Skip to content
Part 48 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Kurabi forest, Balu Thanda Village, Telangana state, South india.

“Oum nabishkar, oum nawaskamaha, oum jejebahawah, oum takdarsukaddam, naleyancifale…”

Wani mutumi dake zaune a gaban wanu kaskon wuta da ke ci ke karanto waɗanan ɗalasiman tsafin, gashin kansa ya taru da yawa an ɗaure shi da wasu zarririka, fatar jikinsa ta yi baƙiƙirin, ga wasu fararen layuka huɗu da aka ja daga gaban goshinsa, an ɗisa ja a tsakiyarsu.

Idonsa a rufe yake, amma bakinsa na furta waɗanan ɗalasiman, yayin da hannunsa na dama ke ɗebowa wani farin gari dake cikin wata kwalla yana zubawa a cikin wutar, a duk sanda ze zuba se wutar ta ƙara ta shi sama, jikinsa babu riga, hakan ya bayyana wasu tarin sarƙoƙi dake rataye a wuyansa, yanayin siffar jikinsa dai kamar mahaukaci.

“…Na miskar waskam, taren minde bani maham….”

Da wani irin sauri ya buɗe jajayen idanuwansa wanda suke kama da garwarwashin wuta. Firgici, razani, tashin hankali da bala’i sune kwance a kan fuskarsa.

Abinda ya haɗa da hannayensa tsawon shekaru talatin da ɗaya shi ne ya karye, wannan abun da ya haɗa shi da kansa dan cimma burinsa shi ne yau aka karya.

Cikin wata iriyar fusata ya miƙe tsaye ya nufi wani rami dake cikin kogon nasu, wata mata dake cikin siffar haske ta shiga binsa a baya, ƙafafunta basa tab’a ƙasa amna tafiya take, duk da ba cira ƙafafunta take ba.

“Ina kuma zaka je ?”

Muryar matar ta faɗi cikin harshen telugu, be ko kulata ba ya ci gaba da tafiya yana taka ciyayin dake ƙasan wajen, har ya kai gaban wata ƙasa da aka tarata gu ɗaya.

An barbaɗa wani jan gari a samanta, ga ƙwarangwal ɗin kan saa an aje a kai, sai wasu lemun tsami da aka kewaye tarin ƙasar da su.

Da sandar hannunsa ya yi nuni ga ramin, nan take kayan kai suke baje zuwa gefe, ramin ya shiga haƙa kansa da kansa, har ya kai ƙarshe.

Wata kwalba ce ta bayyana, wadda take a fashe, jinin dake ciki ya zube, ga wani baƙin hayaƙima da ya fito daga ciki.

Cike da takaici ya ɗaga kansa sama ya ƙwalla wata ƙarar hasalla, wadda ta haddasawa tsintsayen dake a kan bishiyoyin wajen kogon ta shi sama.

“Me ya faru Subhurmanyam?”

Wata murya ta tambaya da ga bayansu cikin harshen telugu, matar da mutumin suka juyo a tare suka kalli tsohon mutumin dake tsaye.

“Kace min idan har na binne wannan abun asirin ba ze tab’a karyewa ba, kace babu wanda ze iya temakonsa a hannu na, amma gashi yanzu asirin ya karye ”

Tsohon ya ɗan karkata kansa kaɗan ya leƙa cikin ramin.

Se kuma ya juya musu baya, sannan ya rufe idonsa, ya shiga karanto ɗalasiman tsafinsa.

“Nimratr, nakamji, biktahne, abhikiratre, ghumbans…..”

Yana yi yana motsa hannunsa a ƙasa.

Wani wawakeken rami ya buɗe, hoton Tafida da ke kwance a kan gadon ɗakinsa da Maryam kwance a jikinsa ya bayyana.

Tsohon ya zaro idonsa yana ja baya, ya kusa faɗuwa dan sai da Subhurmanyam ya kamo shi. Kansa ya leƙa shima yaga a binda mahaifin nasa ya kalla.

“Wacece ita?”

“Ka yi sake Subhu, ka yi babban sake…”

Baban ya faɗi yana girgiza kansa, Subhurmanyan ya juyo da shi suna fuskantar juna.

“Meke faruwa ?”.

“Ka binne asiri tsawon shekaru talatin da ɗoriya, baka waiwayarsa, sai ƙarfin da ka ke ƙara masa da ga gefe, amma baka sani ba har suka aura masa makarin baƙin ruhin da ke jikinsa, yanzu haka ya kusanci yarinyar, kuma daga lokacin asirin ya karye, kowani laifi akwai lokacin karb’ar hikuncinsa, haka kuma ko wani abu da aka binne a ƙarƙashin ƙasa wata rana dole se ya fito, akwai ranar ƙin dillanci Subhu, lokacin ya yi”

A fusace Suhbu ya juya.

“Kullum abinda nake faɗa muku kenan, na sha faɗa muku cewar wanna ba rayuwa ba ce me kyau, na ce daku ku ajeta a gefe amma bakwajina yanzu ga irinta nan…”

Wannan matar ta cikin siffar haske ta faɗa.

“Ya isa haka Mama, ki bari!”

Matar ta yi shiru tana ƙara ta shi sama kafin ta b’ace a iska.

“Ba ze iyu ba, sam ba zai iyu ba, ni bazan karb’i wani hukunci ba, bazan yarda ba…..”

“A’a Suhbu, lokaci ya ƙure”

Cikin fusata ya juyo ya shaƙi wuyan baban nasa da babu riga a jikinsa, jajayen idanuwa sa waje.

“Kai baka isa ka faɗa min abinda zan yi ba, ba zan tab’a faɗuwa ba, dole se na yi nasara”

Ya saki wuyan Manikandan ya na juyawa ya fuskanci wata ƙatuwar gunkiya dake kafe a kogon, hannayenta huɗu, ɗaya ta riƙe wuƙa, ɗayan kuma kan mutum ne, na ɗayan b’angaren kuma wata mashun tsini uku ne riƙe a ɗayan hannun, ɗayan hannun nata riƙe da wani kwano, ta ɗora ƙafarta ta hagu a kan wata gawa dake yashe a ƙasa babu kai, ga damisa tsaye a bayanta, ta zaro harshenta waje tare da zare ido.

“Na rantse da abar bauta Shakti, se na shayar da jininsa ga abin butata, dole ne ya mutu ”

“Subhu Eshaan ba shi ne matsala ba, wannan yarinyar da ke tare da shi ita ce matsala, dole se mun kawar da ita tukunna, domin idan har tana raye ba zamu iya kashe shi ba ” Cewar Manikandam mahaifin Subhu.

A karo na farko Subhu ya ɗago da kansa yana dariya, baƙaƙen haƙwaransa da basa samun arziƙin wanki suka bayyana.

“Zan kuwa kasheta, kuma shi da kansa zan saka ya kasheta”

“Tayaya kenan ?”

“Zuwa gobe ina so ka buɗe ƙofar kogon nan a nigeria, a cikin garin lagos, cikin Alaro city”…

Daga wannan maganar tunaninsa ya ɗauke shi ya yi cilli da shi shekaru arba’in baya…

*****

1983

Univesty of mumbai(Mahrashtra), india*.

“Roshni ga mohanthal ɗin”

Muryar wani saurayi ta faɗi cikin harshen hindi, yayin da yake miƙawa kyakyawar budurwar da yakira da Rashni wani abu a cikin ƙaramin flask ɗin ƙarfe.

Budurwar ta yi murmushi tana karb’a, kanta a ƙasa ta furta.

“Nagode”

Ci gaba ya yi da kallon kyakyawar fuskarta ba tare da yace komai ba, Allah ya sani ya na matuƙar san Roshni, sai dai kuma kamar wani abu na faɗa masa cewar ba ze sameta ba.

“Subhu!, Subhurmanyam!”

Cewar wasu samari na ƙwalo masa kira da ga bayasu, ya juya ya kalli samarin, sannan ya juyo ya kalli Roshni.

“To Roshni, zan ta fi, sai mun sake haɗuwa”

Kanta ta ɗaga tana kallonsa har ya juya.

*****

“Roshni waye wannan ?!”

Muryar Imran yayan Roshni ta faɗi cikin b’acin rai.

A razane Roshni da Subhu suka juya suka kalleshi, tsaye suke a ƙofar gidan su Roshni ɗin, yayin da Subhu ɗin ya kawo mata ziyara.

Cikin inda-inda tace.

“Na’am…umm…ummm..Subhu…Subhu…ne”

Ido waje Imran yake kallonsu.

“Subhu ? Dama wannan shine Subhu ɗin? Ba na raba ki da wannan Subhu ɗin ba ? Ban ce kada ki ƙara kula shi ba!”

Tsawar da yake mata a maganar yasa tuni ta fara hawaye, gaba ɗaya ta tsure, jikinta se rawa yake, ita har ga Allah tana san Subhu, kuma ita a ganinta zata iya sakawa ya musulunta idan har yana santa.

“Dan girman abun bauta Yaya ka yi haƙuri…”

“I min shiru!, ni b ani da wani abun bauta se Allah, kai baka san shi ba, dan haka kada ka ƙara haɗani da wani gunkinka”

Yana ƙarashewa ya janyo hannun Roshni ya figeta zuwa cikin gidan, duka a kan idon Subhu, yanda Roshni ɗin ke kuke ne ya ƙara ɗaga masa hankali.

*****

“Gata nan Maa, so take ta jamana abun kunya !”

Imran ya faɗi a sanda ya wurgar da Roshni ƙasa, wadda take ta gursheƙan kuka, Mahaifiyarsu Parvina ta miƙe daga kan kujerar da take ta kamo Roshni ɗin jikinta.

“Me ta yi Yaya ?”

Yayan Roshni ɗin Irfan, wanda yake a matsayin ƙanin Imran ya tambaya.

“Ka tambayeta ta baka amsa, tsabar yarinyar nan bata da mutunci tana so ta zubar mana da kimarmu da ɗan addinin hindu take soyyaya!”

Parvina ta saki Roshni dake gunjin kuka, Roshni ta kalleta tana girgiza mata kai.

“Wai wannan Subhu ɗin?, Guna(Abokinsa na makaranta) yace min babansa ma boka ne a ƙauyen balu thanda, tsafin da yake ne yasa aka koreshi da ga cikin garin, yanzu haka Guna ɗin yace min a cikin wani kogo yake”

Imran ya haɗe hannyensa biyu alamun roƙo.

“Na roƙeki Roshni da kada ki zubar mana da mutunci, ki duba kimar mahaifinmu da ke ƙarƙasbin ƙasa kada ki mana haka”

Roshni ta ja hanci.

“Wallahi Bhai (yaya) zan iya sauya shi, yana sona sosai, idan na ce ya musulunta ze musulunta wallahi”

Imran ya ɗauketa da marin da sai da yasa jini ya fito daga hancinta, shatin yatsunsa suka fito a kumatunta.

“Ke wata iriyar yarinya ce ?, a ina kika bar karatun da ake mana a masallaci ?, baki san cewa Allah baya karb’ar tuban da yake bana gaskiya ba ?, idan har danke zai musulunta to kisani tubansa be karb’u ba, kuma kin tab’a ganin inda ƴan kanhan suka musulunta, a tarihin india kaf akwai wanda ya tab’a faɗa miki cewar akwai musulmi ɗaya ɗan kanhan?!(wato ƙabilar su Subhu ɗin)”.

Roshni ta miƙe tsaye tana share hawaye, Allah yasani cewa tana san Subhu, amma soyyayar da take masa bazata sa ta rabu da ƴan uwanta ba, ƴan uwanta sun gama mata komai a rayuwa, sanda ta taso bata da uba, su suka zame mata uba, a koda yaushe burinsu su faranta mata.

“Roshni, babu ke babu Subhurmanyam da ga yau!”

A karo na farko tun bayan fara maganar Parvina ta sa baki. Roshni ta goge jinin da ya fito daga hancinta, sannan ta yi murmushi.

“Ina san Subhu, amma soyyayar da nake masa bata kai wadda nake muku ba, kunfi shi matsayi a zuciyata, na haƙura da Subhu har abada, ba zan ƙara kula shi ba, ku yafe min”

Ta ƙarashe tana sakin sabon kuka, tare da haɗe hannayenta biyu🙏.

Imran ya share ƴar guntuwar ƙwallar da ta zubo masa sannan ya ja ƙanwar tasa jikinsa ya rungume, Irfan ma ya zo ya kwanta a bayanta, hakama Mahaifiyar tasu da suke kira da Maa.

***

“Roshni!”

Muryar Subhu ta kira sunan Roshni a karo na barktai, amma taƙi kulashi, tun daga bakin gate ɗin makarantar ya hangota amma taƙi ta ko kalleshi.

Se ransa ya raya masa cewar wata ƙila fishi take, se kawai ya dunƙule hannunsa na dama sannan ya buɗe, wasu taurari masu basheƙi suka bayyana, suna tashi a iska tura mata su ya yi setin fuskarta.

Yana ci gaba da binta amma bata ko kalli taurarin ba.

Abun ya bashi tsoro, ba haka suka saba da ita ba, ya saba a duk sanda ze mata magana bata share shi, kuma ko da ta yi fishi da ga zarar ya mata ƴan tsafe-tsafensa da ya koya daga wajen mahaifinsa zata manta da fishin, ama yau ba haka ba ne.

Se kawai ya sha gabanata, Roshni ta dakata tana kallonsa, ji ta yi zuciyarta na shirin karyewa, kamar hawaye za su zubo mata. Gyara zaman mayafin chickankarin da ke kanta ta yi tana kawar da kai.

“Roshin me ya faru ?”

“Subhu stop it…  Kada ka ƙara min magana”

Daga haka ta rab’a shi ta ci gaba da tafiya, ƙara biyota ya yi ya sha gabanta.

“Amma me yasa ?, nasan cewa kina so na Roshni…”

“Ba na sanka Subhu, ba na…sanka, ka rabu da ni!”

Cikin ƙaraji ta furta maganar har ta ɗauki hankalin waɗan da ke kusa-kusa da su, kamar status haka Subhu ya ƙame, ya na kallon Roshni.

Rab’ashi ta kuma yi ta wuce abunta, Allah ne kaɗai yasan yanda wannan ƙaryar ta tab’a mata zuciya, ita kaɗai tasan abun da take ji, amma tun farko ita ta yaudari kanta da cewar zata canja shi, koma me ya faru da ita, ita ta janyowa kanta, hawaye ta share tana ci gaba da tafiyarta.

A lokacin tana shekarar ƙarshe, kuma har ta gama makarantar Subhu be ƙara kulata ba kamar yanda ta nema, har tama fara mantawa da shi.

Sai dai shi kuma be manta da ita ba, ko da yaushe yana sintiri a unguwarsu.

Har shekaru uku suka shuɗe, amma yana bibiyar ta, a koda yaushe da tunaninta yake kwana yake tashi.

Wata rana yazo unguwarsu da safe zai wuce ta k’ofar gidansu sai ya ga ana decorating gidan, hankalinsa ya tashi a sanda zuciyarsa ta raya masa kode auren Roshni za’ayi?.

Ɗaya da ga cikin masu aikin decorating gidan ne ya fito, Subhu ya dakatar da shi yana tambayarsa.

“Auren wa a ke a gidan nan ?”

Mutumin ya tsaya ya kallashe.

“Ƴar gidance mace, mema sunanta?… yauwwa Roshni”

Wani ƙaton bom ne ya tashi a zuciyarsa, gangar jikinsa ta shiga rawa, tunaninsa ya ɗauke. Bai san sanda ya nufi cikin gidan a fusace ba.

“Roshni!…Roshni!…Roshni!”

Kawai yake ta faɗi, bai ko damu da masu aikin gidan da ke binsa da kallo ba.

“Kai miye kazo kake haɗa mana hayaniya a gida ?”.

Imran ya faɗi a sanda ya fito, bayansa kuma Irfan ne sai mahaifiyar su Parvina.

“Ina Roshni?!”

A hasalle Imran ya ɗauke shi da mari, sannan ya ci kwalarsa ya hankaɗa shi baya.

“Kai waye da zaka zo kana nemanta?, ka fice ka bar mana gida!”

Ran Subhu ya b’aci, ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja, ya miƙe zaune sannan ya ɗa ga hannunsa setin wuyan Imran ya matse, Imran ya dafe wuyan nasa yana jin kamar hannune ya matse shi, Irfan da Maa suka yi kansa suna kiran sunansa sbd azabar da yake ji ko amsawa ma ya kasa.

“Roshni!, ki fito Roshni!…”

Ya ci gaha da kiran Roshni ba tare da ya saki wuyan Imran ba duk da be tab’a shi ba.

Roshni ɗin ce ta fito da ga cikin gidan, sanye take cikin farin chickankari.

Subhu na ganinta ya saki wuyan Imran ya yi gabanta da sauri, Imran ya faɗi ƙasa yana dafe wuya, Parvina da Irfan suka shiga jera masa sannu.

Subhu na kaiwa gaban Roshni ya shiga magana a gaggauce cikin fitar hayyaci.

“Roshni meke faru?!, me…me yasa zaki min…”

Wani Gigittaccen mari da ta ɗauke Subhu ɗin da shi yasa shi yin shiru, wata ƙwalla me ɗumi ce ta silalo da ga idonta, ita gaba ɗaya ma ta manta da labarinsa, ta karb’i sauyin da rayuwa ta zo mata da shi.

A kwanakin nan ta haɗu da wani baƙin fata ɗan ƙasar nigeria da ke zaune a unguwarsu, kuma ya bayyana mata cewar yana santa, sannan itama ta amince da shi, ta damƙa amanar soyyayarta gare shi, ta watsar da wani Subhu. So take ta gina sabuwar rayuwarta da masoyinta Auwal, wanda a yanzu yake daf da zama mijinta.

“Fita mana da ga gida”

Ta faɗi tana nuna masa hanya, da tsantsar mamaki yake kallonta, yayinda hannunsa na dama ke dafe a kan kuncinsa.

“Baka ji ba ne ?, na ce ka fitar mana daga gida”

Ya kasa magana ya kasa motsawa, ita kuma ganin haka yasa ta kama kwalar rigarsa ta ja shi zuwa waje, a bakin ƙofar gate ta hankaɗashi ya faɗi ƙasa. Juyowa ya yi yana kallonta daga zaunen da yake, kuma har lokacin hannunsa dafe da kuncinsa.

“Kada ka ƙara dawowa rayuwata, na manta da kai, kuma kai ma ina fatan zaka manta da ni”

Daga haka ta juya ta koma cikin gidan nasu, ya ci gaba da kallonta har ta ƙulewa ganinsa.

*****

A ranar ya koma garinsu wajen mahaifinsa, wanda ya kasance gawurttacen boka a ƙauyen balu thanda dake can yankin telugu.

Mahaifin Subhu ya kasance babban boka ne me yin baƙin tsafi, a sanda tsafinsa ya gawumta ne shugaban ƙauyen Balu thanda ya koreshi, dan yana zuwa maƙabartar musulmai yana haƙowa kabari ya yi tsafi da gawawwaki.

Bayan an koreshi sai ya koma cikin dajin kurabi, cikin wani kogo ya ci gaba da harkar tsafe-tsafensa. Mahaifiyar Subhu ta mutu sanda yana ƙarami, sbd soyyayar da Manikandan da matar tasa Kundali su ka yi kafin ta mutu yasa shi fasa binne gawarta ya yi tsafe-tsafensa ya mayar da ita fatalwa, ta zauna cikin wata gangar jiki me haske.

Kasan cewar yin karatun Subhu ɗin burin mahaifiyarsa ne yasa Manikandan ya tura shi kudancin india ya fara karatunsa har ya kai matakin jami’a.

*****

“Sun nuna maka halinsu ko ?”

Subhu ya ɗago da idonsa yana kallon mahaifin nasa.

“So nake na ɗau fansa”

Manikandan dake zaune a kan wani dutse ya miƙe tsaye ya isa gaban ɗan nasa.

“Kai ɗa na ne, zan ɗaukar maka fansa”

Subhu ya girgiza kansa.

“A’a, zan ɗauka da kaina, so nake naga bayan Roshni da mijin da zata aura”

“Kai Subhu!”

Muryar Kundali ta faɗi a sanda take sauƙowa ƙasa cikin suffar mace amma kuma haske ne kewaye da ita.

“Ban amince ba, ni bana so ka zama boka, so nake ka yi karatu”

“Ba zan koma rayuwar mutanen gari ba, fansa nake son ɗauka, bazan huta ba sai na ɗau fansata…”

<< Yadda Kaddara Ta So 47Yadda Kaddara Ta So 49 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×