Tace" Anisa dan Allah kiban shawara nabi masoyina , wallahi Anisa mutuwa zanyi in na daina ganinsa, kuma ina jin tsoran guduwa domin banyiwa Uncle adalci ba".
Anisa tayi ajiyar zuciya tace" kiyi hakuri Anisa ko da Uncle Mujahid sanki yake kiyi hakuri ki masa biyayya , domin wannan hanyar ba mai ɓullewa bace , zaku tafi inda ba a sanku ba kuyi rayuwa karshanta ma a dinga yi muku mummunar fahimta".
Shahida ta fashe da kuka tace" Yaya zanyi to , ni fa tunda nazo gidan Uncle ban san wani farin ciki ba , me yasa zan zauna na rusa rayuwata saboda shi, ke. . .