Maryam tana fita daga wajen ta samu wani wari can nesa da mutane, kusa da inda ake ajebmotoci, ta zauna a kan wani dakali, tana ta mitar ƙaran kiɗan da yayi yawa a ciki, Imran ta zaunar gefe tareda kunna masa cartoon a waya, sai kuma ta ɗago tanata bin motocin dake parker kusa da inda take da kallo, wato su masu kuɗin nan basu da wata matsala a rayuwa, ta faɗi hakan a ranta.
Tafida ya fito daga cikin wajen taron, sbd ya gaji da mitar da ake masa, ga jikinsa dake ɗaukar zafi, kuma kansa. . .