Skip to content
Part 49 of 51 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

*****

Present day

House No.122, B3, Alaro city lekki, Lagos

08:50am

TAFIDA POV.

A hankali hannayensa suka ƙara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Maryam a karo na barkatai.

So yake ya ganta, dan da asuba da ya farka sam be ganta ba, yau tashi ya yi ya ji shi free, ya ji yanayin nasa kamar yanda yake ji sanda ze yi sallah, babu wannan nauyin da ke danne shi, ya ji yana iya controlling kansa, duk wata jijiya dake jikinsa ta ware, yana abu cikin ‘yancinsa.

Yanzun ma bata buɗe ƙofar ba, dan haka kawai ya yi amfani a ƙarfinsa ya buɗe ƙofar, sannan be jira komai ba yasa kai.

Maryam na ganinsa ta razana, Allah ya sani tana jin bugun ƙofar tasa,amma bazata iya buɗewa ba, ba zata iya buɗewa ta yarda su haɗa ido ba, dan bayan abun da ya faru jiya ji take bama zata ko iya tsayawa a gabansa ba.

Tunaninta ya dakata a sanda ya tsaya a gabanta, kanta a ƙasa tana shaƙar ƙamshin turarensa.

“Me na yi kuma ?”

Bata amsa shi ba kuma bata kalle shi ba. Yana iya jiyo sautin bugun zuciyarta, sai dai ba sosai ba, bazai ce me yasa ba, ammam baya jin sautin sosai kamar da. Sai de kuma sautin yana fita cike da tsoro, tsoron da sam bai ji shi ba jiya, jiyan da yake kuka yana faɗamata ta rabu da shi.

“Ko jikin naki ne?”

Da sauri ta girgiza masa kai tana ja da baya. Amma se ya saka hannunsa ya fincikota ta dawo jikinsa, Maryam ta rintse idonta tana kawar da kanga gefe.

“Wai menene ?”

Tsoro da kunya sun hanata magana, a jiyan kawai wani shakkarsa da kwarjininsa ne suka ƙara cikata. Fuskarsa ya kai cikin wuyanta sannan yace.

“Dan Allah kice wani abu, idan ba ki yi magana ba bazan sakeki ba”

“Ina kwana”

Ta furta da sauri tana tureshi ganin kamar yana shirin yin nisa, sai ta ga ya yi murmushi.

A lokacin ne fa lura da raunikan dake fuskarsa, wanda tana da tabbacin baƙin ruhin da ya tashi jiya ne ya haddasa masa.

A ruɗe ta ƙarsa gabansa tana dudduba fuskar tasa.

“Me…me yasa be haɗe ba?”

Yana kallonta yace.

“Nima na yi ƙoƙarin haɗe su, amma na gaza”

Kafin ya ƙara tallafo fuskarta, kuma be jira komai ba ya haɗe bakinsa da nata.

Ba shiri Maryam ta ƙanƙame rigarsa ta baya, tana jin kamar wani abu na janta zuwa ƙasa duk da yana riƙe da ita.

Jin yanda harshensa ke motsi acikin bakinta ne yasa ta saka gaba ɗaya ƙarfinta tafice da ga hannunsa.

“Na….n…na gama..a..ab.abinci”

Shima juyawa ya yi yana shafa sumarsa, kafin yace.

“Na makara, sai dai ko idan na dawo”

Sai kuma ya juyo ya dawo inada take, a tsorace Maryam ke kallonsa, ji tayi ya ɗora hannayensa biyu a kan waist ɗinta,sannan ya yi pecking kanta.

“Sena dawo”

Da ƙyar ta iya gyaɗa masa kai, kafin ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, hannayenta suka kewayo ta bayansa, shima ya ƙara matseta a jikinsa, ya kuma pecking kanta, ya saketa kafin ya juya ya fita.

Kuma yana fita ta daddafa ta koma kan gado ta zauna, yau bama za ta yi aikin gidan ba, abincin ma dan shi ta yi, dan ita baza ta iya ci ba.

Ga jikinta da ta ji ya ɗauki zafi, ga ciwon da gab’ob’inta ke mata, dan haka kawai se tabja hijabinta ta saka, sannan ta kwanta, ta dukunƙuna a bargo, bata jima ba kuwa bacci ya ɗauketa.

*11:30am*

MARYAM POV.

Fitowarta kenan da ga bayi taga wata guguwa na turniƙe ɗakin, ɗakin ya yi duhu duk da bawai dare ne ba, bata iya ganin komai a ɗakin sai iskar da ta ci gaba da kaɗawa a ɗakin kamar zata ɗauketa.

Hannunta ta kai ta kare idonta tana karonto addu’a a ranta, wani jan haske ya ci gaba da mamaye ɗakin, ga guguwar dake ƙara yawa kamar ana ingizo ta.

Can kuma kamar ɗaukewar wutar nepa, ta ji ɗip!, iskar ta tsaya, a hankali ba ta tare da ta fasa karanto addu’o’in ba ta sauƙe hannunta.

Gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa, sbd wani mutum da ta gani a gabanta, gashin kansa ya taru da yawa an ɗaure shi da wasu zarririka, fatar jikinsa ta yi baƙiƙirin alamun dauɗa, ga wasu fararen layuka huɗu da aka ja daga gaban goshinsa, an ɗisa ja a tsakiyarsu.

Babu riga a jikinsa sai wani baƙin yadi da ya faffarke ɗaure a ƙugunsa, ƙafafunsa babu takalmi, ga wata sarƙa ta ƙwarangwal rataye a wuyansa, hannunsa na dama riƙe da wata sanda.

Ba suffarsa bace kawai abun tsoron, hatta da kallon da yake mata ma abun tsoro ne. Bayansa ta kalla inda taga wani wawaken rami a wurin, wanda yake nuna cikin wani kogo.

Waye shi? daga ina ya zo ?, me ya ke buƙata a wurinta?.

“Kin gama yawo Maryam ”

Mamaki ya kama Maryam, sunanta ya kira, kuma maganar cikin harshen turanci ya yi, to amma ba wannan ba, cewa ya yi wai ta gama yawo…….

TAFIDA POV.

Ba zai iya kwatanta yanayin da yake ciki ba yau, rabonsa da jin kansa a yanayi irin wannan tun yana ƙarami, a sanda iyayensa suka rasu.

Jinsa yake cikin nishaɗi, kome ze yi yanayi ne bisa ikon kansa, wannan nauyin dake kansa babu shi, wannan igiyoyin da yake jin suna ɗaure shi sun kunce.

Koma waye ya ganshi yau ya san cewa yana cikin farin ciki. Sai Allah-Allah yake dan lokacin tashi a aiki ya yi, saboda ya koma yaje ya ga abarsan, matarsa, farin cikinsa, jigon rayuwarsa a yanzu. Da wannan tunanin har lokacin tashin ya yi, ya haɗa nasa ya nasa ya kamo hanyar gida.

A kai-a kai yake murmushi har ya kawo Alaro city.

Sai dai me ?, yana zuwa ƙofar shiga gidan nasa ya ji gabansa ya faɗi, baya ce ga dalili ba, amma haka kawai se ya samu kansa da jin tsoron shiga gidan, kamar kada ya shiga, dan abinda ze gani a gidan ze iya cutar da shi.

Sai de zuciyarsa dake cike da ɗaukin ganin Maryam ta bashi ƙwarin guwar shiga cikin gidan, hannunsa ya kai ya buɗe ƙofar shiga falon.

Kamar mara lafiya haka ya shiga taku a cikin gidan, i yanzu yasan tana kitchen, dan haka kai tsaye ya nufi can, ammam babu ita bare me kamarta. Haka ya haɗiye wani abu da ba zai ce menene ba, ya fita ta ƙofar baya ya duba garden, nan ɗin ma bata nan.

Ya hau saman gidan, still nan dinma be ganta ba. Se abun ya soma bashi tsoro, dan da alama ma gidan kamar ba’a gyara shi ba yau, dan haka da gudu ya sauƙo ƙasa ya nifi ɗakinta. Sai dr yana saka ƙafarsa a ɗakin ya shiga jin wata murya a kansa na magana.

“Idan har kana so ka ceceta dole kazo, kazo!, ka zo!, ka zo nan matsoraci…”

Kansa ya dafe da duka hannayensa biyu, be san sanda ya durƙushe aƙasa ba. Nan take ƙwayar idonsa ta rikiɗa zuwa ja, wannan fiƙoƙin suka sauƙo masa, ya ɗago da kansa cikin fusata yana kallon balcony, kamar da a kace masa me maganar yana wurin.

“Hmmm, ni ba matsoraci ba ne,zan iya ceto ta, ina kake so nazo, faɗamini inda zan zo”

Har wani huci yake wurin furta hakan, jikinsa na karkarwa.

“Kurabi forest”

Wannan muryar ta faɗi a cikin kan nasa.

Tafida ya ɗaga hannunsa sama yadunƙule shi tare da buga ƙasa.

“Gani nan zuwa”

“To taho mana sakarai”

Kurabi forest, Balu Thanda Village, Telangana state, South india

MARYAM POV.

Zaune take a cikin wasu ƙaraguna da suka kewayeta, a taƙaice de zata iya kiran wurin da kurkuku. Kuka take a hankali sannan tana karanto addu’a.

Tun bayan da mutumin nan yace ta gama yawo bata sake fahimtar komai ba, bata ma san ina kanta ya shiga ba, kawai ta farka ne taganta kulle cikin ƙarafunan wurin.

A halin da take ciki bata jin akwai wani abu da zata iya, babu abinda take ganin ze iya cetonta se ayar Allah, dan haka ta shiga karantota cikin ranta.

Tun ɗazu take ganin wulƙawar wani haske, daga ta ɗanyi karatu sai ta ga ya wunlga, idan ta yi shiru se ta ga ya tsaya.

Dakatawa ta yi da karatun dan tanasan sanin mene hasken. A hankali a hankali suffar wata mata ke bayyana a gabanta cikin suffar haske, kallo ɗaya zaka mata kasan cewa ba’indiyace, dan hatta kayan jikinta ma sari ne.

Kallon Maryam take da tausayawa, har ta iso jikin ƙarfen da Maryam ke kulle ciki.

Ita bata jin hausa, kuma tana da tabbacin Maryam ɗin ma ba jin telugu take ba, dan baka ta yi amfani da tsafinta ta sauya harashe zuwa hausa.

“Magana nake so na miki, amma wannan abun da kike faɗa ya kasa bari na na tsaya, jin sauƙarsa nake kamar ruwan zafi a jikina”

Maryam ta haɗiye yawu ta kuma haɗiyewa, ance wai na zaune be ga gari ba, kuma wai idan da ranka kasha kallo, yaude duk mugun tsoranta se gata a gaban aljanu, dan wannan ba mutun ba ce.

“Ki yi haƙuri kin ji, na san duk yanda a kayi mijinki na nan zuwa, kuma da yardar abun bauta ƙarfin jikinsa se ya yi nasara a kan mijina da ɗana”

Maryam ta kasa cewa komai kawai tana kallon matar, to me take nufi da mijinta nan nan zuwa ?, Tafida ne zai zo ?, kode ƙarya kawai take mata ?, to ta ina ma zai zo ɗin?, ya san inda take ne ?.

Matar ta buɗe tafukan hannunta, nan take wani kwando ya bayyana, wanda yake cike da kayan marmari, a hankali ta tura shi zuwa cikin ƙarfen da Maryam ta ke ciki, kwandon ya sauƙa a gaban Maryam.

“Sunana Kundali, ni ce babar Subhu, ban sani ba ko zaki iya cin wannan, ban san menene abincin garin ku ba, kuma ina da yaƙinin balalle ke ki iya cin abincin mutanen mu ba”

Subhu?, waye Subhu ɗin?, kovde shine wanda ya kawota nan ?, to wai ma ita a ina take ?, me yasa ma shi Subhu ɗin zai kawota nan?, anya ma kuwa zata iya yarda da wannan matar dake gabanta ?.

“Kinga yarinya, ni uwace, ba zan tab’a iya cutar da ke ba, za ki iya yarda da ni….”

“Mama miye haka ?!”

Muryar Subhu ta faɗi a bayansu cikin harshen telugu, Kundali ta ta shi sama tana faɗin.

“Se a zo a aje yafinyar mutane ba a bata abinci ba, shi yasa na kawo mata”

Be ko kula ta ba, ya nufi inda Maryam take, ƙofar wurin ya buɗe sannan ya shiga, ya damƙo kanta da ko ɗankwali babu ya shiga janta zuwa waje.

Tsabar wani wari da hamami da ke tashi a jikinsa Maryam ta ji kamar za ta yi amai.

Janta yaci gaba da yi har zuwa tsakiyar kogon nasu,sannan ya yasar da ita a wurin, ta faɗi har tana fasa goshinta.

Cikin jin raɗaɗi da azaba ta miƙe zaune hannunta na dama dafe da goshinta, ta shiga ƙarewa kogon kallo, akwai haske sosai a wurin, kuma bawai hasken rana ba ne ko na ƙwan lantarki, hasken kaskon wuta ne da ke maƙale a ko wata kusurwa ta kogon.

“What do you want ?”

Ta tambaya da turanci, dan a ganinta ba hausa yake ji ba ba bare ta masa,turancin ma tana mamakin ya akayi ya iya.

Subhu da ke haɗa wani gari ya juyo ya kalleta.

“Fansa, fansa nake san ɗauka!”

Maryam ta ci gaba da kallonsa tana mamakin ƙazantarsa, dan ko wace gab’a ta jikinsa kukan dauɗa take, ga wasu uban faratu da ya tara, ga gemunsa da ya taru ya cukurkuɗe dan rashin gyara.

“A kan wa zaka ɗauki fansar ?”

“A kan Eshaan dama duk wanda ya rab’i Roshni”

Sunan Eshaan ta ji ya kira, haɗi da suna mahaifiyar Eshaan ɗin, wato Roshni, amma miye haɗinsa da su?.

“Me Eshaan ya maka ?“

Ta tambaya a dake, dan yanzu bata ji akwai wani abu da zata gani ya bata tsoro kuma.

Sai Subhu ya zauna a kan wata kujera, sannan ya kira sunan babansa.

Maryam bama ta lura da akwai wani mutum a kogon ba bayan su, sai ta ga ɗan dattijon ya miƙe hannunsa riƙe da wani kwano ya nufi Subhu ɗin.

“Roshni ta lalata rayuwata, na sota kamar raina,amma da ga bisani sai tace bata sona, ba zata iya rayuwa da ni ba, tace na fita sabgarta, ta yi min korar wulaƙanci, ni kuma raina ya b’aci, dan baka na dawo garinmu wurin babana, ya koya min tsafi na tsawon shekaru bakwai, a lokacin Roshni ta yi aure harda ɗa. Ni kuma a lokacin zuciyata banda tafarfasar ɗaukar fansa babu abinda take, dan haka na shirya kasheta ita da mijin nata dama ɗan nata…..”

Se ya yi shiru yana watsa wannan farin garin a cikin wutar gabansa, Maryam data fara fahimtar inda labarin ya dosa ta ƙure shi da ido.

“A lokacin tacje garin su mijinta, suna tafiya ita da shi a cikin mota, ina da ga nan na aika baƙaƙen aljannu suka kifar da motar tasu, har suka mutu, mutuwa irin wadda babu wanda zai ma iya gane kamaninsu. Game da ɗanta kuma na so na halaka shi shi ma, amma kuma Babana ya sanarmin da cewa ba zan iya kasheshi ba. Dan haka na ya ke shawarar lalata rayuwarsa, na yanke shawarar bashi mutuwa ba tare da an binne shi ba, na yanke shawarar saka shi a halin da kowa nasa zai guje shi….”

Ya kuma yin shiru yana watsa wani jan gari yanzu kuma. Sannan yaci gaba.

“Kinsan shekaru nawa na ɗauka kafin na aiwatar da hakan ?”

Maryam da take jin kamar ta tashi ta shaƙe masa wuya ta ci gaba da kallonsa ba tare da ko tari ba ta masa ba, ashe dama duk tsawon shekarun nan shi ne yake azabtar mata da miji ?, shi ne yake aikata duk abinda yake damun mijinta ?.

“Shekara ɗaya na ɗauka ina aiki a kansa, na yanko maƙogwaron zaki, na ciro zuciyar kura, na haɗo da haƙwaran damisa, na shekara ina haɗe su gu ɗaya dan su bani abinda nake so, kafin na samu suka zama baƙin ruhi, kin san menene sunan tsafin ?, baƙin tsafin Diggam, na saka laƙanin a jikin wani baƙin aljani, sannan na binne sauran a cikin wancan ramin….”

Maryam ta kalli ramin da yake nuna nata.

“Wannan baƙin aljanin da na saka masa wannan laƙanin na tura shi jikin Eshaan ɗan gidan masoyiyata ta da…”

Sai ya yi murmushi.

“Na mayar da shi wata hallitar da ban, na banbanta shi da jinsin mutane, na nisanta shi da zama cikin ‘yan uwansa. Bayan wasu satika kuma se ‘yan uwansa suka fara masa magani, baƙin ruhin da na tura jikinsa ya fara rauni…”

Yanzu kam dariya ya yi yana ɗaga kansa sama. Har yanzu Maryam kallonsa take, mamaki take shin dama akwai ɗan adam irin wannan ?, bata tab’a ji ba ko a mafarki, ko a labarai bata tab’a jin ƙiyyaya irin wannan ba.

“Ni kuma da na tashi se na tura wani aljanin jikinsa, wanda yake tare da shi a koda yaushe, idan har aka bashi magani zai sakawa wanda ya bayar ɗin ciwo, koda tsafi za’a masa ba zai tab’a cinsa ba, shi kuma ya hana shi yin karatun addininku, dan yana saka ɗayan baƙin ruhin rauni,ya kuma hana shi komai na karatun addininsa, yake saka masa ciwon kai a duk sanda zai ko ji karatun da ga bakin wani.”

Ya watsa wani abu me ruwa kamar mai a cikin wutar, sannan ya kalli Maryam.

“Ina so rayuwarsa ta lalace fiye da haka, shi yasa na bashi ƙarfin tsafi, domin duk wanda zai ganshi yana tsafi zai ɗauka cewa boka ne, dan haka zai guje shi.”

Faɗowar wani abu ce ta katse maganar tasa, a tare suka kalli inda ƙarar ta sauƙa shida Maryam da Manikandan.

<< Yadda Kaddara Ta So 48Yadda Kaddara Ta So 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×