Skip to content
Part 9 of 40 in the Series Yadda Kaddara Ta So by Salma Ahmad Isah

Idansa ne ya kai kan Galadima wanda yake tafe Dogarai na take masa baya, kallo ɗaya ya masa ya sheƙar, banda shi Galadima ɗin da bai ko kalli Tafidan ba, dan wata iriyar tsanarsa yake kamar idan aka bashi wuƙa yau akace ya kasheshi zai iya, bayasan Tafida ko kaɗan.

Babban abun haushin ma Tafid shine ya san sirrinsa da babu wanda ya sani kaf duniya, ciki kuwa harda Fulani Sadiya, haka suka zo suka wuce opposite, amma babu wanda yakula wani.

Tafida na shiga turakar Fulani, a parlo na uku ya samu Nadra tana kallo, gaishe da shi tayi sannan ta bishi da ƙorafin ƙin tsayawa ya gaisa da ƙawarta da beyi ba, daga nan tai mishi tayin abinci, kuma bai ƙiba amma sai yace bari yaje yayi wanka.

Bayan yaje yayi wankan ya sauya kaya zuwa farar T-shirt da baƙin jogger pants, ya saka baƙaƙen slide sandales a ƙafarsa, ya riƙo wayarsa ɗaya ya fito.

Yana wannan takun nasa na izza da jan aji, har ya ƙaraso parlo na ukun, dan shi bangarensa na parlo na huɗu, yayinda ɗakunan Fulani da na Nadra yake parlo wajen na shida, kuma akwai wani dogon corridor dake haɗa ɗakunan nasu.

Abincin ta zuba masa, shinkafa ce fara wadda aka dafata da green beans da kuma carrot, sai kuma miyar kifi da daffafen kwai, ta zuba masa pineapple juice ɗin da ke aje a wajen, ya kar’ba yana ci yana ɗan danna wayarsa.

Itama sai ta koma gefe tana kallo, bai tambayeta ina Fulani ba, dan yasan tunda baiganta ba to yau itace keda turaka, ya kai hannu ya tura sumar kansa baya, wadda daga ƙasa wajen fade ɗin ta dan taru, alamar yana bukatar aski, gashi kuma a haɗejia babu me iya askin sumarsa, ko a lagos ɗinma yana manege ne kawai.

Babu inda ake masa aski me kyau, irin wanda yake so kamar a india, idan de yaje shi to dama sumarsa ƙalau zai dawo da ita, kuma cio8 kalar askin da yake SO.

“Canza mana wanna tashar mana”

Nadra ta juyo ta kalleshi kamar zata fasa ihu, dan serice ɗin da take so ake haskawa a mbc bollywood, yau suna hidimar biki bata samu ta kalla ba, shine yanzu take ganin maimaici.

“Ayya mana hamma, ban gani bafa da yamma”, “shikenan ci gaba dakallon ki”

Ya faɗi yana ci gaba da cin abincinsa, dan dama kallon ba damunsa yayi ba, kawaide harufan larabcin ne suka ishi kunnensa.

“Lokaci na ƙurewa kije ki kwanta”

Muryarsa ta fito bayan wani lokaci

“Bari to a gama.”

Wani kallo da ya mata ne yasa ta haɗiye maganar a cikinta, gashi ya kafeta da shuɗayen idonsa, dan haka ƙafarta a likafa ta ɗauki wayarta zata tafi ɗaki, sai ta tsinkayi muryarsa.

“Ki dawo ki kashe kallon”

Tafida bawai a fuskarsa yake da kwarjini ba kawai, hatta da muryarsa kwarjini gareta, da wuya yayi maka magana ka musa masa, dan haka ta dawo ta kashe sannan ta nufi ɗakinta tana masa mu kwana lafiya.

“Sleep tight”

Daga haka shima ya miƙe yabi bayanta, ta wuce parlon ta shiga na gabansa, yayinda shi kuma ya buɗe ɗaya daga cikin ƙofofin dake parlon, wanda shine ɗakinsa.

A bakin gado ya zauna yanajin wani abu na taso masa, jin abun na neman fin ƙarfinsa Yasa ya cilla wayarsa kan gado inda ɗayar ma take, ya dafe kansa yanajin maganganu na yawo a kan nasa kamar kullum, sai yaji gaba ɗaya ɗakin na juya masa.

Sai kawai ya rintse idonsa yana san yayi addu’a kamar kullum, saide ya kasa kamar Kullum ɗin, da wani irin sauri ya buɗe idonsa, tuni ya sauya kala zuwa ja, wata iriyar ƙara ya saki, wanda ta saka bakinsa buɗewa.

A hankali wannan doguwar fiƙar take sauƙowa daga haƙwaransa na sama, ya fita a hayyacinsa, sam baya ƙarƙashin ikon kansa, ya dawo under control ɗin baƙin ruhin nan, miƙewa yayi da sauri, Nan take ƙafafuwansa suka rabu da ƙasa yayi sama, sai kuma aka bugashi da bangon gabar, aka dawo da shi na yamma, kansa duka ya fashe sai zubar jini, wani irin ƙara da kururuwa yake, gaba ɗaya ya sauya ya zama dodo.

Nadra dake zaune a ɗaki ta fashi da kuka, ta tashi ta kulle ɗakinta, gudun kada ya shigo ya illa tata.

Yau abun nasa yayi ƙamari, dan glass ɗin balcony ɗin ɗakin ya fasa ya fita cikin wani irin tsalle wanda yafi ƙarfin ace normal mutum yayi shi, ya ɗale saman rufin turakar Fulani khadija, ya saki wata iriyar ƙara, kamar wani zakin da yayi nasara akan wata dabbar daya farauta, kuma haka sautin ƙarar tasa yake fita, kamar na kura ko zaki kuma kamar na gwagwan biri, yana yi yana yakushin jikinsa.

Fulani sadiya dake maƙale a jikin tagar ɗakinta ta saki wani miskilin murmushi, ta tako ta juyo zuwa cikin ɗakin nata tana kallon Galadima.

“Shi ɗin ne ko ?”

Muryar galadima ta tambaya

“Shi ne, da waye dodo a masarautarnan idan ba shi ba ?”

Tayi maganar a sigar tambaya, amma kuma ba tambayar bace, dan daga ita har Dan nata sun san cewa Tafidan ne

“Ai bazan taba barin Tafida ya zauna lafiya ba, sai naga bayan Tafida da duk abinda yake taƙama dashi”

Ta ƙarashe da wani bussashen murmushi a fuskarta.

“Ɗazu ma na ganshi, sai wani faɗi yake yana taƙama kamar wani ubansa shi ne sarki”

Fulani tayi wani kasaittacen murmushi

“Ko ubansa Tafida bai isa ba, bare shi karan ƙaɗa miya”

“hakane mama, nasan zaki iya”

“dole ne gobe na aika jakadiya taje ta amsomin wannan laƙanin, dan ba a bori da sanyin jiki”

“shi yasa a kaf duniya bani da wata kamar ki”

Fulani tayi dariya cike da nishaɗi.

Maryam Pov.

Tunda suka baro event center ɗin kai tsaye gidan Anti Fati suka wuce, ta ɗauki hijabinta ta mayar, har wata ajiyar zuciya tayi ta nutsuwa bayan da hijabin ya rufe jikinta ruf.

Anti Fati tace mata ta zauna taci abincin dare amma sai taƙi, tace yau dambu sukayi a gida dan haka shi za taje taci, Anti Fati tayi ƙorafi akan me yasa bata kawo mata dambun ba, dan inde Maryam ce tayi abinci to baya kwantai a gidansu, kamar wani abune a cikin hannunta idande tayi girki to babu makawa zaiyyi daɗi.

Da zata tafi Anti Fati ta bata kuɗi da wasu kayan abinci wanda ta tambayi mijinta akan zata bawa Maryam ta kaiwa Maanmu idan tazo, kuma ya amince hardama ƙara mata da kuɗi.

Ta rakota har bakin titi ta hau adaidaita, Imran sai kuka yake akan sai ya bita, dan wata ƙauna Allah ya saka a tsakanin ita dashi, wasu lokutan ma Anti Fati ɗin kance da ace Maryam tayi aure to da cewa zatayi Imran ɗanta ne, yaron yana bala’in kama da ita.

A bakin ƙofar gidansu ta iske Sanata, tana ganinsa ta haɗe rai ta ƙarasa ƙofar gidan, shi kuma tunda ya hangota yake washe baki, dama ya aika yaro ance bata nan, shi ne ya tsaya yana jiran dawowarta, dan yasan bazata wuce magariba ba zata dawo.

Ciki-ciki ta gaisheshi, ya amsa mata da fara’a.

“Rannan kinga ban zo ba ko ?”

Taƙi tace komai ta kawar da kanta gefe

“Maryam ya kamata ace kin faɗa min wani abun ko hankalina zai kwanta, ki faɗamin ra’ayinki a kaina dan Allah”

Maryam tayi ajiyar zuciya

“Sanata inaso kayi haƙuri, a gaskiya yanzu banjin zan iya aure ko kuma sarmunta, kayi haƙuri burina shine na gama karatuna, so dan Allah kayi haƙuri ”

Sanata baiji komai a ransa ba, dan tayi masa magana ne cikin lallashi da kuma nutsuwa irin tata.

“Shikenan Maryam, babu komai zan jiraki har zuwa lokacin da Allah zai sa ki fara tunanin aure”

“Na gode daka fahimceni”

“Kada ki damu Maryam, ni a kodayaushe me fahimtar ki ne, na barki lafiya”

Maryam ta gyaɗa masa kai, yayinda yake barin ƙofar gidan nasu, Allah ya sani bawai san sonta ne bata yi ba, ita kawai yanzu bata da niyyar yin auren ne, burinta shine ta gama karatu, ta nemi aiki sannan ta ɗauki nauyin mahaifiyarta da kuma ƙannenta, amma ba dan baka ba babu abinda zai hana taso Sanata, domin bashida wani aibu.

Ta ayyana hakan a rantane ba tareda ta san ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a gobe ba, kaddarar da zata sauya rayuwarta har ƙarshe.

Da sallama a bakinta tashiga gidan, kuma tun daga soro take jin hayaniya da yawa, hakan ke nuna mata cewar baƙi sukayi, ta saka kai cikin gidan tana bin mutanen gidan dake zaune akan tabarma a tsakar gidan da kallo, Maanmu ce itada Muhsin, Hassan, Hussain sai wani Abbalele, ɗan ƙanwar Maanmu wanda yake sa’an su Hassan, kuma dama yana zuwa gidan jifa-jifa.

Ta ƙaraso tana amsa gaisuwar da Abbalelen ke mata, ledojin dake hannunta ta aje a gaban Maanmu tana faɗin

“Maanmu gashi wai injin ya habib” Maanmu ta buɗe tana ta saka masa albarka

“A’a yaya kwalliya kika yi ne?”

Maryam taja ta tsaya tayi tunanin da tayi alwala kwalliyar ta koɗe, ashe bata fita ba, banza tayi da Hussain dake mata tambayar ta shiga ɗaki ta saka wata doguwar rigar atamfa mara nauyi ta fito tayi alwala.

Dan zuwa lokacin an fara ƙiran sallar isha ta koma ɗakinta tayi sallah, tana zaune akan sallaya aka ɗauke nefa, bata ko gamayin addu’o’in data saba ba, ta fito daga ɗakin a guje, Allah ya sani tana da bala’in jin tsoro, musamman ma na duhu.

“Ke Maryam lafiya?”

Maanmu ta faɗi tana kunna fitilar dake aje a gefenta, kamar da tasan za’a ɗauke wuta, ta fito waje da ita, sannan ta aje ta a gefenta.

“Babu komai”

Muryarta ta fito cikin ƙoƙarin seta kanta

“Bari naje gidan Iya” (Wato kakar Badar).

Ta faɗi tana saka takalmanta

“Kada ki daɗe fa! ”

“To”

Ta amsa lokacin da ta kai ƙofa

“Tsorata fa tayi”

Hussain ya faɗi yana dariya ƙasa-ƙasa

“Nasani ai, ban san yushe Maryam zata dena jin tsoro ba, ita tsoron nata yayi yawa”.

*****

“Ke wallahi kallo yayi kyau, da kika ƙi zuwa in faɗa miki anyi ba ke, Tafida yayi hawa kuma na ganshi dan ma ya rufe idonsa da sun glasses shi yasa ban samu damar ganin his beautifull blue eyes ba”

Maryam taja tsaki, tana mitar ita ko fidar yarane ma ina ruwanta ballan tana wani can waishi Tafida.

“Baki ce komai ba”

Badar ta faɗi tana ta’bata ganin tayi shiru

“Me kike so nace ?”

“Say something mana”

Sai ta girgiza kai “I have nothing to say”

“Ai shikenan”

“Ke mu ki kunna mana video mana”

“Wallahi kuwa harda yadda ake biryani na ɗauko” Cewar Badariyyya tana buɗe wayarta kirar sumsung.

<< Yadda Kaddara Ta So 8Yadda Kaddara Ta So 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.