Skip to content
Part 45 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

“Maanmu wa ye ce wannan?”

“Husain ka ɗauko wannan dardumar ta ɗakina ka shimfiɗawa Tafida”

Maanmu ta faɗi memakon ta amsa mata, ita fa kanta ya kulle, ta kasa ganewa.

Sallamarsa ta ji daga waje shida Hassan, Hassan ɗin ne ya fara shigowa sannan shi, kansa a ƙasa har ya zauna a kan dardumar da Hussain ya shimfiɗa masa, suna gaisawa da Maanmu Hassan yace da Maryam.

“Yaya a ina zan aje miki jakar ?”

Ta kalli jakar da ke hannunsa se taga jaka ɗaya, bayan ita tasan da jaka biyu ta taho.

“Ka kaimin ɗakin na”

“Ai yanzu baki da ɗaki a gidan nan, sai dai na Maanmu ”

Maganar Hussain ta ƙara kulle mata kai, amma ba komai zata tambayesu tunda Maanmu taƙi amsa mata, sai kawai tace.

“Kai min ɗakin Maanmun to”

A lokacin Hanne ta fito daga ɗakin Maryam na da, ta ja kujera ta zauna itama suna gaisawa da Tafida.

Duk yanda ya kai da gujewa kada Maanmu ta masa godiya sai da ta masa, shi kuma sbd baya san yawan godiyar yasa koda su Hussain suka turo masa lambarsu bai bawa Maryam d’in ba, dan bayama so ta san da abinda yama ‘yan uwanta.

Har ruwa aka kawo masa amma yace tafiya ze yi, sai da ya tashi ya fita sannan Maanmu ta kalli Maryam.

“Kije ki taka masa mana”

Ita gaba ɗaya rudanin dake kanta ya hanata cewa komai, a kunyace ta miƙe ta fita.

Can ta hangoshi har ya kusa fita daga lungun, ta bi bayansa, sanda ta isa wurin har ya shiga mota.

Ita ma seat ɗin gaba ta buɗe ta shiga.

“Akwai jakata ɗaya”

Ya juyo ya kalleta.

“Na sani ai, amma ai wannan kayan sakawar ki ne”

“Eh kayan sakawar, dama su nake faɗa”

“Keda ba’a nan zaki kwana ba, anjima zan zo na ɗauke ki”

Bata san sada ta furta “Huh?”

“Eh mana, baki da wurin kwana a gidan Maanmu, baki san an bawa wata ɗakin ki a gidan ba?”

Zuwa yanzu kam abun ya gama kulle mata kai, kenan har Tafida ma ya san da zaman waccan matar amma ita bata sani ba ?, to me yake faruwa haka?.

“Kije ku gana da ƴan uwanki, nima zanje na ga nawa“

Ita de ba haka ta so ba, tana san ta kwana a gida yau, a cikin ‘yan uwanta. Dan ta yi kewar kowa a cikin su.”

Ta juya jiki a sanyaye zata fita, caraf ta ji ya riƙe hannunta, ta juyo ta kalleshi, a kan lips ɗinsa ya furta.

“I love you”

Bata ce Komai ba, dan kanta cike yake da ruɗani.

Ya saki hannunta ta buɗe motar ta fita, sai yanzu take kallon yanda jama’a suke binta kallo, gaba ɗaya maƙota an leƙo ana san a ga ƙwaƙwaf.

Ko da ta shiga cikin gidansu se ta ga su Hussain na irga kuɗi.

Ta zauna a inda ta tashi ɗazu tana faɗin.

“Wannan ribar shagon wayar ce?”

“A’a mijinki ne ya bayar yace a bawa Maanmu da Anti Hanne”

Ta ɗanyi murmushi, ita de kam ta ƙagu ta san wacece wannan Anti Hannen, gashi kuma tana zaune a wajen, babu damar ta tambayi su Hussain.

“Hassan ɗauko min jakar nan”

Hassan ya miƙe ya shiga ɗakin Maanmu ya fito mata da jakar, se yanzu Maryam take ƙarewa gidan kallo, har sabon fenti suka sake, an gyara gidan sosai.

Bayan Hassan ya kawo mata jakar ta buɗe ta shiga raba musu kayan tsarabar da ta kawo musu, kowa se murna yake har da Abti Hannen da bata tsara kawo gujirin da ita ba itama ta samu, harda maƙotansu.

TAFIDA POV.

Kai tsaye fada ya wuce, sai da ya yi parking motarsa a babban parking lot ɗin katafariyar fadar, sannan ya buɗe motarsa ya fito.

Kamar yanda aka saba, dogarai da hadima dama bayi sai kirari ake masa da miƙo gaisuwa.

“Tafida ɗan Tafida, ruwan kogi tafi sannu sannu wanda ya yi wargi zai halaka, giwa ta gama da masu ƙarfi ta wuce……”

Haka wani dogari me kaifin murya ya ci gaba da rangaɗowa Tafida kirari har ya shige soron farko.

Ya ci gaba da taka sorayen fadar har ya isa inda yake san isa, wato b’angaren Fulani Khadija.Sai da aka masa iso da ita sannan ya samu ya ganta.

Yana zaune a falo na uku ta fito cikin wannan tafiyar tata ta ƙasaita. Tun da ta fito take binsa da kallo, ya sauya mata sauyi ba ɗan kaɗan ba. Ita a yanda me martaba me bata labarin ya sauya ma sai ta ga ya fi, ya yi ƙiba ya ƙara haske, kai da ganinsa kasan cewa hankalinsa ya kwanta.

Zama ta yi a kan kujera tana amsa gaisuwar da yake mata.

“Ina Nadra?”

Sai da wasu sakkani suka wuce kafin ta amsa da.

“Taje wani bikin ƙawayenta”

Ya gyaɗa kansa.

“Ina Maryam ?”

“Na kaita gidansu, inshaallah zata zo ku gaisa”

Itama kan nata ta gyaɗa.

“Bari na saka a kawo maka abinci”

Muryarta ta faɗi cikin shirun da falon ya ɗauka.

“A’a ranki ya daɗe, sauri nake, dan a can gidana zamu sauƙa, zan shiga na duba jikin Galadima sannan na wuce, kuma dama mun yi magana da me martaba kan sai gobe zamu gaisa“

“Babu matsala, Allah kai mu goben, zaka iya tafiya”

Ya miƙe yana mata sallama sannan ya fice.

Fulani Khadija ta ɗaga kanta tana godewa Allah, zuciyarta cike take fal da farin ciki da kuma murna, murnar ta sauƙe nauyin marayan Allahn da aka ɗora mata, murnar ganin tilon ɗan da zata iya kira da nata na cikin farin ciki bayan wani abu da ta yi a rayuwarsa.

Tafida ya yi sallama a falon Fulani Sadiya, jakadiyar da ta masa iso ce a kan gaba, yayinda shi kuma ke biye da ita.

A gaba ɗaya zamansa a fadar wannan shine karonsa na biyu da ya shiga b’angarenta, na farkoma da Fulani Khadija suka fara zuwa sanda ta haifi Amina, bayan nan bai sake shiga ba.

Bin mutanen dake falon ya yi da kallo kafin ya samu waje ya zauna. Fulani Sadiya, Maimun, Amina da Nabil.

Ɗaua bayan ɗayan suka gaida shi, kafin shi ya gaida Fulani.

“Ya Galadima da jiki ?”

Ya tambaya yayinda suke gaisawa, Fulani Sadiya ta jinjina kai.

“Jiki da dama, sai godiyar Allah”

“To Allah bashi lafiya, ni zan wuce”

Ya ƙrashe yana miƙewa.

Ya kuma musu sallama sannan wuce.

Gidansa ya koma, yaje ya yi wanka sannan ya ƙara fita ya tafi asibitinsa.

*Unguwar Garko*

*Da 08:15pm*

Suna zaune a kan babbar tabarma, abinci suke ci suna hira, Hassan, Hussain da Muhsin suna ci a kwano ɗaya, yayin da Maanmu da Anti Hanne da kuma Maryam suke ci a kwano ɗaya.

Zuwa yanzu Maryam ta saki jiki da matar dan tana da kirki, kuma wani abu ɗaya ne ya gifta a tunaninta kan matar, da alama Abbansu ne ya yi aure, dan ko girkin daren ma ita ta yi.

“Yanzu da bana nan waye yake shara da wanke-wanke ?”

“Da da bakyanan Ko ni ko Hussain, amma bayan zuwan Anti Hanne kullum ita take yi” Cewar Hassan.

Maryam ta kalli fuskar matar ta cikin hasken wutar dake tsakar gidan.

“Hassan cover nake so me kyau“

Hassan ya kai loma yana miƙa mata hannu.

“Muga wayar taki”

Da hannunta ɗaya ta zaro wayar a cikin jakarta sannan ta miƙa masa.

“Inalillahi wa inna ilaihi daji’un Hussain kalli wayarta ka gani!”

Ya ƙarashe yana miƙawa Hussain ɗin.

“Kai miye ya samu wayar tawa ?”

“Babu abinda ya sameta, kawai de kuɗinta muke lissafawa”

“Ai nake gaya maka matar nan ta faso gari, kai baka ga hasken da ta yi ba?”

“Harda ƙiba ma ta ƙara”

Maryam ta girgiza kanta tana tauna abincin bakinta.

“Maryam Iya Ummi ta dawo fa“

Maryam ta tsame hannunta daga cikin trayn da suke cin abinci tana kallon Maanmu.

“Tana gari yanzu haka ?”

Maanmu ta gyaɗa mata kai.

“Tana nan, karkiga abinda ta riƙa yi akan wai anyi auren ki bata gari”.

Iya ummi itace babbar ƙawar Maryam tun tasowa, dan hatta da makaranta basu tab’a rabawa ba, da sukayi candy ne ita Maryam ta ta shiga Binyamuini, ita kuma Iya Ummin ta tafi Gashuwa. Ko sanda akayi bikin Maryam ɗin bata gari.

“Yaya akwai irin cover wayar taki”

“Me kwaliya fa nake so”

“Kar ki damu gobe zan kawo miki”

“Ah-ah su Yaya a india”

Cewar Hussain bayan yaga hoton da ke kan wallpaper wayar tata.

“India ?, mu gani”

Muhsin ya faɗi yana dawowa kusa da Hussain, daga haka kuma se hirar ta koma a kan India, Maryam na ta basu labarai akan wuraren da suka je, ta na yi tana nuna musu hotuna.

“Salamu Alaikum!”

Muryar Tijjani ta rangaɗa sallama daga bakin ƙofa, da gudu Muhsin ya miƙe ya yi kansa, Tijjani ya riƙeshi yana dariya.

“Kasan minene a nan ?” Tijjani ya tambayi Muhsin yana nuna masa ledar da ke hannunsa.

“Yalo ?”

“A’a agwalima ce”

Muhsin ya karb’a yana masa godiya, Tijjani ya ƙarasa shigowa cikin gidan, Hassan, Hussain, Maanmu da Anti Hanne duka suka masa sannu da zuwa, ya amsa yana zama a kan tabarmar shima, Anti Hanne ta miƙe ta kawo masa abinci.

Gaba ɗaya mamakinsu ya hana Maryam cewa komai, Abbansu ya sauya, amma yaushe hakan duk ta faru ita bata sani ba?, abun akwai ɗaure kai.

“Ah-ah ashe mutanen lagos ne a gidan”

Sai yanzu Maryam ta ankara da bata gaida shi ba.

“Abba ina wuni”

Tijjani ya amsa da fara’a kamar ba shi ba, daga haka kuma se ya shiga neman yafiyarta, har da saka mata albarka sannan ya rufe da nasiha.

Abun ya bala’in ɗaurewa Maryam kai, ashe akwai rana irin wannan da zata zo ?, koda a mafarki bata tab’a zaton ta.

*****

MARYAM POV.

Tafe suke ita da su Hussain a lungun unguwar tasu, Bayan Tafida ya kirata yace gashi nan a waje ta fito su tafe, shine su Husaain ɗin suka ce zasu taka mata.

“Hussain wai yaushe aka samu sauyi a gidan nan har haka ?”

Ta tambayi abinda ya maƙale a ranta tun bayan sauƙarta a garin.

“Hummm, ai Yaya tun bayan auren ki komai ya sauya, kin ga da sadakin ki Abba yaje ya auro Anti Hanne a ƙauye, ya kawota gida, ita kuma Anti Hanne tun bayan zuwanta gida sai Allah ya haɗa tata da Maanmu, biyyaya babu kalar wadda batawa Maanmu, duk abinda Maanmu zata ce mata shi take, amma fa a wajen Abba bata masa da sauƙi, dan ita ta saka Abba ya buɗe wani shagon provition, ya dawo shi ne yake kawowa abinci a gida, duka ɗawainiyar gidan ta dawo kansa. Ya setu ya dawo dai-dai, abun de sai alhmd”.

“Wallahi yaya auren ki alkairi ya zama ga gidanmu”

Maryam ta yi murmushi, tabbas aurenta da Tafida alkairi ne ga rayuwarta.

“Amma Hussain me yasa to ni ba’a sanad da duka wannan ba ?, kuma fa muna waya da Anti fati, ko da wasa bata tab’a sabar da ni ba”

“Maanmu ce tace kada wanda ya faɗa miki, wai dan kada a tayar miki da hankali”

Allah sarki Maanmu, Maanmu uwa ta gari.

“To mu zamu juya daga nan, sai gobe, ai zaki zo ko ?”

Cewar Hassan a sanda suka fito bakin titi har suna hange motar Tafida dake tsallake.

“Inshaallah zan zo, sai goben auta”

Ta ƙarashe tana dafa kan Muhsin. Daga haka suka mata sallama gaba ɗayan su suka juya, ita kuma ta nufi motar Tafida.

Yana gidan gaba, ya jingina kansa da kujera, kayan jikinsa ma ya sauya.

Ita kuwa wanka kawai ta yi, amma bata sauya kaya ba, dan kayan nata ya tafi da su.

“Hello!, bacci kake ne ?”

Ta furta a sanda ta shiga cikin motar , A hankali Tafid ya buɗe idonsa ya kalleta, asa’ilin da take rufe ƙofar motar, ƙwayar idonsa ta koma ja, zuwa yanzu Maryam ta saba da wannan abun, dan sam baya bata tsoro. Sun glasses ɗinsa ya janyo sannan ya saka.

“Mts!, ba bacci nake ba”

Muryar sa ta fito kamar me jin baccin, kuma kamar wanda yake a wahale.

“Baka da lafiya ne ?”

Ya girgiza mata kai yanawa motar key.

“Lafiyata ƙalau, kawai yunwa nake ji”

Ta zaro ido cikin faɗin.

“Baka ci abinci ba wai ?”

Ya gyaɗa mata kai, ai dole yaji yunwa, sanda zasu taho daga abuja ma beci abinci ba, cewa ya yi idan ze yi dogon tuƙi baya cin abinci.

Tafiya suka fara, babu wanda yace da wani ƙala, koda suka zo round about ɗin fada se taga ya yanke hanya, tunaninta fada zasu je.

Mamaki be kamata ba sai da taga sun ɗau hanyar Kano road, bata de ce komai ba, a kusa da sabuwar tasha taga yatsaya wajen wani me seda gasashiyar kaza da doya.

Ya fita, ta yaje wajen mutumin, ita batasan cewa mutane irinsa na cin irin waɗanan kayan ba.

Bayan ya siya ya dawo motar, ya miƙe titin express ɗin nan, sannan ya yi kwana ya dawo hanyar shiga gari, sai kuma taga sun ɗau hanyar Maje road, kuma a Maje road ɗin ma ya tsaya ya shiga Wani store ɗin dake kan hanya.

A nan kuma bata san me ya siyo ba se ganinsa ta yi da ledoji niƙi-niƙi, yabuɗe gidan baya ya saka a ciki, sannan ya shiga ya tayar da motar suka ci gaba da ta fiya.

Hanyar Shagari G.R.A taga ya nufa, hakan ke nuna mata cewa gidansa zasu je, gidan da a da sai de ta wuce ta ƙofar sa, wani lokacin har gaisawa suke da masu gadin gidan.

Yau se gata zata shige shi a matsayin matar me gidan. Kafin su kai gidan har bacci ya fara ɗauketa, dan bata ma san sanda suka isa gidan ba.

Ƙarar buɗe ƙofar motarsa ne ya farkar da ita daga gyangyaɗin da ya soma ɗaukarta, ya zagaya ya buɗe mata motar ta fito, sannan ya kuma zagayawa ya ɗebo ledojin dake baya.

“Kawo na taya ka”

Ya girgiza mata kai.

“Ke da kike bacci“

Au ashe ya ganta, se bata sake cewa komai ba har suka shiga cikin gidan, duk da dare ne hakan be hanata ganin kyan gidan ba.

Shine a kan gaba ita kuma na biye da shi, har ɗakin da taga ya shiga, a cikin ɗakin ne kuma taga jakar kayanta. Kai tsaye wurin jakar ta wuce, ta buɗe ta ta ɗauko wasu pyjams riga da wando masu kyau, ta shiga bayi ta saka kayan sannan ta fito.

Sanda ta fito ta iske shi zaune a kan sofa yana cin abinci. Bata ce masa komai ba ta wuce ta ɗauko hijabinta,sannan ta dawo kan gadon ta kwanta, kamar daga sama ta ji muryar sa.

“Ba za ki ci abincin ba ?”

Ta juyo ta kalleshi amma shi ba ita yake kallo ba kamar yanda ya saba. Kuma har yanzu idonsa sanye cikin baƙin glashin nan.

“Naci abinci a gida”

Shi ma be ƙara cewa komai ba, har ya gama cin abincin nasa, ya aje sauran kayan da ya siyo, ya miƙe ya shiga ɗakinsa na gidan, kayansa yaje ya sauya sannan ya dawo ɗakin da ya bar Maryam.

A kan gadon ya kwanta yana kallon fuskarta ta cikin hasken dake ɗakin, hannunsa ya motsa a setin swithch, take wutar ɗakin ta mutu.

Tsoron da ya saba kama Maryam shi ya kamata, dan haka ta matsa kusa da Tafida ta shige jikinsa, shi kuma ya kai hannunsa ya riƙeta, ya mata peck a ka.

“Ka yi addu’ar bacci ?”

Addu’a ?, ita bata san cewa shi ba kamar kowa yake ba ?.

Tana jin kansa da ya girgiza mata.

Kamar yanda ta saba idan suka kwana tare se ta yi addu’ar sannan ta tofa masa.

*****

<< Yadda Kaddara Ta So 44Yadda Kaddara Ta So 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×