Ya dinga wuce falukan dake turakar Fulani kafin ya iso falo na biyun karshe, abinda ya gani ya tayar masa da hankali, jiki a sa6ule yayi sallama, Fulani dake risgar kuka ta ɗago da kai ta kalli inda yake, hakama me martaba, zuwa lokacin nadra ta bar falon dan bazata iya jurawa ganin mahaifiyar tata na kuka ba. Kansa a kasa ya ƙaraso cikin parlon ya zauna a kasa kusa da kafar mai martaba, yana duƙar da kansa, me martaba kuwa tunda ya shigo yake ta binsa da kallo har ya zauna a kusa da ƙafar tasa, duk da. . .