Mama tsaye ta mike cikin fushi ta shiga kitchen wajan Shahida ta janyota ta baya tace” wana ɗan iskan kike kulawa in kin fita har yasan ana takura miki?”.
Shahida da ta shiga ruɗani tsabar tsorata ta kasa magana , duka sosai Mama ta kai mata tana cewa” wato yama ɗiɗi kike dani a duniya ina azabtar dake ko ? to bari nai miki dukan mutuwa naga mai zai iya”.
Ta shiga dukan Shahida ta ko ina Abdull na bata hakuri amma ina? Na’ima ce ta shigo taga abunda ke faruwa tace” hala wani iskancin tayi ko?" Mama ta. . .