Skip to content
Part 33 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Nnamdi Azikiwe International airport, Abuja.

Hanam da Haris ne tsaye a jikin wasu kujeru, yayinda Masarrat, Salwa, Al’amin da kuma Khalil wanda ke riƙe da Arya suke tsaye daga kusa da su suma.

Yau sati biyu kenan da rasuwar Abba, dan haka Masarrat tace su yau zasu koma, kuma tare da Arya zasu tafi, dan Hanam ɗin ta yayeshi, kuma su Al’amin ne suka riƙa mata magiya kan ta bari su tafi da shi, babu yanda za ta yi haka ta amince musu, ita fa tunda Abba ya rasuma jifa-jifa take ganinsa, rabonta da ta ɗauke ke shi kuwa tun ranar da Abban ya rasu.

Amma shi ko a jikinsa harkokinsa yake, bama ya nemanta. Idanuwanta ne suka cika da ƙwalla sanda suke mata sallama, dan haka ta rungume ƙannen nata su duka uku, wanda ta fara sabawa da su a sati biyun, sannan ta shafa kan Arya, bayan ta sumbaci kan nasa, ta miƙa hannu domin ta ɗauke shi, amma sai ya juya kansa yana shirin saka kuka, ido waje tace.

“Aryaan hai amma (Aryaan amma ce fa)”

“Shifti ?, iltillak innu huwa biddu yana wu bas”

(Kin gani ba ?, ai na faɗa miki cewar mu yake buƙata kawai)

Hanam ta dunguri kan Al’amin dake wannan batun.

“Bari kiga” Cewar Haris yana miƙawa Aryaan ɗin hannu, da dariyarsa kuwa yaje wurinsa, gaba ɗayansu suka saka dariya.

“Wato nice baka so kenan ?”

Hanam ta faɗi tana kallonsa.

“Muna makara kuzo mu tafi”

Masarrat ta musu maganar cikin harshen larabci, Haris ya miƙswa Al’amin Aryaan, Hanam ta rungimi Masarrat sannan suka juya suna tura jakukunan su, Hanam sunyi da Masarrat ɗin akan zataje Egypt taga ‘yan uwanta na can, daga nan saita dawo da Aryaan.

Haman ta share gajerar ƙwallar kewar Aryaan da ta sauƙo mata, bata tab’a nisa da shi irin haka ba, a koda yaushe yana tare da ita, amma cikin makokin nan sam bata tare da shi, yau yana wajen su Al’amin gobe wurin su Rafi’a da su Nabila, jibi kuma yana wajen su Kamal gata kuma wajen su Mero, sai wajen su Kamila ƙannen Kamal wato yayunta, wajen Masarrat sai wajen ‘yan hakuɗau, harda wajen Maman Harees wadda ta koma Enugu bayan Anyi bakwai.

An nuna masa soyyayar da bai samu ba a baya, taso ace Abba yana da rai hakan ke faruwa, taso ace ya ga yanda ‘yan uwanta ke santa suna nunawa jikansa ƙauna.

Hannayen Harees ta ji a kan kuncinta yana share mata hawaye, juyowa ta yi tana kallonsa, kafin ta faɗa jikinsa tana sakin siririn kuka. Harees ya shafa kanta cikin rarrashi.

“Ki yi haƙuri mana, na tabbar da Ammi zata kula da shi”.

Ta ɗago da kanta tana share hawaye.

“Muje ?”

Ta gyaɗa masa kai, ya kamo hannunta sannan suka fita daga wurin.

MARYAM POV.

Ta yi ƙwafa yafi sau a ƙirga, zaune take a kan kujera a falo, yayin da wayarta ke riƙe a hannunta tana duba comments ɗin da ake mata.

Daga kan kujerar kuma Tafida ne kwance, ya lanƙwasa ƙafarsa faya, ɗayar kuma ya miƙeta yana kaɗawa, kan cikinsa kuma system ɗinsa ce, yana kallon wani Hollywood movie, me taken The last witch hunter, kansa kuma akan cinyar marya.

Sanye yake da wandon yadin daya saka tun safe, sai dai ya sauya rigar yadin zuwa wata baƙar T-shirt, hannun Maryam na hagu yana motsi a cikin sumar kansa, duk tsaki da ƙwafar da take yana ji, duk da a hankali ta ke yi, sai dai kuma shi yana ji, a zatonta baya ji.

Baisan me a ka mata ba, dan yasan ta, bata da yawan fishi, sai kawai ya ji yana san sanin abinda a ka matan, kuma bisa ga dukkan alamu daga wayar ne taga abun da ya b’ata mata ran.

Duk dan neman tsokana sai ya ciro hannunta daga cikin sumar kansa ya dawo dashi kan cikinsa, amma bata bar kallon wayar ba, daga haka ya fahimci koma de miye a wayar to babbane. Dan haka sai yace.

“Miriam, wai shinkafar ba ta yi ba ?”

Maryam ta sauƙe wayarta sannan ta a jeta a kan coffee table, ta ɗauko pillow ta ɗora kan Tafida akai yayin da ita take miƙewa, bata ce masa komai ba ta nufi kitchen, bata so ta yi magana ya gane cewar ranta a bace yake.

Yana kallonta har ta ɗan shakwanar da zata sada ta da kitchen saida ya ji ta buɗe ƙofar kitchen ɗin, sannan ya miƙe zaune, ya aje system ɗin nasa a kan Coffee table bayan ya danna paused.

ya kai hannu ya ɗauki wayarta, sannan ya shiga dubawa, Ticktock shine inda ta shiga a ƙarshe, da alama de ‘yan comment section ne suka tab’ota.

Dan haka ya mayar da tata wayar ya aje, ya ɗauko tasa sannan ya shiga app ɗin Tiktok ɗin, ya yi searching ‘Miriam’s Cook’, dan shine sunan da suka tsayar ranar da suka dinga rubuce-rubece na neman sunan da za’ayi using da shi.

Last vedion da ta yi posting ya buɗe wanda shine ta yi recipe ɗin cow tail sauce, kuma bayan ta gama tace masa wai ana cewa bata nuna tana cin abincinta, dan haka yazo su ci, loma biyu kawai sukayi recording, kuma iyaka hannayensu ne, banda fuska.

Comment section ya shiga, ya fara karanta abinda aka faɗa mata, duka magana ce a kansa, sai yaba shi ake duk da ba’a ga fuskarsa ba, sai abun ya bashi dariya, wato de kishi take. Ta ɗan jima bata dawo ba, hakan yasa shima yaci gaba da karantawa.

Maryam na shiga kitchen ɗin, ta duba shinkafar da ta bari a wuta, sai da Tafida yace kada ta yi girki yau tunda ba daɗi take ji ba, amma tace masa a’a zata iya.

Sauƙe shinkafar ta yi ta saka masa a plate sannan ta juye tata a flask, dan baza ta iya ci yanzu ba, jar stew ɗin data haɗa, ta zuba masa, wadda taji naman sa, shi da kansa yace mata yana san farar shinkafa da stew.

Dan haka ta dafa masa yau, bata samu lokacin da ta haɗa drink ba yau, dan haka ta ɗauka maza ruwa kwai.

“Ina san soft drinks ”

Maganar ta faɗo mata, dan haka sai ta aje ruwan a gefe, ta buɗe inda ta saba aje drinks ta ɗauko, Fanta, sprite da 5 alive, ta aje su aka island, ta zagaya zuwa jikin stove ta zuge wannan wurin glass ɗin, sannan ta tsinko mint, ta wanke ta tas a sink, ta zubata a karamin plate ta ajeta itama akan islan.

Ta ƙara dawowa wurun fridge ta buɗe, a inda ta saba aje fruit ta ɗauko lemon zaƙi, lemon da cucumber.

Ta ɗauko cutting board, ta shiga yanka cucumber, lemon, da lemon zaƙin nan cikin shape ɗin circle, bayan ta gama ta ɗauko wani bowl me ɗan faɗi, ta juye drinks ɗin a cikin bowl ɗin, sannan ta kawo mint ta saka, sai su lemon ɗin da ta yanaka suma ta zuba, saida ta juyasu sosai, sannan ta ɗauko glass cup ta ta zuba masa masa a ciki.

Sauran kuma ta ajiye shi a cikin fridge ta dawo kan kayan abincin nasa ta jerusu a kan tray ta ɗauka sannan ta fita.

Da fiton Tafida ta fara arba a falon, ta tsaya tana kallonsa, a tsaye yake, wannan gashin kan nasa ya saƙo masa kan goshi, yana sheƙi a cikin fitulun falon, hannayensa biyu manuniya cikin bakinsa yana fito dasu, wato duk ɗabi’ar indiyawa tana jininsa.

Yanda yake fiton da ƙara kai kace usur ne, usur ɗinma irin me ƙaran nan, wanda ‘yan ball suke amfani dashi.

Kanta ta sunkuyar ƙasa sannan ta ƙarasa shiga cikin falon, ta aje masa trayn a kan coffee table, har zuwa lokacin bai dena mata fiton ba.

Saida ta ɗago daga aje plates ɗin ta kalleshi, sannan ya tsaya, sai kuma ya shiga tafa mata, daga baya ya motsa hannunsa na dama cikin wani iron salo da indiyawa ke yi idan zasu yabi abu kokuma suyi tambaya akai.

“Bravo Wifey, Bravo, shabaash (fantastic), Kya bate! (amazing)”

Ita de bata ce komai ba, kanta a ƙasa, dan har yanzu bata dena jin ɗumin lips ɗinsa a kan nata ba, ji take kamar har yanzu lips ɗinsa na kan nata, ɗazu ma da ya dawo da ƙyar ta iya yarda ta haɗa ido da shi, dan tsabar kunyarsa da take ji.

Tafida ya miƙe hannayensa biyu, tare da ɗorasu a kan kafaɗun Maryam, yana kallon cikin idonta.

“Dama haka kike da kishi Miriam ?”

Wata uwar kunya da tafi ta da ta ƙara mamayeta, ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana jin inama ƙasa zata rabe biyu ta nitse a ciki, ta san cewa comments ɗin nan ya je ya duba, tunda ta fara dubawa ranta ke b’aci, gaba ɗaya maganganu a kan mijinta su suka cika wurin, babu wadda tafi bata haushi ma irin wadda ta rubuto.

‘Kai sis, da alama mijinki akwai kyau wallahi, daga hannunsa ma zaki san cewa shi kyakyawa ne, inama zan gashi’…

Sai wanda ke tambayarta kan dama mijinta farin fata ne ?, masu tambaya a kan yau me yasa bata saki sabon recipe ba basu da yawa.

Sai ta ɗan cije leb’enta kaɗan, tare da ɗora hannunta a kan nasa ta ture hannayen nasa tana ja da baya.

“Kaci abincin, na yi shanya ɗazu, bari naje na ɗebo”

Daga haka ta juya ta fita garden ta ƙofar dake falon.

Tafida ya yi ‘yar dariya yana jinjina kai, ya koma ya zauna yana ƙoƙarin fara cin abincin, amma abinda ke cikin glass ɗin shi ya fara ɗaukar hankalinsa, dan haka saida ya ɗauka ya ɗanɗana tukunna, yama kasa gane ainahin taste ɗin, yarasa takameme na miye.

Ya ƙara sha, sai kuma ya lura da idan bai aje ba wata ƙila zai iya shanyewa ba tarevda yaci abincin ba.

Yana zaune a wajen ta dawo daga garden ɗin, hannunta riƙe da basket, ta ɗebo kayan data wanke dazun, shikan yana ga ƙoƙarin Maryam, duk da bata da lafiya amma a yau saida ta musu wanki, dan harda kayansa a ciki.

ironing room ta shiga, bayan ɗan wani lokaci sai ta fito, ta dawo ta zauna a inda ta tashi ɗazu, ta sauki wayarta taci gaba da duba comments ɗin.

Kuma a ciki taga wani daya ɗauki hankalinta, wanda aka rubuta;

Hey!, mrs Tafida!, Badar ce, kimin magana ta chat…

Ai bata ma gama karanata comment ɗin ba ta shiga profile ɗinta, taga hoton Badar ɗin ne akai, wato sabonbaccount ta sake kenan?, ta dubata a wajen message ta aikamat da sakon.

‘Allah sarki Ƙauna, ashe kina duniyar?, na yi kewarki Allah, ki turomin lambarki pls.

Bata san sanda wani murmushi ya sub’uce mata ba, dan da gaske ne ta yi kewar Badar ɗin, tabyi offline, ta janyo littafi zata fara karatu.

Idonta ya sauƙa ak kan rubutun Tafida dake kan bangon littafin, ba yau ta fara ganin rubutun nasa ba, ranar da suke shawara a kan sunan nan ta fara ganin rubutun nasa, wani rubutu me kama da tafiyar tsutsa, gaba ɗaya rubutun a haɗe suke, amma kuma ana ganewa, sai dau ba sosai ba.

Littafin ta buɗe tana Ɗaukewa ƙafarta daga ƙasa zuwa kan kujerar.

“Ke ba zaki ci abincin ba ?”

Taji muryar Tafida ta tambaya, dan haka ta ɗan sauƙe littafin sannan ta kalleshi, shi ba ita yake kallo ba, idonsa na kan system ɗin ne, dan yaci gaba da kallon nasa, kuma abincin yake ci har yanzu, dama ta saba ganin wannan cin abincin nasa da babu sauri, idan yana cin abinci kamar mara laka, tasha rayawa a ranta cewar da ace yana ciyyaya sanda yake makaranta, wata ƙila ko loma ɗaya bazai samu ba za’a cinye abincin.

“A’a zanci amma ba yanzu ba”

“To ki tabbatar de kinci, kuma kin sha maganinki”

Ta gyaɗa masa kai tana ɗago da littafinta.

HARIS POV.

Ɗakin Hanam ya shiga, sbd ya bata abincin da ya siyo, sai ya isketa kwance a kan gado, gaba ɗaya ta kashe wutar ɗakin, da alamama bacci take, sai kawai ya aje mata abincin akan coffee table ɗin dake ɗakin, ya juya zai fita.

“Ina zaka je ?”

Ya tsinkayi muryarta cikin magagin bacci, hakan yasa ya tsaya da tafiyar da yake, ya juyo ya kalli kan gadon, ɗakin babu isashen haske, sai na bed side lamp kawai, kuma shine ya temaka masa wajen ganin fuskarta.

“Abinci na kawo miki, ki tashi ki ci”

Tana daga kwancen ta girgiza masa kai sannan tace.

“No na ci abinci a gida ɗazu”

Sai ya gyaɗa mata kai ya juya zai fati.

“Ina zaka je ne ?”

Sai ya kuma tsayawa ya juyo ya kalleta, yanda daren nan ya yi kam ai tasan de ba shi da inda zaije da ya wuce dakinsa, zuwa ze yi ya kwanta.

“Kwanciya zanje na yi”

Sai yaga ta miƙe zauna, tana murza ido.

“Kazo ka kwanta a nan”

Ta faɗi tana nuna masa gefenta a kan gadon, kamar me tantance abinda take faɗi, uchenna ya kalli kan gadon sannan ya kalleta.

“Gadon zai ishemu fa”

Dariya ta kusa sub’uce masa, ita ta ɗauka cewar gani yake kamar gadon ya musu kaɗan, sai kawai ya jinjina mata kai, ya fara takowa zuwa jikin gadon, ta ɗayan b’arin ya za gaya, ya zana a bakin gadon yana cire crocs ɗin ƙafarsa, sannan ya kwanta yana jan bargon ya bata baya.

Yana jin yanda itama ta ja bargon, kafin yaji sauƙar ɗumin numfashinta a bayansa, sannan hannayenta suka zagaye cikinsa, sai kuma kanta ya sauƙa a gadon bayansa.

“Mu kwan lafiya, Harees”

“Uchenna zaki ce”

Ya ji sanda ta ɗan ɗaga kan ta daga jikinsa, alamun ta kalleshi, sannan ta mayar da kan nata, tana ƙara maƙalƙale hannunta dake kan cikinsa.

“Harees yafi daɗi”

“No Uchenna ne yafi daɗi”

Ya ji sanda ta kuma ɗaga kanta sannan tace.

“Baka san sunayen musulmai ?”

Itama tanaga sanda ya girgiza kai, dan shi take kallo, sannan muryarsa ta fito a hankali cikin shirun daren.

“Ina so mana, kawai dai nafi san Uchenna, sbd uchennna yana nufin sarki, Harees kuma me gadi yake nufi, da sarki da me gadi wannene ya fi ?”

Yana jin sautin murmushinta, sannan muryarta ta biyo baya.

“Sarki kam yabfi”

A hankali Uchenna ya saka hannunsa akan na Hanam, sannan ya raba shi daga riƙon da ta masa, hakan yasa itama ta ɗaga kanta daga bayansa, sai kuma ya juya yana fuskantar ta, sannan ya saka hannayensa biyu, ya janyota jikinsa, kanta ya sauƙa a kan pillownsa, yayin da hannunsa na dama ya ƙankameta daga baya, hannunsa na hadu kuma yana kan ƙugunta ne.

ya jata jikinsa sosai, ta yanda hatta da bugun zuciyarsa tana iya jiyowa, Zuciyarta ta shiga rawa, tana jin sak abinda take ji a duk sanda zata shiga jikinsa irin haka.

“Me ya sameki”

A kalance muryar sa ta fito, kuma ya tambaya ne ganin jikinta na rawa, kanta ta girgiza masa, alamun ba komai, daga haka shima bai ƙara cewa komai ba, ya rufe idon, sannan bacci ya yi gaba dashi.

Hanam taci gaba da kallon kyakyawar fuskarsa, da taga itama hakan bazai kaita ba sai ta lumshe idonta ta ƙara gyara kwanciyar ta a cikin jikinsa.

<< Yadda Kaddara Ta So 32Yadda Kaddara Ta So 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×