Anisa tace" gani nayi kamar da gudu kika shigo ko dai Na'ima kika tsokano?".
Tace" uhumm lallai yarinyar nan kin ma raina ni ".
Ta nemi guri ta zauna tace" bani ƙaramar kula dan Allah ?".
Anisa tace" baki san hanyar da kular take bane ?".
Bata sake cewa komai ba ta mike ta ɗako ta juye alalan nan Anisa ta zuba mata ido.
Ta yi gefe da ita ta zauna tana duban Anisa da ta zuba mata Ido tace "nifa kalon nan ya isheni matar kalamu".
Anisa tace"Shahida alalan waye wannan ?" .
Tai dariya tace" na Yaya Abubakar ne yanzu zai. . .