Ita kuwa Anisa ce ta dube ta tace " wai ke abunda kika fada da gaske kike ? In ya zama mutumin kirki sai ki aure shi ? Kina tunanin hakan mafita ce?".
Tace" Eh Anisa indai zai shiryu zan aure shi , tunda daman matsalar sa daya shaye-shaye kuma kinga nayi jahadi domin in ya gyaru baki san adadin wadanda zasu shiryu a haka ba".
Anisa tace" ashe baki da hankali Shahida ? To tun wuri ki san inda yake miki ciwo , Dan shaye-shaye in yayi nisa anyi asarar kenan , kinaji Kuma yake cewa bazai iya dainawa ba .
Wallahi kiyi tunani tunkan. . .