“Sirikata ga laddu”
Cewar Neha, yayin da suke tsaye a garden ɗin gidan, kuma ba su kaɗai ba ne a wajen, kowa na gidan dama baƙin da suka zo suna garden ɗin.
Daadi dama sauran mutanen sai gabatar da ita suke a wurin baƙin, duk wanda ya zo sai an nuna masa matar Eshaan.
A hankali Maryam ta gyaɗa mata kai, sannan ta kai hannu ta ɗauka.
“Ki ƙara mana”
Ta kai hanni zata ƙara Daadi ta ƙwalawa Neha kira, Neha ta amsa tare da damƙawa maryam kwalin laddu ɗin, sannan ta tafi.
Maryam ta zauna a kan wata kujera tana kallon yanda suke ta nishaɗi, suna guje-guje, ga kalolin da suke watsawa junansu.
A hankali ta ƙara kai dunƙulen laddu guda ɗaya bakinta, kalmar kala data ayyana na ƙara maimaita kanta, a cikin ƙwaƙwalwarta.
“Kada ki yarda ki saka shafa kala da yawa a fuskarki, idan ya kama fuskar mutum baya fita da daɗin rai”
Ɗazun bayan an ƙwanƙwasa ƙofar nan, a hankali Eshaan ya janye bakinsa daga cikin nata, ama kuma fuskarsa haɗe take da tata, suna sauƙe numfashi a tare, yana kalon idanuwanta dake a lumshe.
A hankali Maryam ta shiga ƙoƙarin janye hannunta daga bayan wuyansa, amma sai ya kai hannayensa ya riƙe nata, hakan yasa ta buɗe idonta itama.
A lokacin ya faɗamata waɗanan kalaman, ƙofar aka ƙara ƙwaƙwasawa, hakan yasa ya yi pecking kanta, sannan ya juya dan ya buɗe ƙofar, yayin da ita kuma ta yi saurin juyawa. Neha ce ta shigo a taime ɗin, shine suka fito tare.
Murmushi ta yi tana saka wani laddu ɗin a bakinta. Kamar daga sama ta ji muryarsa suna magana da Neha.
“Bhai wallahi Holi ɗinma ni lami nake jinsa, babu kiɗa babu komai”
“Na sani choti (ƙanwata), amma bari kiga”
Ya ƙarashe yana saka hannyensa a baki ya saki fito me ƙarfi, nan take wasu masu kiɗa suka shigo garden ɗin. Neha ta ɗagawa Eshaan hannu shima ya ɗago mata suka tafa.
“Ku sakar mana ganguna!!”
Masu kiɗan suka fara, kowa ya fara rawa, Maryam ta yi dariya tana kallonsu daga inda take.
Allah ɗaya gari banban, da ace a nigeria ne da yanzu ana ta maganganu, amma kalli yandasu suke rawa abunsu, har da Daadi, a cikinsu ta hangi shi Eshaan, shi ma yana taka tasa rawar.
Ta tintsire da dariya tana ci gaba da cin laddu ɗin, hannu ta kai zata ƙara ɗaukar wani ta ji wayam!, a cikin kwalin, hakan yasa ta kalli kwalin, babu ko ɗaya, ta cinye duka.
Ta rufe ƙaramin kwalin tana murmushi, sannan ta ɗago tana kallon inda su Eshaan suke, sai dai kuma babu shi a ciki, sune kawai.
Tasan kurɗakurɗarsa, yanzu haka wani wajen ya yi, sai kawai ta goge hannunta da tissue ɗin da taga a kan table ɗin gabanta, sannan ta ɗauki wayarta ta shiga tiktok.
Yau ta rantse kan sai ta yi posting hoton da suka yi jiya, in yaso matan da suke yawan damunta a comment section kan mijinta, yau su ganshi, kuma ta musu ƙwalele.
Bim!, saƙo ya faɗo wayarta, Daga lambar Sundar, dan haka ta buɗe tana murmushi.
‘Ki fito waje’
Abun ya ɗaure mata kai, waje ?.
‘Waje ina ?’
Ta tambaya.
‘Ƙofar gate’
Sai kawai ta miƙe tana gyara zaman gyalen kanta, sannan ta fita daga garden d’in.
A kusa da babban gate d’in gidan ta hange shi, babu kowa a wajen, dan hatta da masu gadi ma suna cikin garden.
Shima yana hangonta sai ya gyara tsayuwa, sannan ya buɗe hannunsa d’aya, yana mata alama da ta taho, sai kawai ta yi dariya tana ƙara duba farfajiyar wajen, kamar me neman wani abu.
Sai da ta kusa ƙarsa kusa da shi, sannan ta taka da ɗan gudunta ta isa gabansa, ta kuma kama hannunsa da ya mika mata, kanta a ƙasa tanaa murmushi.
“Muje ko?”
Ta ɗan ɗago ta kalleshi, idanunta na haskawa da mamaki.
“Ina zamu je”
“Unguwa”
Ya ƙarashe yana jan hannunta, bata ƙara cewa komai ba, haka suka fita daga gidan.
A ƙafa suke takawa, wani layi suke bi wanda yake a makekeyar unguwar, kuma unguwar tsit! take babu wata hayaniya, saide kana ɗan jiyo hayaniyar mutane a cikin gidajensu.
Sun yi ‘yar doguwar tafiya, kafain suka shiga wani layi.
A ƙofar wani madaidaicin gida taga sun tsaya, akwai securities biyu a ƙofar gidan, kuma bisa ga dukkan alamu sune masu gadin gidan, dan saida suka sara masa sannan suka buɗe musu gate ɗin gidan.
A sanda gate ɗin gidan ya buɗe a gaban Eshaan, sai wajen ya shiga juyawa a idonsa, hoton ya sauya i zuwa wani lokaci can baya, sanda yana ƙarami, lokacin ya dawo daga makaranta ne, bayan school bus ta sauƙe shi.
Ya fito daga cikin motar da gudu, yayin da Roshni ke tsaye a kan balcony ɗin shiga cikin gidan, sanye take cikin chickankari, gashin kanta kwance a bayanta.
Ta yi dariya a sanda ya kira sunanta, sai itama ta taho da gudun tana su kuyawa dai-dai setinsa, yana zuwa kusa da ita ta ɗauke shi tare da cilla shi sama.
“Yeeeeee!, Eshaan”
“I love you Maa”
“ I love you tooooo Eshaan”
Yaci gaba da jin sautin dariyarta a cikin kunnuwansa, a dai-dai lokacin da suka ƙaraso ƙofar shiga cikin falon, shi ne ya tura ƙofar sannan suka shiga.
Komai na cikin gidan irin na da ne, bisa ga dukkan alamu ba’a sauya komai ba, komai yana nan yanda yake, sede a na kula da gidan sosai, kamar akwai mutane a ciki.
“Ina ne nan ?”
“Gidan mu ne, a nan na fara yarinta ta, a nan aka haifeni, ko wani memories ɗina yana nan gidan”
Maryam ta ci gaba da kallon wurin, kafin idonta ya sauƙa a kan wani bango dake cike da hotuna, kuma mafiya yawan hotunan nasa ne.
Eshaan ya ƙarasa jikin bangon da hotunan suke, sannan ya shiga nuna mata hotunansa yana bata labarin sanda aka ɗauke su, wasu kuma ma baisan sanda aka ɗauke su ba, dan yana ƙarami sosai. A cikin hotunan akwai na iyayensa ranar da aka ɗaura musu aure.
Bayan ya gama bata labarin sai ya dawo inda take tsaye, yana kallonta, Maryam bata ankara da sanda ya ɗago hannunsa ba, sai jin sauƙar tafukan hannunsa ta yi a kan kumatun ta, yana shafa mata kala, a hankali ta lunshe idonta, sannan ta buɗe a kansa.
“Happy Holi Piya!”
Ya faɗi a sanda yake shafa mata a ɗayan kumatun nata, sannan ya sauƙe hannunsa yana sunkuya setinta, a hankali ya juyar da fuskar tata bayan ya riƙo hab’arta, sannan ya kai tasa fuskar ya gogi kalar dake fuskarta ta.
Haka ya yi a ɗayan ban garen ma, kafin ya haɗa goshinsa da nata yana lumshe idonsa.
“I love you”
Ya furta maganar haɗi da sauƙe numfashi, wannan yanayin da Maryam ta saba shiga ya ƙara dawo mata, kafin ta yi ƙarfin halin kai hannunta ta riƙe gaban rigarsa, sannan itama ta furta.
“I love you too…”
Kuma tun kafin ta gama faɗi, ya haɗe bakinsa da nata, sannan a hankali ya shiga kissing ɗinta.
*****
HANAM POV.
“Cut!…”
Muryar director ta karaɗe wajen. Kuma bayan bada umarnin nasa masu ɗaukar sauti da masu ɗaukar hoto da kuma masu haska fitulu suka dakata.
Uchenna dake tsaye a tsakiyar fituluvda kuma gaban cameras ya bar wajen, ya tafi zuwa wurin Hanam dake zaune a can gefe kan wasu kujeru. Har ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita ta na kallonsa.
Bottle watter ta miƙa masa, ya karb’a yana mata godiya.
“Aikin da wahala ne?”
“Akwai mana, sai anyi ace be yi ba a sake, gaba ɗaya na gaji”
Sai ta kai hannunta ta ɗan bubbuga kafaɗarsa.
“Idan ka yi haƙuri zaka ga sakamokansa a gaba, yanzu yanda audio ɗin tayi treding ai vedion sai ta fita trending”
Ya aje bottle ɗin yana gyaɗa mata kai, sannan ya kamo hannunta na dama ya yi kissing.
“Inde kina tare da ni babu wani abun da zai tsorata ni, zan dage na yi duk yanda zan yi ganin na yi abinda ya dace”
*Nisa premier hospotal, abuja*
“Mu shiga”
Cewar Uchenna yana duban Hanam da ta tsaya ta a ƙofar ɗakin, ta ɗago ta kalle shi, sannan ta tura ƙofar suka shiga.
Tun jiya ya faɗa mata cewa an kwantar da mahaifinsa a asibiti, ita kuma tace tana so ta zo ta duba shi.
Iko sai Allah, shine abin da ta faɗi, a sanda ta ɗora idonta kan mutumin dake kwance a kan gadon mara lafiya, badan furfurar dake fuskarsa da kuma tsufan da ya yi ba, babu abinda zai hana tace wannan Uchenna ne, babu wani banbanci a kammaninsu, baƙar fatarsa da tsayinsa da komai irin na mahaifinsa ne.
Daga gefen gadon kuma wani matashi ne da ta riga da ta sanshi, dan yana yawan bata labarin sa, Jude ne.
Zama ta yi a kan kujerar da Jude ɗin ya bata, a lokaci guda kuma yana gaisheta, ta amsa masa sannan ta gaida Baban Uchenna, ya amsa mata yana murmushin ƙarfin hali.
“Uche wannan itace matar taka”
“Eh Baba, itace ”
“To Allah ya muku albarka”
“Ameen”.
*****
Mumbai, India”
08:00pm
“To Daadi, sai bayan saduwa”
Cewar Maryam hannunta cikin na Daadi, yayin da suke tsaye a harabar gidan, me motar da zai sauƙesu a railway na jiransu, dan daga mumbai Eshaan ya faɗa mata cewa Ahmedabad(Amdavad) zasu wuce.
Daadi ta janyo Maryam ta rungume ta, sannan ta saketa tana shafa kanta dake sanye da gyalen chickankari ɗin jikinta.
“Allah ya miki albarka jikata”
Maryam ta yi murmushi, sannan ta juya kan Neha, itama ta rungumeta sunawa juna sallama, daga ita sai Anti Saffah, sai kuma Atif, Kawu Irfan ma ya saka mata albarka.
Mota ta shiga tana jin wani abu me kama da kewar mutanen da bata fi sati da su ba na kamata, suna da kirki sosai, basu duba tazarar dake tsakaninta da su ba, santa kawai suke sbd Allah da annabi.
Tana kallon yanda Eshaan ma ke sallama da su, kafin shi ma ya shigo cikin motar, har motarsu ta fita daga gidan su Daadi na ɗaga musu hannu.
Victoria Terminus Rail way suka nufa, dan a nan Eshaan yasai musu ticket, bayan tafiyar ‘ƴan wasu awwani suka sauƙa a garin Ahmedabad wato Amdavad.
Amdabad ba wani babban gari bane, amma kuma garin a cike yake da mutane daga garuruwa da ban-da ban, kuma kamar yanda Tafida ya faɗa mata ne, sbd gasar world cup ɗin da za’ayi ne.
*Acasa mia, New cairo north house, 90 suez Rd, Cairo, Egypt*
A madaidaicin garden d’in gidan, wani ɗan ƙaramin yaro ne a kan encounter vehicle, yayin da ɗayan yaron ke turo shi ta baya, ƙaramin yaron yana sanye cikin farar hooded knitted jacket da ash jeans trouser.
“Khalil ta’al ila hina, al akli sar jahiz”
(Khalil kazo nan, abinci ya kammala).
Kyakyawar balarabiyar matar da ta fito daga cikin gidan ta faɗi, babban yaron ya waigo ya kalleta, sannan ya juya kan yaron dake kan car toy ɗin, ya kama hannunsa sannan ya sauƙeshi daga kan car ɗin.
Yaron ya shiga taku cikin tafiyarsa da bata gama nuna ba, haka ya ja shi har cikin kyakyawan falon gidan.
Kuma suna shiga babban wansu ya yi caraf ya ɗauke ƙaramin yaron yana juya shi sama. Yaron ya shiga dariya cikin gwalantunsa yace.
“Allamil”(Al-amin)
Al’amin ɗin ya haɗe rai.
“Ba Allamil ba, Baabaa zaka ce”
Cikin harshen larabci ya masa maganar, kuma kullum haka suke yi, shi yaron ba zai dene ce masa Allamil ba, shi kuma kullum yana cikin ce masa sede yace Baabaa, wata Baba.
Wani magidanci ne ya fito daga wata ƙofa yana dariya, ƙarasawa kusa da su ya yi ya karb’i yaron a hannun Al-amin yana masa wasa.
“Baabaa, Baabaaba!”
Magidancin ya ƙyalƙyale da dariya.
“Ka ji batu na Gaskiya, yaro nine Baabaan Aryaan ba kai ba, sai ka ɗau haƙuri”
Al-amin ya b’ata rai, wai shi a dole an b’ata masa.
“Wai zaku zo kuci abincin ne kokuwa ?”
Wannan matar ta ɗazu ta ƙara tambaya, a sanda ta fito daga wata ƙofa, wadda taksance ta kitchen.
“Yaro gwara muje muci abincin nan, kafin Ammin ku ta kawo duka”
Gaba ɗayan su suka dariya. Wata matashiyar yarinya ta taso dafa kan sofa tana fad’in.
“Aryaa?, Abuya kawo shi”
Abuya ya miƙa mata Aryaan din, sannan ya yi hanyar danning, gaba ɗaya kowa yazo ya zauna, Ammi ta zuba musu abincin da ta girka, suna ci suna hira yayinda Salwa da kanta take bawa Aryaan din.
*****
Abuja.
HANAM POV.
“Kinga gaskiya wannan yayi duhu, dan wallahi mu baƙaƙe ba zai mana kyau ba”
Hafsi ƙanwar Kamal, wadda take yaya a wajen Hanam ta faɗa, suna zaune ne ita da Hanam, Na’ima, Zainab, Ummu kulsum, Mariya, Rahina, Firdaus, Hafsin kanta, Rafi’a, Nabila, Kamila, fatima da Aisha a babban falon gidansu, yayin da suke zab’ar kalar lace d’in da zasu saka ranar bikin Kamal dan shirye-shiryen bikin suke.
“Anti Hanam wallahi gaskiya yaya ta faɗa, duk gidan nan babu wanda blue color kewa kyau sai ke, tunda kinga mu gaba ɗayan mu baƙaƙe ne”
Cewar Nabila, Hanam ta tura hoton gaba, wani ya shigo a cikin ipad ɗin.
“Wannan fa ?”
Ta tambaya tana nuna musu.
“Yauwwa, ai gwara farin, shine zai hau da kalar jikin mu”
“Kema de Nabila da wani abu kike, yanda kike ta magana a kan baƙin fatar nan taku sai kace wani shuni”
Gaba ɗayansu suka saka dariya.
“Ai maganar gaskiya ce, kaf gidan nan waye me hasken fata ban da ke ?, sai wannan yarinyar da ta shiga shago ta siyo”
Rafi’a ta faɗi tana ɗakawa Mariya duka.
“Rafi’a bana san iskanci, ni na hana wata cikinku shiga shago ?, kuma idan kuna san farin ku shiga mana”
“Allah stirbiƙui inji kishiyar me doro, Allah tsare mu da shafa mai, ke baki san baƙin fatar mutum yafi kyau ba ?, me ake da wani mai”
Rafi’a ta bata amsa.
“Anti Hanam wai ina Aryaan ne ?”
Aisha ta tambaya, Hanam ta yi murmushi.
“Arya yana Cairo, jibi ma zanje na ɗauko shi, dan bana so a yi bikin nan baya nan”
“Ai kuwa gwara ya zo mu ganshi ”
Wayar Hanam ɗin ce ta yi ringing dan haka ta kai hannu ta ɗauka ‘Benidita’.
Har da saurinta ta miƙe ta bar falon sbd hayaniyar da suke, a ƙofar shiga falon ta tsaya, sannan ta ɗaga wayar.
“Ya ya mijin ki?”
Benedita ta tambaya a sanda suke gaisawa, Hanam ta yi murmushi tunowa da shi da ta yi, shine da kansa ya kawota gida, sannan yace mata zai je ya karb’o musu visa ɗinsu.
“Yana lafiya”
“Kira na yi na sanar miki dama, kinsan Gebriel ya mutu….”
Duk da akwai hasken rana a wajen, Amma sai da Hanam taga kamar wata walkiya ce ta haskota daga sama, bakinta a sake kuma yana rawa ta furta.
“A garin ya ya ?”
“Guba suka sha shi da matarsa, wai dan sbd sun haihuwa, yanzu fa shine labarin dake tayawo a new york baki ɗaya”
Hanam ta damƙe ƙarfen balcony, dan ƙoƙarin faɗuwa da take, ba wai tausayinsa take ba, ba kuma haushi ta ji dan ya mutu ba, kawai de zafin rasa rai ne ya dake ta, haka kuma koda ta ruɗi kanta cewa shi ba baban Arya bane ta sani cewa shi ɗin ne baban nasa, amma, ba musulmi banr, bata san wata kalar addu’a zata masa ba. Sai kawai ta kashe wayar, dan wata ƙila hakan ne mafita.