Skip to content
Part 46 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Cosgrove Estate wuse,st 3, house NO 334

08:40pm

HARIS POV.

Sai da ya tabbatar da ya gama aje komai a yanda yake, sannan ya yi sama zuwa ɗakin Hanam.

Zaune ya samesu ita da Arya, tana waya wadda yake da tabbacin da Masarrat suke yi, dan ya ji tana larabci, pyjams ne a jikinta iri ɗaya da na jikin Arya.

Kanta ta ɗago ta kalle shi a sanda ta aje wayar.

“Ammi tace tana tayaka murna, da waƙarka da ta yi trending a africa baki ɗaya”

Ya yi murmushi yana ɗaukar Arya.

“Godiya nake, muje”

Ta miƙe tare da faɗin.

“Zuwa ina ?”

“Ƙasa mana“

Bata kuma cewa komai ba ta bi bayansa.

Baki sake take kallon falon nasu, wutar falon a kashe take, sai wani haske me kyau da ɗaukar ido kalar purple dake haskawa a farlon, ga katifa an shimfiɗe a ƙasa an rufeta da bed sheet, ga pillows manya manya an kewayeta da su, katangun falon na glass ya sauƙe curtains, sannan ga wani farin bord da aka aje a wajen.

Ga wani table da aka ɗora projector a kai, wanda ke facin farin bord ɗin, a kan coffee table kuma kayan kwaɗayi ne kala-kala aka jera.

“Wow!, amma fa wurin nan ya yi kyau”

Haris ya aje Arya a kan katifar yana faɗin.

“Disney ne suka saki wani sabon film, wai shi ‘WISH’ shi ne nace bari mu kalla“

Hanam ta zauna akan katifar itama, yayinda shima Haria ɗin ya zauna, suka saka Arya a tsaya, ya kunna ya danna wani switch a jikin projectorn, nan take film ɗin ya shiga playing.

MARYAM POV.

Yau da safe da suka ta shi bayan sun shirya gidan Wani abokinsa Muktar ya kaita ta gaisa da matarsa har da ɗansu da suka ce mata me sunan Tafidan ne.

Sun ɗan jima a gidan, kafin suka tafi, kuma daga nan unguwarsu taga ya nufa, a ƙofar lungunsu ya yi parking.

“Se yau she kenan ?”

Ya tambaya idonsa a kanta.

“An jima mana”

Se ya gyaɗa mata kai yana cije lips ɗinsa.

“To a dawo lpy”

“Ameen Allah ya sa”

“Ki gaida Maanmu da Abba da Anti Hanne”

Maryam ta fita daga motar a ranta tana faɗin wato shima ya san Anti Hanne, itace ba ta da labarinta, koma me ya faru lefin Anti Fati ne, ai suna waya ya kamata a ce ta faɗa mata.

“Yauwwa shigo, ai kinganni nan sammako na yi yau, tun da an ce mana ganinki se an cike file”

Muryar Iya Ummi ta faɗi bayan Maryam ta yi sallama, da gudu Maryam ta yi kanta tana dariya.

“Allah sarki ta gidana, na yi missing ɗinki wallahi”

“Ba wani nan, ɗagani ni, ai da ace kin yi kewata ba zaki koma lagos ki yi zaman ki ba”

“To ai keɗince baki da waya..”

“Inji ub*n wa ?, to wallahi na yi waya”

Ta ƙarashe tana miƙo mata wayartata, Maryam ta karb’a.

“Iyeee?, ki ce Iya Um…”

“Ke ke dakata dallah!, na soke wannan sunan, sunana Hafsa, idan kuma bazaki ce Hafsa ba ki barshi”

Maryam ta ɗaka mata duka tana juyawa wajen Maanmu.

“Maanmu ina kwanan ku”

“Lafiya”

“Anti Hanne ina kwana”

“Lpy Maryam ”

Anti Hanne ta amsa mata da fara’a, bata tambayi ina su Hussain ba, dan tasan akwai school.

“Ina gujirin nawa”

Maryam ta miƙe tana faɗin.

“Muje ɗaki na baki”

“Ke ta gidana kinga yanda kika yi kyau?, kin yi fresh a binki, ko dan wa ya sani ma ko akwai ƙaramin Tafida a cikin ki….”

Maryam ta ɗaka mata duka a sanda suke zama a kan gadon Maanmu.

“Wallhi Hafsa bana san iskanci, ke tsiyata da ke kenan, baki iya bakin ki ba”

“Yau ai gaskiya na faɗa, kinsan ni ba’a ƴar b’oye-b’oye da ni ehee“

“Ah!, me hali ba ze fasa ba”

“Se na dawo na iske ƴar iskar nan ta bar gari”

Maryam ta yi dariya.

“Ko ba Badar ba ?, ta koma kano wallahi”

“Umm!, Maryam yanzu duk yanda ƴan matan Haɗeji ke zilamar Tafida kece kika yi wuf da shi, ke nifa ko hira ake se na ce ƙawata ce ta auri Tafida”

Maryam ta tintsire da dariya, dan tasan wannan ba ƙaramin aikin Hafsa ba ne, idan aka ce ta yi fin haka ma ba za’a musa ba.

“Wannan tabon na fuskarki fa”

Maryam ta kai hannu ta tab’a gefen fuskarta, dede inda ta ji rauni sanda Heleen ta daketa.

“Faɗuwa na yi”

“Oooh!,Muga wayar taki to”

Maryam ta miƙa mata, hoton wallpaper farko ta gani, wanda na Maryam ne ita da Tafida, da a ka musu a Mumbai, a Marine drive.

“Oh ni duniya, wai dama Maryam har indian kuka je ?”

Maryam ta janyo wata jaka a cikin kaya da ta zo da shi tana faɗin.

“Mun kusa wata ma a can, bamu fi kwana huɗu da dawo ba”

“Kai ƙawata Allah saka mu a danshin ku”

“Ga wannan shine gujirin ki”

Hafsa ta aje wayar Maryam ɗin dake hannunta, ta miƙe tsaye ta ware rigar da Maryam ta bata, ta kara a jikinta baki buɗe. Ta aje rigar sannan ta ɗauko ɗan kunnen da ta haɗa mata da shi ta gwada.

“Kai na gode amaryar Tafida, irin wannan kyauta haka….”

Sallamar Anti Fati suka ji a gidan,Maryam ta fito da saurinta har da ɗan gudu, tana ganin Anti fati ta faɗa jikinta.

“Oyoyo ƙaunar Imran”

Anti Fati ta faɗi cike da jin daɗin ganin ƙanwar tata, Maryam ta saketa tana karb’ar Imran dake hannunta, Anti Fati ta shiga ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta sauya, ta ƙara ƙiba ta ƙara fari.

“Anti fati sannu da zuwa”

Muryar Hafsa ta faɗi daga bakin ƙofar dakin Maanmu, Anti Fati ta amsa mata su na shigowa cikin gidan.

Imran na wasa da ɗankwalin kan Maryam ya ja shi baya, ɗankwalin ya faɗi, gashin kanta da bata nannaɗe shi ba ya baje a bayanta.

“Kai ni kuwa yau naga ikon Allah, wai da ya kai ki indian gashi suka sake miki ?”

Hafsa ta faɗi tana kallon gashin Maryam ɗin.

“A’a wallahi babu wani gashin da na sake, in faɗa miki gyara makawai ya ji”

Maryam ta faɗi a sanda ta miƙawa Anti Fati Imran, ta ɗauki dankwalinta tana ɗaurawa.

“Ai ko baki ga yanda gashin kan naki ya yi kyau ba”.

*****

TAFIDA POV.

“Ki fito ga ni na zo”

Yana faɗin hakan ya aje wayar sa ke kare a kunnensa, yanzun kusan ƙarfe shida ne na yammma, dan yau kusan yini ya yi a asibiti.

Tun da suka doso motar yake kallonsu ita da wata da besanta ba har suka iso wurin motar.

Ƙofar gaban ya buɗe ya fito, gaisawa suka yi da wadda ya gansu taren.

“Sundar ƙawata ce, sunanta Hafsa”

Tafida ya juya ya kalli Hafsa.

“Sannu ƙawarmu ya kike, ya al’amura”

Hafsa na washe baki tace.

“Wallahi komai lpy”

A hankali ya gyaɗa kansa sannan ya kalli Maryam.

“Muje Miriam”

Daga haka kuma ta yi sallana da Hafsan sannan ta shiga motar ya tayar suka tafi, sai ta ga ya ɗauki hanyar unguwar kantin waje.

Har suka kai wani gida bata ce masa komai ba. A parking lot ya yi parking suka fito a tare.

“Gidan Mairama ne, ƙanwar mahaifi na”.

Sun kusan kaiwa minti goma zaune a makeken falon gidan, kafin wata hamshaƙiyar mata ta fito tana taku cike da isa da ƙasaita, kallo ɗaya Maryam ta mata ta gano kamarta da me martaba.

Cike da girmamawa Maryam ta duka gaisa da Maryam, kafin tasa a yiwa yaranta magana suka zo suka gaisa da Maryam ɗin, wata ce wai ita Asiya ta bi Maryam da kallon raini sannan ta miƙe zata bar falon.

“Ke Asiya, ba ki gaida matar wanki ba”

Asiya ta juyo tana wani yatsina fuska.

“Saboda Allah wannan zan gaisar ?, jibeta fa, wata villager da ita…”

“Asiya bana san iskanci, ke da da aka ce ki aure shi ba ƙi kika yi ba, se yaunzu za ki zo kina wa mutane iyayin banza da wofi, ki bata haƙuri yanzun nan”

Ba haka Asiya ta so ba,amma koda wasa basu isa musu da Mairama ba,dan haka tace.

“Sorry”

Daga haka kuma ta juya, Mairama ta sallami sauran yaran nata sannan ta dubi Maryam.

“Ki yi haƙuri takwarata”

Maryam ta girgiza mata kai.

“A’a ranki ya daɗe babu komai ”

Maryam da ke kallon window ta ji hannun Tafida ya riƙo nata, ta juyo ta kalke shi.

“I am sorry Miriam, ba ta san wacece ke ba shi yasa tace haka, ita fa ƴar uwata ce, kwanaki aka ce ta aureni, amma tace ita bata san monster”

Sai kuma ya yi murmushi me sauti.

“A time ɗin ban ji haushinta ba, amma yanzu na ji, sbd nasan ni ba monster ba ne, Tafida Eshaan ɗin Miriam ne”.

Maryam ta yi murmushi, wato yanzu baya san sunan da yake kiran kansa da shi a da, se de a cikin ranta ta ayyana irin wannan abun da take gudu tun sanda aka ɗaura aurenta da Tafida.

“Kuma duk da ina monstern, amma ke naga kina so a haka”

Dama ita tasan da walakin, dan bisa ga dukkanin alamu sun nuna cewa Asiya fa kishi ta ke. Bata cemasa komai ba kawai ta ci gaba dakallonsa.

Fada ta ga su nufa, kuma ta ji daɗin hakan dan ko ba komai zata je ta ga Fulani da Nadra.

“Nadra bamu waje”

Wannan Muryar ta Fulani ta faɗi a sanda ta shigo falon da Maryam da Nadra ke ciki, Nadra ta saka Maryam a gaba se zance take mata.

Sim-sim Nadra ta fice daga falon. Fulani ta nemi kujera ta zauna kusa da Maryam tana mata murmushi.

“Babu abinda zance da ke Maryam se godiya, dan sosai na ga canji a tare da ɗana, naga har wata ƴar ƙiba ya yi”

Maryam ta yi dariya tana sunkuyar da kai.

“A’a ranki ya daɗe, ba ni ya kamata a godewa ba, Allah zamu godewa, kuma akwai wata magana da nake so na miki…..”

Fulani bata ce komai, ta yi ahiru tana jinjina hankali da tarbiyar yarinyar.

“Ranki ya daɗe ya kamata a ce kina jansa a jiki, ciwonsa yana buƙatar ja a jiki, yana buƙatar ya samu wanda ze riƙa faɗawa damuwarsa, yana san a ja shi a jiki sosai, ta haka ne ze faɗa miki duk wani abu dake damunsa”

Fulani ta kasa cewa komai, ta kafe Maryam da ido kawai.

“Salamu alakimu”

Sallamar Tafida da ga waje ta katse musu hanzari.

Ya shigo ciki ya zauna.

“I dan kun gama zamu iya tafiya?”.

“Muna ƴar hirar tamu zaka ɗauke min sirikar tawa”

Ba Tafida ne kawai ya yi mamakin sakewarta ba, harda Maryam da ta bata shawara, bata tab’a zaton zata ɗauki shwarar ta haka da sauri ba.

“A’a kawai dr naga dare ya yi ne, shi yasa nace zamu koma”

Bisa ga mamakinsu sai suka ji ta yi dariya.

“Babu damuwa, zaku iya ta fiya, ammam dan Allah ku dawo gobe”

Muryarta a sake kuma cikin raha, Tafida xai iya rantsewa da Allah bai tab’a jin muryarta cikin wannan yanayin ba.

Unguwar Garko

12:00pm

“Da Allah wace zan samu ta min lalle idan zamu tafi ?”

Cewar Maryam yayin da take saka alkakin da Maanmu ta saka aka mata a cikin leda.

Yau kusan satinsu ɗaya a haɗejia, kuma suna sa ran tafiya zuwa jibi, ta yi ziyara sosai, dan har dangin Abban su seda suka je, hatta da gidan kawu usman da da bata san zuwa sbd ƴaƴansa da suke mata kallon reni, dan ita bata san a renata.

Amma kuma wannan zuwan da ta yi haba-haba aka riƙa yi da ita, gaba ɗaya mutanen gidan sun sauya mata, bata ce ga dalili ba, amma wata ƙila dan ta yi aure ne, ko suna mata dan ta auri me kuɗi, ko kuma ma dan matsayin wanda ta aura ɗin.

“Ga Ummi me funkaso, ai har yanzu tana yi”

Hafsa ta amsa mata tana tayata kwashe al’kakin.

“Ni fa ɗan gam nake so”

“Duka ta na yi, zan mata magana se ta zo har gida ta miki”

“Yaushe kenan ?“

“Gobe ya yi ?”

“Allah kaimu goben to”

“Amma ba za ki yi kitso ba ?”

Cewar Maanmu dake aje musu bokiti cike da dubulan, dan takanasa ra kano ta sa aka yiwa Maryam ɗin dubulan da al’jaki, dan ta san tana san su.

“A’a Maanmu banda kitso…..”

Caraf Hafsa ta yi tace.

“Ina ita in yin kitso gashin kanta ya koma irin na indiyawa”

Maryam ta girgiza kanta, Iya Ummi bazafa tab’a sauyawa ba.

“Yaya ga farar”

Maryam ta kai hannu ta karb’i ledar da Muhsin ke miƙa mata, dan ita ta aike shi ya siyo mata fara, sbd tana san fara sosai.

“Yauwwa Autan Iyarsa, na gode”

“Maanmu, Hafsa, Anti Hanne fara ”

“Wa ?!, ni jikar Haruna, kin tab’a ganina naci wata fara?“.

Cewar Maanmu.

“Miƙo min na ci”.

Hafsa ta faɗi tana tsane hannunta daga cikin bokitin dibulan.

“A’a alhamdulillah“

Anti Hanne ta faɗi a sanda take kunna gas, dan yanzu sun ma bar aiki a ice a gidan.

TAFIDA POV.

Yau be samu dama ya je ya ɗauki Maryam ba, dan tace masa lalle za’a mata, kuma shima abubuwa sun masa yawa ga shi gobe zasu bar garin.

Ko abinci be samu ya ci ba, haka ya dawo gidan cikin sa fanko, gashi a gidan babu abinci. Kwanciya kawai ya yi a falo yana saƙe-saƙe.

Jin an turo ƙofar yasa shi miƙewa zaune, Maryam ce ta shigo bayanta biye da masu gadi sun ɗauko mata kaya, ita ta nuna musu inda zasu aje mata sannan ta musu godiya suka fita.

Kallonsa kawai take Tana san gane meke damunsa.

“Me ya faru ?”

Tatambaya a sanda take zama kusa da shi, tare da aje flask ɗin hannunta. Ya furzar da iska.

“Wallahi yunwa nake ji”

“Allah sarki, kaga kuwa na taho maka da abinci, dan nasan yanzu ba samun damar ci kake ba”

Ta ƙarashe tana janyowa flask ɗin ta buɗe.

“Muga lallen”

Ya kama hannyenta data riƙe murfin flask ɗin da su, ya shiga jujjuya hannun yana kallo lallen, da aka tsantsaramata shi, wanda ya kwanta a kan farar fatar ta.

“Ya yi kyau sosai”

Ta ɗanyi murmushi.

Janta ya yi zuwa cikin jikinsa, wannan abun da ya saba kai kawo a cikin kan Maryam ya shiga aikinsa.

“Bani abincin to”

A hankali ta kai hannunta ta janyo flask ɗin, sannan ta shiga bashi abincin tana masa hira.

<< Yadda Kaddara Ta So 45Yadda Kaddara Ta So 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×