Wasa-wasa Mujahid ya sauyawa Shahida , ya takurata sosai komai tayi idonsa na kanta.
Har makaranta yanzu ya hanata koyarwa, Anisa tazo gidan bisa tilastawar Abubakar da Ridwan da tun randa akaje neman masa auranta bai kara ganinta ba.
Anisa tayi kuka taji tausayin halin da taga Shahida duk ta rame.
Abubakar kuwa kusan birkicewa yayi gaba ɗaya rashin Shahida ya ɗaga masa hankali ,kuma yanajin lokacin da Uncle dinta ke mata fada duk baya cikin nutsuwarsa.
Hakan yasa yake zuwa kofar gidan ko makaranta amma shiru baya ganinta.
Shine ya lallaba Anisa duk in tazo Anti Maryam. . .