Skip to content
Part 3 of 22 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Tsaye take a cikin babban kitchen ɗin gidan nasu, tana haɗawa aryasn elecare, wani nau’in abincin yara, tana bashine Saboda mama baya isarsa, kumama yana ƙara girma dan haka take haɗa masa da sauran kayan abinci yara. Sanye take da green cargo pants, sai wata baƙar shirt mara hannu, ta ɗaure gashin kanta da rubber band.

Fitowa tayi daga kitchen ɗin tana fifita abinda ta zuba a cikin wani sabon bowl da taga a kitchen ɗin, a lokacin masu aikin dafa abinci na gidan suna jera abinda suka dafa a kan danning table, waje ta samu tana aje bowl ɗin, yayin da take amsa gaisuwar da masu aikin suke mata.

Dakinta ta koma wanda yake haɗe da ɗakin aryaan ɗin, ta shiga ta sameshi zaune cikin munchkin baby cradle ɗinsa yana jujjuyashi, yayinda yake tsotsar pacifier ɗin dake bakinsa “Ahhh, Aryaan Ammy”

Ta faɗi tana masa wasa tare da ciro shi daga cikin Baby Cradle ɗin, ta sabashi a kafaɗa, wayarta dake cikin aljihunta ce ta shiga ringing ta sa hannu ta ɗauko wayar, ganin abbabnta ne yasa tayi murmushi, ta ɗaga kiran ta gaisheshi, baya ha amsa yace “Maman Babanta, mamarki ta….” tun kafin ya karasa ta katse shi “la Abba hiya manu Ummi” ( a’a Abba ita ba mahaifiyata ba ce) “to Matata, shikenan?”

Ta gyaɗa masa kai kamar yana gabanta sannaan shima ya ce haba “ta kawo min kararki, wai kin mari ɗanta” Ta ɗan gyara riƙon da ta yiwa Arya a hannunta da babu wayar “eh hakane”, “to Maman Babanta me yasa?”

“Abba Arya ya kira da shege, ni kuma na gaza jurewa shi yasa na mareshi”, “to Maman Babanta a dinga haƙuri dai, kinga shi yayanki ne, ya girmeki, kuma ko ba haka ba shi namiji ne, a dinga ƙoƙarin sarrafa shi” “uhum” daga haka kuma suka ɗan tattauna daga bisani suka yi sallama bayan ya faɗa mata cewar gobe zai dawo, ta aje wayar sannan ta fito daga ɗakin zuwa ƙasa.

Zama tayi ta shiga bashi baby feed ɗin tana masa wasa, zuwa lokacin mutanen gidan sun fara fitowa, arya sai ƙyal-ƙyala dariya yake har haƙwaransa biyu na sama da suka fara fitowa na bayyana “kutumar dumdum”. Hanam ta tsinkayo muryar Hajiya Mero a bayanta na ƙunduma ashar bata ko juyo ba taci gaba da yiwa ɗanta wasa tana bashi abincin “ya sa kika damawa shegen ɗanki abu a cikin sabon kwano na ? Ko ke kika siyomin?” Nan da nan Hanam ta tsuke fuska ta aje bowl ɗin ta juyo ta fuskanci Hajiya Meron da kyau “kika ce kwanan ki, yau ai ni inajin duk cikin ku babu wadda tazo koda da cokaline gidan nan, ko waccen ku haka aka wanko kafarta ziƙa-ziyau aka kawota, kuma kina zancen naki tunda ya riga ya shigo cikin gidan ubana ya riga ya zama mallakinsa, kuma ma faɗa min sana’ar me kike da kika samu kuɗin siyan bowl ɗin ? Babu ko ? Nasan ai kudin ubana ne, dan baka babu ruwanki da ni”

“Lalle Hanam wuyanki yayi kauri, yanzu ni kika dubi ƙwayar idona kike faɗa min wannan maganganun? Na ji ni haka ziƙa-ziyau aka kawoni gidan ubanki, me gidan uba, shiyasa naga taki uwar ta gudu ta barki cikin zanin goyo”

A fusace Hanam ta miƙe tana kallon cikin idon Mero.

“Mero bari kiji na faɗa miki, ni bani da uwa abba shine uwata kuma shine ubana, waccan matar ba uwata bace, watace can da ban, kuma magana ta ƙarshe kada ki kuskura ki ƙara kiran ɗana da shege, ɗana ba shege bane yana da uba, kuma nice ubansa, fatan kin fahimta?” Tana kaiwa nan ta bar wajen bayan ta ɗauki ɗanta.

Maryam Pov.

Da misalin karfe 7:30am. Maryam na zuba musu abinci a kwanuka, dan Hassan da Hussain da Muhsin duka sun shirya domin zuwa makaranta. Abincin ta gama zubawa tazo ta aje musu a gabansu. “Yaya ke yau ba za ki je makaranta ba ne ?”

Hassan ya tambaya ganin sam ba tayi shirin zuwa makarantar ba “aa Hassan bazanje ba, registretion mukayi ai” “ Oh na gane” “Au ni kin tuna min ma, idan kin gama ki kiramin Kawu Usman ɗin nayi masa maganar kuɗin” cewar Maamu.

Kawu Usman shine babban yayan su Maamu, kuma tun lokacin da tijjani ya tsiri rashin mutunci shine ya dawo yake kula da Maamun da yaran nata, kuma yanzu haka shine yake ɗaukar dauyin karatun Maryam ɗin, dan a yanzu haka ta gama ND 1, zata shiga ND 2, kwana nan suka gama siwes ma.

“To, in anjima zanje gidan su Badar, jiya nace mata zanje amma banje ba…” Bata ko gama rufe bakinta ba saiga sallamar Badar, tana shigowa ta gaida Maamu ta shiga aikawa Maryam sakon harara. “Badariyya zo mu ci taliya”

“A’a wallahi Maamu, a ƙoshe nake, dade ɗumame ne” “Ke wai yau ba za ki je makarantar ba?” “Ban sani ba”, Badariyya ta faɗi tana kawar da kai “ke kiyi haƙuri wallahi jiya aiki ne ya riƙeni shiyasa banzo ba”.

“Hassan kuyi sauri ku gama ku miƙamin yaron nan makarantarsu, kar ya makara su dakar min shi”, “ai da zasu dake shi ma da ba haka ba” cewar Hassan yana wurga masa harara “wai dan Allah me Auta ya tare muku ne?”

“Babu wallahi kawai mugunta ce irin tasu” cewar Maryam.

Bayan sun gama cin abinci su Hussain suka fita su da Muhsin, su suna ss3 ne a makarantar government day garko, yayinda shi kuma Muhsin yake primary 3 a garko islamiyya, duka makarantun nasu basu da nisa da gida.

*****

“Ke tura min sabbabin vedios ɗin”, cewar Maryam yayin da suke zaune a ɗakin Maryam ɗin “ke Aliyu ne zai zo jibi”, cewar Badariyya, Aliyu shine saurayin Badariyya, kuma a yobe yake da aiki, amma mahaifinsa ɗan Hadjia ne, aikine ya kai shi can.

“To Allah kawo shi lafiya,“ “girki nake so ki masa”.

“Badariyya, ina rabaki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu, ba wai girkin ne bana san miki ba, tsorona duk ranar da kuka yi aure yace ki masa girki irin wanda kika saba masa lokacin kina budurwa, kika yi bai kai nawa ba yaya za ki yi?” “Ke rabu dashi wallahi, ni bazan iya ba, kawai ki masa”.

“Shikenan, me za a masa ?”

“Kinga last time fried rice aka masa yanzu kawai a masa Awara me Sauce”.

“Shikenan amma ki kawo da wuri, dan nima jibi zan raka Anty Faati gidan auren ‘yan uwan mijinta,” “Ai shikenan.” Badariyya ta faɗi tana duba mata sabbabin videos ɗin girkin data samo mata a tiktok.

Tafida Pov.

Zaune yake a mazaunin me zaman banza, yayin da abokinsa Mukhtar yake tuƙa motar, dan dama shine yaje ya ɗauke shi a airport bayan ya sauƙa a kano, idanunsa sanye da wani sun glasses, ya boye kalar ƙwayar idansa data koma ja tunda safe, duk da Mukhtar yasan halin da yake ciki amma baya san ya ɗagawa kowa hankali.

Ya ɗora hannunsa akan bakinsa yana nazari, nazarin abinda zai iya faruwa a Hadjia, yanzu ya shiga cikin wani irin hali da baƙin ruhin dake cikinsa yake tashi akai-akai, a da sai yayi wata da watanni bai tashi ba, amma a kwanakin nan abun ya ta’azzara.

Mukhtar ya d’an kalleshi da gefen ido “tunanin me kake ?”

A hankali ya sauke hannun daya ɗora akan bakinsa ya juya yana kallon window, sai ya lura da har sun shigo ƙofar garin Hadejia ta farko “Babu komai…”

“Aa Tafida, akwai wani abun”.

Hakane, kamar yadda Mukhtar ɗin ya faɗa akwai wani abun, jikinsa ne ke bashi cewar akwai wani abu dazai faru, to amma taya zai faɗa masa cewa jikinsa na bashi cewar wani abu zai iya faruwa.

Bai amsa shi ba, sai hannu da ya kai ya cire sun glasses ɗin dake idonsa, a lokacin suka karaso dai-dai round about ɗin na malam zangi, babban round about ɗin Hadejia.

Tun daga ganin lambar motar matasa suka gane cewa TAFIDA ya shigo gari, tun bayan daya dawo daga india, aka naɗa shi akan sarautar mahaifin sa ta TAFIDA, yayi hawan doki matasan garin dama ƴan mata suka ganshi, shikenan suka samu abun magana, kaf ƴan matan garin Haɗejia babu wadda bata san Tafida ba, samari na matukar sansa, hakan tasa a duk lokacin da za’ayi hawan sallah ko na kilisi dakarun Tafida sunfi na kowa yawa, Saboda rabi da kwatan matasan had’ejia suna sansa, Allah ya masa wannan farin jinin, ga kuma tarin ƴan matan da zaka gani a wajen idan har yayi hawa, kowa zaka tambaya zai baka labarin Tafida a haɗejia.

Juyowa yayi ya kalli Mukhtar da jajayen kwayoyin idonsa, Mukhtar ɗin ma ya jiyo ya kalleshi, saida gabansa ya faɗi yayinda yayi arba da kalar idon nasa, duk da ya saba ganinsa da idan kwayar idon nasa ta sauya, amma na yau yafi ja, jan har yayi yawa.

“Tafida kayi addu’a” yayi murmushi me ciwo yana kawar da kai, “itace abun da ako yaushe nake sanyi, amma kuma daga zarar na shiga irin wannan halin bana iya yinta, bakina nakeji yamin nauyi, hatta da harafi ɗaya na larabci bana iya furtashi”

Mukhtar ya girgiza kai cike da tausayin abokin nasa, wata iriyar rayuwa yake me cike da ban tausayi.

Hannunsa ya mika baya, ba tareda ya taba bottle ɗin ruwan dake kan kujerar baya ba, bottle ɗin ta taso da kanta zuwa cikin hannunsa, ya dawo da hannun nasa gaba riƙe da bottle ɗin ya buɗe ya kafa kai yana sha, zuwa yanzu sun shigo cikin kofar garin had’ejia, kuma sun hau titin fada, so yake ya samu yayi yaƙi da sheɗanin ruhin nasa kafin su karasa fada.

Bottle ɗin ya aje a gaban motar, ya dafe kansa da hannuwansa, da Mukhtar yaga haka sai ya shiga tofa masa addu’a duk wadda tazo bakinsa, bayan ɗan wani lokaci ya jiƙe sharkaf da gumi, har ya jiƙa rigar yadin dake jikinsa.

A hankali ya ɗago ya jingina da jikin kujera, yanajinsa ya dawo dai-dai, shed’anin ruhin nasa ya tafi, ƙwayar idansa ta dawo ainihin blue ɗinta.

Da haka suka karasa katafariyar fadar garin hadeji, Hadejia ginsau birnin doki, ta ɗan abubakar sarki babba. Inji ja’e haɗejia.

A gate ɗin farko wanda aka tanada domin aje motoci Mukhtar yayi parking, suka fito a tade, Mukhtarb ya ɗauka masa jakar dayazo da ita, gaba ɗaya harabar fadar a cike take fal da jama’a, Saboda bikin da za’a gudanar na yar sarki gimbiya Amina,isarsa ba jimawa labari ya karaɗe fada akan Tafida ya shigo garin.

Kofa ta biyu suka zo wucewa dogarai da hadimai sai kwasar gaisuwa suke, duk da shi Tafidan baya san hakan sam, shi baya d’aukan kansa daban da kowa, gani yake shi dai-dai yake da kowa, amma haka ƙa’idar take, dan haka babu yanda zaiyyi face ya amsa, su kuma suna gaisheda shine Saboda suna sansa, dan yafi yarima ɗan uwansa halin arzik’i.

Daga wannan gate na biyu suka shiga soro na farko a fadar wanda ya kasance soron masu gadi da tsaron fada a da, amma yanzu babu kowa a wajen sai masu wucewa, daga soron farko sai na biyu wanda shi kuma ya kasance soron malamai a zamanin da, wanda shima a yanzu babu kowa, sai kuma soro na uku wanda shi kuma ya kasance na ƙoramai, sai soro na huɗu wanda yake d’auke da wata babbar karaga ta sarkin Hadejia, daga kasan kujerar wani lallausan yashine zube, sannan kujera a samansa, a duk lokacin da sarki ya sauko daga sallar jumu’a yakan tsaya a wajen ya zauna ayi fadanci sannan a tashi, daga shi kuma sai soron bayi, wanda kuma a yanzu yake ɗauke da tsofaffun bayi na da, wanda har yanzu akwai sauransu, gaba ɗaya saida Tafida yabisu ya gaisar sunata saka masa albarka sannan ya wuce, daga nan kuma wani tamfatsetsen filine, wanda ya kunshi hanyoyi hud’u, daya wadda zata sadaka da 6angaren matan sarki da kuma turakar sarkin, ɗaya kuma wadda zata kaika ai nahin majallisun sarki, sai kuma wadda zata kaika 6an garen bayi da kuyangu na fadar, Sai ta murin dominan sarki.

Nan ɗin ma a cike yake da jama’a haka suka yanki hanyar da zata sadasu da 6an garen matan sarki, wata uwar doguwar tafiya suka yanka kafin suka iso ainahin inda bangarorin matan sarkin suke guda uku, wanda yafi kowanne girma suka nufa, kowanen gini akwai beni, amma kuma kuma irinsu ɗaya sai na tsakiyarsu daya yafi girma.

Aminttaciyarta suka samu tana fitowa daga ƙofar shiga, ta gaishe su tareda faɗi bari tai musu iso, Mukhtar sai ya tsaya yana faɗin “na gama nawa aikin, na kawoka gida lafiya, dan haka sai anjima idan ka samu fitowa”.

Tafida ya juyo yana kallonsa, sai kuma ya tabe baki cikin ɗaga kafaɗa, dan Mukhtar ba bako bane, shi ɗan gidane, ya karbi jakar tasa sannan ya saka kai cikin kofar parlon, tuntuni an masa iso wajenta, dan haka ya saka kafarsa cikin parlon kai tsaye daga parlon farko ta wuce na biyu, a nan yayi birki, kamshin turaren wutane ya fara ziyartar hancinsa, kafin a hankali ya fara bin parlon da kallo, baiga kowa ba sai himilin tarin kayan abinci akan coffee table, wanda yake da tabbacin nasa ne, yayi murmushi yana juya kai kafin a hankali ya ƙaraso cikin parlon saida ya shiga ya zauna, sannan ya lura da ashe bai rufe kofar ba, dan haka yayi nuniga kofar ya motsa hannunsa nan take kofar ta rufe kanta tareda motsawar hannun nasa.

A lokacin ne kuma ta shigo cikin parlon, bakinta ɗauke da sallama, ya ɗaga kai ya kalleta yana mata murmushin me tsada, wanda ba a ko yaushe yake irinsa ba, dan har hakwaransa na bayyana, itama murmushin take har ta ƙaraso ta zauna a kujera kusa dashi, cike da girmamawa ya gaishe ta, sannan suka ɗan ta6a hira kaɗan, dan ita izzar mulki ta mayar da ita muskila, shi kuma jinin mulki dake yawo a jikinsa yasa baya zantuka barkatai, abici ta fara gabatar masa sannan ta tashi ta bashi waje yaci abinci.

Fulani Khadija kenan, matar sarkin Hadejia Alhaji Abdullahi Abubakar Masu (c.o.n) shugaban hukumar sarakunan jahar jigawa, itace matarsa ta farko,bayan ita yanada wasu matan har guda biyu, Fulani Sadiya itace me bi mata sai kuma Fulani Usaibatu, Fulani Khadija sau ɗaya ta taba haihuwa, itama kuma bayan sun shafe shekaru samada ashirin ita da me martaba da aure, tukunna ta samu, inda ta haifi ƴarta mace me suna Nadra.

Ita kuma Fulani Sadiya yaranta huɗu a gidan, Habibu shine na farko, kuma shine babba a cikin ƴaƴan me martaba, wanda yake riƙe da sarautar Galadima a yanzu, hakan tasa ake kiransa da sunan, ko kuma ace yarima, sai maimun wadda tayi aure suna zaune da mijinta a buja, sai Amina da za’ayi aurenta yanzu, sai autansu Nabil wanda ya kasance karamine bai wuce 10 yrs ba.

Fulani Usaibatu kuwa yaranta biyu, Abbas da kuma Amra, suke nan iyalan gidan me martaba Alhaji Abdullahi Abubakar  Masu (c.o.n).

Abincin ya buɗe ya ɗan ɗiba kaɗan domin baya jin yunwa, idan kuma yace bazai ci ba Fulani bazataji daɗi ba.

Nadra ce tayi sallama tana shigowa cikin parlon, wani uban tsalle ta saki haɗi da ihu yayinda tayi arba da Tafida zaune a parlo yanacin abinci.

Bata san da Labarin zuwan sa ba, yanzu haka tana garden ne taji wasu bayi suna hirar wai Tafida yazo, shine tace bari tazo ta ganewa idonta, kansa tayi da gudu ta rungumeshi, ya aje plate ɗin dake hannunsa shima ya riƙeta yana murmushi me kama da dariya “ Hamma yaushe ka zo?” Ta faɗi tana sakinsa tareda zama a gefensa, “jiya na zo”

Tayi dariya, inda sabo ta saba da wannan halin na Tafida, ya iya mannawa mutum magana, idanta ne sauƙa akan ƴar Hadejian dake kwance a gefen fuskarsa, kusa da kunnensa gefen sajensa, ƴar Hadejia tsago ukune sirara da haifaffun haidejia kanyi a gefen fuskarsu, kusa da sajensu wajejen kunnensu, hakan tasa aka sanya mata ‘yar Hadejia

“Laa Hamma kalli ‘yar Hadejian ka ta kusa bacewa, dama nice, Allah ba karamin cutar mutane suke ba da suke musu wannaan ƴar hadejan”

Tafida ya kai abincin bakinsa yana murmushi, kowani ɗa dake fadar inhar ya haɗa jini da fadar walau mace ko na miji to sai ka sameshi da wannan zane, kuma bama fada kawai ba har mutanen gari.

Hannunsa ya kai ya tura sumar kansa baya, bawai dan ta sauko masa kan goshi bane, saide dan hakan ta zama ɗabi’arsa a duk lokacin da kansa yake babu hula. “To ko zamuyi changing face?”

“A’a Hamma rabani, ni da irin fuskarka ai duka samarin Hadejia dawowa zasu yi suce suna sona, kamar yanda kaima kaf ƴan matan Hadejia ke sanka”, maganar tata ta bashi dariya, amma kawai sai yayi murmushi, “au haba ? Ni ɗin suke so kuma ?”

“Eh mana, akwai wata class mate ɗina ma datake yawan damuna da zancenka, tace Tafida kaza, Tafida kaza, har cewa ta yi idan tazo bikin nan dan Allah na haɗaku ku gaisa, nace mata kanajin hausa ta ƙaryata ni, wai ai kai Indian ne taya zaka iya hausa”

“Kai min jakata bangarena pls, i am tired of wannan surutan naki”

Nadra ta miƙe tana jan jakar tasa dan ta sani yayan nata baya san surutu da yawa, hakama Mumzy gashi kuma ita Allah yayi ta da magana.

<< Yadda Kaddara Ta So 2Yadda Kaddara Ta So 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×