Skip to content
Part 28 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

HANAM POV.

Jiki a sab’ule ta shigo cikin gidan, gaba ɗaya ta rasa wani tunani ya kamata ace ta yi, haƙiƙa ta cutar da Uchenna tsawon zamansu, amma shi a kullum burinsa ya ga ya faranta mata ita da ɗanta, kaico!, kaiconta da ta zama me san kai da yawa, tana zarginsa kan abida bai aikata ba, to waima ina tunaninta ya tafi ne, me yasa har take zaton cewa Abba zai iya kawo wani abu na cutarwa a rayuwarta…

Tunaninta ya katse sanda ta iske Uchenna da Arya auna wasa a falo, sai dariya suke ƙyalƙyalawa, zuciyarta ta matse gu guda, wani abu ya shiga mata kaikawo a zuciya.

“Uche…uchenna zaka ce…”

Uchenna ke taya Arya gwalantu, yana koya masa sunansa.

“Arya kace papi!…”

Daga yaron har Uchenna suka juyo suka kalleta, ganin yanayinta kamar mara lafiya yasa Uchena miƙewa da sauri, yayin da ya aje Arya akan sofa, a ruɗe ya ƙarasa gabanta yana tab’a goshinta wai ko zaiji zafi, amma sai yaji babu zafin face sanyi.

Tunda ya miƙe Hanam ke binsa da kallo har ya tsaya a gabanata haka. Duk abinda ta saurara akansa ya dawo mata, a lokacin kuma Arya ya saka kuka, Uchena ya juya da sauri ya je inda yake yana ɗaukansa tare da faɗin.

“Me ya same ka aboki…?”

Maganar ta maƙale, sbd wani hannu daya zagayo daga baya ya naɗe cikinsa, ya tsaya cak, numfashi yana neman ɗauke masa, sbd kan Hanam daya ji a gadan bayansa, ga wata iska da take fitarwa daga bakinta yayinda take kuka, ga yanda ta maƙalƙale shi, ga kukan Arya.

Gabaɗaya sai yanayin ya taro ya masa yawa, uwa na kuka ɗa ma na kuka, ya rasa me zeyi, a hankali ya shiga jijjiga Arya, still hannun Hanam na kewaye da shi kuma tana kuka, saida Arya ya yi shiru sannan ya aje shi akan sofa ya bashi teddyn da suke wasa da shi ɗazu.

Sai da ya haɗiye wani abu da ƙyar kafin ya kai hannunsa ya b’anb’are na Hanam, tareda janyota gaba yana fuskantar ta, kuka take shab’e-shab’e, kuma tana kallonsa, hannunsa na karkarwa ya ɗago da shi yana share mata hawayen cikin fadin.

“Me ke faruwa ?”

Hanam ta girgiza kai, sannan ta ƙara kankame shi, wannan karon kanta ya sauƙa a kirjinsa, ya kuma lumshe ido, wani ɗan ƙaramin yaƙi yana aukuwa a zuciyarsa, yana jin kamar ya saka ƙara, dan ya kasa jure yanayin.

Sake ɗago da ita ya yi yana ƙara share mata hawayen, kafin yaja hannunta ya zaunar da ita akan kujera shima ya zauna yana fuskantar ta. Se da ya juya ya kalli Arya dake zaune akan ɗayar kujerar, wasan sa kawai yake, kafin ya juyo ya kalleta.

“Ki dena kuka, idan kema kina kuka to Arya ma ze yi kuka”

Ta share hawayenta, tana ci gaba da kallonsa, Uchenna ya kalli hannunta dake cikin masa, combination ɗin fari da baƙi, dan kuwa shi baƙi ne, gashi ita kuma fara ce, farar ma fat kamar ba’indiya. A hnakli ya ɗago ya kalleta.

“Ki nutsu ki faɗa min abinda ke damunki”

Hanam ta gyaɗa kai sannan tace.

“Dan Allah Harees ka yi haƙuri, ina me baka haƙuri, ka yafe min….”

Tunda yaji ta kirashi da Haris yasan cewa yanzu tasan komai a kansa, komai yana nufin harda rayuwar da ya yi a baya, kuma yasan ko Abba be faɗa mata ba, wata rana anti Hajiya maƙociyarsu zata faɗa mata, kansa ya kawar gefe yana sakin hannun ta, amma ita sai ta yi sauri ta kama nasa hannun, tana zamewa ƙasa.

“Dan Allah ka yafemin Harees, ka yafe min”

Uchenna ya girguza mata kai yana kamo kafaɗunta, tareda mayar da ita ya zaunar a inda ta zame hannunta ya ƙara riƙewa yana so ya kwantar mata da hankali, inama zata tema ke shi ta dena kukan, dan bata san yanda yake jin kukan nata ba.

“Ba kimin komai ba Hanam, babu abinda kika min”

Hanam ta share hawaye tana ci gaba da kallonsa.

“A ina kuka haɗu da Abba?…”

E gaskiya ko ni ina san naji ina suka haɗu da Abba.

Hanam ta yiwa Uchenna tambayar dake cikin ranta tun ɗazu, sai taga ya yi murmushi, kafin muryar sa ta fito.

“Ranar da Babana ya kore ni na bar gida, naje na hau kan titin kaduna road, ina so na mutu, a lokacin gani nake kamar mutuwar sai tafi min sauƙi, domin ni kaɗaine a cikin duhu, rayuwata bata da wani amfani, duka buruka na sun bi iska, burina shine na yi karatu na zama wani abun a gobe, na rasa wannan, burina na biyu kuma shine waƙa, ina matuƙar san na yi waƙa tun ina ƙarami, amma shima ya rushe, sai naga to ai bani da amfani a duniyar, dan haka na tsaya ƙyam a tsakiyar titi, na lumshe ido ina jiran fitar raina.

Wata mota ta nufoni gadan-gadan, amma kuma tana zuwa saitina ta taka birki, saide duk da haka saida suka ɗan bige ni, kin san waye a motar ?…”

Ya ƙarashe yana kallonta, Hanam ta ƙara matse hannunta cikin nasa tare da faɗin.

“Abba ne?”

Shima kan nasa ya gyaɗa.

“Ƙwarai Abba ne, shi ya kaini asibiti, na yi kwana ɗaya a can, kafin ya tambaye ni iyaye na, nace masa bani da kowa sai de maƙociyar mu, yace na nasa kwatance dan yaje ya sanar mata, na masa kwatancen gidan Anti Hajiya, shi da kansa yaje ya sameta, Anti Hajiya ita ta bashi duka labarina, kuma daga haka Abba yace zai riƙe ni, zai ɗauki nauyina, na faɗa masa me nake so, karatu nake san yi ko aiki, nace da shi ni aiki nake so, ba b’ata lokaci Abba ya bani matsayin PAn sa, kuma shi da kansa ya saimin wannan gidan tun a wancan lokacin, Abban ki mutumin kirki ne, ba kamar nawa mahaifin ba, babana baya sona, ya tsaneni, kullum yana cikin tsine min, ya dake ni ya daki mom ɗina, mts rayuwa a gidanmu babu daɗi…”

Ya ƙarashe yana jingina da jikin kujera, duk abinda ya faru da shi a baya yana dawo masa sabo, saide har yanzu Hanam hawaye take, ya ɗan karkato da kansa yana kallonta. Da ido ya mata alamar miye ?, sai yaga ta girgiza kai kawai tana haɗiye sauran hawayen.

Zamansa ya kuma gyarawa ya daurewa kansa ya kai hannu ya riƙo fuskarta sannan yace.

“Ki manta da baya, duk wasu abubuwa marasa daɗi da suke faruwa da mu manta su muke, idan kuma mukace zamu ci gaba da tunasu, to bazamu tab’a ci gaba ba a rayuwa, so smile”

Ta yi wani ɗan guntun murmushi, tana ƙarewa fuskarsa kallo, bata tab’a ganin fuskar tasa a kusa haka ba, yau har wani abu taga a goshinsa me kama da tabon sallah, Allah kenan, me fitar da me kyau daga cikin mara kyau, sannan ya fitar da mara da kyau a cikin me kyau.

Ya janye hannunsa daga kan fuskar ta, dan wannan kallon da take masa zai iya sakawa ya rasa nutsuwarsa, ya juya gefe yana faɗin.

“Abba ya kira ki ?”

Ta girgiza masa kai.

“Ai yace ma yau zai dawo”

Ya gyaɗa mata kai, kuma kafin ya sake cewa wani abu, wayarsa ta yi ringing, hannu ya kai ya ɗauka tare da kara wayar a kunnensa.

A wani irin Hanzarce ya mike tsaye, bayanin da ake masa a wayar ya kasa shiga ƙwaƙwalwar sa sam, wayar hannun nasa ya sauƙe ba tare da yace komai ba, ɗaya bayan ɗaya yake lalubo ma’anar kalaman da na wayar ta faɗa masa.

Hanam ta mike tsaye tana dubansa.

“Harees meke faruwa ?”

Idanuwansa da suka rine nan take ya ɗago ya zuba mata su, ta ya zata fahimce shi?, ta ina zai fara?, me ma zaice mata ?, yaya zata ɗauki zancen ?, kawai sai ya kalli tsabar idonta ya fafa mata cewar mahaifinta ya rasu?.

Dama haka lamarin Allah yake, a sanda suke ganin kamar wahalhalunsu na rayuwa sun ƙare, a sannan wani yake barin duniya, tafiya irin ta har abada, tafiyar da babu dawowa, tafiyar da kuɗin ka, mulkinka, ƴaƴanka ko ikonka basu isa komai a cikin ta ba. Ayyukanka da kyawawan halayenka sune zasu finsheka.

Allah yasa mu cika da kyau da imani.

*****

Lagos

St. Nicholas Hospital

Da 10:15am

“Khabir ina Tafida ?”

Khabir yaci gaba da kallon Heleen dake tsaye a gabansa, tana masa wannan tamabayar, kansa ya kawar gefe tare da faɗin.

“Sun shiga operation”

Heleen ta gyaɗa kai.

“Ok bari na jira shi”

“Am…He…Heleen, d…dama i…ina….san na fada mi…miki….ne”

Jin yana inda-inda yasa Heleen gyara tsaiwa tana dubansa.

“Menene ?”

Khabir ya haɗiye wani abu sannan yace.

“Dama z…zan faɗa miki c…cewar..dama Tafida ya …..yi au.. ya yi aure”

Kamar yanda aradu ke sauƙa a kan bishiya ko dutse haka Heleen ta ji sauƙar maganar tasa, ta ƙanƙance ido tare da karkatar da kanta gefe tana dubansa, kalaman nasa ɗaya bayan ɗaya suka samu waje suka yi gini a cikin ƙaramar kwakwalwar ta, Tafida yayi aure ?, kalaman suka ƙara rubuta kansu da manyan baƙi a cikin ƙwaƙwalwarta kanta.

Sai ta ware idonta sannan ta tsaida kanta dai-dai, tana murmushi, tare da cije leb’enta na ƙasa.

*Da misalin 05:30pm*

MARYAM POV.

Tafe suke ita da su Zara, yau gaba ɗaya sun zama silent, sun kasa yarda ko ido su haɗa da ita, muguwar kunyarta suke ji kamar me, ita kuma sai jansu take da hira tana nuna musu cewar komai fa ba komai bane, amma sunƙi sakin jikinsu da ita.

Saida suka zo dai-dai block ɗinsa sannan ta tsaya ta kallesu.

“Sai gobe”

Da ƙyar Aisha ta amsa.

“Wai ku me ya same ku ne yau ?, gaba ɗaya kun canja min”

“Haba Maryam, ba dole mu canja miki ba, irin maganganun da muka yi ta yi akan mijinki kuma a gabanki, ai dole ne muji kunyar ki”

Zara ta faɗi cikin sinne kai, Maryam ta yi dariya.

“Wallahi kude kun cika abun dariya, wai kunya ?, to miye a ciki, irinku nawa ne suke irin wannan maganar akan sa, ya kai ayi magana akansa ne, ni ban isa na hana ƴan mata ganinsa ko magana akansa ba….”

Sude basu yarda sun ƙara haɗa ido da ita ba suka mata sallama suka yi gaba.

*****

Yau babu gajiya sosai a jikinta, dan haka tana shiga gida wanka ta fara yi, sannan ta sauya kaya, tana tsaye a gaban mirror ta ɗauko wannan hair pin ɗin da Fidar Yara ya bata jiya, yace mata na maansa ne, ita ba wani iya gyaran kai ta yi ba, dan haka kawai ta naɗe gashin nata cikin bun, sannan ta saka pin ɗin, me shape ɗin rose flower a gefen bun ɗin, ta ɗaura ɗankwalinta.

Ba ta yi kwalliya ba kamar yanda ta saba, sai kawai ta fito, yau tana hutun sallah dan haka bata ɗau azumi ba, ta shiga kitchen kawai tana shirin dafa abinda zasu ci da daddare.

Wayarta dake maƙale jikin ring light ce ta shiga ruri, dan haka ta dakatar da abinda take ta ɗauki wayar, ganin ‘SUNDAR’ rubuce a kan screen ɗin yasa ta amsa da murmushi.

“Asslamu Alaikum”

Tayi sallama sanda ta kara wayar a kunnenta.

“Wifey”

Taji ya kira sunanta cikin wata kasallaliyar murya, kamar wanda ya tashi daga bacci, kuma kamar a gajiye yake.

“Ummm”

Ta amsa masa a hankali.

“Kin dawo daga school ?”

“Eh”

“Ya exams ?”

“ Alhamdullilah”

“Me zaki dafa yau da daddare ?”

Maryam ta yi dariya, dama tasan zancen gizo baya wuce na ƙoƙi, zancen abinci zai mata, idan taga yanda yake cin abinci yana bata mamaki sosai.

“Danderun kaza da dambun couscous”

“Yauwwa matar arziƙi, sai me kuma ?”

Ya faɗi hakan da zumuɗi, dan ya tuna sanda ta fara masa danderun kaza, daɗin da abincin ya masa bame faɗuwa ba ne.

“Sai mocktail….”

Ta ɗan dakata sakamakon ƙofa da ta ji ana bugawa.

“Waye ?”

Muryar Tafida ta tambaya daga cikin wayar, dan shima yaji bugun kofar, dan ba a hankali aka buga ƙofar ba, wayar na kare a kaunnen Maryam ta wanke hannunta tana bashi amsa da.

“Ban san ko waye ba, bari naje na duba”

Ta goge hannunta still wayar na kare a kunnenta, kuma shima bai kashe wayar ba.

Maryam ta ɗan ja baya ganin matar dake tsaye a ƙofar gidan, Sanye cikin baƙin leggings, ga wata tank top a jikinta itama baƙa, gashin kanta kalabar attachment ce pink color, ta ɗaureta a tsakiyar kanta, fuskar ta fayau babu kwalliya, sai wani nose ring dake maƙale a tsakiyar hancin nata.

Maryam ta tsorata da irin kallon da matar ke mata, amma sai ta dake, dan zama da Tafida yasa ta rage tsoro, ta kai hannu ta sauƙe wayar dake kare a kunnenta ta riƙe a hannu, kuma har lokacin kiran Tafida na tafiya, bai kashe ba yana sauraron ta.

“Baiwar Allah wacece ke ?”

“Heleen!”

Wani shaftararen yanki na zuciyar Tafida ya yanke ya faɗo ƙasa, kamar yanda ƙasa take shaftarewa a sanda ruwa ya zaizaye ƙasanta. Heleen ?,yaushe ta dawo ?, waye ya faɗa mata cewar ya yi aure ?, dama yasan tasan gidansa, wanna ba abun mamaki bane, matsalar ɗayace yasan cewa Heleen muguwace, zata iya komai domin ta cutar da Maryam.

Ba tare da tunanin komai ba, ya miƙe yana faɗin.

“Hello Miriam!, Daaso ?, Maryam ?, Maryam!”

Amma shiru, baya iya jin komai, saide gashi kiran na tafi, keyn motarsa ya fin cika ya yi waje.

*****

“Wa kike nema ?”

“Ke nazo nema…”

Heleen taƙarashe tana kaiwa Maryam naushi, wanda yasa wayar dake hannunta yin kan sofa, ita kuma ta faɗi a ƙasa, matar ta ƙarasa shigowa cikin gidan, a lokacin da Maryam ta miƙe da gudu ta yi kan stairs, Heleen ta biyo bayanta, ta riga ta yanke cewar bazata bar yarinyar nan da rai ba, tun da har itace zata iya zuwa ta mata shigege a lamura.

Maryam ta shige ɗakinta tare da banko ƙofar, ta saka sakata, tare da fashewa da kuka tana ja da baya, hannu ta kai ta tab’a gefen fuskarta taga jini a hannunta ta ƙara ruɗewa.

Ji ta yi matar na buga ƙofar ɗakin kamar zata b’allata, Maryam ta ƙara curewa a gu guda tana kuka.

“Is better for you to open this door, dan idan har kika bari na buɗeta da kai na, to zamu kwashi ƴan kallo da ke”

Maryam ta ƙara tsurewa, wacece ita ?, me yasa take so ta halakata ?, me ta mata ?, ita da bata tab’a ganinta ba ma.

Tunaninta ya katse a sanda ta ji ƙarar bindiga daga wajen, ta kalli wurin sakatar taga yanda aka harbi wurin, sakatar ta b’alle, kafin ƙofar ta buɗe a hankali, sannan wannan matar mara imani ta bayyana a bayanta, hannunta na dama riƙe da bindiga.

TAFIDA POV.

Ganin ƙofar gidan a buɗe ne yasa shi ƙara razana, a dugun zume ya shigo cikin gidan yana ta bude-dube, ganin jini akan tiles ne ya ƙara har gitsa masa tunani, zuciyarsa ta mara gudu fiye da kima, dubansa ya kai kan wayarta dake yashe a kan sofa.

Kunnensa duka biyu ya motsa, ya jiyo bugun zuciyarta a cikin ɗakinta, amma kuma zuciyar tata a raunane take bugawa, kamar mara kafiya.

A ɗari uku da sittin ya yi saman, ƙofar ɗakin nata ma a buɗe ya ganta dan haka ya kutsa kai, mutuwar tsaye ya yi yana kallonta yashe a ƙasa, hannunta na dama a kan wuyanta, jini na fita daga bakinta da hancinta, numfashinta ma da ƙyar yake fita, ga idanuwanta dake barazanar rufewa, amma tana buɗe su da ƙyar.

Tafida ya ji sauƙar wani abu a kansa kamar ƙaton dutse, kamar da aka saka baƙin ƙyalle aka rufe masa ido haka yake ganin baƙi, ga wani gumi daya shiga tsatsafo masa, ƙafafunsa kuwa kamar da aka mannasu a wajen, nan take ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja dan tsabar tashin hankali, da b’acin rai.

*****

Zaune yake a bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da Maryam, gaba ɗaya gaban pink Oxford shirt ɗin dake jikinsa ya b’aci da jini, hannayensa biyu dunƙule a kan bakinsa, jijiyoyin kansa sun fito raɗau-raɗau, ga gashin kansa daya sauƙo masa kan fuska.

Ƙwayar idonsa tana nan a ja bata dawo blue ba. Ba zai iya duba Maryam a halin da yake ciki ba, dan Allah ne kaɗai yasan abinda yake saƙawa da wanda yake kuncewa a ransa.

Shi yasa yana ɗaukota ya kawota st. Nicholas hospital, yanzu haka su Dr. Ola ne a kanta, a ransa yake hasaso irin abinda ze yiwa Heleen, bata san shi bane, shi yasa take masa abinda ta gadama.

A da tana yawan takura masa, ta zo office ɗinsa taje filin cricket ɗinsu, taje gidansa, babu inda yake zuwa da bata bibiyaraa wurin, amma baya kulata, haka zata zo ta ƙaraci haukanta amma fimm!, bazai ce mata ba.

Wato tana ɗaukar shirunsa a matsayin rauni, gani take kamar baisan abinda yake ba, ko da ace Maa da Appa sun tsine masa kafin su mutu babu abi da ze yi da Heleen, karuwa mazinaciya, ƴar daba, me kisa, duk ita kafai, kuma ta yi zaton zai sota a haka ?, ta yiwa kanta ƙarya wallahi…

“Tafida kayi haƙuri pls…”

Muryar khabir ta katse shi, dama shi yake jira, dan haka ya miƙe, bai kalleshi ba, hasalima gefe yake kallo, dan baya so yaga kalar idonsa.

“Heleen ta zo ?”

Khabir ya haɗiye wani abu, jin wata wutar masifa na kamawa a cikin ɗacin muryar tasa.

“Eh tazo, kuma nine na faɗa mata cewar ka yi aure, na faɗa mata hakan ne kawai dan ta rabu da kai, amma ban san cewa zata ci gaba da bibiyarka ban…”

Ya dakata yana kamo hannun Tafida dake shirin barin wajen.

“Ina kuma zaka je ?, ka zaun…”

Ɗif!!, maganar tasa ta ɗauke, ganin yanda Tafidan ke kallonsa, ga yadda ƙwayar idonsa ta koma ja, cikin Khabir ya ɗuri ruwa wata iska ta shiga kai kawo a maƙogwaron sa, ba shiri ya saki hannun Tafidan.

Kuma daga haka Tafida ya juya yaci gaba da tafiya, Khabir yabi bayansa da kallo a razane.

<< Yadda Kaddara Ta So 27Yadda Kaddara Ta So 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×