Skip to content
Part 4 of 26 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Da misalin ƙarfe goma na dare, Fulani Khadija na zaune a ɗakinta tana karatu, taji wata iriyar razannaniyar ƙara, wadda ko tantama batayi daga ɗakin Tafida ta fito, a ruɗe ta aje littafin hisnul-muslim ɗim da take karantawa, ta fito da sauri.

A hanya taci karo da Nadra, wadda ko tantama batayi itama jin ƙarar ne yasa ta fito, basu cewa juna komai ba, suka ɗunguma zuwa ɗakin nasa dake can nesa da nasu.

Nadra ce ta murɗa handle ɗin kofar kuma har lokacin sunajin gurnanin da yake, da sauri taja kofar ta rufe tana fashewa da kuka, ko fulani bata tambaya ba tasan me tagani, wannan abun ya saba faruwa dashi a wasu lokutan, amma kuma sam bayayin irin wannan abun.

Matsar da ita tayi daga Jikin kofar ta kama kofar ta buɗe, ta ganshi yana murƙususuwa a kasan ɗakin, kwayar idonsa ta koma ja, dogayen fiƙoƙin nan sun fito masa, gaba ɗaya ya hargitsa ɗakin, gurnani yake da fisge-fisge, nan take kwalla ta ciko idonta, tausayin ɗan nata na ƙara rufeta, shi kuma haka Ƙaddara Ta So ya kasance, a yanzu babu temakon da zata iya bashi, domin tana kusantarsa zai iya halakata, dan wannan ba shi bane, shaiɗanin ruhin nan ne, kuma da zarar ya shigeshi, baya gane ɗan uwa, aboki, ƙawa, uwa, uba ko masoyi.

A baya ta taba kokarin kusantarsa lokacin da yake cikin irin wannan halin, abinda ya mata har yau bata manta ba, dan saida ya buga mata kai da bango, kuma har yanzu akwai raunin a goshinta.

A duk lokacin da abun ya tashi rikiɗewa yake ya koma dodo, kofar ta janyo hawaye na mata zuba, addu’a ta shiga masa dan ita kaɗaice abun da zata iya masa a yanzu, jiki a sabule ta koma parlo, yayinda Nadra ke biye da ita, suka zauna sukayi jigum-jigum, banda kuka babu abinda Nadra take, duk da ba yau ta saba ganinsa cikin irin wannan halin ba.

Fulani kuwa hawaye kawai take gogewa, gashi yau ba itace keda turaka ba. Dolene ma gobe ta nemi ɗan masani, lokaci yayi da zai faɗa mata yarinyar data dace, ya kamata a kawo karshen wannan abun, ta gaji, bazata iya zama tana ganin ɗan nata cikin wannan halin ba.

Maryam Pov..

Yau islamiyya ta tafi, domin ta ɗan kwana biyu bataje ba, Kuma tun bayan da tayi sauƙa ma ba sosai take zuwa ba, yau ta samu space hakan yasa tace bari taje makarantar.

Kuma bayan sun taso ne tana tafe a hanya ita ɗaya, kamar kullum sanye cikin dogon hijabi, sai taga sanata a gabanta yana mata murmushi.

“Hajiya Maryam, barka da yamma”

Ta ɗan kawar da kai gefe sannan tace “yauwwa barka”

Ta amsa ba yabo babu fallasa

“Maryam kinƙi ki bani dama, kullum cikin bayyana miki sirrin zuciyata nake amma kinƙi ki gane, wallahi maryan ina sanki, ki yarda dani”

Ta ɗan juyo ta kalleshi “amma sanata kasande bai kamata ace ka tsareni a titi kana min magana ba ko ?”

Sai ya shiga sosa ƙeya “to kiyi haƙuri zanzo gida na sameki”

Tafiyarta taci gaba dayi, ta barshi tsaye a nan, yana binta da kallo, shide nan duniya baiga wadda yake soba kamar Maryam, komai nata ya masa, nutsuwa, kamala, ilimi, haƙuri ga kuma kirki, ta haɗa komai da namiji yake buƙata a mace.

Tana zuwa gida ta aje jakar islamiyyar a ɗaki tareda hijabin ta fito tsakar gida, Maamu tana ban ɗaki, muhsin ne kawai zaune a tsakar gidan nasu data sha shara ƙaƙal, kamar ka suɗe, yana wasa, ta zauna kusa dashi tana kakka6e kurar dataga a kansa, yayinda shi yake ci gaba da wasan nasa.

“Auta me yasa bakaje islamiyya ba yau ?”

“Malam Shawwal ne yake duka na”

Ya bata amsa ba tare da ya bar wasa da motar gorar da Hussain ya haɗa masa ba.

“kuma yanzu auta dan malam shawwal na dukanka sai ka dena zuwa?, haƙuri zakayi ka ci gaba da zuwa kaji,? “To dukana yake yaya”

“Ka de daure kaji ?, ko baka san shiga aljanna ?”

Ta faɗi tana ɗago da kansa ya fuskance ta, “ina so mana”, “da kyau yaran kirki, to sai ka daure ka riƙa xuwa kaji?“ ya gyaɗa mata kai, a lokacin ne kuma Maamu ta fito daga banɗakin.

“Maamu wai su Hussain basu kawo komai ba yau?” “Aa sun kawo shinkafa, kuɗin kayan miyane dai babu, amma ai akwai mai da yaji sai muci haka”

Maryam ta miƙe tana faɗin “ina shinkafar take ?, sai na dafa kinga magariba na ƙoƙarin yi”

“Duba ɗakina tana kan loka, kuma nayi magana da kawu yace zai turo miki ta account”

Maryam ta shiga ɗakin Maamu tana faɗin “to a taya ni godiya”

Hussain ne yayi sallama, sannan Hassan, Maamu tana zama kusa da muhsin ta ɗaga kai ta kallesu tana amsa sallamar, karasowa sukayi suma suka zauna akan tabarmar, Hassan ya miƙawa Maamu ledar dake hannunsa yana faɗin

“Maamu gashi kayan miyar ne aka samu, harda nama”.  A lokacin ne kuma Maryam ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da ledar shinkafar data ɗauko.

“Nama?” Muhsin ya faɗi yana washe baki, Hassan ya ranƙwanshwshi a ka, “eh nama kuma ba za ka ci ba”

Ya fashe da kukan shagwaba yana shura ƙafa, Maamu ta janyoshi jikinta, “Kasan Allah Hussain zan sabar maka, ka fita idona akan auta, tam”,mya juya kai yana dariya, Hassan ya miƙe ya nufi inda Maryam take “Hassan inji dai ba bashi kuka ci ba”.

Maamu ta faɗi tana duban Hassan ɗin, bayan ta buɗe ledar, tsayawa yayi sannan ya jiyo ya fuskanceta “aa ba bashi muka ci ba, wani muka yiwa gyaran mota kuma bai biya ba sai yau”

“To Allah yayi albarka”

Duka suka amsa da ameen, Hassan ya ƙarasa wajen Maryam “wayarki zaki aramin yaya”, “me za ka yi da ita?” Ta tambaya ba tare da ta dube shi ba, tana wanke shinkafar data cire a ledar, “ke dai dan Allah ki aramin, abu zanyi”

Ya faɗi yana ƙara ƙasa da murya, ta ɗago ta kalleshi “ammafa ka sauya min screen gard, dan ya faffashe”, “har cover zan sauya miki, ke dai ki bani”, “yaushe zaka dawo min da ita?”

“Gobe da safe”, “shikenan, dan Allah ka biya ta wajen Alos ka turomin littafin Sanadin Caca, kuma kace masa wanda pinkish lady ta karanta nake so”, “to”

Ta miƙe ta shiga ɗaki ta fito sannan ta miƙa masa wayar.

Hanam Pov.

Zaune take a office ɗinta, tana zane a ipad ɗinta, Secretary ɗinta ta shigo bayan ta nemi izini, ta aje ipad ɗin tana kallonta, “Madam an gama haɗa rigar”, “ok muje na gani”.

Ta faɗi tana mikewa, haɗi da gyara botton ɗin suit ɗin jikinta, secretary ɗin ta juya zata fita har suka kusan cin karo da me shigow, ta bashi haƙuri sannan ta fice, Hanam ta Ta tsaya tana kallonsa, ya ƙaraso har gabanta ta harɗe hannayenta tana ci gaba da kallonsa.

“Magana nake san muyi”

“Babu abinda ya rage da zamu yi magana akai Jabeer”.

“A’a Hanam, akwai ya kaamata ki saurareni“, “faɗi ina jinka”

Ta faɗi tana gyara tsaiwarta, “ya kamata mu zauna tukunna”.

“Nop, ka faɗi abinda zaka faɗa anan, inkuma ka manta abinda kazo faɗine zanje nayi aikin dake gabana”.

“Dan Allah Hanam ki saurareni, a da mun shirya yanda zamu rayu tare, muntsara duk yanda zamuyi rayuwarmu ta aure, amma cikin shekaru biyu komai ya sauya, kika watsar dani, dan allah Hanam ki dawo ainahinki, Hanam ɗin dana sani a baya”

“Ka gama? Ni zanje nayi aikina” tayi maganar tana duba digital watch ɗin dake hannunta, bai haƙura ba yaci gaba.

“Hanam dan Allah ki tuna, munyi alƙawarin zamu rayu tare, zamu haifi yara mu tsufa tare, komai zamuyi tare, zamu haɗa gidanmu, daga ni sai ke sai kuma ƴaƴan da zamu haifa….”

Bata ko tsaya ta ƙarasa jin bayanen nasa ba, ta rabashi ta wuce, ta buɗe kofar ta fita tana faɗin. “Idan ka gama zaka iya fitowa daga office ɗin”

Jabeer ya sandare a wajen tsabar mamaki, Hanam ta gama shayar dashi ruwan mamaki, ya rasa gane kanta, ya rasa abinda yake damunta.

Saida taje ta gama na zarin sabuwar rigar da ɗaya daga cikin designer ɗin fashion house ɗin nata ya ɗinka, sannan ta nuna inda bai mata ba da inda take so a gyaggyara, sannan ta fito daga inda akaware domin yin ɗinki kawai a fashion house ɗin.

Ta kamo hanyar dawowa office ɗin, kukan aryaan taji daga cikin ɗakin data ware domin kula dashi, wanda a da ya kasance office ɗin wani ma’aikaci, kofar ta buɗe ta shiga, kuma tun kafin ta buɗe ɗin taga karima naani ɗin nasa ɗauke dashi tana jijjigashi, kasan cewar wajen glasa ne “me ya faru ?”

Ta tambaya tana karasawa ciki “kuka yake tayi, nayi tunanin yunwace shine na bashi custard amma yaƙi karba”

Karima ta koro bayanin yayin da Hanam ke karbarsa daga hannun Kariman, “bari na shayar dashi”

Karima ta risina tana kwashe kayan wasan daya barbaza, ita kuma Hanam ɗin ta zauna akan armchair ɗin dake wajen, tareda saka mishi mama a bakinsa, ya karba ya fara tsotsa, a lokaci guda yana wasa da perndat ɗin sarkar dake wuyanta, ta kai hannu ta cire hular sanyin dake kansa me kunnuwan teddy bear, ta shiga shafa gashin kansa wannda yake baƙi siɗik, kuma me taushi, sai kuma ta dawo da hannunta ta riƙe dogon hancinsa irin nata sak tana faɗin, “za ka sani duk ranar dana maka yaye.”

Sai taga yayi murmushi, still kuma maman na bakinshi, kamar wani wanda yasan me take cewa, itama sai ta masa murmushin.

Tafida Pov.

Kirari da kuma maganganun hadimai yayinda suke gaisar da me martabane ya ankarar da fulani cewa mai marta ne ya shigo bangaren nata domin su gaisa, dan hakan al’adarsa ce duk safiya yakanbi ɗakunan matansa su gaisa, kasan cewar suna falo na biyu ne yasa ta iya jin maganganun nasu, kafin kuma kofar ta buɗe, a lokacin da hayaniyar ta ragu, wanda hakan ke nuna mata cewar hadiman sun fita falo na farko, mai martaba ya shigo cikin shigarsa ta alfarma, tris yaja ya tsaya yana kallonsa ɗaya bayan ɗaya.

Ga abinci tile a gabansu su duka amma sam basu ko taba ba, fulanice ta ɗago da rinnanen idonta ta kalleshi, hankalinsa ya tashi, amma kwarjininsa da kuma kamewarsa irinta mulki batasa ya nuna hakan ba, ƙarasowa yayi zuwa cikin parlon ya zauna akan kijera kusa datata.

Nadra ta zame daga kasan kujera tana gaisheshi, ya amsata yana ci gaba da binsu da kallo, kuma ko bayan ya amsata ɗin bata mikeba, tana nan durƙushe a wajen kanta a kasa, ya juyaga fulani, tun kafin yace komai yaga ta fashe da kuka.

Yasan cewa Tafida ya dawo, domin tun a jiya Tafidan ya nemi da su haɗu amma kuma yace masa saide da safe, dan hakama ya shigo da kansa dan su gaisa, kuma kukanta ke nuna masa cewar koma miye ya faru to Tafida ne, Fulani bata kuka akan komai sai akan Tafida.

***

“Eshaan jeka ɗauko min waccan ball ɗin”

Muryar Roshni mahaifiyar eshaan a wancan lokacin ta faɗi, wani karamin yaro ɗan shekara huɗu ya ɗago ya kalli kyakywar matar wadda take ba’indiya, ya ɗaga manuniyarsa ya nuna ball ɗin tareda faɗin “yeh ? (wannan?)” ya tambaya cikin harshen indiyanci, matar na murmushi ta gyaɗa masa kai, ya fita da gudu yayi wajen da ball ɗin take, matar kuma ta biyoshi da gudu itama tana dariya tareda faɗin “eshaan kabi a hankali, eshaan!!… eshaan!! …eshaan!!!!”

“Maa! Maaaa! Maaaaaaaa!….”

Yana fisge-fisge yake furta maganar, a razane ya mike zaune, Idanuwansa gaba ɗaya sun firfito waje sai haki yake, duba yakai ga hannunsa na dama, sai yaga wutar nan daya saba gani naci a tafin hannun nasa, idanunsa ya lumshe a hankali sannan ya dunƙule hannun nasa ya buɗe tareda idonsa nan take wutar ta bace, hannunsa yakai jikinsa yana shafawa.

Yaji t-shirt ɗin daya kwanta da ita jiya gaba ɗaya ta jiƙe da gumi, ya kuma lumshe ido, fuskar mahaifiyarsa ta dawo masa tunanin sa, a hankali ya buɗe ya sako kafafunsa ƙasan gadon ya saka slide sandales ɗinsa dake kasan gadon, hasken dake shigowa ɗakin ta windows ɗin dakin sune suke nuna masa cewar gari ya waye.

Idonsa ya kai inda ya aje wayarsa jiya daddare, kafin abinda ya sameshi jiya ya faru, yasan cewa dole ya hargutsa abubuwa da yawa a ɗakin, amma kuma gashi an gyara komai tun kafin ya tashi daga bacci, tafin hannunsa ya buɗe sannan ya miƙa hannunsa zuwa ga inda ya aje wayar dake can a kan wata chest drawer, nan take wayar ta tashi daga kan chest drawer ɗin da take a aje ta iso ta sauka akan tafin hannun nasa kamar wani magnet ne ya janyota.

Charger ya janyo ya sakata a chargy bayan ya cire ɗayar a chargy, ya miƙe tsaye ya shiga ban ɗaki yayi wanka haɗi da alwala ya fito yayi sallar asubar data wuceshi, sannan ya miƙe ya koma ban ɗakin yayi brush ya fito ya buɗe jakar dayazo da ita ya fito da wasu riga da wando na farar shadda, yau za’ayi hawan angwance, ya saka kayan sannan yaje ya tsaya a gaban dressing mirror ya shiga gyara gashin kansa kamar yanda ya saba kula dashi a kullum, sannan ya feshi jikinsa da tirare, ya ɗauki hularsa zanna bukar me aikin blue da fari ya saka a kansa sannan ya saka flat shoes blue ya d’auki wayoyinsa sannan ya fito.

<< Yadda Kaddara Ta So 3Yadda Kaddara Ta So 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×