Skip to content
Part 41 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

No. 45, Janjira St, Mumbai, india.

“Yanzu ina zamu je ne ?”

Cewar Neha lokacin da suka fito daga shagon da aka musu gyaran kai, suna tsaye a bakin titi.

“Muje muci pani puri”

Eshaan ya bata amsa.

“Kai wallahi bhai ka haɗu!, nayi kewarsa dama, to kaga mu ɗan ƙara gaba, akwai wani me siyarwa a can”

Ita de Maryam ba ta saka musu baki, kuma daga haka suka yi gaban. Tun ɗazu Maryam ta ƙi yarda su haɗa ido da Eshaan, dan da ga zarar ta kalli fuskarsa zata tuna cewa jiyafa a tsakiyar hannayensa ta kwana, sai kunya ta lullb’eta har ƙafa.

“Lefi na miki Piya (lover)?”

Jiya cutie!, yau kuma Piya ?, sunaye biyu kenan tsakanin jiya da yau, sai kawai ta sunkuyar da kanta ƙasa, yayin da suka tsaya da tafiyar, Dan sun iso wurin, Neha ce ta ƙarasa wajen me pani puri ɗin tana siyo musu.

Tafida yaci gaba da kallonta, daren jiya na ƙara dawo masa cikin tunaninsa, yanda Maryam ta ƙanƙame shi bayan da ya faɗa mata cewar yana santa.

“Kinyi shiru”

“Babu komai”

Saumar hannunsa ta ji a kan kumatun ta, ta yi saurin ɗagowa tana kallon wajen da suke, akwai mutane dan bakin hanya ne wurin, amma kuma kowa harkar gabansa yake, babuma wanda ya ko lura da su.

“Ko kissing ɗinki zan yi a nan babu me ce mana ƙala”

Maryam ta zaro ido tana zame fuskarta daga cikin hannunsa.

“Baki yarda ba na gwada miki ?”

Da sauri ta girgiza masa kai, tana mayar da bakin mayafin da ya sauƙo mata kan kafaɗarta.

“To faɗa min me na yi ake hukunta ni ?, or you are shy of me ?….”

“Ga pani puri”

Muryar Neha ta dakatar da abinda yake san faɗi, shi ya kai hannu ya karb’i ɗan ƙaramin kwanon dake hannun Neha ɗin, yayin da ita Neha ɗin ta ƙara komawa wajen me pani puri ɗin.

“Miriam akwai yaji, zaki ci ?”

Ta kalli abun da ke riƙe a hannunsa, ita fa cikinta ba ya san baƙon abu, yanzu sai ta yi amai, dan haka ta yi saurin girgiza masa kai.

“Good, bana san ki ci yajinsa ya dame ki”

Tana kallo suka ci shi da Neha, har santi suke.

Bayan sun gama da wajen suka wuce gate way of india, suka bawa barayen dake wajen abinci harma sukayi hotuna a wajen. Sun ɗan jima a wurin, Eshaan nawa Maryam bayani a kan tarihin wurin.

Kafin suka wuce marine drive, tekun dake gefen titi, kuma a tsakiyar garin mumbai, nan kuma hotuna kawai su ka yi.

Daga nan suka wuce Victoria terminus railway station, sun yiwa Maryam bayanin tarihin wajen, kafin suka si yi tiket ɗin jirgin ƙasa wanda zai kaisu byculla, dan jj hospital suka nufa.

*****

Eshaan ne ya fara shiga bakinsa ɗauke sa sallama, sannan Neha da Maryam suka shiga.

Me martaba, Fulani Sadiya, Maimun sune suka amsa. Fulani Sadiya tabi wanda ya shigo da kallo, zata iya cewa kusan shekararta uku rabon da ta ganshi, dan ba sashenta yake shiga ba, ita kuma ba ko ina take fita ba balle har su haɗu.

Kuma ganin ta da shi na ƙarshe tun sanda Me martaba ya tarasu gaba ɗaya a kan bikin ƴar gidan Chiroma da za’ayi. Kuma duk da ta jima bata ganshi ba tasan ya sauya, ya yi ƙiba, ya ƙara haske.

Shi ɗin da take duk wani ƙoƙarin ganin bayansa, yau shine ya zo yake duba ɗanta da bashi da lafiya, shi ɗin da take so taga ya faɗi ƙasa shine Allah ya ɗaukaka, sannan ɗan nata da take ji da shi shine ya faɗi ƙasan.

Tafida ya gaida Me martaba, Harda Fulanin da bata son haɗa ido da shi, kuma baisan dalili ba, yasan cewa sam matar bata san sa, tun yana ƙarami take nuna masa ƙyama, sannan itace mutum ta farko data fara faɗa masa cewar shi ba mutum bane.

Amma ko daga yanayinta yau yasan cewa ta yi laushi, kuma wata ƙila sbd jinyar ɗan nata ne, ko kuma shi ta yiwa abun ya dawo kan ɗanta, dan yasani, kuma yana gani a mafarkinsa, duk sanda zata masa wani asirin.

Wannan karon ne Allah be sa ya gani ba, wani abu da ya ƙara bashi mamaki shine gaida shi da Maimun ta yi, yarinyar da ko ganin inuwarsa bata san yi.

Ya amsa yana kallon Galadima dake kwance a kan gado.

Sai a lokacin su Maryam suka gaidasu baki ɗaya, Me Martaba yana ta kallonta, dan shi bai tab’a ganinta ba ma, yau ya fara ganinta, sannan Fulani Khadija ta faɗa masa yanda Tafida yace mata jikinsa ya yi sauƙi.

Kuma shima yaga hakan da idonsa, dan ba ƙaramin sauyawa ya yi ba. Fulani sadiya ta shiga kallon ƴan matan biyu, ta gane ɗayar de, dan ta tab’a zuwa haɗejia, kuma tana kama da Tafidan, kenan ɗayarce matar Tafidan.

Tafida ya ɗauki file ɗin Habibu yana dubawa, sannan yace da Me martaba.

“Ranka ya daɗe ai babu abinda aka rubuta a nan, bayanai sun nuna cewa babu abinda ke damunsa”

Me martaba ya gyaɗa kansa.

“Haka suka ce”.

“Amma ina da shawara, sam wannan jinyar tasa bata kama da ta asibiti, kamar aikin aisiri haka ko jinni”

Ƙulululu!, cikin Fulani Sadiya ya yi, ta haɗiye wani abu da bata san sunansa ba, kuma dama Tafida da biyu ya faɗi hakan, dan yaga reaction ɗinta.

“Nima haka nake zato”

Cewar Maimun tana kallon ɗan uwan nata cike da tausayawa.

“To bari likitocin su zo, sai muyi magana da su”

cewar Me Martaba.

Su Tafida sun ɗan jima a asibitin, kafin suka yi sallama a kan Tafidan zai dawo gobe. Daga nan kuma shopping suka wuce, inda suka yi da Arjit kan zazu haɗu a can.

“Wannan ya yi bhai?”

Cewar Neha tana gwada wata sarƙar ƙafa, ya girgiza mata kai.

“Ko kaɗan ki sauya”

“Ok to… Sauya min”

Ta ƙarashe tana miƙawa me sarƙar wadda ta gwada ɗin, tun da har yace ba ta yi ba to ba ta yin ba, tun suna yara shine yake zab’a mata sarƙar ƙafa.

“Kefa Miriam ba kyasan sarƙar ƙafa ?”

Maryam ta ɗago daga danna wayarta da take ta kalli Eshaan dake maganar.

“Na zab’o miki ?”

Ta gyaɗa masa kai. Shi da kansa ya zab’o mata, sanna yace ta gwada, gwadawar ta yi kuma ta karb’i ƙafar tata.

“Wow sirikita amma fa ta miki kyau, kina ji ?, ki riƙa saka sarƙar ƙafa da waist beads bhai yana sonsu”

Maryam ta juyo ta kalleshi, shi ba su yake kallo ba, dan waya ce kare a kunnensa yana magana da wani Arjit.

Suna tsaye a wajen Arjit ɗin da ake waya da shi ya zo, inda ya gabatar mata da shi a matsayin abokinsa. Arjit ɗin baya jin hausa, sai da turanci suka gaisa, wannan turancin nasu dake bawa Maryam dariya, dan ascent ɗin akwai ban dariya.

Sai da suka yi siyyayar kayan sakawa sosai sannan suka bar mall ɗin, ko da wasa Maryam taƙi ta ɗauki saree, hatta da lehenga ma ƙin ɗauka ta yi, chickankari ɗin da take gani shine dai-dai ita su ta ƙara ɗauka.

UCHENNA POV.

Wayarsa ce ta yi ringing hakan yasa ya dakata da kaiwa abincin da ya ɗebo bakinsa, ya kalli screen ɗin wayar ‘JUDE’.

Ya ɗanyi murmushi, dan sun kwana biyu ba su yi waya ba, dan yanzu makaranta Jude ɗin ke zuwa, ya ansa wayar da faɗin.

“Ɗan makaranta!, to ya school ɗin ?”

“Lafiya, Baba ne yake san ganin ka”.

Second ɗaya…biyu…uku.

*****

Unguwar Rafin Cinnaka

Da 03:00pm

Uchenna ne zaune a kan kujera, yayin da yake facing mutumin dake kwance a kan gado. Mutumin da ya shafe kwanakin rayuwarsa yana tsine masa, mutumin da ya koreshi daga gidansa yace ba ya buƙatarsa, wanan mutumin da ya ce ba zai tab’ayin albarka a rayuwarsa ba, kuma de shine wannan mutumin da tsawon shekaru goma da be yi a gidansa ba be nemeshi ba. Yau shine ya saka a nemo shi, ya sa a kirashi.

“Ya jikin naka ?”

Aja Johnson ya yi murmushi cikin raɗaɗin ciwo.

“Jiki babu daɗi Uchenna, ina shan wahala sosai, na saka Jude ya kiramin kai ne dan na nemi yafiyarka, ina so ka yafemin Uche, ban sani ba ko bazan ta shi ba, ka kuma roƙa min Rashidat da ta yafe min”

Uchenna ya rintse idonsa yana kawar da kansa gefe, yana jin wani abu me kama da allura na tsikarar zuciyarsa, yaji zuciyar tasa tana ɗaukar ɗumi, kamar da ake gasata a cikin oven. Bayan tsawon shekaru, Aja ya dawo yana neman yafiyarsu.

“Na yafe maka, kuma dama ni baka tab’a min komai ba, nide kawai ina so ka musulunta ne”

Aja ya kuma yin murmushi.

“Kada ka damu da wannan, tun wata huɗu da suka wuce na musulunta, wannan karon ba dan Rashidat ko dan soyyayarta ba, ba dan kai ko ƴan uwanka ba, tuba na yi tsakanin da ubangiji, sakamakon nasihar da Jude ke min a kullum ”

Ƙwalla ta zubo daga idon Uche, ya sha jiran irin wannan ranar, ya sha mafarkin ranar, ranar da mahaifinsu zai musulunta, ranar da zai ce su yafe masa.

Miƙewa ya yi ya ƙarasa kan gadon kusa da shi ya zauna, kuma bai jira komai ba ya rungume shi, ya saki kukan da ya jima be yi irinsa ba, hasali ma shi rabonsa da ya yi kuka tun rabar da Ajan ya kore shi daga gidan, sai a mutuwar Abba.

Jude ne shima ya ƙaraso ya kwanta a bayansu yana sakin nasa kukan.

Aja ya yi murmushi yana shafa kan ƴaƴan nasa gaba ɗaya.

“Allah ya muku Albarka“

Hausawa sunce komai ya yi farko yana da ƙarshe, a sanda za’a b’ata maka za ace ka yi haƙurui, sai dai a lokacin gani za ka yi kamar an cuce ne, amma kuma ai ance haƙuri me tadda rabo, idan aka haƙura za’a dace.

Uchenna ya ja hanci, wannan bakin da a kullum cikin tsine masa ya ke, yau shine ke saka masa albarka, yau Aja ne yace Allah ya masa albarka.

“Ameen”

*****

Survey NO 1433 Shiv Mandir Talo St, Chikoli Mumbai, India

08:40

MARYAM POV.

Fitowa ta yi daga banɗaki, bayan da ta saka farin chickankari ɗin da suka siyo ji ya, daga wandon har rigar duka farare ne, rigar ta kai guwarta, wandon kuma yanada faɗi.

Eshaan da kansa ke sanye da wannan hular sanyin tun jiya ya juyo yana kallonta, ita ta rasa me yasa yake saka wannan hular, kuma tun jiya bai cireta ba, da itama ya kwana.

Yau tun safe suka tashi da kai kawon mutane a gidan, da ta tambayi Neha sai tace mata ƴan uwansu ne, sun zo su yi bikin Holi ne tare.

Kuma tun jiya daddare akewa gidan decoration, kuma taga kowa sai farin kaya yake sakawa, dan kuwa harda Eshaan shima farin kayan ya saka. Kamar yanda yake kallon nata itama shi take kallo.

Riga da wandon kurta ne a jikinsa, rigar ta kawo masa guwa, daga gefe da gefen rigar akwai tsaga. Kayan sun amsheshi sosai, sai ya fito mata a matsayin Eshaan ɗinsa.

A hankali ƙafafun Maryam suka ci gaba da takowa zuwa cikin ɗakin, yayin da idon Eshaan ɗin ke kanta. Dressing mirror ta ƙarasa sannan ta zauna a kan stool ɗin, kuma shi har yanzu yana kallonta.

“Wai me yasa baka cire hular nan ba”

Ta tambaya a sanda take ɗaure sumarta me laushi da ribbon.

Memakon ya amsa mata sai ya tako inda take, yana motsa kunnensa, ya dafa kafaɗarta a sanda ya ƙarasa kusa da ita, sai kuma ya ɗauke hannun nasa daga kafaɗarta ta, ya cire ribbon din da ta saka, ya kama ƙarshen gashin nata ya mata braid (kalaba) guda ɗaya.

Sannan ya saka mata ribbon a ƙarshen gashin, ya ɗaga hannunsa na dama sama, ya dunƙule sannan ya buɗe, wasu ƙanan stars masu sheƙi suka bayyana, ya shiga jera mata su a gaban gashin nata. Style ɗin ya yiwa Maryam kyau sosai, kuma duk abinda yake ta cikin mirror take ganinsa.

Yasan ba kwalliya take ba shi yasa ya ɗauki gyalenta dake kan kafaɗarta ya ɗora mata a kanta.

Da hannu ya mata alama da ta yi kyau, Maryam ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Sannan ta miƙe tsaye ta juyo tana kallonsa.

“Naga wata da wuri zata tsufa”

Sai kawai ta yi dariya, dan tasan me ya gani, wannan silin farin gashin na kanta ya gani.

“Kuma dan mutum yana da furfura sai akace zai tsufa da wuri?”

Ya kai hannunsa ya tallafo fuskarta yana kallon cikin idanuwanta.

“Kinyi kyau Cutie, kamar kullum”

Yanzunma murmushi ta yi tana sunkuyar da kanta, sai kuma ta ɗago da kanta ta dube shi, da alama bazai cire hular kansa ba, sai kawai ta yi tattage, kamar me san kissing ɗinsa ta kai hannunta ta fisge hular sanyin nasa.

Sannan taja baya tana dariya, a lokaci guda tana kallon kan nasa. Eshaan ya kai hannu ya shafa kansa yan murmushi.

Askin da ya saba yi shi aka masa, wato high fade ga kuma razor part daga gefe, da aka aske masa gashin sai ta ga ya sauya, yanayin kyan fuskar tasa ya ƙara fitowa, kammaninsa suka ƙara bayyan.

Sai kuma kunnuwansa da suka ƙara fitowa, dan an aske gashin dake musu rumfa. Bisa ga dukkan alamu su yake b’oyewa.

“Baki ga yanda na koma ba, bani hular pls”

Maryam na ja da baya tana girgiza masa kai a lokaci guda tana masa dariya.

Shima bin nata yake amma taƙi ta tsaya, bata ankara ba ta ji an rabata da ƙasa, an ɗagata sama duka, ta shiga yawo a iska, tana dariya ta kalli Eshaan da ya ɗaga hannayensa a setinta, alamun de shine ya ɗagata.

Kafin kuma a hankali ya sauƙeta ƙasa, kusa da shi, kuma be jira komai ba, ya kai hannunsa na dama ya riƙo waist ɗinta, ɗayan kuma ya tallafo fuskar ta, kafin ya aika Maryam duniyar da ya saba turata a duk sanda zai yi kissing ɗinta.

Ba shiri Maryam ta damƙe hular dake hannunta, yanda ya motsa harahensa cikin bakinta ne yasa ta saki hular, itama bata san sanda ta ɗago hannayenta duka biyu ba, ta ratayasu a wuyansa.

Tana jin kamar komai ya tsaya a duniyar, kamar babu kowa sai su, su biyu kawai, daga ita sai shi.

Ƙwan,ƙwan,ƙwan!

<< Yadda Kaddara Ta So 40Yadda Kaddara Ta So 42 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×