Bismillahir Rahmanir Rahim
Shimfida
Assalamu Alaikum Warahmatullah. Barkan ku da jimirin saurare na, bayan hutun da naje In shaAllah a yau ni Rukayya Yusuf Ibrahim wato (A.Y.M Novel Palace) Na shirya tsaf domin kawo muku sabon littafina mai suna Yanayi. Yanayi littafi ne wanda na kirkire shi domin jin daɗin ku, Akwai fadakarwa sosai , tausayi , zazzafar soyayya , ilimantarwa tare da nishadantarwa. Ina mai tabbatar muku wannan littafi yasha banbam da wanda kuka saba ji, domin kuwa akwai abubuwa masu taɓa zuciya wanda zaku ji. . .