Skip to content
Part 6 of 33 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Masarautar Hadejia

Da misalin ƙarfe biyu da rabi na rana.

Ɗan Masani ne zaune a kan lallausan carpet ɗin dake malale a parlo na biyu wanda yake bangaren Fulani, hannunsa na dama riƙe da wani makeken littafi, wanda sarkin haɗejia Sule Karo ya rubuta da kansa, kasan cewar mutanen da sun riƙi tsafi da duba a matsayin al’ada hakan yasa ko bayan zuwan musulunci basu watsar da wasu al’adun nasu ba.

Sai bayan zuwan Shaihu Usman ɗan Fodio, to hakama tsohon sarkin haɗejia Sule Karo a nasa zamanin an faɗa masa abunda zai faru da wani daga cikin ahalinsa da zasu zo a gaba, kuma tun a lokacin yasa aka masa bincike aka gano maganin matsalar.

Tun a lokacin da Tafida ke ƙarami alamomun baƙin ruhin dake jikinsa suka fara bayyana, kuma tun a lokacin ne sarki ya gano cewa tabbas shine wanda ɗaya daga cikin iyayensu na da yayi rubutu akai.

Sannan tun a lokacin suka duba maganin matsalar, kuma sun gano cewar aura masa wata yarinya da za’ayi shine maganin wannan baƙin ruhin, a lokacin sam bai kai aure ba, dan haka sukayi haƙuri suka duƙufa akan masa magunguna da addu’o’i.

Kuma sai aka dace, ya zamana sam abun baya tashi sai idan ransa ne ya baci, amma a kwanakin nan abun ya ta’azzara, hakan yasa Fulani taji ba zata iya jurewa ba, dolene ta nemi Ɗan Masani, wanda ya kasance shine Masanin Tarihin fada.

Daga wata kujera dake nesa da ɗan Masani kuma Fulani Khadija ce zaune, cikin zama irin na ƙasaita da mulki, kallon Ɗan Masani kawai take, tana jiran ya buɗe littafin ya faɗa mata menene mafita.

Ɗan Masani yayi gyaran murya, yana shimfiɗe katoton littafin a kan carpet ɗin, sannan ya shiga buɗewa, yana wuce tarihin abubuwa masu muhimanci da suka faru a masarautar haɗejia a wancan zamani, Da haka har ya ƙaraso shafin da bayanai akan bakin ruhi yake.

“Na samoshi ranki ya daɗe”

Fulani tayi a jiyar zuciya a ranta, a fili kuma sai ta gyara zamanta, alamun ina jinka.

“Kamar yanda muka faɗi a wancan lokacin yanzu ɗinma hakane, wannan yarinyar data dace ya kamata a nemo a haɗashi aure da ita, ita wannan yarinyar Allah ya temakeki itace makarin bakin ruhin dake jikinsa, daga zarar sunyi aure, ya samu ya kusanceta koda sau ɗayane, to baƙin ruhin zai fara rauni, a hankali a hankali kuma zai bar jikinsa”

Fulani ta ƙara numfasawa a ranta, a fili kuwa ko gezau batayi ba, ta kafe Ɗan Masani da idanuwanta tana nazarin kalaman dayake faɗa mata, kafin muryarta ta fito cikin izza da kasaita.

“Taya zamu iya gane yarinyar data dace ?”

“Allah ya temakeki ai kawai alamomin yarinyar a nan”

Ya faɗi yana ƙara ƙanƙan da kai, kuma Fulani batace masa komai ba, dan haka yaci gaba.

“Alamomin sune, tanada tawadar Allah me faɗi a wuyanta, kuma shekarunta basu wuce 22 ba, a sanda za’ayi auren kenan, sannan kuma akwai wata tawadar Allar a gefen gashinta, sai sirin farin gashin guda daya a a kanta daga gaba”

Yanxuma Fulani batace komai ba, taya za’ayi su iya samo yarinya me waɗannan siffofin a faɗin garin haɗejia, bama haɗejia kawai ba a duniya ma baki ɗaya, shin wanyama kuwa suna kan daidai ?, ganin sun amince da abinda yake gaibu, Dan wannan gaibu ne, to yaya zasuyi ?, Idan aka bashi addu’a matsala, idan aka barshi babu addu’a ma matsala, a ganinta wannan ita kaɗaice mafita.

*****

“Jakadiya Babba Ɗan Masani ya bani alamomin yarinyar da za’a aurawa Tafida, saide ina ganin kamar bazamu sameta ba”

Muryar Fulani khadija ce ke koro wannan jawabi, bayan ta sallami Ɗan Masani, Jakadiya Babba ta ƙara dunƙule hannunta sama tana ƙara duƙar da kanta ƙasa.

“Allah ya ƙara miki yawan rai, uwar jigiyata ai wannan me sauƙi ne”

“A’a Jakadiya, wannan abun bame sauƙi bane, a ina zamu samu Yarinyar ?, kawai dan munsan cewa akwai tawadar Allah a wuyanta da kuma gashinta sai shekarunta, farin gashin dake kanta sai mu samota ?”

“Ba haka nake nufiba uwar gijiyata, insha allah zamu samota da yardar Allah, Allah ya ƙara miki girma, Fulani matar sarki Abdullahi Abubakar Masu, uwar gimbiya Nadra da Tafida”

Fulani ta kawar da kanta tana meda dubanta ga tv, abun duniya yabi ya isheta.

“Yashi ki tafi na sallameki”

“Godiya nake matar Saifullahi takobin allah”

Jakadiya ta faɗi tana miƙewa haɗi da ci gaba da korowa Fulani kirari. Tana fitowa bangarensu na bayi ta nufa domin ta shirya, dan yau za’a gabatar da bikin kamu na gimbiya Amina, kuma dole dasu za’ayi komai.

Maryam Pov.

Cikin nutsuwarta data zamemata jiki take tafiya, kuma kamar kullum sanye take da hijabi har ƙasa, kuma fuskarta babu kwalliya dan dama can batayi, hannunta na dama riƙeda baƙar ledar data siyawa irfan, ɗan gidan anti fati karas.

Tris taja ta tsaya, sbd kofar gidan Tafida da take iya hangowa, kuma ga wasu mutane a ƙofar gidan, hakan ke nuna mata cewar yana gidan, sa6anin da da bazaka tadda kowa a ƙofar gidan ba sai masu gadu.

Kuma ganin mutanen ya nuna mata cewar an sauƙo daga kilisa. A da tana san ta wuce ta ƙofar gidan kodan ta samu ta kalli kyakyawan gidan dayafi kowanne kyau a cikin jerin gidajen dake layin, amma yau sai taji bata san wucewa ta ƙofar gidan, dan haka ta juya ta shiga wani layi tayi wani uban zagaye kafin ta samu ta ƙaraso gidan Anti Fati, duk tabi ta gaji, kuma dama daga gidan Tafidan zuwa gidan Anti Fatin akwai nisa amma kuma zagayen da tayi shine ya ƙara mata nisan tafiyar tata.

Da sallama a bakinta ta shiga gidan, babu kowa a tsakar gidan dan haka ta shiga cikin parlon, inda muryar Anti Fati take fitowa cikin amsa sallamar da tayi, a parlon kuwa ta sameta zaune tana kwalliya.

Itama kujera ta samu ta zauna tana gaisheda Anti Fatin, sai kuma tabi parlon da kallo tana mamakin sanda aka sauya kujerun parlon, koda yake ta jima bata zo gidan ba, kuma dama mijin Anti Fatin yanada rufin asirinsa dan yaron Kawu Usman ne, kuma shine ya haɗa su auren, hatta da kayan ɗaki dana kitchen shine yayi mata.

“Anti Fati ina Luluwa?”

Tana nufin ɗan anti fatin, dan haka suke kiransa a gidansu, sbd yaron yanada jiki ga kuma kumatu, shine Hussain ya saka masa Lulu suma kuma suke kiransa da Lulun.

“Yana ɗaki yana min ta’adin daya saba”

Maryam tana dariya ta miƙe ta shiga ɗakin aiko a bakin gado ta sameshi yana wargaza kayan da suke cikin wani kwando

“Ƙaunar Anti Maryam”

Ta kirashi da sunan da ita kaɗai take kiransa dashi, yaron ɗan wata tara ya jiyo ya kalleta sai kuma ya 6an gale baki yana dariya, Maryam ta ƙarasa inda yake ta saka hannu ta ɗaukeshi.

Wani ikon sai Allah, idan ka kallesu tare cewa zakayi Maryam ce ta kawo shi duniya, komai na fuskarta ya d’auko, hatta da tawadar Allahn dake goshinta shima yanada akwai.

Parlon suka dawo suka zauna, sai ta iske Anti Fati ta gama kwalliayar, tana yafa mayafi.

“Kije ki zubo abinci a kitchen kici sai mu tafi”

“A’a saida naci abinci sannan na taho, idan kin gama kawai muje”

Maryam ta faɗi tana zama a kan kujera, yayinda take bawa imran karas ɗin data siyo masa, galala Anti Fati take kallon Maryam ɗin da bata ma san tanayi ba.

“A haka zamu tafi?”

ta faɗi tana nuna Maryam ɗin, Maryam ta kalli jikinta da kyau.

“Eh mana…”

Tun kafin ta karasa ta katseta da cewar.

“Muje ina a hakan ?, kinsan kuwa inda zamuje Maryam ?”

Ta faɗi cikin kama baki, kuma bata jira cewar Maryam ɗin ba tace.

“Bikin ƴar gidan sarki fa za muje”

Girar Maryam ta haɗe waje guda alamun kokwanto.

“Ba haka kikace bikin dangin mijinki bane ?”

“Eh mana, ai mijin da zai auri ƴar sarkin shine dan uwan su habib ɗin”

Maryam ta juyar da kai gefe, tasan yanzu Anti Fati zata sakata ta cire hijabin jikinta, kuma tunanin nata bai je ko ina ba, abinda take saƙawa a ranta ya faru.

“Bari na kawo miki gyale ki saka”

Ta faɗi tana shiga dakinta, Maryam ta ta6e baki, tana cigaba da karyawa imran karas ɗin da baya iya cinsa duka.

Jim kaɗan Anti Fati ta fito ta miƙa mata wani baƙin babban gyale, babu yanda zatayi haka ta kar6a ta mike tsaye ta cire hijabin jikinta tana ninkewa, Anti Fati na cewa.

“Maca har mace, diri har diri amma kina boye shi cikin hijabi”

 Ita dai Maryam bata ce mata komai ba, ta yafa mayafin.

“Muje ?”

Anti Fati ta dafe goshi cike da ta kaicin kanwar tata.

“A kullum ana miki kallon wayyayya amma sam Maryam baki waye ba, dan Allah kalli daurin dankwalin kanki, kalli fuskar ki”

Maryam ta kawar da kai

“Ke idan bakya san kiyi aure to mu muna so, kullum ke cikin boye jiki fuska a koɗe kamar matar takaba ta ina wani zai gani yace yana so, zauna nayi miki kwalliya”.

Maryam bata iya musu ba, dan haka ta zauna.

“Amma dan allah kada kimin da yawa”

Anti Fati ta zauna ta shafa mata hoda, ta bata kwalli ta saka da kanta, ta saka mata lip gloss, sannan ta daura mata dankwalli, kasan cewar atamfar tata me ɗan kyauce bataji jiki ba yasa Anti Fatin bata nemi data sauyata ba.

“Haba dan Allah, kalli kanki kiga”

Maryam ta dauki mudubi tana duban fuskarta, tunda ta taso tayi wayo bata taba kwalliya a fuskarta ba, koda kwalli bata ta6a sakawa ba, amma yau gashi itace harda hoda, kuma ba zatayiwa kanta ƙarya ba, yau tayi kyau.

“Ki gafa yadda kika yi kyau”

Wannan kalma ta kyau bata taba dosar inda take ba, babu wanda ya taba ce mata tana da kyau, dan ba kwalliya take ba, bare ace tayi kyau, karewarta ma Hussain cewa yake da a ace bata da hasken fata da ba zata ganu ba.

<< Yadda Kaddara Ta So 5Yadda Kaddara Ta So 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×