Skip to content
Part 47 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

11:30

Maryam na jere kayan sakawarta a cikin jakar da ta zo da ita. Ƙofar ɗakin a ka turo, kuma ko bata kalle shi ba tasan shine, dan haka bata kalle shi ɗin ba, ta ci gaba da jera kayan.

Tana jin takunsa har ya tsaya a bayanta, kuma shima be jira komai ba, ya saka hannayensa biyu ya ɗaga ta sama, yay mata ɗaukan bride style.

Maryan ta zare ido tana kallonsa, sannan ta cilla ɗankwalin atamfar da ke hannunta cikin jakar.

Tafiya ya fara yi da ita har zuwa kan gado, ya kwantar da ita yana shirin rufa mata bargo. Ta yi sauri ta miƙe zaune.

“Kaya fa nake haɗawa….”

“Sshhhhh, ki kwanta kawai sai da safe”

Ya faɗi yanaa ƙara kwantar ta, Maryam ta ƙara miƙewa.

“Idan na ce sai gobe makara zan yi”

Shima kuma ya ƙara kwantar da ita, sannan ya kwanta a gefenta, ya motsa hannunsa ya kashe wutar ɗakin.

Maryam da kanta ta murgina kusa da shi, dan gwara ko motsinsa ne ta ji a cikin duhun nan.

“Baki dena tsoro ba har yanzu ?”

Ya tambaya yana motsa kunnensa. Yana jin kanta da ta girgiza masa, shima kuma se ga gyara kwanciyar tasa yana sakata a cikin jikinsa.

“Ina nan tare da ke, hmmmm?”

Ta kuma gyaɗa masa kai.

HARIS POV.

“Kai Uchenna aiki na kyau“

Cewar Falaƙ, a sanda suke duba comments ɗin masoyan waƙar sa ta biyu da ya saki, waƙoƙinsa yanzu sune ke zagaya duniya baki ɗaya. A cikin wattanin ba ƙaramar shahara ya yi ba.

Albarkoki daga ko ina zuwa suna ta zuwa, yazu ya sauya musu gida, amma kuma a cikin cosgrove ɗin ya sauya, kawai de ya bar nasa na da, ya koma wanada ya fishi, hatta da Babansa ya sai masa gida. Babu abinda zai ce sai dai ya godewa Allah dan waƙa ba ƙaramin karb’arsa ta yi ba.

“Muna tayaka murna Uche”

Djn studio ɗin ya faɗa. Ya miƙa masa hannu suka gaisa, sannan ya shiga gaisawa da sauran abokan aikin nasu.

Wajejen ƙarfe 8pm ya koma gida, a falo yaga Arya shi ɗaya yana wasa.

Aryaan na ganinsa ya shiga daga masa hannu, alamun ya ɗauke shi, Uchenna ya masa dariya yana ɗaukansa, tare da dan ƙa masa chocolate ɗin da ya shigo da shi.

Ya san cewa war haka Hanam tana kitchen, dan haka kai tsaye ya wuce kitchen ɗin, a nan kuwa ya sameta tana ta faman haɗa girki.

Bata ma san da shigowar su ba sai da ta ji hannu ɗaya ya yi hugging ɗinta ta baya, se da taja wata iska, sannan ta juyo tana kallonsu, dan tasan ba shi kaɗai ba ne.

“Kufa bakwa jin magana, so kuke se kun sa na makara a girkina”

Haris ya yi dariya.

“Yau makara ta nawa kuma ?, takwas fa ta yi, amma baki gama girki ba”

“Ku min shiru ni, kuje waje ku jira ai na kusa gamawa”

Memakon su fitan kamar yanda tace, sai suka zauna a kan kitchen island, ya shiga yi wa Aryaan wasa, yana yi yana bawa Hanam labarin nasarar da aka samu.

Har ta gama abincin ta juye musu a kwano ɗaya, dan yanzu duk rintsi a kwano ɗaya suke cin abinci su duka ukun.

*****

House No.122, B3, Alaro city lekki, Lagos

MARYAM POV.

Hannunta ya saka riga ta ƙarshe a cikin wardrobe ɗinta. Sannan ta rufe wardrobe ɗin.

Dawowa ta yi ta zauna a kan gadonta, tana ɗaukan wayarta, ji ta yi zuciyarta na ta shi, hakan yasa ta miƙe da gudu ta yi banɗaki.

Ta shiga kela amai kamar zata ƙarar darm ruwan dake jikinta. A galab’aice ta miƙe tana kunna famfon sink, ta wanke bakinta, sannan ta fito.

Kusan karo na biyu kenan tana amai a yau ɗin nan. Yau da safe suka sauƙa a lagos, bayan sun tsaya a abuja, sannan suka iso lago ɗin.

Kuma suna dawowa Tafida ya tafi shopping shi da David, ba zata ce ga takamemen abinda yasa take aman ba, amma kamar tana tunanin pizzar da suka ci a air port ne, sai da tace ba zata ci ba amma Tafida ya takurata se da taci.

Ita tasan dama cikinta ba san baƙon abu yake ba. Ji ta yi ma zaman ɗakin ba ya mata daɗi, dan haka kawai ta fita, kuma bata tsaya a ko ina ba se saman gidan, dan tana ganin wata ƙila zata samu daddaɗar iska a wajen.

Ta ɗan jima zaune a waurin tana shan iska, kafon ta hangi shigowar motar Tafida, dan haka ta miƙe ta sauƙa.

Tana tsaye a falo ta ji sanda ya buɗe ƙofar kitchen ta baya. Bayan ɗan wani lokaci kuma ya shigo cikin falon ta ƙofar gaba.

Yana ganinta ya buɗe mata hannayensa biyu, alamun ta taho ta yi hugging ɗinsa, kunya tasa ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Shi kuma be ce mata komai ba har ya ƙarsa inda ta ke, kuma yana isa inda take ya ja hannunta ta faɗa jikinsa sannan ya ƙanƙameta, kansa ya sauƙa a kan kafaɗunta.

“Ke biki yi kewata ba ko ?”

Mamaki ya kama Maryam, dan be wani jima da fita ba. Ya saketa yana kallon fuskarta, a hankali Maryam ta tsirawa idonsa ido, ganin yanda yake ƙifƙifta shi, kuma se da abinda baya so ɗin ya faru. Wato ƙwayar ta koma ja.

“Ba yanzu ka fita ba?”

Se ya ɗauke hannunsa da ga ƙugunta, ya dawo da shi gefen fuskarta yana motsa shi a hankali.

“Baki sani ba ne Miriam, ko da da minti ɗaya idan na matsa daga kusa da ke kewarki ce ke kamani, bana san na yi nesa da ke ko kaɗan”.

Maryam ta kwantar da kanta a hankali a kan ƙirjinsa, tana jin sautin bugun zuciyarsa a kunnuwanta.

Ji ta yi ya yi pecking kanta sannan ya ƙara riƙeta cikin jikinsa.

“I love you, Miriam”

Maryam ta kewaye hannyenta biyu a bayansa.

“I love you too Shona(sweetheart).

*****

MARYAN POV.

01:00am

Bige-bigen da Maryam ke jiyowa yasa ta buɗe idonta, da ƙararma jinta take kamar a mafarki, a hankali ta shiga baza idonta a cikin duhin ɗakin, dan babu haske se na farin wata da ke shigowa da ga balcony.

Hannunta ta kai ta laluba inda tasan Tagifa na kwace, dan tare suka kwanta.

Kafin ƙwaƙwalwata ta faɗa mata cewar baya gadon wani gurnani ya shiga cikin kunnuwanta.

A zabure ta miƙe zaune, ta kai hannu ta kunna wutar ɗakin, baya cikin ɗakin, to amma yaushe ya fita ?.

Wani irin gurnani da ta ji yana yi ne ya ƙara tsoratata, a cikin ranta take karanta duk addu’ar da tazo bakinta.

Kafin wata ƙwalla me ɗumi ta sauƙo mata. Ta kai tsawon minti biyar a haka, kafin ta ji ya saki wata ƙara.

Bata san sanda ta miƙe tsaye ba, idonta ya ƙafe, babu ko ƙwayar tsoro. Ba tare da tunanin komai ba ta kama hanyar barin ɗakinta.

Fita ta yi da ga ɗakin nata, sannan bata bari komai ya dakatar da ita ba ta buɗe ƙofar ɗakinsa.

Hasken fitilun da ke ci a ɗakin suka haska mata shi, duk da babu wani wadattacen haske, durƙushe yake a ƙasa, yana karta faratan hannunsa a kan carpet, duk da baya ya bata amma tana iya jiyo gurnanin da yake.

A hankali ƙafafunta suka shiga taka tiles ɗin ɗakin har zuwa kan carpet, duk wani tsoro da tasan an haifota da shi ta ji ya gushe, babu wani abu kuma da take ji ko ganin ze iya tsoratata.

“Eshaan!”

Tafida dake durƙushe a wajen ya motsa kunnensa yana sakin wani irin gurnani kamar zaki, kafin ya ɗago jajayen idanuwansa.

Yana miƙewa tsaye ba tare da ya juya ba yasa hannunsa ya buge Maryam, ta faɗi can a gefe, yayin da ta saki ƙarar a zaba, sbd hannunta da kanta da suka bugu.

Se a sannan ya juyo, Maryam zata iya rantsewa da Allah kayan cikinta sunyi juyin waina, kafin ta ji wani abu na shirin sub’ucewa a mararta. Sakamakon kallon da yake mata, ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja, fiƙoƙi guda biyu sun sauƙo daga haƙwaransa na sama.

Se huci yake yana gurnani kamar bear, da ƙyat Maryam ta miƙe tsaye. Bata fasa abinda ta yi niyya ba ta shiga takawa zuwa gabansa, shi kuma be fasa kallonta ba, yana huci da gurnani.

“Kaga Eshaan, ka saurare ne”

Muryarta ta faɗi cikin wani irin sauti wanda yake nuna daf take da fashewa da kuka.

Tafida ya ɗaga hannunsa ya damƙi wuyanta, tareda ɗaga ta sama, Maryam ta shiga kakarin azaba, hannayenta a kan nasa da suka shaƙeta.

“Esh…Eshaan…..Esh…Esho!”

Cikin wani wahallalen sauti ta furta hakan, tana faɗi tana kallon idonsa, kalmar sunan ‘Esho’ da ta shiga kunnensa ta haske masa da wani zamani daya shuɗe.

_ “Kada ka damu Esho, zan dawo, kaide ka kula da kanka”_

“Maa!”

Ya furta hakan a iya kan leb’ensa, Maryam dake wutsil-wutsil da ƙafafunta tana kallonsa.

A hankali wani abu kamar haske ya gifta ta idon nasa, jan ya shiga washewa nan take, sannan ya saki Maryam ta faɗo ƙasa tana dafe wuyanta haɗi da tarin azaba.

Gani ta yi ya faɗi ƙasa shima, yana dafe kansa.

“Maa!, Meri Maa!, Maa kyu?!kyu Maa?!”

(Maa, Maana, Maa me yasa ?, me yasa Maa?).

Kan nasa ya ƙara dafewa yana rintse ido, hayyacinsa na dawowa cikin jikinsa.

A tarihin rayuwarsa baƙin ruhinsa be tab’a tashi ya tafi cikin sauƙi haka ba.

Ya kai minti goma durƙushe dafe da kansa, Duka Maryam dake dafe da wuyanta tana kallonsa.

Kafin kuma tashi ɗaya kamar wanda aka zabura ya miƙe zaune yana dube-dube, Maryam ta yi saurin ƙarasawa kusa da shi tana dafa shi.

“Eshaan lafiya?”

Tsayawa ya yi yana kallonta, sai kuma abinda ya mata daki-daki ya shiga dawo masa, a hankali wata ƙwalla ta silalo masa.

Kafin ya saka hannunsa ya ture na Maryam dake jikinsa.

“Maryam ki yi haƙuri”

Cikin kuka ya furta hakan yana sunkuyar da kansa, Maryam ta shiga girgiza masa kai tana ƙara kamo hannunsa amma se ya fisge yana ja baya da ita daga zaunen da yake.

“Dan Allah Maryam ki yi haƙuri, ni ban dace da ke ba, kina buƙatar mijin da ya cancanceni amma ba irina ba, ni ban kamace ki ba”

Maryam ta ƙara matsayawa kusa da shi tana share hawayenta.

“A’a Eshaan, ni kai ne naga ka kamace ni, kai na ke so Eshaan….”

“Ni kuma Maryam cutar da ke zan yi, ba za ki iya zama da ni ba, i am monster Maryam, i am beast, lalata miki rayuwa kawai zan yi, ni ban kamaci zama da kowa ba….kaɗaici ne ya dace da ni, na yi kuskure da na saka kika fara so na, na yi kuskure da na fara sanki, ban kamaceki ba Maryam, sam ban kamace ki ba”

Muryarsa har wani sarƙewa take sbd kukan da yake, jikinsa na jijjiga sosai, dan kuka yake bil haƙƙi da gaskiya, kuka yake wanda rabonsa da ya yi irinsa ya manta, kuka yake na rabuwa da Maryam, zuwa yanzu yasan cewa idan har yaci gaba da zama da ita to cutar da ita kawai zeci gaba da yi, sam Maryam bata kamace shiba.

“Ni mara amfani ne…”

Ya shiga marin fudkarsa yana faɗin.

“Ni annoba ne, lalata rayuwar kowa nake….”

Yanda Maryam ta haɗe bakinta da nasa ne yasa shi yin shiru, kusan a tare suke fitar da ƙwalla masu zafi, Maryam ta ja da kanta baya kaɗan, sannan ta tallafe fuskarsa da hannayenta biyu.

“Kana da amfani Eshaan, kana da matuƙar amfani a gare ni, kai ba anno ba ba ne, kai mijina ne, abun alfaharina, madubin kallo na, gobe na dama komai nawa kai…….ne”

Wata sabuwar ƙwalla na cika masa ido ya kama fuskarta sannan ya ƙara haɗe bakinsa da nata.

Yana kissing ɗinta kamar ba ze dena ba, kafin ya saketa yana meda numfashi.

“Ina sanki Maryam, ina mutuƙar sanki, dan Allah kada ki rabu da ni, idan kika rabu da ni wallahi zan iya mutuwa…”

Da sauri Maryam ta miƙe a akan guwowinta, sannan ta rungume kansa a ƙirjinta, shi kuma ya kewaye hannayensa a ƙugunta yana ƙara matseta a jikinsa, hawaye na ƙara tsananta a fuskarsa.

“Bazan rabu da kai ba, trust me, ina nan tare da kai”

Kafin ta saki kan nasa tana dawo tana kallon fuskarsa, a hankali ta shiga share masa hawayen da yake.

Sannan ta kara goshinta a kan nasa, ta lumshe idonta, shi kuma ya yi amfani da hakan wajen riƙe fuskarta, ya haɗe bakinsa da nata ya shiga kissinga sosai.

Kafin ya motsa hannunsa a setin switch. Duhu ya mamaye ɗakin, babu haske se wanda yake shigowa ta balcony.

A wannan daren abubuwa da dama suka warware, a wannan daren abubuwa da dama suka gyaru. Babin ƙaddarar ya zo ƙarshe, littafin ya rufe, aka buɗe wani sabo, wannan daren ya zama mabuɗin wara sabuwar ƙaddara da zara tu karosu wadda basu da masaniya a kanta. Kuma Allah ya riga ya hukunta faruwarta.

A wannan daren.

*****

Haɗejia Emirates

Galadima na kwance a kan gadonsa, yana baccin a zaba kamar yanda ya saba kullum, dan har yanzu jikinsa ba sauƙi, kullum jiya i yau.

Kawai ji ya yi ƙashin bayanasa na ƙara, hakan yasa ya buɗe idonsa, a hankali a hankali yake jin kasusuwan jikinsa na komawa inda suke, kamar da sab’a su a ka yi, yanzu kuma suke warewa cikin ƴancinsu.

Yana jin yanda ƙafarsa ta miƙe ƙalau, ya ji sanda hannunsa ke komawa yanda yake da, ya ji bakinsa na dawowa yanda yake, komai nasa ya dawo normal.

Kamar bacci ya kwanta kuma ya farka, kamar idonsa ya ƙifta sannan ya dawo dai-dai, babu shiri ya miƙe tsaye, ya yi tsalle a kan ƙafarsa dan ya tabbatar.

Aiko yana gani haka ya fita da gudu, be yi birki a ko ina ba se tsakiyar ɗakin Fulani Sadiya, wadda take sallar tsakar dare.

Bata ko idar ba ta miƙe tsaye tana kallonsa, mamakinta ya kaa b’oyiwa a fuskarta, tsabar farin ciki haka ta rungume ɗan nata tana sakin kuka.

Kafin kuma ta sake shi ta yi sujjada tana godewa Allah, shima ganin hakan yasa ya yi tasa godiyar.

Allah kenan ƙadurin ala man yasha’u, daga ranar Fulani ta ƙudirce a ranta cewar ba zata sake jifan wani da sharri ba, ba zata ƙara shiga sabgar kowa ba a masarutar ma.

Dan taga ishara da ayara Allah, ta ƙara jaddada girman Allah a ranta, ta ji tsoron lahirarta ya ƙara kamata.

A wannan daren dai.

*****

<< Yadda Kaddara Ta So 46Yadda Kaddara Ta So 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×