RNo.202,Taj Skyline Hotel, Ahmedabad, India
09:30am
ESHAAN POV.
Zaune yake a kan wata sofa, hannunsa riƙe da littafin Aakhoki Gustakhi, wanda Saree ya rubuta, littafin yake karantawa, yayin da yake jiran fitowar Maryam da ga banɗaki, so yake ta yi sauro ta fito su tafi, dan yau za’ayi final, kuma wasa ne tsakanin India da Australia.
Sannan yana sa ran a gobe zasu wuce Delhi, dan jibi ne ɗaurin auren Mahesh abokinsu.
Tunaninsa ya katse tare da karatun da yake, a sanda Maryam ta fito daga banɗakin sanye cikin chickankari, rigar orange color ce, kuma ta sauƙo mata har kan guwa, yayinda wandon ya kasance fari, kuma wandon yana da faɗi, ta yafa farin mayafin kayan a kanta, ta rataya shi zuwa bayan kafaɗarta.
Ƙafarta sanye cikin fararen boots, kamar kullum fuskarta babu kwalliya, amma shi a hakan da take tafi masa kyau, dan yafi san ya ganta a yanda take, haka ɗin nan nata, dan hausawa sunce wai dai-dai ɗin wani, karkattaccen wani. Litafin ya rufe tare da aje shi a kan coffe table, ya miƙe yana shafa sumarsa.
“Kin shirya?”
A hankali ta gyaɗa masa kai.
Narendra Modi stadium, Ahmedabad, India
12:00pm
Hayaniyar masoya da kuma magoya bayace ke tashi, sai kuma masu bayyana yanda wasan ke kasancewa, gaba ɗaya stadium din cike take maƙil da mutane, daga tsakiyar fili kuma ƴan wasan india da na australia ne ke fafatawa, dan yanzu haka ana zagayen ƙarashe ne.
Daga cikin kujerun ƴan kallo, akwai ta Eshaan da Maryam, wanɗan da suka zuba ido suna so suga yanda wasan zai kaya, a farkon fara zuwansu wajen babu abunda Maryam take ganewa a wasan.
Amma a hankali a hankali ta fahimci kan wasan, kuma kamar Eshaan itama tana fatan ace india ce ta lashe wasan, dan yanda ta ga indiyawa nasan wasan cricket idan suka fad’i wata ƙila Ahmadabad ta kama da wuta.
Wajen ya yi wani irin shiruu, kamar mutuwa ta ratsa, kamar da ba wajen ne ake ta hayaniya ba, sun yi shirun ne saka makon Rohit Sharma babban ɗan wasa india, da ya riƙe bat a hannunsa ya ɗau matsayarsa yana jiran Jones ɗan wasan austrelia ya cillo ƙwallo.
Jones ya ɗan ja da baya kaɗan, kafin ya tako a guje, kuma yana zuwa tsakiyar filin ya cilla ƙwallon, wani irin duka da Roshi Sharma yayiwa ƙwallon saida ta fita daga ginin stadium ɗin.
Kamar magoya bayan india jura suke, sai suka saka ihu, ana tafi ana fito, india taci wasa, bakin Eshaan kamar ya rabe biyu dan tsabar murna, Maryam ma ta taya su murna sosai. Da a wajen su abun farin ciki ne sosai, dan indiawa na martaba wasan cricket.
*****
Cairo Internacional airport
05:40pm
HARNAM(Harees and Hanma) POV.
A tare suka fito daga cikin terminal, yayin da Haris ke riƙe da jakukunansu, gaba ɗaya hanam ta ƙagu taje taga Arya, so take taga yanda ya sauya, dan tana da tabbacin ya sauya sosai.
Haris ne ya tsare muasu taxi, sannan suka shiga, kai tsaye Acasa Mia suka nufa.
Ta ta haddace address ɗin gidan, dan haka taxi na sauke su ita ta fara shiga gidan.
“Aryaan?!”
Shine abinda ta fara faɗi, a sanda idanuwanta suka gane mata shi suna wasa shi da Al-amin,Salwa da Khalil a garden ɗin gaban gidan.
Da gudu ta yi inda suke ta sure shi tana rungume shi, kafin ta dago shi daga jikinta tana kissing face ɗinsa, ta yi kewarsa sosai, fiye da yanda baki zai iya furtawa.
Jikinsa tabi da kallo tana ganin yanda ya sauya, bakinsa taf cike da haƙwara, girma ya ƙara bayyana a tare da shi.
“Arya Ammi ta yi kewarka”
“Ammi ?”
Cikin gwarancinsa ya furta hakan, Hanam ta yi dariya tana sake rungume shi.
“Eh Ammi, Amminka ta yi kewarka”
“Papi ma ya yi kewarka”
Ta juya ta kalli Uchenna dake bayansu, hannu ya kai ya karb’i Arya daga hannunta yana rungume shi shima, sai a sannan ta dawo kan ƴan ƙanenta data ga a wajen, ɗaya bayan ɗaya tabi ta rungume su suna gaisawa da ita.
09:30pm
“Ba ni ɗayan”
Muryar Masarrat ta faɗi, a sanda suke tsaye a kitchen ita da Hanam. Hanam ta ɗauko plate cike da cabbege ta miƙa mata.
Saida Masarrata ta juye cabbege ɗin, sannan ta rufe pot ɗin, ta jiyo ta kalli Hanma.
“Ana biddi ahki ma’ak bi maudu’u daruri”
(Ina so nayi magana da ke akan wani abu me muhimanci).
Hanam bata ce komai ba sai ci gaha da kallonta da ta yi alamu ina ji.
“Waye mahifin Arya ?, dan inada tabbacin cewa Harees ba shine mahaifinsa ba”
Bisa ga manakinta sai taga Hanam ɗin na murmushi. Dama sai da ta ayyana hakan a ranta, tasan cewa dole zata tambaya.
Sai kawai ta ɗago da hannayenta ta sunkiyar da kanta tana kallonsu, yayin da ta haɗesu waje guda tana wasa da su.
“A sanda naje New york wani aiki, na haɗu da wani, kuma shine yayimin fyaɗe, har na samu cikin Arya”
Kalaman basu da yawa, amma kuma sun yiwa Masarrat nauyi a ka, gani take kamar ko wani ƙunci da ya faru a rayuwar Hanam itace sila, kamar duk wata damuwa da Hanam ɗin ta shiga duk ita ta ja. Nan da nan ta fara hawaye, Hanam ta ƙarasa kusa da ita sannan ta rungumeta tana shafa bayanta.
“A’a Ammi, ba kuka za ki yi ba, komai ya wuce yanzu, dan Allah ki dena saka damuwa a ranki”
Kafin ta saketa, Masarrat ta kai hannu ta share hawayenta, sannan ta dafa kafaɗar ta.
“Allah ya miki albarka, muje muci abinci, zuwa gobe zaki zaga dangi”
Hanam na murmushi ta ɗauki wani bowl ta fita, a falo ta same su duka suna hira.
“Yauwwa abinci yakammala, wallahi yunwa muke ji, ya yi kyau yarinyata, Allah ya miki Albarka ”
Dr. Taiyyab Abu Al-aminya faɗi, Hanam ta yi dariya, dan mutumin yana da kirki, kamar Abbanta, Abbanta ?, a ranta ta yi masa addu’a kamar yanda ta saba a duk sanda zai shigo cikin tunaninta.
A hankali ta juya ta kallesu su duka, Abuya kamar yanda ta ji su Al-amin na faɗa masa, Harees, Arya, Al-amin, Salwa da Khalil dukan ninsu suna cikin farin ciki.
A da ita kaɗai take rayuwa, daga ita sai Abba, bayan Abba sai Arya ya zo, daga shi kuma sai ga Harees, wanda zuwansa ya zama sanadiyyar shiryawarta da mahaifiyarta, bayan kuma ta shirya da mahaifiyar tata sai ta samu ƙanne harda mahaifi.
A cikin ranta ta godewa Allah, a sanda ta tuna abinda Abba yake faɗa mata a kullum.
“Bayan wuya sai daɗi Bannute”
Haƙiƙa baka ne, bayan wuya sai daɗi, dan a yanzu tajita a matsayin cikakkiyar ƴar adam, ta samu komai, babu abinda take nema, kewar Abba kaɗai ta dame ta.
*****
No.803, Tolstoy Rd, New Delhi, India
05:00pm
MARYAM POV.
Zaune take daga kan wata sofa, ta yi tagumi tana bin ƴan matan wajen da kallo ɗaya bayan ɗaya, yaren hindi suke wanda ita sam bata fahimta, ko magana za ta yi da su saide ta musu da turanci, su kuma su amsa mata da turancin nan nasu dake bata dariya.
Tun safe take tare da ƴan matan, waɗanda suka kasance ƙawayen amarya Komal, kamar yanda Eshaan ya faɗa mata sunanta.
Dan jiya suka sauƙa a delhi, kuma ya faɗa mata cewa yau za’a ɗaura auren abokin nasa, shi yasa suka taho tun safe, ya danƙata a hannun amaryar shi kuma tun bayan nan bata ƙara ganinsa ba.
Sai biryanin da ya aiko mata dan yasan ita ba komai take iya ci ba, sai laddu ɗin da sukai ta bata. Hayaniyar ƙawayen amaryar ta cika mata kunne, dan yanzu haka amarya suke shiryawa.
Sai kawai ta ɗauki wayarta ta buɗe ta shiga message, kusan jarin mesages uku tana turawa Eshaan amma ba ya replying.
Dan haka kawai sai ta fito daga wajen ta aika masa kira, amma de kamar ɗazu bai ɗaga ba.
“Mts, ina ya shiga ne?”
Babu me amsa mata dan haka kawai sai ta meda wayar cikin jakarta ta ci gaba da kallon ƴan matan, kyawawa wanda babu ɗaya da zaka iya cillarwa a cikinsu, domin babu baya a cikin.
“Wow…, a ina kika si yi wannan saree ɗin”
Maryam ta juyo ta kalli budurwar, sannan kuma ta kalli jikinta, nan take tunanin ta ya dawo mata da abinda ya faru a ɗazu.
Tana zaune a bakin gado tana cin abinci, Eshaan ya shigo ɗakin hotel ɗin da suka sauƙa, hannunsa riƙe da wani kwali, yacemata saree ne a ciki, kuma nata ne, so yake ta saka.
Ta faɗa masa cewar ita fa bata iya ɗaura saree ba, shi kuma yace taje ta saka blouse da skirt ɗin tazo sai ya ɗaura mata.Yanda aka ɗaura saree ɗin nema bata san tunawa, dan yau d’an guntun hankalin da take ji Tafida ya bar mata shi seda ya zube, notukan kanta suka karasa kuncewa.
“Kin gane saree ɗin Krishan?, shine fa wannan wanda na taya a Metropolitan Mall, amma na fasa sbd tsadar da ya min”
Maryam ta kuma kallon ƴan matan, sannan ta ƙara kallon saree ɗin, jar kala ne, an masa ado da wasu golden stones, kuma yadin sa silk ne, hakan ke ƙara nuna mata tsadarsa, duk da ba wani sanin kan saree d’in tayi ba.
“Ba ni na siya ba, mijina ne ya siyo min”
“Aiko mijiniki yana sanki, saree ɗin ki kud’insa ɗaya da na amarya”
Maryam ta kalli sareen da ke jikin amaryar sannan ra kalli nata, kusan kallarau ɗaya ma, dan hatta da kalar blouse d’in iri ɗaya ce, kawai de yanda aka jera stones d’in jiki ne ya banbanta.
“Kai ga tawagar ango sun iso…”
wata matashiyar budurwa da Maryam ta ji suna kira da Rakshi ta faɗi baki washe.
Ƙawayen amarya suka shiga gyarta, dan dama jama’a sun jima da fara taruwa, ita Maryam ba wannan ne ha dameta ba, duk da tasan cewa ba al-adarsu ɗaya ba, dole de ango idan zai zo wajen ya taho da abokansa, kenanan Eshaan na tare da su?.
Ba ta yi tunanin komai ba ta miƙe, ta ɗauki wayarta da wani golden mayafi ta yafa a kanta, dan bazata iya yawo kanta a buɗe ba haka.
Ta cikin tarin firmitsin jama’ar da suka taru a gidan tabi har zuwa bakin ƙofa inda take jiyowa kiɗe-kiɗe.
Waje ta ja ta tsaya tana kallon ikon Allah, ango da abokansa dama ‘yan uwansa sun iso gidan, sai tiƙar rawa ake ana watsa kuɗi. Ga masu kiɗa suna aikinsu.
Cikin abokan ango ta hango Eshaan,sai daj shi ba rawar yake ba, tafi kawai yake yana fito.
Cikin tarin jama’ar wajen ya hangota a gefe, ba zai ce yasan daliliba, amma se yaga babu kowa a wajen, duk wannan hayaniyar da ke tashi a wajen babu ita.
Babu kowa sai itan da yake gani, sanye cikin red silk saree, me ratsin golden, wuyanta hannayenta da kanta dauke da jawellies, babu wata kwalliya da yawa a fuskarta. Amma kuma ta yi kyau, domin ta yafa wani golden ɗin viel a kanta.
A hankali ƙafafuwansa suka shiga takawa setin inda take, kallonsa take yayin da shima yake kallonta.
“Ina ka shiga Sundar ?” Muryar Maryan ta tambaya da ɗan ƙarfi ta cikin kiɗa da hayaniyar da ke tashi a wurin.
Eshaan ya lumshe ido sannan ya buɗe yana ci gaba da kallonta.
“Kinyi kyau Wifey”
Sai ya faɗi hakan me makon ya amsa mata tambayar da ta masa.
Me ?, ɗazuma fa sai da ya faɗamata hakan, me yasa yanzu ze sake ?.
“Mu shiga ciki, za’a fara gudanar da ɗaurun auren ”
Muryar sa ta faɗi, ta cikin hayaniya da kiɗan dake tashi a wajen, hannunta ya kama ya shiga janta har zuwa cikin farajiyar gidan inda za’a gudanar da ɗaurin auren.
A kijerun gaba suka zauna, har yanzu idonsa a kanta ya kasa janyesu, hannunsa ya kai ya gyara nata zaman veil ɗin.
A lokacin kuma ango da ƴan uwansa suka ƙaraso wajen, har yaje ya zauna a wajen da aka tana da domin shi, Suwami ya shiga jero addu’o’i.
Kafin aka kawo amarya, itama ta zauna a kusa da ango, aka ci gaba da yin addu’o’i, sannan aka bawa ango red Tikka (wannan jan garin da matan auren ƴan addinin hindu ke sakawa a tsakiyar gashinsu, alamun suna da aure).
Ango Mahesh ya sakawa Amarya Komal tikka a tsakiyar gashinta daga gaba, sannna aka maƙo mangalsutra, (sarƙar aure). Ango ya sakawa amarya, sannan suka miƙe, mahaifin amarya ya zo ya ɗaure mayafin amarya dana kafaɗar ango, sannan suka shiga zagaya wuta.
A lokacin kuma aka shiga rabawa jama’a fure suna watsawa amarya da ango, yayina da shima Swami ya miƙe yana karanto addu’ar aure.
“Mangalan fagbani bishnu mangalan madradda shar, mangalin gundari fakshar mangala yatarobari……” Har zuwa ƙarshe.
Eshaan da Maryam suka miƙe a sanda suma aka miƙa musu fure suka shiga watsawa amarya da ango.
Maryam na watsa kamar kowa sai ji ta yi ita kuma ana watso mata, ta juya ta kalli Eshaan, yayin da kowa ke watsawa amarya da ango shi kuma ita yake watsawa.
Ta saba ganin irin wannan auren a Tv, yau gashi a gaban idonta tana ganin yanda ake ɗaura shi.
*****
ESHAM
R 78, TC Maurya Hotel, New Delhi, India
11:15pm
“Dama Mahesh ba musulmi ba ne?”
Muryar Maryam ta tambaya, yayin da take shirya kayan sakarwarsu a cikin jaka.
Eshaan da ke zaune a kan gado yana danna system ya juyo ya kalleta.
“Eh, ɗan addinin hindu ne, ai ina jin kaf abokamu daga ni sai Arjit ne musulmai”
Ta gyaɗa kanta tana zipping ɗin jakar, sannan ta ajeta a ƙasa kusa da wardrobe.
Ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala, ta fito ta saka hijabinta, sannan ta kwanta a,kan gadon, tana kallon Eshaan dake gefen gadon har yanzu yana danna system.
“Yanzu gobe gida zamu koma ?”
Sai ta ga ya dakata da danna systen ɗin, kafin ya juyo yana kallonta ta cikin ɗan guntun hasken da ya rage a ɗakin.
“Indian ta isheki ne ?”
Sai ta gyara kwanciyarta tana girgiza masa kai.
“Naga mun gama komai ne, to me zamu jira ?, ko akwai inda zamu sake tafiya ?”
Sai ya girgiza kansa yana rufe laptop ɗin, sannan ya ajeta a kan bedside drawer.
Ya kwanta yana jan bargon, kansa na kallon sama yace.
“Mun gama zuwa ko ina, kawai de ina ga ya kamata a ce mun ɗan yi yawo a delhi”
Ya ƙarashe ya na juyowa ya kalleta, itama shi take kallo.
“Ina zamu je to?….”
Ta tambaya a sanda yake kashe sauran fitulun da suka rage a ɗakin, Maryam ta rintse idonta tana ƙanƙanme pillown da take kwance a kai, har yanzu bata dena tsoron duhu ba, kullum zai kashe wuta sai ta tsorata.
Hannunsa ta ji yana lalubar nata, kafin ya haɗe tazarar dake tsakaninsu ya janyota jikisa, kanta ya sauƙa a kan kafaɗarsa, hannayensa biyu duka suka kewaye waist ɗinta.
Maryam ta ƙara duƙunƙunewa a cikin jikinsa, a hankali ya lalubo kunnenta sannan yace.
“Akwai wurare da yawa da zamu iya zuwa a Delhi, Qutub Minar, India gate, safdarjung tomb, Humayun’s tomb, lodhi art district suna da yawa sosai, ina so ki yi yawo sosai a india”
Maryam ta ƙara matse jikinta dake cikin nasa, har wa yau ta kasa sabawa da wannan yanayin.
“Yanzu de ki kwanta ki huta, dan a gobe zamuje mu zaga gari, kuma a goben jirgin mu zai koma nigeria, kinsan idan mun koma lagos kwana biyu za mu yi mu tafi haɗejia”.
*****