunan da ya kirata dashi.

<< Yadda Kaddara Ta So 25Yadda Kaddara Ta So 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×