Chida Event Center, Jabi, Abuja, Nigeria
07:40pm
HANAM POV.
Babban ɗakin taron a cike yake maƙil da jama maza da mata, daga can wajen zaman amaryam da ango kuwa Kamal Muhammd Hakuɗau ne da amaryarsa Kalisa Usman.
Daga b’angaren zaman dangin ango kuma gaba ɗaya ƴan uwansa ne maza da mata sai hira ake ana cin abinci, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci cewa suna cikin tsantsar farin ciki.
A cikin su kuma akwai Hanma. Wanda itama ke sanye cikin irin nasu kayan, kuma harda ita ake hirar.
“Ya Hanam wai ki zo inji Ya Harees!”
Nabila ta faɗa mata da ɗan ƙarfi, kasan cewar hayaniya da kiɗan dake tashi a wajen. Ta juya ta kalleta sannan ta miƙe tsaye.
“Hanam wai Ina Aryaan ne ?”
Ta juyo ta kalli Hafsi, sannan kuma ta shiga hange-hange ko zata hango shi, ita rabonta da shi tun da safe. Allah ya temaketa ta hango shi zaune a kan wani table.
Ƙanenta maza ne gaba ɗaya a kan table ɗin, hatta kayan da ke jikinsa ma irin na su ne. Ta nuna wajen da hannunta.
“Gashi can a wajen su Hafiz”
“Bari naje na karb’o shi, ai basu kaɗai suke san sa ba”
Hanam ta yi dariya tana tafiya, sai kuma ta tsaya ta juyo ta dawo wajen tana faɗin.
“Nabila yana ina ?”
“Ni dai a waje na ganshi, ki duba cikin motarsa”
Sai ta gyaɗa kanta, sannan ta fita daga wajen da ƙyar sbd tarin mutanen dake wurin.
A parking lot taga motarsa dan haka ta je ta buɗe zata shiga gaba, amma sai taga baya gaban, yana baya, ta rufe ƙofar gaban ta buɗe ta bayan sannan ta shiga. Kuma tana shiga ya janyota jikinsa ya rungume.
“Wai bakwa tausayi na ne?, kun barni daga ke har Arya ”
Hanam ta saƙala hannayenta ta wuyasa a sanda ya saketa.
“Kamar baka ci abinci ba ma”
Sai ya gyaɗamata kai.
“Tun safe banci komai ba, kinsan mu ne abokan ango, duk gwagwarmayar da akayi da mu akayi ta”
“Awwww, Alah sarki rex (king), sannu”
Ya kai hannunsa yana janyo wata leda dake gidan gaba na motar, ya aje mata ledar a kan cinyarta bayan ya ɗauko.
“Ga abincin nan, a bani na ci”
Ta ɗanyi dariya tana buɗe kayan dake cikin ledar. Sannan a lokaci guda ta ɗago ta kalleshi cikin hasken futulun waje dake shigowa cikin motar, farar shaddace sanye a jikinsa, kansa harda hula, kuma ta ga kayan da ke jikinsa irinsa ne a jikin ango, dan yanzu sun ɗiki, aminta suke shi da Kamal kamar waɗan da suka ta so tun yarinta.
“Ni fa na yi tunanin Mama zata zo”
Uchenna ya jingina da jikin kijerar motar yana cire hular kansa, sannan ya shafa kansa.
“Wai Zakiyya ce za ta yi graduate, shi yasa bazata zo ba”
Hanam ta buɗe wata roba tana saka spoon a ciki.
“Ai mu ma kuwa ya kamata a ce munje, ka je wurin Baba yau ?”
Ta kai masa lomar farko tana masa tambayar, ya haɗiye abicin da ya gama taunawa sannan yace.
“Da safe kawai naje, amma ban koma ba, wata ƙila kafin mu koma gida sai muje”
“Kaida wa ?”
“Ni da ke”
Ya amsa mata yana karb’ar abincin da take ba shi.
“A’a ni yau bazan kwana a gida ba”
“Da izinin wa ?”
Sai kuma ta yi shiru, dan ya kamata a ce shi sai da ta tambaye shi tukunna.
“A ina za ki kwana ?”
“A gida, su Ya Kamila ma duka a can zasu kwana”
“Shikenan tun da kina so bazance a’a ba, sai yaushe kenan?”
Spoon ɗin hannunta ta aje a cikin robar abincin sannan ta riƙe fuskarsa da duka hannunta biyu, ta yi pecking fuskarsa.
“Thank you mi rex (my king)”
Hannunsa ya kai ya kamo waist ɗinta ta baya, sannan ya shiga kissing ɗinta, da ƙyar ta samu ta ja baya da shi.
“Ka ci abincin”
Ta faɗi kanta a ƙasa, sai ya yi murmushi yana karb’ar abincin.
“Ina Arya ?”
“Yana wurin su Hafiz”
“Kwaliyarki ta yi kyau, me yasa kika dena kwalliya yanzu?, ba ki ga yanda ta miki kyau ba”
“Sanda na kusa zama uwa na dena, kuma har bayan da na zama uwar ma ban ci gaba ba”
Hannunta ya kama, sannan ya ƙara matsota cikin jikinsa sosai.
“Yanzu kuma kin zama mata, mijinki yana so, dan Allah dan shi ki riƙa yi”
A hankali kamar me raɗa ya furta hakan, yana yi yana shafa gefen fuskarta da ta ɗau heavy make-up.
Kafin ya kuma kissing ɗinta kaɗan, ya ɗan ja baya yana haɗe fuskarsa da tata, suka shiga musayar numfashi.
“I love you Rex”
Ya ɗan ja baya da fuskarsa kaɗan,sannan ya yi pecking gefen fuskarta.
“I love you too”.
*****
House No.122, B3, Alaro city lekki, Lagos
09:56pm
MARYAM POV.
A hankali ta fitar da gaba ɗaya kayan da ta siyo na gujirin da zata kaiwa ƴan gidansu, jiya suka dawo daga India, kuma basu bar delhi ba sai da ya kaita duk inda ya lisaafa mata harma da inda be faɗi ba, kuma har kasuwa suka shiga, a nan taga takalma da ɗankunnaye ta tsaya ta si yi wanda zata kawowa ƴan uwanta, tun da yace gobe zasu wuce Haɗejia.
Jiya ta tambaye shi me yasa zasu je haɗejia.
“Kinga hutun dana ɗauka da saura be ƙare ba, kuma idan hutun nan ya ƙare bana jin za’a ƙara barina na ɗauki wani hutun kwana kusa, kuma kema kinga hutun ki da saura, kafin ya ƙare se muje mu dawo”.
Idan aka bincika zuciyarta cike take fal da farin ciki a sanda ya bata wannan amsar. Bayan wasu watanni zata je ta haɗu da Maanmu, Hussain, Hassan da auta.
A cikin jakar da za ta yi tafiyar ta saka kayan, sannan ta ɗauki hijabinta ta saka ta fito ƙasa.
Tafida baya gidan, dan ya faɗa mata cewar zai je asibiti ya dawo, kitchen ta shiga dan ta sama masa abinda zai ci, dan ita bata jin yunwa, taci abincin da Maman Ilham ta aiko mata, duk da babu wasu kayan girki a gidan, dole ne bayan sun dawo da ga haɗejia su yi siyyaya.
TAFIDA POV.
Da sallama a bakinsa ya shigo parlon, amma be samu kowa ba kuma dama yasan cewa ba zata wuci kitchen ba, dan haka kai tsaye ya wuce kitchen ɗin.
Har ya buɗe ƙofar bata san ya shigo ba, sai ji ta yi anyi hugging ɗinta ta baya.
wata iriyar iska ta shaƙa, wadda ta taho mata da ƙamshinsa, a hankali ta ɗora hannunta a kan nasa, a sanda shi kuma yake saka kansa a cikin wuyanta.
Ba shiri ta yi saurin juyowa a cikin hannayensa ta riƙo gaban rigarsa, hannayenta da ke b’ace da fulawa suka b’ata gaban rigar, sai kuma ta janye hannun nata ganin ta b’ata masa jiki.
Sai ta ga yana dariya, hannayen nata biyu ya kamo ya ƙara meda su kan kirjinsa, sannan ya kara fuskarsa a tata.
“Borrow me a kiss Miriam”
Maryam ta zaro ido tana jan fuskarta baya, amma sai ya saka hannayensa yana dawowa da ita.
“To ba bashi, kiss me then”
Zaburar da ta yi yanzu tafi ta ɗazu. Kansa ya gyaɗa mata.
“Kiss me pls, i like your soft lips”
Roƙon da yake mata yasa bazata iya musawa ba, dan haka sai ta ɗago da hannayen ta ta kama fuskarsa har tana bata masa ita da garin fulawar dake hannun nata, ta ɗan yi kissing saman lips ɗin nasa kaɗan, sannan ta sake shi tana ja baya.
”Me ki ka yi wannan ?, wannnan ai ba kiss ba ne Miriam, bari na koy…”
A guje ta zare ta fice da ga kitchen ɗin, Tafida na dariya ya juyo ya kalli fulawar da take kwabawa, be san me zata ta yi da ita ba, amma sai ransa ya ba shi kamar ɗan ƙwantalaka za ta yi, dan ga manja da yaji nan ta aje.
Da ƙarfinsa ya yi amfani ya yi girkin da kansa, bayan ya gama ya zuba mata a warmer, sannan ya zauna yaci nasa.
Har kusan sha ɗaya bai ganta ba, hakan ke nuna masa cewar wata ƙila ta yi bacci, shi kuma ta barshi gadin gida.
miƙewa ya yi da ga kan kujerar da yake, ya kashe duka wutar gidan, sannan ya koma ɗakinsa ya yi wanka ya saka kayan baccin sa ya kwanta.
Sai yaji baccin ya gagare shi, dan a kwanakin nan ya saba sai da ita yake bacci, ko jiyama da ya iya yin bacci shi ɗaya gajiya ce a jikinsa.
A zaune ya miƙe, sannan ya sab’a slide sandals ɗinsa, ya fita ta balcony ɗin ɗakinsa ya yi wani irin talle da ba duka ɗan adam ze iya ba, ya dira a balconyn ɗakinta.
Kamar yanda ta saba yau ma bata kashe wutar ɗakin ba, a kan gado ya ganta ta duƙunƙuna cikin bargo.
Kamar yanda shima ya kasa baccin haka itama ta kasa, ita ko jiyan ma ba ta iya yin baccin ba. Jin gadon yana motsi yasa ta yi saurin juyawa, aiko ta yi kyakyawan gani, dan tana juyawa Tafida ya janyota jikinsa ya ƙanƙame kamar me shirin medata ciki.
“Me yasa za ki tafi ki barni”
Ya faɗi yana ƙara ƙanƙameta, Maryam ma ta saka hannayenta biyu tana rike shi.
hannunsa ya ɗaga setin switch ɗin ɗakin ya motsa, wutar ta mutu, yau ɗinma sai da ta razana, amma kuma Tafida ya riƙeta da kyau, yana shafa kanta har sai da ta yi bacci.
Shi kuma se ya kasa baccin, kawai ya saka ta a gaba yana kallo, duk da babu wani wadataccen haske a ɗakin.
jinta a jikinsa da kuma kallonta da yake irin haka yafiye masa baccin.
*****
Kano Road, Hadejia Emirates
05:20pm
Wata kyakyawar mota ce fara sol take tafiya a nutse. Daga cikin motar kuma Tafida ne da Maryam zaune.
Jiya suka sauƙa a gidan baban Neha dake abuja, kuma a can suka kwana, a jiyan Maryam ta gano dalilin da yasa Neha da Eshaan suke kama, dan baban Neha ɗin kamarsa ɗaya da Tafidan.
Bayan gari ya waye suka yi shirin tafiya, kuma Baban Neha ɗin wanda Maryam ta ji Tafida na kira da Appa shi ya basu motarsa, har gidan Neha ɗin ma sunje, wani gida Me kama da fada inji Maryam.
Dan gidan ba ƙarami ba ne, sbd ba su kaɗai ke rayuwa a ciki ba, akwai ƴan uwan mijinta a gidan.
Duk da ta gaji amma waƙoƙin motar sunfi gajiyar mata da kunne, dan haka ta shiga daddana botton ɗin sauyawa.
Kuzo gidan Ahmen ku gani
Na Garba me nasara a Ruwa
Maryam ta tintsire da dariya a sanda waƙar ta shiga playing, ita irin wannanƙoƙin a wurin Maanmu ko kakarsu Jaruwa ta saba jinsu, ashe shima yana jin irin su. Ta jiyo ta kalleshi a sanda ta ji yana rera waƙar shima, harda wani turo hula gaban goshi.
Mutum da ganin motar A ruwa…
Tilas yaka ba giwa hanya, yasan akwai manya a ciki
Na Garba me nasara A Ruwa, Kuzo gidan Ahamen mugani
Maryam kam me za ta yi in ba dariya ba, Tafida ya juyo ya kalleta.
“Cikkaken ɗan gargajiya ake faɗa miki”
Tana girgiza kai ta kai hannu ta sauya waƙar.
Gadar gayan Mamman ɗan sha’aibu
Gadar Gayan Mamman ɗan sha’aibu
Mota ki dakata ki aje ni a birnin gadar Gayan…
Direba dan dakata kaɗan zan sauƙa a birnin gadar gayan…
Yanzun ma dariya ta yi tana kallonsa, yanda ya dage bilhaƙƙi da gaskiya ya na bin waƙar.Ta sauwa waƙar wata ta shigo.
Khadal yen khabiye, ni yen arugul ban dale
Fasi faga bai maride, ani bani yallem madu fogum
“Wato har waƙoƙin Telugu kake saurare?, dan na san wannan ba hindi ba ne,yafi kama da Telugu”
Se ya tura hular kansa baya kaɗan, yana gyaɗa mata kai.
“Ai ina jin Talugu ɗin ma, sanda muna makaranta akwai wani abokin mu Srinivas, ɗan talugu ne, kuma Mahesh ma yana jin Telugu, dan Babarsa ‘yar telugu ce”
Ta gyaɗa kanta tana sauya waƙar dan ita har yanzu bata samo wadda take nema ba.
“Yare nawa ka ke ji a India”
Ya ɗan ɗaga kansa sama kaɗan yana tunowa, can kuma sai ya sauƙe.
“Mts, ina jin kamar biyar ne, Kinga inajin Hindi, Talugu, tamil, urdu sai bengali”
Maryam ta gyaɗa kai tana sauya wata waƙar.
Wataran wata rana, za’a kaiki gidana
Matsayin matata, kece madarata…
Na matsu, na matsu, na matsu naga wannan rana,na matsu…
Allah kaimu, Allah kaimu, Allah kaimu ranar nan…
Maryam ta kuma sauyawa.
You hit my heart, oh, hit it like a heart attack…
We talking all the time like insomniac…
“Mts!”
Eshaan ya juyo ya kalleta.
“Me ya faru ?”
“Ni ban samu waƙar da nake so ba”
Sai ya yi murmushi.
“Mun shigo gari ai”
Maryam ta kalli inda suke, bakinta ya buɗe cikin dariya, ta yi missing gida, ta yi bala’in kewar komai na haɗejia.
Farin cikinta be ƙara ninkuwa ba sai sanda taga sun wuce ƙofar fada sun nufi Garko. A ƙofar lungunsu ya yi parkinga.
Se da Maryam ta riga shi fita daga motar, bakinta fal murna, ta tsaya a wajen tana ta bin unguwar tasu da kallo.
A sannan Tafida ya zagayo inda take tsaye bayan ya fito mata da jakarta dake booth. Matasan dake zaune a kan bencina suna ganinsa suka ta so suka rufe shi suna ta miƙo gaisuwa.
Tafida be iya shariya ga matasa ba, seda ya tsaya suka gaisa har ya musu ihsani, sannan suka barshi ya tafi, Maryam kam har ta yi gaba, saida ya haɗa da sauri sannan ya cin mata.
A ƙofar gida taga auta da abokasa suna wasa, tamanta da wani Tafida dake binta a baya ta ruga da gudu inda suke tana faɗin.
“Auta!”
Shima jin Muryar yayar tasa yasa ya miƙe da sauri, yana ganinta ya ruga inda take shima yana dariya, suna haɗewa suka rungume juna, Maryam ta ɗaga shi masa tana juyi da shi, tuni batun zuwan Maryam ya karaɗe unguwa.
Maƙota da ƴan mata duka aka loƙo ana ganin Maryam da Tafida.
Sai da Maryam da auta suka gama yarintar tasu sannan ta ja hannunsa suka shiga cikin gidan.
“Maanmu wata sabuwar Ps5 ce ta fito…”
Hussain be ko ƙarashe ba, Maanmu da wata mata dake zaune a kan tabarma suka saka dariya, harda Hassan da ya fito daga banɗaki.
Ya kalli kwanon dambun da ke gabansa sannan ya kallesu.
“Ni fa ba santi nake ba, labarine kawai nake san baku”
Matar da ke zaune kusa da Maanmu tace.
“Babu wanda yace kana santi ai, kawai de labarin naka ne abun dariya ”
Sai kawai shima ya yi dariya yana kai loma.
“Wato anti Hanne ai a gidan nan babu girkin da za kuyi ya saka ni santi, Yaya ce kawai take yin girkin da ke sakani santi”
Kamar daga sama suka ji sallamar Maryan da Muhsin.
Gaba ɗayansu suka sakawa bakin ƙofar ido, ko amsa sallamar an rasa wanda ze yi.
Ita ɗince kuwa ta shigo, sede wannan Maryam ɗin tana da banbanci da waccan, wannan Maryam ɗin tana da jiki, kuma tafi waccan fari, amma maganar da ta yi yasa suka fahimci cewa ita ɗin ce.
“Wai baku ji muna sallama ba ne ?”
Ta ƙarashe tana zama kusa da Maanmu tare da rungumeta, Anti Hanne ta miƙe tsaye tana faɗin.
“Ko wannan itace Yayan?”
Ihun da su Hussain suka saka shi ya tabbatar mata da maganarta. Gaba d’aya suka zauna a gaban Maanmu suna ta yi Maryam sannu da zuwa.
“Kuma ina Yaya ?”
Maryam ta kalli Hussain, tana so ta tuno waye Yaya, nan take ƙwaƙwalwarta ta hasko mata Tafida dake tsaye a bakin ƙofa riƙe da jakarta. Ita ɗaukin ganin ƴan uwanta ma ya mantar da ita shi. Ta dafe goshinta.
“Oh!, yana waje, kaje ka shigo da shi ”
“Auta bani hijabina gashi can”
Muhsin ya miƙe sannan ya ɗauko mata hijabin, Maanmu ta karb’a ta saka, sai bin Maryam take da kallo yanda ta ga tasauyamata, duk da dama Anti fati tana fad’a mata yanda Maryam d’in tace suna zaman lafiya da mijinta, amma ganin ‘yarta ta ya k’ara tabbatat mata da waccan magana.
“Sirikin mu ne zai shigo ?”
Maryam ta juya ta kalli matar da kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa bafulatana ce.
“Eh Hanne, mijin Maryam ne“
“Ah to nima bari na je na saka hijabi“
Cike da kokwanto Maryam ta bita da kallo har ta shige ɗakinta na da. Ta juyo ta kalli Maanmu.